11.09.2024 Views

Matakai Zuwa Wurin Kristi_

Saboda haka, Yesu Kristi yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a. Da mika hannu da murya mai ƙauna, Yesu ya miƙa gayyatar: “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta. Yayin da kuke kusa da giciyen akan, za ku ga ƙauna marar misaltuwa. Kamar yadda ta wurin bangaskiya kuka fahimci ma'anar hadayar da aka yi akan gicciye, kuna ganin kanku mai zunubi ne, wanda shari'ar Allah ta karya. Yin tsayayya da jarabar Shaiɗan ba abu ne mai sauƙi ba. Yana kira zuwa ga tsayin daka ga Allah. Kristi ya ci nasara akan kowace jaraba da Shaiɗan zai iya kawowa a kan mutum. Shi ne hanya, gaskiya, kuma rai.

Saboda haka, Yesu Kristi yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a. Da mika hannu da murya mai ƙauna, Yesu ya miƙa gayyatar: “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta. Yayin da kuke kusa da giciyen akan, za ku ga ƙauna marar misaltuwa. Kamar yadda ta wurin bangaskiya kuka fahimci ma'anar hadayar da aka yi akan gicciye, kuna ganin kanku mai zunubi ne, wanda shari'ar Allah ta karya. Yin tsayayya da jarabar Shaiɗan ba abu ne mai sauƙi ba. Yana kira zuwa ga tsayin daka ga Allah. Kristi ya ci nasara akan kowace jaraba da Shaiɗan zai iya kawowa a kan mutum. Shi ne hanya, gaskiya, kuma rai.

SHOW MORE
SHOW LESS

Create successful ePaper yourself

Turn your PDF publications into a flip-book with our unique Google optimized e-Paper software.

New Covenant Publications: Hausa

Copyright © 2020. New Covenant Publications International.

An kiyaye duk haƙƙoƙi. Ba wani ɓangare na wannan littafin da za a iya sake bugawa ko

watsa shi ta kowace hanya ko ta kowace hanya ba tare da takamaiman izini daga

marubucin ba, sai dai a cikin taƙaitaccen magana da ke kunshe a cikin labarai masu

mahimmanci da sharhi. Da fatan za a mayar da duk tambayoyin da suka dace ga

mawallafin.

An kiyaye duk haƙƙoƙi. Ba wani ɓangare na wannan littafin da za a iya sake bugawa ko

watsa shi ta kowace hanya ko ta kowace hanya, na lantarki ko na inji, gami da yin kwafin

hoto, rikodi, ko ta hanyar adana bayanai da tsarin dawo da bayanai - sai ta mai nazari ko

mai bincike wanda zai iya kawo taƙaitaccen bayanin da za a buga. a cikin mujallu,

mujallu ko mujallu.

ISBN: 359-2-85933-609-1 ISBN:

359-2-85933-609-1

Kataloji a cikin Bayanan Labarai

Edita da Tsara ta: Sabon Alkawari Publications International Group

Buga a cikin United Kingdom.

Buga Farko 26 Mayu 2020

An buga ta: New Covenant Publications International Ltd.,

Kemp House, 160 City Road, London, EC1V 2NX

Ziyarci gidan yanar gizon: www.newcovenant.co.uk

Yesu ya kasance baƙo mai daraja a teburin masu karɓar haraji; Ta hanyar tausayawa da

jin dadin jama'a Ya nuna cewa ya gane darajar mutum; kuma mutane sun yi marmarin

samun cancantar amincewarSa. A cikin zukatansu masu ƙishi, Kalmominsa suna da iko

mai ba da rai. An tada sabbin buƙatun, kuma akwai yuwuwar sabuwar rayuwa ga

waɗannan ɓangarorin al'umma KE 271.3

Yesu ya nuna ikon koyarwar ƙarya ta kawar da sha’awar gaskiya. "Ba wanda ya sha

tsohon ruwan inabi," in ji shi, "nan da nan, yana son sabon, gama ya ce, tsohon ya fi."

Dukan gaskiya da aka bai wa duniya ta wurin kakanni da annabawa ta haskaka da sabon

ɗaukaka a bakin Almasihu. Amma malaman Attaura da Farisawa ba sa son sabon ruwan

inabi mai daɗi. Da zaran sun bar tsofaffin al'adu, al'adu da ayyuka, ba za su sami wuri

a cikin zukatansu ko zukatansu ga koyarwar Kristi ba. Sun manne da busassun siffofi,

kuma suka bijire daga gaskiya mai rai da ikon Allah. KE 277.3

An bar wannan shafin da gangan babu komai.

New Covenant Publications

International Ltd.

Littattafai na Gyaran; Sabbin Tunani

New Covenant Publications International Ltd.,

Kemp House, 160 City Road, London, EC1V 2NX

Imel: newcovenantpublicationsintl@gmail.com

Godiya

Wannan littafi sadaukarwa ce ga Allah.

Gabatarwa

Wannan ma'aikatar Kamfanin buga Littattafai na Sabon Alkawari [New Covenant

Publications International Ltd.] tana fadakar da mai karatu shirin Allah mai tsarki

wanda ke haɗa sama da ƙasa kuma yana nuna madawwamin yanayin dokar ƙauna.

Tambarin, akwatin alkawari, yana wakiltar kusanci tsakanin Almasihu Yesu da

mutanensa da kuma mahimmancin dokar Allah. Kamar yadda aka rubuta: “Amma

wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni

Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama

Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.” (Irmiya 31:31-33; Ibraniyawa 8:8-10).

Lallai, sabon alkawarin yana tabbatar da ceto, wanda aka haifa ta wurin fafutikar da

ba ta ƙare kuma ana tabbatar da shi da jini…

Na tsawon ƙarni da dama, mutane da yawa sun sha wahala da azabtarwa mara

misaltuwa, an shirya don kawar da gaskiya. Musamman a cikin Zamanin Duhu,

wannan hasken ya sha wahala sosai kuma an yi masa rufa-rufa da al’adun ɗan adam

da kuma jahilcin jama'a baki ɗaya, saboda mazaunan duniya sun raina hikima kuma

sun karya alkawarin. La'anar cin hanci da rashawa da yawaitar munanan abubuwa sun

taso irin wannan rashin adalci da zalunci mara misaltuwa, har mutane da yawa sun

rasa rayukansu, suna ƙin miƙa yancin lamiri. Duk da haka, ilimi da aka rasa an farfaɗo

da shi.

Koyaya, ta wannan littafi, mutum zai sake gano mahimmancin wannan Gyarawa

na ƙarni na 16 halin daga hangen nesa na Masu Gyara da wasu jaruman jagorori. Daga

labaransu, mutum na iya fahimtar yakokin da suka addabi duniya, dalilan da ke

ƙarƙashin irin wannan adawa mai tsanani da kuma shiga tsakani na sama.

Taken mu: “Littattafai na Gyaran; Sabbin Tunani,” ya nuna muhimmancin

zamanin gyarawa, littattafansa da tasirinsa ga dukan duniya. Hakanan yana jaddada

gaggawar gyara kai, haihuwar sabo, da kuma sauyi. Kamar yadda na’urar buga

takardu ta Gutenberg da fassarar littattafai suka baza addinin da aka sake fasalin sa,

kimanin shekaru 500 da suka gabata, litattafan dijital da kafofin sada zumunta suna

yada gaskiyar waɗannan lokuta na ƙarshe.

Matakai Zuwa Wurin Kristi

1

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Teburin Abubuwan Ciki

BABI NA 1 – Kaunar Allah Zuwa ga Dan-Adam .............................................................. 3

BABI NA 2 – Mai-Zunubi Yana da Bukatar Yesu ............................................................. 7

BABI NA 3 – Tuba ............................................................................................................ 10

BABI NA 4 – Fadin Zunubi .............................................................................................. 18

BABI NA 5 – Tsarkakewa................................................................................................. 21

BABI NA 6 – Bangaskiya da Yarda .................................................................................. 24

BABI NA 7 – Gwaji na Almajiranci ................................................................................. 28

BABI NA 8 – Yin Girma Cikin Kristi ............................................................................... 33

BABI NA 9 – Aiki da Zaman Rai ..................................................................................... 39

BABI NA 10- Sanin Allah................................................................................................. 43

BABI NA 11 – Amfanin Addu’a ....................................................................................... 47

BABI NA 12 – Abin da za a yi da Shakka ........................................................................ 54

BABI NA 13 – Yin Farinciki Cikin Ubangiji ................................................................... 59

2

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 1 – Kaunar Allah Zuwa ga Dan-Adam

Halitta da wahayi duka suna shaidar kaunar Allah. Ubammu na sama shi ne masomin

rai, da hikima da farin-zuciya. Dubi abubuwa masu ban al’ajibi da jimali na halitta. A tuna

da dacewarsu ga dukan bukace-bukace, ba na dan-Adam kadai ba, amma na duk sauran

abubuwa masu rai. Hasken rana da ruwan sama masu wartsakad da kasa, tuddai da tekuna

da sararin duniya, duka suna bayyana mana kaunar Mahalici. Allah ne ya ke biyan dukan

bukatar halittarsa yau da gobe. A cikin kalmomi masu dadi, Mai-Zabura ya ce:

“Idanun dukan mutane suna sauraro a gareka,

Kana kuwa ba su abincinsu a kan kari.

Kana bude hannunka,

Kana biya wa ko wane mai rai muradinsa.” Zabura 145:15, 16.

Allah ya halicci dan-Adam cikakke cikin tsarki da farin zuciya, ita duniya kuwa

sa’anda Mahalici ya sifanta ta da hannuwansa ba ta da wani digo na rubewa ko wani

duhuduhun la’ana. Ketare dokar Allah ne — dokar kauna — ya jawo bakin ciki da mutuwa.

Amma dai, a tsakiyar shan wahalar da zunubi ya jawo, kaunar Allah a baiyane ta ke. An

rubuta (cikin Farawa 3:17) cewa Allah ya la’anta kasa sabili da mutum. Su wadannan kaya

da Tsarkakkiya — abubuwa masu wuya da gwajegwaje wadanda suka sa zaman duniyan

nan ya zama na wahala da damuwa—an yi su ne domin jin dadin nan ya Adam, watau sashi

ne na cikin horon da a ke bukata a cikin shirin da Allah ya yi domin tada dan-Adam daga

cikin kaskancin da zunubi ya kawo. Amma, ko da shike duniya ta fadi, ba bakin ciki da

dacin rai ne kacfai suka rage ba. A cikin halitta kanta akwai sako masu yawa na bege da

ta’ aziya. Akwai furarruka bisa sarkakkiyan, fure mai kamshi kuma ya baibaye kayayuwan.

“Allah kauna ne” a rubuce ya ke bisa ko wane furen da ya kusa bucfewa, da bisa ko

wane sabon reshen ciyawa. Kyawawan tsuntsaye da su ke cika sararin sama da muryoyin

wakokinsu na farin ciki, da furarruka da su ke dad ada iska da kamshinsu, da dogayen

itatuwa na jeji da su ke rufe duniya da ganyayensu, duk suna shaida kauna irin na ma-haifi

na Allahnmu, suna kuma shaida cewa muradinsa ne ya sa ‘ya’yansa su yi farin ciki.

Magnar Allah tana baiyana bayyana halinsa. Shi da kansa ya furta kaunatasa mara

iyaka da tausayinsa. Sa’anda Musa ya yi addu’a ya ce “Ka nuna mani darajarka,” Allah ya

amsa “Zan sa dukan nagartata ta gibta a gabanka.” Fitowa 33:18, 19. Wannan shi ne

daukaka — tasa. Ubangiji ya gibta ta gaban Musa, ya yi shela ya ce “Ubangiji, Ubangiji,

Allah ne chike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinkai da gaske.

Yana tsaron jinkai domin dubbai, yana gafarta laifi da sabo da zunubi.” Fitowa 34:6, 7. Shi

mai-jinkirin fushi ne, mai yalwar alheri.” (shi “Allah mai nasiha ne, cike da juyayi” Yunana

4:2) “Domin yana jin dadin jinkai.” Mikah 7:18.

3

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Allah ya daure zukatanmmu hade da kansa ta wajen alamu marassa iyaka a cikin sama

da bisa kan duniya. Ya nemi ya baiyana kansa garemu ta wurin ayyukan halittansa. Amma

ko su ba su baiyana mana sosai yadda ya kamata ba. Kuma ko da shi ke an nuna wadannan

shaidodi ta hanyoyi daban daban, makiyin dukan abu mai kyau ya makantar da hankulan

‘yan-Adam har ya sa suna duban Allah a tsorace. ‘Yan-Adam suna tunawa da Allah kamar

wani mai tsanani wanda ba ya gafara. Shaitan ya sa ‘yan-Adam suna sifanta Allah kamar

alkali mai tsanani, ko kamar mai bin bashi mara siyasa wanda ba ya rangwame. Shaitan ya

sifanta Allah kamar wani ne wanda ya ke zura idanu na kishi kan ko wane irin tuntube ko

kuskure da ‘yan-Adam suka yi, domin ya ziyarce su da hakunci. Sabili da a shafe wannan

inuwa mai dufuntawa ne tawurin bayyana kaunar Allah mai-girma ga duniya. Yesu ya zo

ya zauna tare da’ yan-Adam.

Dan Allah ya zo daga Sama domin ya baiyana Uba. “Ba wanda ya taba ganin Allah

dadai, Da haifaffe kadai wanda ke chikin kirjin Uba, shi ya bada labarinsa.” Yohanna 1:18.

“Kuma ba mai- sanin Uban, sai Dan da dukan wanda Dan ya nufa shi bayana masa.” Matta

11:27. Sa’ad da daya daga cikin almajiran ya ce “Ka nuna mana Uban,” Yesu ya amsa ya

ce “Na dade wurinku hakanan Filibbus, kai kwa ba ka san ni ba? Wanda ya gan ni ya ga

Uban; kaka fa kana chewa ka nuna mamu Uban? Yohanna 14:8, 9-

A cikin baiyana sakonsa ga duniya, Yesu ya ce “Ubangi ji ya shafe ni da zan yi shelar

bishara ga talakawa: ya aikeni domin in yi ma damraru shela ta saki, Da mayaswar gani ga

makafi, in kwance wadanda an kuje su.” Luka 4:18. Aikinsa ke nan. Ya yi ta tafiy ako ina

yana aikin nagarta, yana warkas da dukan wadanda Shaitan ke wahalshe su. Akwai

kauyuka masu yawa lafiyayyu inda ba a jin wani nishi na rashin lafiya a ko wane gida,

domin ya ratsa ta cikin su, ya warkas da duk marassa lafiyan da ke ciki. Aikinsa ya shaida

lallai shi shafaffe ne daga sama. A cikin ko wane aiki nasa an baiyana kauna, da jinkai da

tausayi. Zuciyatasa ta nuna taushin juyayi zuwa ga ‘yan Adam. Ya daudi kama irin ta dan-

Adam domin ya iya gane bukace-bukacen dan-Adam. Matalauta da kaskantattu ba su ji

tsoron kusance shi ba. Har ma yara kanana sun je wurinsa. Su kan so su haye kan

guwawunsa, su dube shi a fuska sosai, fuska wadda ta ke cike da kauna.

Yesu bai danne ko magana guda na gaskiya ba; amma a ko wane lokaci yana furta ta

cikin kauna. Cikin dukan dawainiya tasa da jama’a, ya kan yi zurfin tunani. Bai taba yin

gatse cikin magana tasa ba, ko ya yi wani furci mai tsanani ba tare da dalili ba, ko ya dauki

zafin rai ba dalili. Ya kan facfi gaskiya amma cikin kauna. Ya haramta riya, da rashin

bangaskiya, da laifi, amma da hawaye cikin murya tasa sa’adda ya ke tsawatawa. Ya yi

kuka sabo da Urushalima, birnin da ya ke kauna, birnin da ta ki ta karbe shi, shi wanda ya

ke shi ne hanya, shi ne gaskiya, shi ne rai. Su sun ki shi, Mai-ceto, amma shi ya dube su da

idon rahama, da tausayi. Zamansa na duniya zama ne na musun kai da tunanin abin da zai

amfani wacfansu. Ko wane mai rai yana da daraja a wurinsa. Ko da shi ke a ko wane lokaci

4

Matakai Zuwa Wurin Kristi

yana kame kansa da kwarjinin nan irin na Sama, yana kulawa da sauran iyalin Allah. A

ganinsa dukan ‘yan-Adam fadadcfu ne, wadanda ya zama wajibi ne a gareshi ya cece su.

Haka aka baiyana halin Kristi cikin irin zaman da ya yi. Wannan ne halin Allah. Daga

cikin zuciyar Uban ne rafuffukan tausayi, yadda Kristi ya baiyana, su ke gudanowa zuwa

ga ‘yan-Adam Yesu, mai-ceto, mai tausayi, Allah ne ya “Bayana chikin jiki.” 1

Timothawus 3:16.

Domin a panshe mu ne Yesu ya zo duniya, ya sha wahala, ya mutu. Ya zama “mutum

mai bakin ciki,” domin mu zama masu taraiya cikin farin ciki har abada. Allah ya yarda

Dansa kaunatacce, wanda ya ke cike da nasiha da gaskiya, ya fito daga duniya wadda

darajatta ba ta misaltuwa, ya zo duniya wadda ta yi baki kirin da zunubi, wadda ta dufunta

da inuwar matuwa da la’ana. Ya yarda masa ya bar jin dadi na kirjinsa na kauna, da bangirman

da mala’iku su ke ba shi, domin ya sha kunya, da ba’a da kaskanci, da kiyayya, da

mutuwa. “Foro kuma mai-kawo lafiyarmu a kansa ya ke; ta wurin dukansa da ya sha mun

warke.” Ishaya 53:5. Ga shi can a cikin jeji, ga shi can a Gethsemane, ga shi can bisa giciye!

Dan Allah mara tabo ya sa kansa daukar Kayan zunubi. Shi wanda daya ya ke da Allah, ya

ji a cikin ransa wannan irin mugun rabuwa da zunubi ya kawo tsakanin ransa Allah da dan-

Adam. Wannan ne ya sa ya furta cikin radadi ya ce, “Ya Allahna, ya Allahna, Dom mi ka

yashe ni?” Matta 27:46. Kayan zunubi ne, da sananin girma kayan zunubi, da sananin

rabuwa da ya kawo tsakanin Allah da ruhohin ‘yan-Adam — sananin wannan ne ya karya

zuciyar Dan Allah.

Amma fa ba a yi wannan babban baiko domin a halicci kauaa zuwa ga dan-Adam a

cikin zuciyar Uban ba, ko don a sa shi ya yarda ya yi ceto. A,a, Ba haka ne ba ko kadan.

“Gama Allah ya yi kaunar duniya har ya bada Dansa haifafe shi kadai.” Yohanna 3:16.

Uban yana kaunar mu, ba domin wannan babban pansa ba, amma shi da kansa ya yi tanadin

wannan pansar domin yana kaunar mu. Yesu shi ne hanyar da Allah zai iya kwararo kaunar

ta gangaro bisa duniya wadda ta kangare. “Allah yana chikin Kristi yana sulhunta duniya

zuwa kansa.” 2 Korinth. 5:19. Allah ya sha radadi tare da Dansa. A cikin racfadi na lambun

Gethsemane, da cikin radadin mutuwa a Kalvari, a can ne zuciya mai kauna mara iyaka ta

biya tamanin pansan mu.

Yesu ya ce “Domin wannan Uba yana kamnata, sabada ina bada raina, domin in amso

shi kuma.” Yohanna 10:17. Watau “Ubana ya kaunace ku har ya fi kaunata domin ba da

raina da na yi domin pansarku. Ta wajen zama lamuni domin ku, wajen ba da raina

dungum, ta wajen daukar basusuwanku, da laifofinku, Ubana ya kaunace ni; domin ta

wajen ba da kaina da na yi ya zama hadaya, a iya baratad da Allah, kuma shi ne mai baratad

da wanda ya ba da gaskiya ga Yesu.”

Ba mai iya pansar mu sai Dan Allah kadai, domin Shi kacfai ne da ya ke daga zuciyar

Allah zai iya ba da labarinsa. Shi kadai ne da ya san tsawo da zurfi na kaunar Allah zai iya

5

Matakai Zuwa Wurin Kristi

baiyana ta. Babu wani abu wanda ya fi baikon da Kristi ya yi domin dan-Adam facfadcfe

da zai iya furta kaunar Uban zuwa ga ‘yan-Adam batattu.

“Allah ya yi kaunar duniya har ya ba da tilon Dansa haifaffe.” Ya ba da dansa ba wai

domin ya zauna tsakankanin ‘yan-Adam ne kadai ba, ko domin daukar zunubansu ne kacfai

ba, ko don ya mutu watau hadaya kadai ba, amma ya ba shi domin daukacin ‘yan-Adam

duka. Dole ne Kristi ya mai da kansa da tabi’a da dukan bukace-bukace irin na ‘yan-Adam.

Shi wanda ya ke a da daidai da Allah ya ke, ya tswafa kansa hade da ‘yan-Adam da igiyoyi

wacfanda ba za a tsunke su ba. Yesu “Domin wannan fa a gareshi ba wani abin kumya ba

ne shi che da su yan uwa.” Ibraniyawa 2:11. Shi ne Hada- yanmu, Mai-roko sabili da mu,

Dan-uwanmu, yana tsaye da jiki irin namu a gaban kursiyin Uban, kuma haka zai kasance

cikin sifar abin da ya pansa — Dam-Mutum. Dukan wannan kuwa domin a dagad da dan-

Adam daga kaskancin zunubi ne, domin ya haskako kaunar Allah kuma ya zama mai

tarayya cikin farin ciki na tsarki.

Tamanin da aka biya domin pansarmu, da baikon da Allah ya yi mana cikin ba mu

Dansa ya mutu domin mu, sun isa su dagad da hankulan mu ga irin matsayin da za mu kai

ta wurin Yesu. Kamar yadda aka baiyanawa Yohanna Manzo tsawo, da zurfi, da fadi na

kaunar Uba ruwa ga ‘yan-Adam masu hallaka, ya cika da yabo da ban girma mara iyaka,

shi kuwa da ya rasa abin magana game da wannan abin mamaki, game da girma, da taushi

na wannan Kaunar, sai ya kira halitta dukata dubi irin wannan kauna, ya ce “Duba irin

kamna wadda Uba ya bayas garemu, da za a che da mu yayan Allah.” I Yohanna 3:1.

Wannan abu ya sa tamanin Dan-Adam ya yi tsada ainun. Ta wajen bata shari’a ‘yan-Adam

suka zama talakawan Shaitan. Ta wajen bangaskiya cikin pansar hadayar Yesu, ‘yan-Adam

za su iya zama ‘ya’yan Allah. Sabili da daukar tabi’ar ‘yan-Adam, Kristi ya dagad da ‘yan-

Adam. An dagad da fadaddu, ta wajen haduwa da Kristi ya dagad dasu, an sa su a matsayin

da za su cancanta da sunan ” ‘yanyan Allah.”

Wannan kauna ba ta da abokin gami. ‘Ya’yan Sarki na Sama! Alkawari mara gami

wajen tamani. Abu ne wanda ya kamata a zauna a yi tunani mai zurfi a kan sa. Kauna mara

abin kwatantawa zuwa ga duniya wadda ba ta kaunace shi ba. Wannan tunani kansa Abu

ne mai sa ruhu yasadduda, mai sa zuciya ta kasance cikin bautar nufin Allah. Gwargwadon

yadda muka yi binciken halin mahalici ta wurin giciye, gwargwadon yadda za mu ga jinkai,

juyayi, da gafara an cucfe su tare da shari’a, gwargwadon kuma yadda za mu iya ganin

shaidodi marasa iyaka na kaunar nan mara iyaka, da juyayi mai tsanani wanda ya fi juyayin

kaunar da mahaifiyya za ta nuna ga danta wanda ya kangare.

6

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 2 – Mai-Zunubi Yana da Bukatar Yesu

A cikin farko am ba Dan-Adam iko da hankali kintsatstse. Cikakke ya ke cikin tabi’a

tasa, da cikin jituwa da Allah. Dukan tunaninsa sahihai ne, abubuwan da ya ke buri kan su

kuma tsarkakakku ne. Amma ta wajen rashin biyayya tasa aka karkatadda ikonsa, kuma

son kai ya dauki matsayin kauna. Tabi’arsa kuma ta ci gaba cikin rashin karfi sabo da laifofi

har ya zama ba shi yiwuwa a gareshi, cikin karfin kansa, ya iya sayaiya da ikon mugunta.

Ya zama kamame na Shaitan, da kuwa ya kasance cikin wannan matsayi im ba domin Allah

ya shiga tsakani ba. Nufin mai jaraba ne ya rusa wannan shiri da mahalici ya yi wajen

halittar dan-Adam, domin ya cika duniya da kaito da lalacewa. Kuma nufinsa ne ya rataya

duk wannan magunta kan halitta mutum da Allah ya yi.

Acikin kasancewarsa tun zunubi bai shigo ba, mutum yana zance da Allah cikin farin

ciki da shi “Wanda an boye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi chikinsa.” Kolosiyawa 2:3.

Amma bayan aikata zunubinsa, ba zai kara iya samun farin ciki tsarkaka ba, domin haka

ya nemi ya buya daga fuskar Allah. Har yanzu kuwa haka zuciyar da ba ta sabonta ba ta

ke. Ba ta cikin muwafaka da Allah, kuma ba ta jin wani dadi cikin yin zance da shi. Mai

zunubi ba zai iya farin ciki a gaban fuskar Allah ba; sai ya ja da baya daga taraiya da

tsarkakun halitta. Da ma za a bar shi ya shiga sama ba wai samu wani dacfin rai ba. Ruhu

na kauna mara iyaka da ya ke mulki a sama — inda ko wace zuciya tana muwafaka da

Zuciyar kauna mara iyaka — ba zai iya motsa komai da zai iya nuna alamar rai a zuciyar

mai zunubi ba. Dukan tunaninsa, da abubuwan da ya ke so, da nufinsa, za su zama baki ga

mazauna a can. Sai ya zama tsirkiya wadda amonta ta fita daban da na sauran wakokin

sama. A gareshi sama za ta zama wurin azaba, zai yi marmari a boye shi daga fuskar shi

wanda ya ke Shi ne haske da tsakiyar farin ciki na aljanna. Ba wata shela ce ta tilas wadda

Allah ya yi ba da za ta hana miyagu shiga sama, rashin isa su zama abokan taraiya shi zai

rufe musu kofa. Darajar Allah a garesu sai ta zama wuta mai hallakaswa. Za su fi kaunar a

hallakansu domin su buya daga fuskar shi wanda ya mutu domin ya panshe su.

Abu ne wanda ba shi yiwuwa mu, don ikon kammu, mu tsira daga ramin zunubi inda

muka riga muka nutse. Zukatammu cike su ke da “mugunta, ba kuwa za mu iya sake su

ba.“Da ma ya yiwu abu mai- tsabta shi fito daga chikin mara-tsabta! amma ko daya babu!”

‘ ’ Domin himmantuwar jiki gaba che da Allah; gama ba ta chikin biyayya ga shari’ar Allah

ba, ba ta iya kwa.” Ayuba 14:4; Romawa 8:7. Ilimi, al’ada, nufi kokarin dan-Adam, ko

wane yana da nasa amfani muhimmi, amma ba su da wani karfi .Ya yiwu su nuna halin

Kristi a fuska, amma ba su iya sake zuciya, ba su iya tsarkake mabulbulan rai. Dole a samu

wani iko mai aiki daga can ciki, sabon rai daga sama, kafin a sake ‘yan-Adam daga zunubi

zuwa ga tsarkaka. Kristi shi ne ikon. Alherinsa kadai ya iya ya rayadda matattun tabi’u na

ruhu, ya jawo shi zuwa ga Allah, zuwa ga tsarkaka. Mai-ceto ya ce Im ba a haifi mutum

daga bisa ba, ba shi da iko shi ga mulkin Allah ba.” Yohanna 3:3- Fadin da akan yi cewa

tabi’a ce kawai. za ta ci gaba da kirkin da ke cikin dan-Adam mugun rudi ne kawai.

7

Matakai Zuwa Wurin Kristi

“Mutum mai-tabi’ar jiki bashi karba al’amura na Ruhun Allah ba: gama wauta su ke a

gareshi; ba shi kwa da iko shi san su gama ana gwadasu chikin ruhaniya.” “Kada ka yi

mamaki da na che maka Dole a haife ka daga bisa.” 1 Korinthiaywa 2:14; Yohanna 3:7.

An rubuta game da Kristi cewa “A chikinsa akwai rai, rai kwa hasken mutane ne,’ “Gama

babu wani suna kalkashin sama, da aka bayas wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” Yohanna

1:4, Ayukan Manzani 4:12.

Gane halin alherin kauna na Allah, da kyauta tasa, da sonsa irin na ma-haifi ba su isa

ba, Gane hikima da adalcin shari’a tasa, da lura da cewa a kan kyakkyawan tushe mai karfi

na kauna aka gina su bai isa ba. Bulus manzo ya gane wadannan duka sa’adda ya ce “Na

amsa shari’a mai-kyau che.” “Sharia tsatsarka che.” “Amma ni ba jiki ne, sayayye ne

kalkashin zunubi.” Romawa 7:16, 12, 14. Ya yi marmarin ya kai ga matsayi na tsarki, da

adilci, wanda ba shi yiwuwa ya samu don ikon kansa, sabo da haka ya yi kuka ya ce

“Kaitona, ga ni mutum, abin tausayi! Wannene za ya tsamo ni daga chikin jikin nan na

mutuwa?’’ Romawa 7:24. Irin kukan da ya hau sama ke nan, daga cikin zukata labtattu,

cikin dukan kasashe kuma tun adun adun. A garesu duka amsa guda ce, “Duba, ga Dan

rago na Allah wanda yana dauke da zunubin duniya!” Yohanna 1:29.

Akwai alamu da yawa da Ruhun Allah ya nemi ya kwatanta wannan tattibin gaskiya

ta wurin su, kuma ya baiyana su a tili ga zukatan da su ke marmari su ‘yantu daga kayan

zunubi. Sa’anda Yakubu ya gudu daga gidan ubansa bayan zunubin da ya yi na rudin Isuwa,

ransa ya yi nauyi da zunubin da ya yi. Ko da ya ke yana cikin kadaici, yasashshe, ya rabu

da duk irin abin da su ke kawo farin ciki da dadin zaman duniya, abin da ya fi tunawa gaba

da komai a lokacin shi ne tsoron cewa zunubi ya raba shi da Allah. Cewa Allah ya yashe

shi. A cikin wannan matsayi na bacin rai ne ya kwanta bisa tsandaurin kasa, kewaye da shi

sai duwatsu kawai, a sama kuwa sai hasken taurari. Yana cikin barci, sai wani irin haske

ya baiyana gareshi cikin wahayin da ya ke ciki, ga shi kuwa, daga nan sararin da ya ke a

kwance, ya ga kamar inuwar matakai sun nufi sama har kofar sama, a kan matakan kuma

ya ga mala’ikun Allah suna kai da komowa daga sama zuwa dasa, kuma daga darajar da ta

ke sama, aka ji murya na samaniya da sako na ta’aziya da bege. Ta hakanan aka sanas da

Yakubu da abin da zai biya masa muradin zuciya tasa wadda ya fi bukata a lokacin — Maiceto.

Da farin ciki da godiya ya ga aka baiyana masa hanyar da shi mai zunubi, a iya maida

shi cikin zumunci da Allah. Wannan wahayi na asiri da ya gani cikin mafarkinsa yana

kwatanta Yesu ne, wanda Shi ke Shi kadai ne hanyar ma’amala tsakanin Allah da dan-

Adam.

Wannan ne alamar da Kristi ya ke nufi a cikin zancensa da Natanayilu sa’anda ya ce

“Za ka ga sama a bude, malaikun Allah kuma suna hawa suna sabka bisa Dan mutum.’*

Yohanna 1:51. A kan wannan rami mai fadi da ke tsakani, ba za a iya wani ma ma’amala

ba. Amma ta wurin Kristi an sake hada duniya da sama. Ta wurin isar kansa Kristi ya gina

kadarko bisa wannan rami wanda zunubi ya haka, domin mala’iku masu hidima su iya

8

Matakai Zuwa Wurin Kristi

shiga ma’amalla da dan-Adam. Kristi yana hada dan-Adam fadadde, rarrauna, mara

madogara, yana hada shi da Masomin iko mara iyaka.

Amma dukan mafarke-mafarken ‘yan-Adam da ci gaba, da ko wane kokari nasu na

cfaga matsayinsu a banza su ke idan suka bar wannan masomin bege da taimako domin

fadaddu. “Ko wache kyakkyawar baiwa da kowache cikakkiyar kyauta daga bisa take.”

Yakub 1:17. daga Allah su ke. Babu wani hali mafifici na gaskiya illa daga gareshi. Kristi

ne kuwa hanya daya kacfai zuwa ga Allah. Kristi ya ce “Nine hanya, ni ne gaskiya, ni ne

rai.” Yohanna 14:6.

Zuciyar Allah ta kallafa kanta bisa ‘ya’yansa na duniya da kauna wadda ta fi karfin

mutuwa. Cikin ba da Dansa, ya zubo mana dukan sama cikin kyauta guda cfaya tak. Zaman

Mai-ceto da mutuwa tasa da roko da ya ke yi sabili da mu, hidimar mala’-iku, da godon da

Ruhu ke yi, kuma da Aikin da Uban ya ke yi bisa duka ta wurin duka kuma, da kulawa na

mazauna cikin sammai, duk sai da aka hada su domin pansar dan-Adam.

Kai! bari mu tsaya mu yi tunani a kan wannan baiko mai ban mamaki da aka mika

sabili da mu! Bari mu yi kokari mu gane wahala da kwazo wadda Samaniya ta ke batarwa

domin ta dawo da batattu ta komo da su gidan Uban. Ba wasu nufe nufe ko wadansu

hanyoyi da suka fi su, da za su iya sa wannan abu ya abku; mafificin lada sabo da yin abin

da ke daidai, farin cikin sama, zama tare da mala-iku zumunci da kauna na Allah da na

Dansa, dagawar da dada facfada ikommu har abada — wadannan duka ba manyan

abubuwa ne da suka isa su zuga mu, kuma su karfafa mu, domin mu ba da hidimar kaunar

zuci ga Mahalicimmu da Mai-pansarmu ?

Idan kuwa muka duba ta wata hanya, hukuncin Allah da ya furta gaba da zunubi,

sakamako wanda ba shi kawuwa, kaskancin hallimmu, da hallaka daga karshe, duk an nuna

su cikin Maganar Allah domin a facfakad da mu gaba da hidimar Shaitan.

Ashe bai kamata mu kula da Alherin Allah ba? Me kuma ake bukata ya dacfa yi wanda

ya fi wannan! Bari mu sa kammu cikin dangantaka da shi wanda ya kaunace mu da kauna

mai ban mamaki. Bari mu yi amfani da hanyar da aka bucfa mana, domin a sabonta mu

cikin kamaninsa, a komar da mu cikin zumunci da malaiku masu hidima, cikin sulhuntaka

da taraiya da Uban da Dan.

9

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 3 – Tuba

Yaya dan-Adam zai zama adili ga Allah? Yaya za a mai da mai zunubi adili? Sai ta

wurin Kristi ne kadai za a iya kawo mu cikin sulhu da Allah, cikin sulhu da tsarkaka; amma

ta yaya za mu kai ga Kristi? Dayawa suna yin tambaya daidai da wadda runduna masu

yawa suka yi a ranar Pentecost, sa’anda suka ji zunubi ya kashe su, suka ta da murya, suka

ce, “Me za mu yi?” Kalmar da ta fara fitowa daga bakin Bitrus game da amsa wannan

tambaya ita ce “Tuba.” Ayukan Manzani 2:38. Ba a jima ba kuma, bayan ya ci gaba da

jawabinsa, ya sake cewa “Ku tuba . . . ku juyo, domin a shafe zunubanku.”

Bakin ciki sabo da zunubi a hade ya ke da tuba, da kuma juyawa ga barin aikata

zunubi. Ba shi yiwuwa mu yi musun zunubi sai mun gane kazanta tasa, idan ba mun guje

masa daga cikin zuciya ba, ba shi yiwuwa wani abu ya sake daga irin zamammu na da.

Akwai mutane dayawa da ba su gane hakikanin azancin tuba ba. Dubbai suna bakin

ciki sabo da sun yi zunubi, har ma su kan nuna sabon hali daga waje, domin suna jin tsoro

cewa ayyukan da su ke aikatawa da ba daidai ne ba za su jawo masu wahala. Amma wannan

ba shi ne ma’anar tuba kamar yadda ya ke a cikin Litafi Mai- tsarki ba. Wahalarsu suke

kuka, amma ba suzubin ba. Irin wannan ne bacin ran da Isuwa ya yi sa’anda ya ga gadonsa

na haifuwa ya bace masa har abada. Bala’am sabili da tsorata da ya yi sa’anda mala’ika ya

tsare masa hanya ya hana shi wucewa da takobi a zare, ya fadi laifinsa domin gudun kada

a kashe shi ne kawai; amma babu sahihin tuba na zunubin a gareshi, babu juyawa daga

nufin da ya yi, babu dyamar mugunta. Yahuda Iskariyoti, bayan ya ba da Ubangijinsa, ya

ce “Na yi zunubi, da shi ke jini mara-aibi ne na bashe shi.” Matta 27:4.

Sanin la’ana na laifinsa da tsoron hakunci, su suka sa wannan furta laifi ya fito daga

cikin ransa. Sanin abin da zai same shi sabili da abin da ya aikata shi ya cika shi da tsoro,

amma fa ba wani zurfin bakin ciki na karayar zuciya a cikin ransa cewa ya ci amanar Dan

Allah mara tabo, ya yi musun Mai-tsarki na Isra’ila. Sa’anda Fir’auna ya ke shan wahalar

hukuncin Allah a kansa ya amsa laifinsa domin ya tsira daga hakuncin da ke gaba, amma

ya koma kan kangara ga Allah nan da nan bayan an tsaida aloba. Su wadannan duka sun yi

kukan abin da zunubi ya jawo, amma ba su yi bakin cikin ainihin zunubin kansa ba.

Amma sa’anda zukata suka sada kansu ga ikon Ruhun Allah, nan da nan lamiri ya kan

rayu, sa’annan mai zunubi zai iya rarrabewa da irin zurfin, da kuma irin tsarkin dokar Allah,

wadanda su ke su ne tushen mulkinsa a cikin samaniya da duniya. “Wanda yana haskaka

kowane mutum, yana zuwa chikin duniya.” Yohanna 1:9 ya kan haskaka asirtattun lollokai

na ruhu, kuma yana nuna boyayyun abu- buwa na dufu a sarari. Tabbatawa ya kan kama

hankali da zuciya. Mai zunubi ya kan gane adilcin Yahweh kuma ya kan ji fargaban

tsayawa, cikin laifinsa da kazamtarsa, a gaban Mai-binciken zukata. Ya kan ga kaunar

Allah, da jimalin tsarki, da farin cikin tsarkaka, ya kan yi marmarin a tsarkake shi, a maishe

shi cikin zumunta da Allah.

10

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Addu’ar da Dauda ya yi bayan faduwa tasa tana kwatanta bakin ciki na gaske sabo da

aikata zunubi. Tubansa sahihi ne mai zurfi kuma. Babu wani zukewa ko neman ba da hujja

kan laifinsa. Ba neman tsira daga hukunci ne ya sa shi yin wannan addu’a ba, Dauda ya.

ga kasaitar laifin da ya yi. Ya ga kazantuwar ruhunsa. Ya yi Kyamar zunubinsa. Ba sabo

da gafara ne kadai ya yi addu’a ba, amma sabo da tsarkakewar zuciya. Ya yi marmarin

farin ciki na tsarkaka — a maida shi cikin jituwa da zumunci da Allah. Ga kalmomin da

suka fito daga zurfin zuciya tasa:

“Mai-albarka ne mutum wanda an gafarta masa laifofinsa, wanda an rufi zunubinsa.

Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji ba ya lissafta mugunta gareshi ba, wanda ba shi da

algus chikin ruhunsa ba.” Zabura 32:1, 2.

“Ka yi mani jinkai, ya Allah, bisa ga rahamarka, Bisa ga yawan jiyejiyenkanka ka

shafe laifofina. Ka tsarkake ni daga zunubina. Gamma ina sane da laifofi na: Zunubi na

yana gabana tutur. Ka tsarkake chikina da zofa, zan tsarkaka kuma. Ka wanke ni, zan kwa

fi snow fari Daga chiki na ka halita zuchiya mai-tsabta, ya Allah: Ka sabonta dai-daitachen

ruhu daga chiki na. Kada ka yashe ni daga gabanka, kada kuma ka dauke mani ruhunka

mai- tsarki. Ka mayas mani da farinchiki na chetonka; Ka tokare ni da ruhu na yardan rai.

Ka cheche ni daga alhakin jini, ya Allah, Allah na chetona; Harshena kuma zaya raira

labarin adilchinka da karfi.” Zabura 51:1-14.

Tuba irin wannan ya fi karfin ikon kammu ya sa mu kai gareshi. Daga wurin Kristi

kawai ya ke samuwa, wanda ya hau bisa cikin sama, ya kuma ba da kyauta masu yawa ga

‘yan-Adam.

Amma ga wani wuri inda mutane dayawa su kan yi kuskure, ta haka kuwa sai su rasa

karbar taimakon da Kristi ya ke da nufi ya ba su. Suna tsammani ba za su iya zuwa ga

Kristi ba sai sun fara tuba, kuma wai tuba shi ke shirya hanyar gafarar zunubansu. Lallai

kam tuba shi ke gaba kafin gafarar zunubai, domin kuwa kar- yayyar zuciya mai tuba ce

kadai za ta iya jin bukatar wani Mai-ceto. Amma dole ne mai zunubi ya dakata sai ya tuba

kafin ya iya zuwa wurin Yesu? Ashe ya kamata a sa tuba ya zama abin tuntube tsakanin

mai zunubi da Mai-ceto?

Littafi Mai-Tsarki bai koyas da cewa sai dole mai zunubi ya tuba kafin ya kasa kunne

ga kiran Kristi ba. “Ku zo gareni, dukan ku da ku ke wahala, da masu nauyin kaya, zan

kuwa ba ku hutawa.” Matta 11:28. Alherin da ya ke fita daga Kristi shi ne ya ke bayaswa

zuwa tuba na gaskiya. Bitrus ya baiyana abin a fili a cikin jawabinsa zuwa ga ‘ya’yan Isra’

ila sa’anda ya ce “Wannan Allah ya daukaka shi da hannun damansa shi zama sarki da

Mai-cheto, domin shi bada tuba ga Israila, da gafarar zunubai kuma.” Ayukan Manzani

5:31. Ba shi yiwuwa mu tuba im ba tare da Ruhun Kristi ya farkad da lamirin mu ba kamar

yadda ba shi yiwuwa mu samu gafara im ba tare da Kristi ba.

11

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Kristi shi ne masomin ko wane tunanin da ke dai dai. Shi ne kadai zai iya dasa kiyayya

da zunubi cikin zuciya. Ko wane nufi domin gaskiya da tsarki, ko wane tabbatawa da sanin

kasancewa zunubammu, shaida ne cewa Ruhunsa yana motsawa bisa zukatammu

“Yesu ya ce, “Ni kwa idan an tada ni daga chikin kasa, zan jawo dukan mutane zuwa

kaina.” Yohanna 12:32. Dole ne a baiyana Kristi ga mai zunubi kamar Mai-ceto wanda ke

mutuwa domin zunuban duniya, kuma idan muna duban Dan Rago na Allah bisa giciye a

Kalvari, asirin pansa zai komo ya soma bude hankulammu, sai kuma alherin Allah ya bishe

mu zuwa ga tuba. A cikin mutuwa tasa domin masu zunubi Kristi ya nuna kauna wadda ba

shi yiwuwa a gane ta, kuma idan mai zunubi ya ga wannan kauna, sai zuciya ta yi taushi,

hankali ya ga shaida, ya jawo tarayan ruhu.

Gaskiya ne wani lokaci ‘yan-Adam su kan ji kunyar irin zaman da su ke yi na zunubi,

har ma su bar wadansu miyagun tabi’u nasu, kafin su farga cewa ana jan su ne a hankali

zuwa ga Kristi. Amma fa a ko wane lokacin da suka yunkura domin ‘su sake zamansu, da

sahihin nufi kuma su yi abin da ke daidai, ikon Kristi ne ya ke jawo su. Wani irin iko yana

nan wanda ba za su farga da shi ba, shi ne ke aiki bisa zukatansu, sai lamiri ya farka, irin

zama na waje ya gyaru. Kuma a lokacin da Kristi ya ke jawo su domin su dubi giciyensa a

sa’ilin da ya ke jawo su su dube shi wanda zunubansu suka soke Shi, sai doka ta komo gida

wajen lamiri. Irin mugun zaman da su ke yi, irin zurfin da zunubi, ya kafa gindinsa a cikin

rayukansu, za su fito fili a gabansu. Sai su fara gane wani abu na adilcin Kristi, su ce “Mene

ne zunubi, har da zai bukaci irin wannan baiko kafin a panshi wanda ya zama bawansa?

Ashe, dukan kaunar nan, dukan wannan shan wahala, dukan wannan kaskanci, am bukace

su ne domin kada mu hallaka, amma mu samu rai na har abada?”

Mai zunubi yana iya tsayaiya da wannan kauna, yana iya ki a jawo shi zuwa ga Kristi,

amma idan bai yi tsayayya ba, za a iya jawo shi zuwa ga Yesu, sanin shirin da aka yi domin

ceto zai bi da shi zuwa ga kafafun giciye cikin tuba sabo da zunubansa, wadanda suka jawo

radadi ga Dan Allah kaunataccensa.

Wannan hali na sama mai aiki bisa abubuwan halitta shi ne dai ya ke zance da zukatan

‘yan-Adam, yana halittar wani irin marmari mai tsanani domin wani abu da ba su da shi.

Abin da duniya ba za ta iya biya musu marmarin nan nasu ba. Ruhum Allah yana rokon su

su bidi irin abubuwan da su kacfai ne za su iya ba da salama da hutu — alherin Kristi, da

farin ciki na tsarki. Maicetonammu tutur yana aiki ta hanyoyi daban daban da ake gani da

ido da wadanda ba a gani, domin ya jawo hankulan ‘yan-Adam daga nishatsi na zunubi

wadanda ba su korsarwa zuwa ga albarka mara iyaka da zai zama nasu a cikinsa. Ga dukan

rayukan da su ke kokari na banza su sha daga tuluna na wannan duniya, sako daga sama

yana fada masu cewa Mai-jin kishi kuma, bari shi zo. Wanda ya ke so, bari shi diba ruwa

na rai kyauta.” Ruya ta Yohanna 22:17.

12

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Ku wadanda a cikin zukatanku kuna da marmarin wani abu da ya fi wanda duniyar

nan za ta iya bayarwa kuna gane cewa wannan marmarin muryar Allah ce zuwa ga

zukatanku, ku roke shi ya ba kutuba, ya baiyana muku cikin kauna tasa mara iyaka, cikin

cikakken tsarkinsa. A cikin zaman duniya na Mai-ceto ne aka nuna cikakkiyar shari’a ta

Allah — kauna zuwa ga Allah da dan-Adam. Alheri da taimako da kauna mara son kai, su

ne kurwar ruhunsa. Sai mun dube shi, sa’anda haske daga Mai-cetommu ya facfo bisa

kanmu sa’annan za mu ga zunubin zukatanmu.

Ya yiwu mu yabi kammu, kamar yadda Nikodimus ya yi, mu ce ai mu zamammu

daidai ya ke, mu ce mu halayemmu na kirki ne, kuma mu yi tsammani cewa ba mu da

bukatar mu kaskantar da zukatammu a gaban Allah kamar ko wane mai-zunubi, amma

sa’anda hake daga Kristi ya haskaka cikin zukatammu za mu ga yadda ba mu da tsarki ko

kadan; za mu gane son kai na nufi; za mu gane magabtaka da Allah wanda ya kazamtad da

ko wane aiki na zaman duniya. Sa’annan za mu gane cewa hakika adilcimmu kamar daud

an tsummoki su ke, sa’annan ne za mu gane jinin Kristi ne kadai zai iya tsabtace mu daga

kazamtar zunubi, ya kuma sabonta zukatammu cikin kamannin kansa.

Komai kankantar haske na darajar Allah, komai kankantar dan kyalli na tsarkin Kristi,

wanda zai huda ya shiga rayukammu, ya isa ya baiyana a fili ko wane digo na kazamta,

kuma ya baiyana a fili laifofuka na haleyemmu, Ya kan baiyana a fili rashin tsarki na

muradodimmu, da rashin aminci na zukatammu, da rashin tsarkin lebunammu. Ayukan mai

zunubi na cin amana wajen wofinta dokar Allah, za su tonu ga idanunsa, sai rai ya wahala

karkashin ikon Ruhun Allah. Sai ya ji kyamar kansa sa’anda ya dubi tsarki da rashin tabo

na halin Kristi.

Sa’anda Annabi Daniel ya ga daukakar da ta ke kewaye da Manzo na sama da aka

aiko wurinsa, ya cika da sanin rashin karfinsa da rashin cika tasa. Sa’anda ya ke kwatanta

abin da ya gani mai ban mamaki, ya ce “Ba sauran karfin da ya rage a chikina kwa; gama

jamalina ya juya a chikina, ya zama ruba, ba ni da ringin karfi.” Daniel 10:8. Ruhun da aka

tabe shi haka zai yi kiyaiya da son kansa, zai ji kyamar kaunar kansa, zai kuwa nema, ta

wurin adildn Kristi, ya samu tsarkin zuciya wadda ta ke cikin zumunci da dokar Allah da

hallin Kristi.

Bulus ya ce “Ga zanchen adilci da ke chikin shari’a.” Filibiyawa 3:6, amma sa’anda

aka gane ruhaniyancin halin shari’a, ya ga kansa mai zunubi ne.

Idan aka duba abin da shari’a ta shar’anta kamar yadda ‘yan- Adam suka dauka game

da abubuwa na waje kawai, lallai ne Bulus ya yi nisa da zunubi; amma sa’anda ya duba ya

ga zurfin sharudanta, ya kuma ga kansa kamar yadda Allah ya gan shi, ya sunkuya cikin

ladabi da kaskantar zuciya ya fadi laifinsa. Ya ce “Ni ma da da rai ni ke da ba shari’a ba:

amma sa’anda doka ta zo, zunubi ya sake rayuwa, na kwa mutu.” Romawa 7:9. Sa’anda ya

13

Matakai Zuwa Wurin Kristi

ga ruhaniyancin tabi’ar shari’a sai zunubi ya baiyana a cikin muninsa, sai kuma yabon kai

nasa ya bace.

Allah ba ya daukan zunubi a kan cewa duk girmansu daya ne. Akwai bambantar

girman laifi a wurinsa, haka kuma ga ‘yan-Adam; amma komai kankantar laifi a idanun

‘yan-Adam, ba zunubin da ya ke da kankanta a gaban Allah. Gani na dan-Adam ba cikakke

ba ne, amma Allah yana jarraba komai daidai yadda ya ke. Ana raina mashayi, ana ce masa

ba zai shiga sama ba, amma sau dayawa ba a tsautawa alfarma da son kai, da kyashi. Wadan

nan kuwa su ne suka fi ba Allah haushi; gama su akasin alherin halinsa ne, su ne akasin

kaunar nan mara son kai wadda ta ke kamar iskar da ta cika dukan halitta. Ya yiwu shi

wanda ya fada cikin zunuban da suka fi girma ya ji kunya, ya kuma ji talauci, ya kuma ji

bukatar alherin Kristi; amma alfarma ba ta kan ji irin wannan bukata ba, domin haka tana

rufe zuciya ga Kristi da albarka tasa mara iyaka wadda ya zo ya bayar.

Shi matalaucin nan mai karban haraji wanda ya yi addu’a ya ce “Ya Allah, ka yi mani

jinkai, ni mai-zunubin.” (Luka 18:13.) ya ga kansa kamar kasaitaccen mugun mutum, a

haka ne kuwa wadansu ke dubansa; amma ya ji bukatarsa a rai, da wannan kaya kuwa na

laifinsa, da kunya, ya zo gaban Allah, yana bidar jinkansa. Am bude zuciya tasa domin

Ruhun Allah ya yi aikin alherinsa, ya ‘yantad da shi daga ikon zunubi. Amma addu’ar da

ba-Farisi ya yi, cike da ruba, da yabon kai, ta nuna cewa zuciya tasa a rufe ta ke kuble ta ji

wani iko na Ruhu Mai-tsarki. Sabili da nisan da ke tsakaninsa da Allah, ba shi da wani

ganewa na kazamta tasa, akasin cikakken tsarki na sama. Bai ji wani bukata cikin ransa ba,

don haka bai karbi komai ba.

Idan ka ga zunubinka, kada ka tsaya ka ce sai ka yi dama-dama. Ina misalin yawan

wadannan da su ke tsammani ba su isa su zo ga Kristi ba! Kana tsammani ka iya kai kanka

gaba da inda ka ke ta wurin kokarin kanka kadai? “Ba-kushi ya iya sake launin fatassa, ko

damisa rodi rodinta? In hakanan ne, ku kuma ku a yi nagarta, ku da kuka saba da mugunta,”

Irmiya 13:23. Sai a cikin Allah ne kadai taimakommu ya ke. Kada mu jira wai sai an ciwo

kammu, ko sai mun samu dama wanda ya fi wanda mu ke ciki, ko kuma sai lokacin da

muka ji mun yi tsarki. Ba za mu iya yin komai mu da kummu ba. Dole mu zo ga Kristi a

matsayin da mu ke ciki.

Amma fa kada wadansu su rudi kansu da tsammani cewa Allah, cikin kauna tasa da

jinkansa masu girma, zai ceci ko su wadannan da suka ki karbar alherinsa. Sai ta wurin

hasken giciye ne kadai za a iya gane rashin kyaun zunubi. Idan ‘yan-Adam suka tsaya a

kan cewa nagartar Allah ta fi karfin ya jefas da mai zunubi, to, ya dubi Kalvari. Sabili da

babu wata hanya ne da za a iya ceton dan- Adam, domin im ba da wannan hadaya ba, ba

shi yiwuwa yan-Adam su tsira daga ikon kazantarwa na zunubi, har a mayar da su cikin

zumunci da masu tsarki — ba shi yiwuwa a garesu su zama masu taraiya na zaman ruhaniya

— Sabili da wannan ne Kristi ya dauka wa kansa laifin marassa biyayya, ya sha wahala

madadin mai zu¬nubi. Kauna, da shan wahala, da mutuwar Dan Allah, duka suna shaida a

14

Matakai Zuwa Wurin Kristi

kan kasaisar zunubi, kuma suna facfi cewa babu samun rai sai mun bada zuciyarmu ga

Kristi.

Wani lokaci marssa tuba su kan yi wa kansu hujja suna magana game da Mai-bin

Kristi suna cewa, “ai ni ma daidai da su ni ke wajen nagarta. Ba su fi ni musun kai ba, ba

su fi ni kamewa ba, ba su fi ni lura da twinkaya cikin irin zaman duniya ba. Ai su ma suna

kaunar jin dadi da nishacfi kamar ni.” Ta haka su kan kawo hujja su ce laifin wadansu shi

ya hana su yin abin da ya kamata su yi. Amma zu¬nubai da kasawa na wadansu ba shi

yiwuwa su zama hujja ga kowa, domin Ubangiji bai sa mana dan-Adam mai kuskure ya

zama abin da za mu yi koyi da shi ba. Dan Allah mara tabo ne aka bayar ya zama misali a

garemu, kuma su wadannan da su ke ganin kuskure na masu bin Yesu su ne ya kamata su

fi zaman kirki su kuma zama misalai nagari da za a kwaikwaya. Idan sun mai da matsayin

zaman mai bin Yesu yana da girma haka, ashe wannan baya shaida girman zunubansu ba?

Sun san abin da ke daidai amma sun ki aikatawa.

Yi hankali da yin sakachi. Kada ka dakatad da aikin rabuwa da zunubinka da neman

tsatstsarkar zuciya ta wurin Yesu. Ta nan ne dubbai bisa dubbai suka yi kuskure, har ya ja

musu bata na har abada. Ba zan tsaya a nan kan zancen in nuna gajarta da rashin tabbatar

zaman duniya ba; amma akwai hadari mai ban tsoro — hadarin da ba a gane shi yadda ya

kamata ba — hacfarin jinkiri ga biyewa muryar roko ta Ruhu Mai-tsarki na Allah, hadarin

zaben zama cikin zunubi, gama haka jinkirin ya ke. Zunubi, komai kan- kanta tasa, in aka

dinga aikata shi zai jawo bata na har abada. Abin da ba mu ci nasara bisa kansa ba, zai ci

nasara bisa kam mu, ya jawo mana hallaka.

Adamu da Hauwa’u sun rinjayi kansu cewa don an ci dan itace kawai wanda aka hana

ba zai jawo babban abin tsoro kamar yadda Allah ya fadi ba. Amma fa shi wannan abu

kankani ketare doka ne mai tsarki na Allah wadda ba ta sakewa, ya kuwa raba dan-Adam

da Allah, ya bucfe kofofin ruwaye na mutuwa da bakin ciki mara iyaka bisa duniya. Zamani

bisa zamani, shekara bisa shekara, kuka da makoki suna tashi tutur daga duniya zuwa sama,

duk halitta kuma ba hana ka juyowa kadai ya ke yi ba, amma yana sa ka kasa gaba da Allah.

Kalvari a tsaye ta ke kamar shaida na wannan baiko mai ban mamaki da ake bukata domin

a samu gafara sabo da ketare doka mai-tsarki.

Ko wane aiki na ketare doka, ko wane kyaliya ko kin alherin Kristi yana komowa bisa

kanka; yana taurare zuciya, da hankali, ga juyowa dungun zuwa ga kokarin nan da Ruhu

Mai-tsarki na Allah, kuma ba hana ka juyowa ka dai ya ke yi ba, amma yana sa ka kasa ga

rokon da ya ke yi dominka.

Wadansu su kan kwantar da hankalin lamirin da ya damu da cewa sua iya sake hanyar

mugunta duk sa’ad da suka ga dama, ko su yi wasa da kira na jinkai yadda su ke so. Suna

tsammani bayan sun aikata abu gaba da alherin Ruhun, bayan sun ba da karfinsu ga Shaitan,

za su iya sake hanyarsu. Amma ba abu ne mai sauki ba. Tabi’o’i da hanyar da aka bi duk

15

Matakai Zuwa Wurin Kristi

cikin zaman duniya sun rigaya sun mulmula hali har zai zama kadan ne su kan so su karbi

Yesu. Ko laifi guda daya ne kawai wanda ya shafi hali, ko marmari guda daya tak, idan

aka nace yinsa, yana iya tsaida ikon bishara. Ko wane nishadi na zunubi yana dada karfafa

rai gaba da Allah. Shi wanda ya nuna hali na kangarewa, ko rashin kula da gaskiya ta sama,

girbin abin da ya shuka ya ke yi Cikin dukan littafi Mai- tsarki ba inda aka fi fadakarwa da

kantata girman mugunta kamar kalmomin nan na mai-hikima cewa “Za ya riku da igiyoyin

zunubinsa.” Misalai 5 :22.

Kristi a shirye ya ke ya ‘yatand da mu daga zunubi, amma ba ya tilasa hankalimmu,

kuma idan ta wurin ketare doka a ko wane lokaci, hankali ya kallafa ga aikata mugunta,

har ba mu da marmarin a yantad da mu ko idan muka ki mu karbi alherinsa me kuma zai

yi? Mun hallaka kammu ke nan ta wurin kuduri na kin karbar kauna tasa. “Gashi, yanzu ne

lokaci na alheri; ga shi, yanzu ne ranar cheto.” “Yau, kadan kun ji muryatasa, kada ku

taurare zukatanku.” 2 Korinthiyawa 6:2; Ibraniyawa 3:7, 8.

“Gama mutum yana duban aini, amma Ubangiji yana duban zu- chiya.” 1 Samuila

16:7; zuciyar dan-Adam, cike ta ke da iskanci; raddadun tunane-tunanenta na farin ciki da

bakin ciki; mazaunin rucfi da rashin tsarki. Ubangiji ya san tunaninta, da kulle- kullenta,

da nufenufenta. Je ka wurinsa da ruhunka komai rashin tsabtarsa. Ka bude lollokin

zuciyarka ga idanun mai ganin komai, kamar yadda Mai-zabura ya yi, ka ce, “Ka yi

binchikena, ya Ubangiji, ka san zuchiyata, ka auna ni, ka san tunani na: Ka duba ko da wata

hanyar mugunta daga chikina, ka bishe ni chikin tafarki na har abada.” Zabura 139:23, 24.

Mutane da yawa su kan karbi wani irin imani wai shi addinini na cikin kwakwalwa,

zuciya kuwa ba ta gyaru ba. Bari wannan ya zama addu-arka, “Daga chikina ka halitta

zuchiya mai-tsabta, Ya Allah; ka tsabonta daidaitachen ruhu daga chikina.” Zabura 51:10.

Ka yi wa ruhunka gaskiya. Ka yi anniya da naciya kamar yadda za ka yi in kana cikin

hacfarin ranka na wannan duniya. Wannan matsala ce da ya kamata a daidaita ta tsakanin

ruhunka da Allah, a dai- daita ta har abada. Bege mara tushe kawai zai zama hallaka gareka.

Ka koyi kalmar Allah da addu’a. Wannan Kalma ta Allah tana baiyanawa a gabanka,

ta wurin dokar Allah da zaman duniya na Kristi, jigajigai na zaman tsarkaka, wadanda im

ba su “Babu mutum da zashi ga Ubangiji im ba tare da ita ba.’’ Ibraniyawa 12:14. Koyon

kalma tasa tana sa mu tabbata da kasancewar zunubi, tana baiyana tafarkin ceto a fili. Kasa

kunne gareta, karmar muryar Allah mai magana da ruhunka.

Idan ka farga da girman zunubi, idan ka ga kanka kamar yadda ka ke, kada ka fid da

zuciya. Masu zunubi ne Kristi ya zo ya ceta. Ba mu ne za mu sulhuntu ga Allah zuwa

kammu ba — ya kauna mai ban al’ajibi — Allah ne cikin Kristi “yana sulhunta duniya

zuwa kansa.” 2 Korinthiyawa 5:19. Shi ne ya ke panshe zukatan kangararrun ‘ya ‘yansa ta

wurin kaunar tasa mai tsarki. Ba wani ma-haifi na duniya da zai yi hakuri da laifofin

‘ya’yansa, kamar yadda Allah ya ke yi da wa- cfanda ya ke nema ya ceta. Ba wanda ya fi

16

Matakai Zuwa Wurin Kristi

shi mahawara da masu laifi. Ba lebunan dan-Adam da suka fi furta mahawara masu taushi

ga batattu kamar Shi. Duk alkawaransa, da fadakunsa, numfashi ne na kauna tasa wadda ta

fi gaban furta wa.

Idan Shaitan ya zo ya fada maka cewa kai babban mai zunubi ne, ka daga ido ka dubi

Mai-pansarka, ka yi zancen nagarta tasa. Duban haskensa shi ne zai taimake ka. Ka amsa

zunubinka, amma ka ce wa abokin-gaban “Kristi Yesu ya zo chikin duniya domin cheton

masu zunubi.” 1 Timothawus 1:15, kuma ya yiwu a cece ka ta wurin kauna tasa mara abin

kwatantawa. Yesu ya tambayi Siman a kan mabarta biyu. Daya uban-gidansa yana binsa

kudi kadan, dayan kuwa uban-gidansa yana binsa kucfi masu yawa, amma uban-gidansu

ya yafe musu duka baki cfaya. Kristi kuwa ya tambayi Siman ya ce cikin su biyun nan

wanne ne zai fi ka unar uban — gidansa. Siman ya amsa ya ce “Ina tsammani, shi wanda

aka yafe masa mai-yawa.” Luka 7:43. Mu manyan masu zunubi ne, amma Kristi ya mutu

domin a gafarta mana. Kyawawan abubuwa na baikonsa sun isa a mika su ga Uban sabili

da mu. Wadanda aka gafarta musu zunubai masu yawa su za su fi kauna tasa, za su kuma

fi tsayawa kusa da kursi- yinsa su yabe shi domin kauna tasa mai girma da baikonsa mara

iyaka. Sai lokacin da muka fi gane kaunar Allah za mu gane kazantar zunubi. Idan muka

ga tsawon sarka da aka zuraro domimmu, idan muka gane kadan daga cikin baikon da

Kristi ya yi domimmu, sa’annan zuciya za ta narke, ta yi nadama sabo da zunubi.

17

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 4 – Fadin Zunubi

“Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba; amma dukan wanda ya fade su ya

kwa rabu da su za ya sami jinkai.” Misalai 28:13.

Sharudan samun jinkai daga Allah masu sauki ne, masu adilci. Ubangiji ba ya bukatar

mu yi wasu ayuka masu tsannani domin mu samu gafarar zunubai. Ba lalai ba ne mu yi

tafiya mai nisa domin yin haji, ko mu yi wancfansu ayuka masu wuya na tuba, ko mu kocd

rayukammu ga Allah na sama ba, ko mu biya wani abu domin laifofimmu; amma shi wanda

ya fadi zunubansa ya kuma rabu da su, zai samu jinkai.

Yakubu Manzo ya ce “Ku fadi zunubanku ga juna fa, ku yi ma juna addu’a, domin ku

warke.” Yakub 5:16. Ku fadi zunubanku ga Allah, wanda shi ne kadai ya iya gafarta su,

laifofinku kuma ku facfa wa juna, Idan ka yi wa abokinka, ko makwabcinka laifi sai ka

amsa laifinka, shi kuwa wajibi ne a gareshi ya yafe maka. Sai kuma ka nemi gafarar Allah,

domin Shi dan-uwan nan naka da ka yi wa laifi dukiyar Allah ne, kuma a cikin yi wa danuwan

nan naka lahani ka yi zunubi gaba da Mahallici da Mai-pansa. An kawo karar a gaban

Matsakanci wanda “an jarabce shi ta ko wace fuska kamar mu, saidai banda zunubi,” kuma

wanda yana “tabuwa da tarayyar kumamanchin mu,” Ibraniyawa 4:15 shi kuwa yana iya

tsabtacewa daga ko wane tabo na rashin adilci.

Wadannan da ba su kaskanta zukatansu gaban Allah ba ta wurin amsa laifofinsu, ba

su cika abin da ake bukata na farko game da sharakin karba ba. Idan ba mu tuba a cikin

ranmu akan abinda da baza mu taba ba, kuma idan ba mun fadi zunubammu cikin tawali’u

na gaskiya da karayar ruhu domin zunubammu ba, ba mu kuma yi kyamar zunubammu ba,

lallai ba mu taba bidar gafarar da gaskiya ke nan ba; idan kuwa ba mu taba bida ba, bamu

taba samum salamar nan ta Allah ke nan ba. Dalili guda daya ne kadai da ya ke sa ba mu

samun kwancewar zunubi, shi ne rashin yarda mu kaskanta zukatammu da bin sharadun

Kalmar Allah na Gaskiya. Am ba da cikakken umurni game da wannan matsala. Fadin

zunubi, ko a gaban jama’a, ko cikin boye, ya kamata ya zama na zuci, a kuma fade shi da

yardan rai. Kada a iza mai zunubi ya fadi kamar cikin dole. Fadin znunbi wanda ya ke daga

cikin tushen ran mutum ya fito, ya kan samu hanya zuwa wurin Allah mai jinkai mara

iyaka. In ji Mai-Zabura, ya ce “Ubangiji yana kusa da masu karyayyar zuciya, kuma yana

ceton irin wadanda su ke da ruhu mai tuba.” Zabura 34:18

Fadin zunubi na gaskiya daban ya ke, kuma yana yarda da zunubi. Ya yiwu irin

wadannan zunbai sai gaban Allah kawai za a fade su, ya yiwu kuma wadansu irin zunuban

za a fade su ne ga mutanen da aka yi musu wannan laifi, ba a fade su a fili gaban jamma’a

ba, ya yiwu kuma wadannan laifofin da suka shafi jama’a duka, dole kuwa a fade su a fili

gaban jama’a. Amma ko wane irin amsa laifi ko fadinsa dole ne a yi shi cikin gaskiya.

18

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Cikin zamanin Annabi Samu’ila ‘ya’yan Israila suka yi nisa da Allah. A lokacin sun

sha hakkin zunubi, domin bangaskiyarsu cikin Allah ta bace masu, ganewa da ikonsa, da

hikima na mulkin al’amura duka suka bace masu, amincewarsu da shi cewa zai iya kare su

ya bace. Suka juya daga bin babban Mai-mulkin halitta, suka nemi a mallake su kamar

sauran al’umman da ke kewaye da su. Kafin su sami salama sai da suka fadi zunubinsu

suka ce “Gama mun kara ma dukan zunubanmu wannan mugunta da muka bida ma kammu

sarki.” I Samuila 12:19. Dole ne su fadi zunubin nan da aka same su da laifin sa. Rashin

godiyarsu ya nawaita rayukansu, ya yanke su daga Allah.

Allah ba zai karbi fadin laifi im ba tare da tuba da sake zama ba. Dole irin zama ya

sake, dole a share ko wane abu mai ba da haushi ga Allah. Wannan shi ne abin da ya kamata

ya abuku idan aka ji bakin ciki domin aikata zunubi. An kaiyade mana ayukan da za mu yi

a fili a gabammu game da wannan; “Ku yi wanka, ku tsabtata; ku kawas da muguntar

ayukanku daga gaban idanuna: ku bar yin mugunta; ku bidi shari’a, ku hana zalumchi, ku

shar’anta maganar marayu, ku taimaki da’awar gwamraye.’’ Ishaya 1:16, 17. “Watau, idan

shi mugun ya mayas da jingina, ya koma da abinda ya kwache ya bi kaidodi masu kawo

rai, ba ya aika wani laifi ba; lallai rai zaya yi, ba zaya mutu ba.” Ezekiel 33:15. Bulus, game

da zaman tuba, ya ce, “Bachin zuchiya da aka yi maku irin da Allah ke sa, duba irin karfin

hankali da ya aika a wurinku; i, duba, wache irin kariyar kai, i, wane irin haushi, i, wane

irin tsoro, i, wane irin dauka pansa, i, wane irin bege, i, wache irin himma! Ga kowane abu

kuka nuna kanku kubutattu a chikin wannan matsalla.” 2 Korinthiyawa 7:11.

Sa’anda zunubi ya matas da gababuwan ganewa na mutunci, mai aikata mugun abu

ba ya kan gane tauyewar halinsa ba, ko ya gane girman muguntar da ya aikata, kuma, idan

ba ya biye ma ikon hakikantarwar na Ruhu Mai-tsarki ba, sai ya zauna cikin makantar

ganin zunubinsa. Facfin laifofinsa ba za su zama na gaskiya ba, ba kuma da himma ba. Ga

ko wane amsa laifi guda sai ya kara da wata ‘yar hujjar dalilin aikinsa, ya ce im ba domin

haka da haka ba, da bai yi haka ko haka ba, akan abinda an yi masa facfa.

Bayan Adamu da Hauwa’u sun ci daga cikin ‘ya’yan itacen da aka hana su, sai suka

cika da kunya da tsoro. Tunaninsu na farko shi ne hujjar da za su bayar domin zunubinsu,

da kuma tunanin hanyar da za su tsere wa hakuncin mutuwa. Sa’anda Ubangiji ya tambaye

su a kan zunubinsu, Adamu ya amsa ya ce “Macen da ka ba ni domin ta zauna tare da ni,

ita ce ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci.” Ita macen kuma ta sa laifin kan maciji ta ce,

“Macijin ne ya rude ni, ni kuwa na ci.” Farawa 3:12, 13. Dom me ka halitta macijin? Dom

me ka bar shi ya zo cikin Addini? Wadannan su ne kamar hujjoji da ta bayar cikin amsa

dalilin zunubinta, wato ta sa alhakin faduwarsu duka a wuyan Allah. Wannan hali na

baratad da kai daga uban karere ya faru ga duk ‘yan-Adam kuwa, maza da mata, sun

baiyana shi. Irin wacfannan facfin laifi ba Ruhu Mai-tsarki ne ya ke sa a yi su ba. Allah

kuwa ba zai karbe su ba. Tuba na gaskiya ya kan sa mutum ya dauki laifinsa da kansa, ya

fade shi ba tare da ha’inci ko riya ba. Kamar shi mai karban harajin nan wanda ko daga

19

Matakai Zuwa Wurin Kristi

kansa sama bai yi ba, amma ya yi kuka ya ce “Ka yi mani jinkai ya Allah, ni mai zunubi.”

kuma su dukan wadanda suka amsa laifinsu za a baratad da su, gama Yesu zai yi roko sabili

da ruhohinsu da suka tuba ta wurin jininsa. Misalai cikin Maganar Allah na tuba mai

gaskiya da tawali’u sun baiyana cewa ruhu mai fadin laifi ba ya ba da hujjar aikata zunubi

ko ya yi kokarin baratad da kai. Bulus bai nemi kare kansa ba. Ya shafa wa zunubinsa bakin

duhu, ya nuna shi kamar bakin tukunya ya ke, bai kuma saukaka laifinsa ba. Ya ce “Na

kuble tsarkaka dayawa chikin kurkuku, bayan da na karbi izni daga wurin manyan

malamai; sa’anda a ke kisansu kuma, ni kan bada bakina gaba da su. Lokachi dayawa kuma,

chikin dukan majami’u ina gwada masu wuya, anni- yata in sa su su yi sabo; kuma domin

na fai hauka sabada su, na bi su da tsanani har ga wadansu biranai na ketaren iyaka.”

Ayukan Manzani 26:10, 11. Bai yi shakkar fadin cewa “Kristi Yesu ya zo chikin duniya

domin cheton masu-zunubi; chikinsu kwa ni ne babba.” 1 Timothawus 1:15.

Mai tawali’u da karyayyar zuciya, kasashshe ta wurin tuba mai gaskiya, zai gane wani

abu daga cikin kaunar Allah da tamanin Kalvari; kuma kamar yadda da ya kan fada wa

ubansa mai kauna tasa, hakanan mai tuba na gaskiya zai kawo dukan zunubansa gaban

Allah. Kuma an rubuta “Idan mun fadi zunubanmu, shi mai-alkawali ne, mai-adilchi kuma,

da za shi gafarta mamu zunubanmu, shi tsar¬kake mu daga dukan rashin adilchi.” I

Yohanna 1:9.

20

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 5 – Tsarkakewa

Alkawarin Allah shi ne “Za ku neme ni, ku same ni kuma, lokacin da ku ke nemana

da zuchiya daya.” Irmiya 29:13.

Sai a ba da dukan zuciya ga Allah, im ba haka ba, sakewar da ake bukata wadda za ta

maishe mu ga soyaiya tasa ba za ta samu ba. Bisa ga tabi’a mu kebabbu ne daga Allah.

Ruhu Mai-tsarki ya kwatanta matsayimmu da wadannan maganganu: “matattu cikin laifofi

da zunubi.” “dukan kai yana ciwo, dukan zuciya ta yi suwu”; “babu lafiya a ciki.” A rike

mu ke tsantsan cikin tarkon Shaitan, “Yayinda ku ke matattu ta wurin laifofinku da

zunubanku,” “dukan kai yana chiwo, zuchiya duk ta yi suwu;” “tun daga tafin tsawu har

zuwa kai babu lafiya a chikinsa,” “Da shike bawan Ubangiji ya kama su da rai zuwa nufin

Allah.” Afisawa 2:1; Ishaya 1:5, 6; 2 Timothawus 2:26. Allah yana so ya warkas da mu,

ya ‘yantad da mu. Amma tun da ya ke ana bukatar sakewa dungum, da sabontuwar

tabi’armu, sai mu bada kammu dungum zuwa gareshi.

Yaki tsakanin dan-Adam da kansa shi ne yaki mafi tsanani da aka taba yi. Sai an yi

kokawa mai tsanani idan ana so a ba da kai dungum cikin biyaiya da nufin Allah. Amma

dole ne ruhu ya saduda Allah kafin a sabonta shi cikin tsarki.

Mulkin Allah ba kan makantaccen biyaiya aka kafa shi kamar yadda Shaitan ya kan

sifanta shi ba, ba kuma mulki ne mara ma’ana ba. Mulkin nan ya shafi hankali da lamiri.

“Mu zo yanzu, mu yi binchike tare, in ji Ubangiji.” Ishaya 1:18. shi ne kiran da Mahalici

ya ke yi ga halitta tasa. Allah ba ya tilasa nufin halittattunsa. Ba zai iya karbar sujada wadda

ba tare da son rai da hankali aka yi ta ba. Baiyaya na tilas ya kan hana ci gaba na

kwakwalwa da hali. Irin wannan ya kan mai da danAdam kamar keke da aka sa ya yi aiki

ko da mai lurad da shi ko babu, kamar agogo. Ba wannan ne nufin Mai-halitta ba. Nufin sa

ne dan-Adam, wanda shi ne gaba cikin halittasa, ya ci gaba ya kai matukar cin gaba. Ya sa

matsayin albarkar da ya ke so ya kai mu ta wurin alherinsa a gabammu. Yana kiram mu

mu ba da kammu gareshi, domin ya aikata nufinsa a cikimmu. Ya rage a wurimmu mu zaba

ko za a yantad da mu daga bautar zunubi, mu zama masu taraiyar ‘yanci mai daraja na

‘ya’yan Allah.

Cikin ba da kammu gareshi, dole ne mu bar duk irin abubuwan da za su raba mu da

shi. Sabo da haka ne Mai-ceto ya ce, “Hakanan fa kowanene da ke chikinku da ba ya rabu

da dukan abinda ke nasa ba, ba shi da iko shi zama mai-bina ba.” Luka 14:33. Sai a bar ko

wane abin da zai janye zuciya daga Allah. Duniya ita ce gumkin ‘yan-Adam masu yawa.

Kaunar kudi, son wadata, su ne sarka ta zinariya da ta daure su hade da Shaitan. Wadansu

kuwa samun suna da girman duniya su ke yi wa sujada. Wadansu kuma zaman son kai mai

sauki da rashin daukar nawaiyar komai su suka mayar gumakansu. Amma dole a tsintsinka

wadannan igiyoyi na bauta. Ba shi yiwuwa rabim mu ya zama na Allah, daya rabin kuwa

ya zama na duniya. Mu ba ‘ya’yan Allah ba ne sai mun ba da kammu dungum. Akwai

21

Matakai Zuwa Wurin Kristi

wadansu da su ke ce suna bauta wa Allah, amma suna dogara ga karfin kansu wajen biyaiya

da doka tasa, suna dogara ga karfin kansu su yi hali mai kyau, suna dogara ga karfin kansu

su samu ceto. Zukatansu ba su motsu da sanin zurfin kaunar Kristi ba, amma suna nema su

aikata abubuwan da ya kamata Mai bi ya aikata kamar shi ne abin da Allah ya ke bukata

daga garesu kafin su samu mulkinsa. Irin wannan addini bai dada komai ba, ba shi kuwa

da wani amfani. Sa’anda Kristi ya shiga ya zauna cikin zuciya, ruhu zai cika da kauna tasa

zai cika da farin cikin zuciya da taraiya da shi, har ya manne masa, kuma cikin tunawa da

shi, sai ya manta da kansa. Kauna zuwa ga Kristi shi ne zai zama masomin aiki. Su wadanda

suka ji rinjayar kaunar Allah ba sua tambayar kankantar abin da za a bayar domin a cika

muradin Allah, ba su’a tambayar matsayi na kasa, amma suna da burin cikakken muwafaka

da nufin Mai-pansarsu.Da himma su kan ba da duka, kuma su nuna kulawa tasu

gwargwadon tamanin abin da su ke bida. Furta ban- gaskiya ga Kristi ba tare da wannan

kauna mai zurfi ba, maganar lebe ne kawai, busashshen abu, aikin wahalaswa kawai.

Kana ji a ranka cewa bayar da duka ga Kristi babban hadaya ne da bai kamata ba?

Tambayi kanka wannan tambaya, “Me Kristi ya ba ni?” Dan Allah ya ba da duka, — rai,

da kauna, da radadi, — domin pansarmu. Ya zama fa mu, wacfanda ba mu cancanci

wannan babbar kauna ba, mu hana shi zukatammu? Ko wane minti na zama- mmu na

duniya muna diba daga cikin albarkar alherinsa, sabili da wannan ne ba za mu iya gane

zurfin jahilci da bacin zuciyar da aka tsamo mu daga ciki ba. Mua iya dubansa wanda

zunubammu suka soka, sa’annan mu ki yarda mu aikata nufin kaunarsa da hadaya tasa?

Idan muka duba kaskancin da Ubangijin daraja ya sha, ya yiwu mu yi wani gunaguni idan

ya zamana kafin mu samu rai sai mun sha gwagwarmaya da kaskantar da kanmu.

Tambayar da masu fadin rai su ke yi shi ne, “Me zai sa sai na tuba na kaskanta kaina

kafin in samu tabbatawar cewa Allah zai karbe ni?” Na ce ku dubi Kristi. Shi ba shi da

zunubi, kuma har ya fi haka, Shi sarkin sama, amma domin dan-Adam ya zama zunubi

sabo da jama’a. “Aka lissafta shi wurin masu-laifi: duk da haka ya dauki zunubi na mutane

dayawa, ya kuma yi roko sabili da masu- laifi.” Ishaya 53:12.

To, amma me muka bari idan muka bayar da duka? —Zuciya kazantacciya da zunubi,

domin Yesu ya tsarkake, ya tsabtace ta ta wurin jininsa na kansa, kuma ya cetar ta wurin

kauna tasa mafi abin kwatantawa. Amma duk da haka ‘yan-Adam suna tsammani abu ne

mai wuya a bayar da duka. Ina jin kunya in ji an fadi haka, kuma ina jin kunya in rubuta

hakanan.

Allah ba ya so mu bar irin abin da shi ke yana da amfani a garemu wanda ya yiwu mu

rike. Cikin dukan abin da ya ke yi, jin dadin ‘ya’- yansa shi ne ya sa a gaba. Duk sammai

suna kula da jin dadin dan-Adam. Ubammu na sama bai rufe wa ko wane daga cikin halittattunsa

kofofin jin dadi ba. Bukace-bukacen Allah su ne yana kiram mu mu bar nishacfnishacfe

da za su jawo mana wahala da karayar zuciya, wacfanda za su rufe mana kofofin

farin ciki na sama Mai-pansar duniya yana karban yan-Adam yadda su ke, da bukace-

22

Matakai Zuwa Wurin Kristi

bukacensu, da rashin cikassu, da rashin karfinsu, kuma ba tsabtace su daga zunubi da ba su

pansa ta wurin jininsa kadai zai yi ba, amma zai biya dukan muradin wadanda suka yarda

suka sa karkiya tasa a wuyansu, suka yarda su dauki kayansa. Nufinsa ne ya ba da salama

da hutu ga dukan wadanda suka zo wurinsa domin su samu gurasa ta rai. Ayyukan da ya

ke bukata daga garemu su ne wadanda za su bi da sawayen mu zuwa ga matukar albarka

wadda kangararru ba za su iya kaiwa ba dacfai. Farin ciki mai gaskiya na ruhu shi ne samun

Kristi ya sifantu daga cikin zuciya, ya zama begen daraja.

Dayawa suna tambaya “Yaya zan ba da kaina dungum ga Allah?” Kana da nufin ka

ba da kanka gareshi amma ba ka da karfin ran da za ka yi hakanan in kana cikin bautar

shakka, kuma idan tabi’unka na zunubi su na mulki da kai. Dukan alkawaranka da

kudurinka kamar igiyoyin rairayi ne suke. Ba ka iya mulkin tunaninka da tunanin da su kan

zo maka farat daya ba tare da shiri ba, ba ka da iko kan nufe-nufen zuciyarka. Sanin karya

alkawaranka da lamuninka da ka dauka su kan raunana bangaskiyarka cikin gaskiyar

nufinka, su kan sa ka ji a ranka cewa Allah ba zai karbe ka ba, amma kada ka fid da zuciya.

Abin da ya kamata ka gane shi ne karfin gaskiya na nufi. Wannan shi ke mulki bisa tabi’ar

dan-Adam, ikon zartaswa ko zabe. Komai ya rataya ga aikatawa daidai na hankali. Allah

ya ba ‘yan-Adam ikon zabe, nasu ne su yi aiki da wannan iko. Ba shi yiwuwa ka sake

zuciyarka; ba shi yiwuwa don kanka ka ba Allah kaunar nan ta zuci, amma ka iya zaben ka

bauta masa. Ka iya ba shi hankalinka, a sa’annan ne zai iya aiki ya sa ka nufa ka kuma

aikata daidai da jin dadinsa mai kyau. Ta haka nan za a kawo duk tabi’arka karkashin ikon

Ruhun Kristi; duk kaunarka za ta tattaru bisa kansa, tunaninka za su zama cikin muwafaka

da shi.

Nufin aikata abin kirki da kasancewa cikin tsarkaka daidai ne don kansu, amma idan

ka tsaya nan ba za su dada komai ba. Dayawa za su bata idan suka tsaya kan bege da nufin

su zama masu bin Kristi kawai. Ba su kai ga matasayin ba da hankalinsu ga Allah ba. A

yanzu ba su zabi su zama masu bin Kristi ba.

Ta wurin aiki da hankali yadda ya kamata za ya yiwu ka sa ke irin zamanka dungum.

Ta wurin ba da hankalinka ga Kristi, sai ka shiga cikin amana da iko wanda ya fi dukan

mulkoki da ikoki. Za ka samu karfi daga bisa wanda zai rike ka a tsaye sosai, kuma ta

wajen ba da kai dungum ga Allah za ka iya zaman sabon rai, i, zaman ran nan na

bangaskiya.

23

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 6 – Bangaskiya da Yarda

Da shi ke Ruhu Mai-tsarki ya rayad da lamirinka, ka ga wani abu na muguntar zunubi,

ka ga ikon zunubi, da laifinsa, da kaitonsa, kuma kana duban sa da kyama. Ka ji a ranka

cewa zunubi ya raba ka da Allah, kuma kana cikin bautar ikon mugunta. Gwargwadon

kokarin ka tsere, gwargwadon ganewar rashin iyawarka. Nufe-nufenka ba su da tsarki,

zuciyarka ba ta da tsabta. Ka gani zamanka na duniya cike ya ke da son kai da zunubi.

Kana marmarin ka samu gafara, a tsabtace ka, a ‘yantad da kai. Muwafaka da Allah, zama

kama tasa — Me za ka yi ka samu wannan?

Salama ne ka ke bukata — Gafaran Ubangiji da salama da kauna cikin zuciya. Kudi

ba zai iya saye ba, hankalin kwakwalwa ba zai iya samo shi ba, hikima ba za ta kai gareshi

ba, ba shi yiwuwa ka yi ko bege, ta wurin kokarin kanka, cewa za ka kai gareshi. Amma

Allah ya ba ka shi kamar kyauta “Ba da kurdi, ba da abin biya ba.” Ishaya 55:1. Naka ne

idan dai ka yarda ka mika hanunka ka kamo shi. Ubangiji ya ce “Ko da zunubanku sun yi

kamar mulufi, za su yi fari kamar snow: ko da suna jawur kamar garura, zasu zama kamar

adbuga.” Ishaya 1:18. (tsakiyansa) “Sabuwar zushiya kuma zan ba ku, sabon ruhu kuma

zan sa a chikinku.” Ezekiel 36:26.

Kun fadi zunubanku, kuma a cikin zukatanku kun jingine su waje daya. Kun kudurta

za ku ba da kanku ga Allah. To, ku je wurinsa yanzu, ku roke shi ya wanke zunubanku, ya

ba ku sabuwar zuciya. Sa’ annan ku gaskanta ya aikata wannan domin ya rigaya ya yi

alkawari. Wannan shi ne abin da Yesu ya koyas sa’anda ya ke duniya, cewa kyautar da

Allah ya ba mu, dole mu tabbata mun karba, kuma namu ne. Yesu ya warkas da mutane

daga cuce-cucensu sa’anda su ke da bangaskiya cikin ikonsa; ya taimake su cikin

abubuwan da suka iya gani, ta haka ya hura musu bangaskiya cikinsa a kan abubuwan da

ba su iya gani ba — wato biyas da su zuwa gaskanta ikonsa na gafarar zunubai. Ya fadi

wannan a fili sa’anda ya ke warkas da mai ciwon inna; “Amma domin ku sani Dan mutum

yana da iko a duniya shi gafarta zunubai (daga nan ya che ma mai-chiwon inna), Tashi, ka

dauki shimfidarka, ka tafi gidanka.” Matta 9:6. Haka kuma Yohanna Manzo ya fadi sa’anda

ya ke magana a kan ayyukan al’ajibi na Kristi, “Amma an rubuta wadannan, domin ku bada

gaskiya Yesu Kristi ne, Dan Allah, chikin bada gaskiya kuma ku sami rai a chikin

sunansa.’’ Yohanna 20:31.

Daga labaru masu sauki na cikin Littafi Mai-tsarki wadanda aka bayar a kan yadda

Yesu ya warkas da masu ciwon za mu iya koyon wani abu na yadda za a ba da gaskiya

gareshi domin gafarar zunubai. Bari mu juya ga labarin mai ciwon inna a Bethesda. Shi

wannan mai ciwo ba shi da hanyar taimako; shekara arba’im-biyu-babu bai yi amfani da

gababuwansa ba. Duk da haka Yesu ya ce masa “Tashi, dauki shimfidarka ka yi tafiya.”

Ya yiwu mai ciwon ya ce “Ubangiji, idan za ka iya warskas da ni, na yi biyaiya da kai.”

Amma bai fadi haka ba, ya gaskanta maganar Kristi, ya gaskanta an warkas da shi, ya kuwa

24

Matakai Zuwa Wurin Kristi

yi kokarin tashi nan da nan, ya kudurta ya yi tafiya cikin ransa, ya kuwa yi tafiya. Ya aikata

bisa ga cewar Kristi, Allah kuwa ya ba shi ikon yin haka. An warkas da shi.

Ta hakanan kuma ka ke mai zunubi. Ba shi yiwuwa ka samu gafarar zunubanka na da,

ba shi yiwuwa ka sake zuciyarka, ka mai da kanka mai tsarki. Amma Allah ya yi alkawari

zai yi maka wadannan duka ta wurin Kristi. Ka gaskanta wannan alkawari? Ka fadi

zunubanka, ka ba da kanka ga Allah. Ka yi kuduri za ka bauta masa. Muddan ka yi wannan,

Allah zai cika nasa alkawarin. Idan dai ka gaskanta alkawarin — ka gaskanta an gafarta

maka an kuma tsabtace ka — Allah yana ba da tabbatawa; an maishe ka lafiyayye, daidai

kamar yadda Kristi ya ba da iko ga mai ciwon inna ya yi tafiya sa’anda shi mutumin ya

gaskanta an warkas da shi. Ya rage kai ka gaskanta.

Kada ka jira sai ka ji an maishe ka lafiyayye, amma ka ce, “Na gaskanta an warkas da

ni, hakannan ne, ba domin ina ji a jiki ba, amma domin Allah ya alkawarta.”

Yesu ya ce, “Dukan iyakar abinda ku ke addu’a kuna roko kuma, ku bada gaskiya kun

rigaya kun karba, za ku samu fa.” Markus 11:24. Akwai sharad’i game da wannan alkawari

— Shi ne mu yi addu’rf daidai da nufin Allah. Amma nufin Allah ne ya tsabtace mu daga

zunubi, ya maishe mu ‘ya’yansa, ya kuma sa mu iya zama na tsarki. Domin haka muna iya

rokon wandannan albarka, ku kuwa gaskanta mun karbe su, mu kuma gode wa Allah domin

mun karbe su. Daidai ne, kuma haka ne, ba mai ikon hana mu zuwa wurin Yesu domin a

tsabtace mu, kuma mu tsaya gaban shari’a ba tare da jin kunya ko nadama ba. “Babu

kayaswa fa yanzu ga wadanda ke chikin Kristi Yesu.’’ Romawa 8:1.

Daga nan gaba kai ba naka ne na kanka ba, an saye ka da tamani “Ba da abubuwa

masu-lalachewa ba, da su azurfa ko kwa zinariya, . . . amma da jini mai-daraja, kamar na

dan rago mara-aibi; mara- chikas, watau jinin Kristi.” I Bitrus 1:18, 19. Ta wurin wannan

sassaukan aiki na ba da gaskiya ga Allah Ruhu Mai-tsarki ya haifi sabon rai cikin zuciyarka.

Kai kamar jariri ka ke da aka haifa a cikin iyalin Allah, yana kuwa kaunarka kamar yadda

ya ke kaunar Dansa.

Yanzu fa da shi ke ka ba da kanka ga Yesu, kada ka ja da baya, ka da ka kawas da

kanka daga gareshi, amma ko wace rana ka ce “Ni na Kristi ne, na ba da kaina gareshi,” ka

kuma roke shi ya ba ka Ruhunsa, ya kiyayye ka ta wurin alherinsa. Da shi ke kuma ta wurin

ba da kanka ga Allah, da kuma bangaskiya cikinsa, ka zama da a gareshi, don haka ne za

ka zauna a cikinsa. Manzo ya fadi ya ce “Tun da shike kuka karbi Kristi Yesu Ubangiji, sai

ku yi ta tafiya a chikinsa hakanan.” Kolosiyawa 2:6.

Wadansu su kan ji ya kamata su kasance cikin kwanaki na gwaji, kuma wai sai dole

sun tabbatarwa Ubangiji cewa sun sake kafin su ruski albarka tasa. Amma suna iya ruskar

albarkar Allah ko a yanzu. Dole ne su samu alherinsa, su samu Ruhun Kristi domin ya

taimaki rashin karfinsu, im ba haka ba ba za su iya tsayawa mugunta ba. Yesu yana kaunar

mu zo gareshi yadda mu ke, cike da zunubi, raunanu masu neman madogara. Ya yiwu mu

25

Matakai Zuwa Wurin Kristi

zo da dukan rashin karfimmu, da wautarmu, da zunubammu, mu fadi a gabansa cikin tuba.

Darajatasa ce ya rungume mu cikin hannuwan kauna tasa, ya daure raunukammu, ya

tsabtace mu daga dukan rashin tsarki.

Ga inda dubbai su kan gaza: ba su gaskanta cewa Yesu ya gafarta musu don kansu su

kacfai ba. Ba su cfaukan Allah kan maganatasa. Wajibi ne ga dukan wadanda suka cika

sharudan kan su su sani don kansu cewa gafarar nan kyauta ake mika ta sabo da ko wane

zunubi. Ku jinginar da ko wace shakka na cewa alkawaran nan na Allah ba domin ku ba

ne. Alkawarai ne domin ko wane mai zunubi da ya tuba. An tanada karfi da alheri ta wurin

Kristi domin mala’iku masu hidima su kawo su ga kowane ruhu mai ba da gaskiya. Ba

wanda zunubansa suka yi yawa har da ba zai iya samun icarfi, da tsarkakewa, da adilci

cikin Yesu ba, wanda ya mutu domin su. Yana jira ya yaye musu tufafinsu da suka yi dauda

da kazanta cikin zunubi, ya kuma yafa musu fararen sutura na adilci, yana cewa su rayu,

kada su mutu.

Allah ba ya yi da mu kamar yadda dan-Adam ya ke yi da wani dan-Adam Tunanetunanensa

na jinkai ne da kauna, da juyayi. Allah ya ce “Mai-mugunta shi saki hanya tasa,

mara-adilchi kuma shi bar tunaninsa: shi komo wurin Ubangiji, shi kuwa za ya jikansa;

wurin Allahnmu, gama za ya yi gafara a yalwache.” “Na shashafe laifofinka kamar hadari

baki kirin, kamar girgije kuma zunubanka.” Ishaya 55:7; 44:22.

“Ga ma ba na jin dadin mutuwar kowa, in ji Ubangiji Yaweh: ku tuba fa, ku yi rai.”

Ezekiel 18:32. Shaitan a shirye ya ke ya saci tabbatattun alkawaran nan masu albarka na

Allah. Nufinsa ne ya dauke ko wane dan kyalkyali na bege, da ko wane dan haske mai

haskakawa daga cikin zuciya, amma dole mu ki yarda ya yi haka. Kada ku kasa kunne ga

mai-jaraba, amma ku ce “Yesu ya mutu domin ni in rayu. Yana kauna ta, kuma ba nufinsa

ba ne in hallaka. Ina da Uba na sama mai tausayi; kuma ko da shi ke na zagi kauna tasa, ko

da shi ke na batar da albarkar da ya bayar a lalace, duk da haka “Ni tashi, in tafi wurin

Ubana, in che masa, Ubana na yi zunubi gaban sama, da kuma gabanka: ban isa ba a kara

che da ni danka: a maishe ni kamar wani a chikin barorinka.’’ “Amma tun yana da nisa

tukuna, ubansa ya hange shi, ya yi juyayi na tausayi, ya yi ta yi masa sumba.” Luka 15:19-

20.

Duk da haka ko shi wannan misali, da ban tausayinsa, bai kai munzulin nuna juyayi

mara iyaka na Uba na sama ba. Ubangiji ya fadi ta bakin annabinsa ya ce “Hakika, na yi

kamnarka da mada- wamiyar kamna; domin wannan na jawo ka da rahama.” Irmiya 31:3.

Tun mai zunubi yana nesa da gidan Uban, yana batar da dukiya tasa a can wata bakuwar

kasa, zuciyar uban tana nan tana begen sa, kuma ko wane marmari da ya zocikin zuciya

don ya sa a koma ga Allah, roko ne na Ruhu Mai-tsarki, yana nema, da naciya, yana roko

yana jawo mai-gantalin zuwa ga zuciyar Ubansa ta kauna.

26

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Da sauran yin shakka duk da wadatattun alkawaran nan na cikin Littafi Mai-tsarki a

gabanka? Kana iya gaskanta cewa sa’anda mai zunubi, abin tausayi, ya yi marmarin

komowa, ya yi marmari rabuwa da zunubansa, Ubangiji zai hana shi zuwa kafafunsa cikin

tuba? Yi nesa da wadannan tunane-tunane! Ba abin da ya fi ji ma ranka ciwo kamar ka bar

wadannan tunane-tunane cikin ranka game da Ubammu na sama. Allah ya ki zunubi, amma

yana kaunar mai zunubi, kuma ya ba da kansa cikin surar Kristi domin duk wanda ya ga

dama ya tsira, ya samu albarka na har abada cikin mulkin sa mai daraja. Wacce murya ce

ta fi karfi ko taushi da za a yi amfani da ita wadda za ta furta kauna tasa zuwa garemu? Ya

furta cewa,

“Ya yiwu mache ta manta da danta mai-shan mama, har da ba za ta yi juyayin dan

chikinta ba? i, ya yiwu wadannan su manta, amma ni ba ni manta da ke ba.” Ishaya 49:15.

Ku ta da kanku ku dubi sama, ku da ku ke shakka kuna rawan jiki, gama Yesu yana

da rai domin ya yi roko sabili da mu. Ku gode ma Allah domin bada Dansa kaunatacce, ku

yi addu’a kuma domin kada ya zama ya mutu domimmu a banza. Ruhu yana kiranku yau.

Ku zo ga Yesu da dukan zuciyarku, ku ruski albarka tasa.

Idan kuna karanta alkawaran nan, ku tuna kalmomi ne masu furta kauna tasa da tausayi

wadanda ba a iya fadin su da baka. Ana jawo babbar zuciya ta kauna mara iyaka zuwa ga

mai zunubi tare da tausayi mara iyaka “Wanda muna da pansarmu a chikinsa ta wurin

jininsa, gafarar laifofinmu.” Afisawa 1:7. Hakika, sai ku gaskanta kawai Allah ne mai

taimakonku. Yana so ya mayar da sifa tasa cikin dan- Adam. Idan kuka kusanto gareshi da

fadin zunubi da tuba, shi kuma zai kusanto gareku cikin jinkai da gafara.

27

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 7 – Gwaji na Almajiranci

“Idan fa kowane mutum yana cikin Kristi, sabon halitta ne: tsofofin al’amura sun

shude; ga kwa sun zama sabobbi.” 2 Kor. 5:17. da suka sa dan-Adam ya fara juyawa, ba

zai tabbatar cewa mutum bai juya ba. Kristi ya ce da Nikodimu “Iska ya kan hura wajen da

ya ke nufa, kana jin motsinsa kuma, amma ba ka sani wajen da ya ke fitowa, da inda za shi

ba: hakanan ne dukan wanda an haife shi daga chikin Ruhu.’’ Yohanna 3:8. Kamar iska,

wanda ba a gani, amma ana ji, ana kuwa ganin aikinta, haka Ruhun Allah ya ke cikin

aikinsa bisa zuciyar ‘yan-Adam. Ikon sabontuwa wanda ba idon dan-Adam da zai iya gani,

shi ya ke haifan sabon rai cikin zuciya, yana halitta sabon rai cikin kamannin Allah. Kuma

ko da shi ke aikin Ruhu ba a ganinsa da ido haka kuma jin motsinsa, amma ana lura da bain

da ya aikata. Idan zuciya ta sabontu ta wurin Ruhun Allah, irin zaman mu ba da shaidar

sakewa. Ko da shi ke ba mu iya yin komai domin mu sake zukatammu, ko mu kawo kammu

cikin muwafaka da Allah; ko da shi ke dole ne mu ki yarda da kam mu ko ayyukammu

masu kyau, zamammu zai nuna ko alherin Allah yana zaune cikim mu. Za a ga sakewa

cikin haleyemmu, cikin tabi’o’immu, da abin da mu ke ciki. Bambancin zai fito a fili ya

nuna yadda halayemmu na da su ke da yadda su ke a yanzu. Hali zai baiyana ba ta wurin

ayyuka masu kyau ko marassa kyau lokaci lokaci ba, amma ta wurin zama tabi’a ga hali

cikin magana ko aikatawa.

Gaskiya ne ya yiwu a ga halaye na kirki daga waje amma ba tare da ikon sabontawa

na Kristi ba. Son girma ko marmarin a ce wane shi ne wane, yana iya sa ya yi zaman

kimtsuwa. Ta wacce hanyace fa za mu iya aikata abubuwa nagargaru? Ta wacce hanyace

fa za mu iya tabbatar da sashin da mu ke tsaye? Neman mutuncin kai zai sa mu kauce wa

mugun zama na zunubi a waje. Zuciya mai son kanta ta iya aikata abubuwa nagargaru.

Wane ne ke da zuciyarmu? Tare da wa tunanimmu su ke? Kan wa mu kan so ku yi

tadi? Wa ke da kaunarmu da kwazommu? Idan mu na Kristi ne, tunannimmu a wurinsa su

ke, kuma tunane- tunanemmu masu dacfi a wurinsa su ke. Duk abin da mu ke da shi da

yadda mu ke mu kammu, an tsarkake dominsa. Muna marmarin mu samu shaidar kama

tasa a jikinmmu, mu yi numfashi cikin Ru- hunsa, mu aikata nufinsa, mu sa ya ji dadi cikin

ko wane abu da muka aikata.

Wadannan da suka zama sababbin halitta cikin Kristi za su fito da ‘ya’yan Ruhu,

“Amma diyan Ruhu kamna ne, farinchiki, salama, tsawon jimrewa, nasi ha, nagarta,

aminchi, tawali’u kamewa.” Galati- yawa 5 :22, 23. Ba za su kera kansu bisa ga kwadayi

na da ba, amma ta wurin bangaskiya na Tan Allah za su bi cikin gurbin sawunsa, su nuna

halinsa kamar ta cikin madubi, kuma su tsarkake kansu kamar yadda shi ke mai tsarki.

Abubuwan da su ke ki a da su su ke kauna yanzu; abubuwan da su ke kauna a da kuma, su

su ke ki yanzu. Mai alfarma da shishigi a da ya zama mai tawaliu da kaskantar zuciya. Mai

girman kai da alfarma ta banza a da ya zama mara shishigi. Bugagge ya zama mai hankali,

28

Matakai Zuwa Wurin Kristi

mara kunya kuma ya zama mai tsarki. Al’adu da yayin duniya na banza sai a jingine su

waje daya. Masu bin Yesu ba za su bidi adonsu “ya zama na waje” ba “amma boyayyen

mutum na zuciya, cikin tufafi wadanda basu lalacewa, na ruhu mai ladabi mai lafiya.” 1

Bitrus 3:3, 4.

Babu shaidar tuba na gaskiya sai da ayuka na sakewa. Idan ya mayar da lamuni, ya

mayar da abin da ya kwace, ya fadi zunubansa, ya kaunaci Allah da ‘yan-uwansa ‘yan-

Adam, sai mai zunubi ya tabbata ya ketare daga mutuwa zuwa rai.

Sa’nda mu, kangararu, masu zunubi, muka zo ga Kristi muka zama masu taraiya cikin

alherin gafararsa, kauna za ta bulbulo daga cikin zuciya. Ko wane kaya ba shi da nauyi,

domin karkiyan da Kristi ya ayyana mai sauki ne. Abin da ya wajaba ya zama abin farin

ciki, baiko kuma abin murna. Tafarkin da ya zama rufe da duhu a da ya zama mai haske

daga hasken Rana ta Adilci.

Za a ga kyaun halin Kristi a cikin masu binsa. Murna ce a gareshi ya aikata nufin

Allah. Kauna zuwa ga Allah, kwazo domin daraja tasa, su ne iko mai bayaswa cikin zaman

duniya na Mai-cetommu. Kauna ita ce ta kawata, kuma ta cfaukaka dukan ayyukansa.

Kauna ta Allah ce. Zuciyar da ba a tsarkake ta ke ba, ba za ta iya gane wannan ba. A cikin

zuciyar da Yesu ya ke mulki ne kawai a kan samu. “Muna kamna, domin ya fara kamnache

mu.” I Yohanna 4:19. A cikin zuciyar da aka sabonta ta wurin alheri na sama, kauna ita ce

muhimmin abu cikin aiki. Ita ta ke tausa hali, ita ta ke mulki bisa sababbin tunanetunnanemmu,

da nufe-nufen zuciyarmu, nagar¬garu ko miyagu, ita ta ke nasara bisa

magabtaka, ta kuma daukaka soyaiyarmu. Wannan kauna, abin tunawa cikinzuciya, tana

dadada zaman duniya tana watsa iko mai tsarkakewa ko ina kewaye.

Akwai wadansu kuskure guda biyu wadanda ‘ya’yan Allah — musamman su

wacfanda suka zo suka amince da alherinsa yanzu — ya kamata su lura da su. Na fari,

wanda aka riga aka yi magana akansa, shi ne duba ayyukansu, suna amincewa da ko wane

abu da za su iya aikatawa, domin su kawo kansu cikin muwafaka da Allah, Shi wanda ya

ke kokarin ya zama mai tsarki ta wurin yyukansa na kiyaye doka, yana kokarin yin abin da

ba shi yiwuwa ne faufau. Duk abin da dan-Adam zai yi im ba tare da Kristi ba kazantacce

ne da son kai da zunubi. Alherin Kristi ne kawai, ta wurin bangaskiya, zai iya maishe mu

masu tsarki.

Kuskure na biyu kuwa wanda shi ma yana da hatfari mai yawa shi ne cewa bangaskiya

cikin Kristi yana daukewa ‘yan-Adam kiyaye dokar Allah, ku kuwa cewa tun da shi ke ta

wurin bangaskiya ne kadai za mu zama masu taraiya cikin alherin Kristi, ayyukammu ba

su hada komai da pansarmu ba.

Amma fa lura a nan cewa biyayya ba abu ne kawai na waje da za a aikata ba, amma

bauta ne na kauna. Dokar Allah hanya ce ta furta aininhin tabi’arsa, shi ne ya ke kamanta

manyan muhimman abubuwa na kauna, domin haka shi ne tushen mulkinsa cikin sama da

29

Matakai Zuwa Wurin Kristi

duniya. Idan zukatammu sun sabonta cikin sifar Allah, idan aka dasa kauna ba-samaniya

cikin zuciya, ashe ba dokar Allah ce za a aikata cikin zaman duniya ba? Sa’anda aka dasa

muhimman abu¬buwa na kauna cikin zuciya, sa’anda aka sabonta dan-Adam cikin surar

Mahallicinsa, an cika alkawaran sabon alkawari, “In sa doko- kina a bisa zuchiyarsu, a bisa

hankalinsu kuma in rubuta su.’’ Ibrani- yawa 10:16. Idan kuwa aka rubuta dokar bisa

zuciya, ashe ba sai ya sake sifanta zaman duniya ba? Biyaiya — bauta da zaman aminci ga

kauna — shi ne alama na gaskiya na almajiranci. Littafi Mai- tsarki ya ce “Gama kamnar

Allah kenan, mu kiyaye dokokinsa, ‘ “wanda ya che, Na san shi, amma ba ya kiyaye

dokokinsa ba,makar yachi ne; gaskiya kwa ba ta chikinsa ba.” I Yohanna 5:3; 2:4.

Maimakon kawas da yan-Adam daga biyayya, bangaskiya ce kacfai take maise su masu

tarayya cikin alherin Kristi, ita ce take sa mu yi biyayya.

Ba mua samun ceto ta wurin biyaiyarmu; gama ceto kyauta ne daga Allah, wanda 2a

a karba ta wurin bangaskiya. Amma biyayya diyar bangaskiya ce “Kun sani aka bayana shi

domin daukan zunubai, a chikinsa kwa babu zunubi. Dukan wanda ya ke zamne chikinsa

ba shi aika zunubi ba: dukan wanda ya ke aika zunubi ba ya taba ganinsa ba ba ya san shi

kuma.” 1 Yohanna 3:5, 6. A nan ne gwaji na gaske ya ke. Idan muna zaune cikin Kristi,

idan kaunar Allah tana zaune cikim mu, abin da mu ke ji cikin rammu, tunane-tunanemmu,

ayyukammu, duka za su zama cikin muwafaka da nufin Allah yadda aka fade su cikin

dokarsa mai tsarki. “Yayana kankanana, kada ku bar kowa shi bashe ku daga hanya: wanda

ya ke aika adilchi mai- adilchi ne, kamar yadda shi mai-adilchi ne.” I Yohanna 3:7. An

dada ba da azancin adili bisa ga matsayin dokar Allah mai tsarki, kamar yadda aka fadi

cikin dokoki goma da aka bayas a bisa dutsen Sinai.

Irin bangaskiyar nan cikin Kristi wadda za ta dauke wa ‘yan- Adam biyaiya ga Allah,

ba bangaskiya ba ce, rudi ce. “Bisa ga alheri an checheku ta wurin bangaskiya,” “Hakanan,

kwa bangaskiya, im ba ta da ayuka ba, matachiya che chikin kanta.” Afisawa 2:8; Yakub

2:17. Yesu ya fadi a kansa kafin ya zo duniyar nan ya ce “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya

Allahna, Hakika, shari’arka tana chikin zuchiyata.” Zabura 40:8. Kuma ba a dade kafin ya

koma cikin sama ba ya sake cewa “na kiyaye dokokin Ubana, ina zamne kwa chikin

kamnatasa.’’ Yohanna 15:10, Littafi Mai-tsarki ya ce, “Ta wurin wannan mun sani mun

san shi, idan muna kiyaye dokokinsa . . . Wanda ya che yana zaume chikinsa ya kamata shi

da kansa ya yi tafiya kamar yadda shi ya yi tafiya.” 1 Yohanna 2:3-6. “Gama Kristi kuma

ya sha azaba dominku, yana bar maku gurbi, ku bi sawunsa.” 1 Bitrus 2:21.

Sharadin rai na har abada a yanzu daidai ya ke kamar yadda ya ke tun tuni — kamar

yadda ya ke a sama kafin faduwar iya- yemmu na fari — watau cikakken biyaiyya ga dokar

Allah, cikakken adilci. Idan aka ba da rai na har abada a kan sharadin da bai kai wannan

ba, farin cikin dukan halitta zai shiga babban hadari. Hanya za ta budu domin zunubi, da

dukan abokan tafiyarsa, su ne bakin ciki da wahala, za su kuwa dauwama har abada.

30

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Ya yiwu ga Adamu, kafin faduwa tasa, ya yi halin adilci ta wurin yin biyayya da dokar

Allah. Amma ya kasa yin haka, kuma domin zunubinsa, tabi’ummu sun fadi, ba kuwa za

mu iya maida kammu masu aikata adilci ba. Tun da shi ke muna da zunubi, ba mu da tsarki,

ba mu iya yin biyaiya da doka mai tsarki daidai. Ba mu da adilci na kammu wanda za mu

bayar musayar abin da dokar Allah ke nema a garemu. Amma Kristi ya nuna mamu tafarkin

tserewa. Ya yi zaman rashin zunubi. Ya mutu domin mu, yanzu kuma ya lamunta ya dauki

zunubammu ya kuma bamu adilcinsa. Idan kuka ba da kanku gareshi, kuka karbe shi shi

ne Mai-cetonku, a sa’annan, komai zunubin zamanku na da, sabili da shi za a lasafta ku

adilai. Halin Kristi ya tsaya maimakon halinku, kun zama abin karba gaban Allah kamar

ba ku yi zunubi ba.

Fiye da haka, Kristi yana sake zuciya. Yana zaune cikin ku ta wurin bangaskiya. Sai

ku rike wannan mahadi tsakaninku da Kristi ta wurin bangaskiya da ba da nufinku dungum

gareshi; muddan kuna yin haka kuwa, zai yi aiki a cikin ku ya nufe ku ku aikata bisa ga jin

dad’ insa. Domin haka za ku iya fadi ku ce. “Yanzu kuma ba ni ba ne ina rayuwa, amma

Kristi ke rayuwa daga chikina: wannan rai kwa da ni ke rayuwa chikin jiki yanzu ina

rayuwa chikin bangaskiya, bangaskiya wadda ta ke chikin Dan Allah, wanda ya kamnache

ni, ya bada kansa kuma domina.” Galatiyawa 2:20. Haka Yesu ya ce da almajiransa, “Gama

ba ku ne kuna fadi ba, amma Ruhun Ubanku ne mai fadi a chikinku.” Matta 10:20. Sa’nnan

tare da Kristi yana aiki a cikin ku, za ku baiyana daidai irin halin, kuna kuma aikata ayyuka

daidai irin su ayyukan adilci da biyaiya.

Domin haka ba mu da wani abu a cikim mu da za mu yi ruba da shi. Ba mu da hanyar

daukaka kammu. Hanyar begemmu guda cikin adilcin Kristi muka samu, da kuma cikin

abin da Ruhunsa ya aikata a cikim mu ko ta wurimmu.

Idan muna maganar bangaskiya, akwai bambanci da ya kamata mu lura da shi. Akwai

wani irin abin da akan gaskanta wanda ya bambanta da bangaskiya. Kasancewar Allah da

ikonsa, kasancewar Magana tasa (Kalma tasa), tabbatattun abubuwa ne da ko Shaitan da

rundunarsa ba su musantawa a zuci. Littafi Mai-tsarki ya ce “Aljanu kuma suna

gaskantawa, suna kwa rawan jiki.” Yakub 2:19, amma wannan ba bangaskiya ba ne. Inda

ba gaskantawa cikin Maganar Allah ne kadai ba, amma da ba da zuciya gareshi, inda aka

ba da zuciya gareshi, aka kallafa kauna gareshi, to akwai bangaskiya — bangaskiya wadda

ta ke aiki ta wurin kauna, ta tsarkake ruhu. Ta wurin wannan bangaskiya ana sabonta zuciya

cikin surar Allah. Zuciyar kuwa da ta ke matsayinta na rashin sabontuwa a da, ba ta

karkarshin dokar Allah, ba shi yiwuwa kuwa ta zauna karkashin dokar Allah cikin wannan

matsayi; yanzu sai ta yi farin ciki cikin dokokinsa masu tsarki; ta kuwa furta tare da maizabura

ta ce “Ina kamnar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.” Zabura

119:97. Kuma an cika adilcin shari’a a cikim mu “Babu kayaswa fa yanzu ga wadanda ke

chikin Kristi Yesu. ’ ‘ Rom 8:1.

31

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Akwai wadansu da suka san kaunar nan mai yin gafara na Kristi, wadanda hakika suna

da marmarin su zama ‘ya’yan Allah, amma duk da haka sun gane cewa halayansu ba

cikakku ba ne, zamansu yana da aibu, a shirye kuwa su ke yi shakkan ko Ruhu Mai-tsarki

ya sabonta zukatansu. Ga irin wacfannan bari in ce, Kada ku ja da baya cikin fid da zuciya.

Tilas ne safai mu sunkuya mu yi kuka a kafafun Yesu sabo da tauyewarmu da kuskuremmu,

amma kada mu karaya. Ko makiyi ya fi karfin mu, ba a yashe mu ba; Allah bai rabu da mu

ko ya ki mu ba. A, a; ba a yashe mu ba; Allah yana lura da mu. A, a, Kristi yana hannun

dama na Allah, yana roko sabili da mu. In ji Yohanna kaunataccen ya ce, “Wadannan abu

ni ke rubuta maku domin kada ku yi zunubi. Idan kowa ya yi zunubi, muna da Mai-taimako

wurin Uba, Yesu Kristi mai-adilchi.” 1 Yohanna 2:1. Kuma kada ku manta da jawabin

Kristi da ya ce, “Gama Uba da kansa yana kamnarku.” Yohanna 16:27. Yana marmarin ya

koma da ku ga kansa, ya ga tsarkinsa yana haskakawa kamar madubi a cikin ku. Idan kuwa

kuna ba da kanku gareshi, Shi wadda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da yin

haka zuwa ranar Yesu Kristi: Ku yi addu’a da kwazo; bangaskiya ta dada yawa.

Gwargwadon rashin amincewa da ikon kammu, bari mu amince da ikon Mai-pansar mu,

za mu kuwa yabe shi, wanda shi ke Shi ne lafiyar fuskokinmu.

Gwargwadon matsowar ku ga Yesu, gwargwadon ganin laifofinku, domin kuwa

ganinku zaizama sosai, rashin cikarku zai fito daban cikin gwaji da cikakkiyar tabi’arsa.

Wannan shi ne shaida cewa rudin Shaitan sun rasa ikonsu, kuma ikon Ruhun Allah mai

rayaswa yana farkad da ku.

Babu wata zuzzurfar kauna domin Yesu da za ta zauna cikin zuciya wadda ba ta lura

da zunubin kanta ba. Ruhun da aka sabonta ta wurin alherin Kristi zai so halinsa basamaniya;

amma idan ba mu ga tauyewar halayem mu ba, wannan shaida ne wadda babu

tantama cewa ba mu ga kayu da jimali na Kristi ba.

Gwargwadon rashin ganin wani abin girmamawa cikin kammu, gwargwadon abu mai

yawa da za mu gani cikin tsarki da jimali na Mai-cetommu, Ganin zunubammu zai kora

mu zuwa gareshi wanda zai iya gafara, kuma a lokacin da ruhu, cikin gane rashin karfinsa,

ya mika hanu zuwa ga Kristi, Shi zai baiyana kansa cikin iko. Gwargwa¬don yadda

hankalimmu mai bukata ya ke kora mu zuwa garesi da zuwa wurin Maganar Allah,

gwargwadon ganin daukaka da za mu yi wa halinsa, gwargwadon dada haskaka sura tasa

kamar cikin madubi.

32

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 8 – Yin Girma Cikin Kristi

Sake zuciya wanda ta wurinsa mu ke zama ‘ya’yan Allah ana kiransa haifuwa a cikin

Littafi Mai-tsarki. Kuma, ana misalta shi da sabon siro na iri mai kyau wanda manoma

suka shuka. Bisa ga wannan misali haka sabobin masu juyawa ga Kristi su ke, kamar

“jarirai sabobin haifuwa,” “mu yi girma hikin abu duka zuwa chikinsa.” 1 Bitrus 2:2;

Afisawa 4:15 sai sun kai munzulin maza da mata cikin Kristi Yesu. Ko kuma kamar iri mai

kyau da aka shukka cikin gona, za su yi girma su ba da ‘ya’ya. Ishaya ya ce za a ‘ ’ che da

su itatuwa na adilchi, dashe na Ubangiji, domin shi daukaka.” Ishaya 61:3. Domin haka

ana cfauko misalai dga abubuwa na halitta, domin su taimake su gane asirtattun gaskiya na

zaman ruhaniya.

Komai hikima da gwaninta na dan-Adam ba zai iya ba da rai ga ko wace irin halitta

ba komai kankantar ta. Ta wurin rai da Allah ne da kansa ya hura, itatuwa da dabobi su ke

iya rayuwa. Haka kuma sai ta wurin ran da ya fito daga Allah ne kadai a ke haifan rai na

ruhaniya cikin zuciyar ‘yan-Adam. “Im ba a haifi mutum daga bisa ba.’’ Yohanna 3:3. ba

zai iya zama mai taraiya cikin ran da Kristi ya zo bayarwa ba.

Kamar yadda ya ke game da rai haka ya ke game da yin girma. Allah ne ya ke kawo

curin fure har ya bude ya zama fure sosai, furen kuma ya yi ‘ya’ya. Ta wurin ikonsa ne iri

ya ke girma, “Soshiya tukuna, kana zangarniya, bayan wannan zangarniya da kwaya

nunnana a chiki.” Markus 4:28. Annabi Hosea kuma ya fadi a kan Isra’ila cewa “Zasu

murmure kamar hatsi, su yi fure kamar kuringar anab.” Hosea 14:7. Yesu kuma ya ce mana

“Ku lura da fure fa, girman da su ke yi.” Luka 12 :27. Itatuwa da furarruka suna girma ba

da wani kokari ko iko nasu na kansu ba, amma ta wurin karban abin da Allah ya tanada

domin ya yi hidimar rayukansu. Jariri ba zai iya kara girman jikinsa ta wurin ikon kansa

ba. Haka kuma ba ku iya sa wa kanku girma na ruhaniya ta wurin kokarin kanku. Ko itace,

ko jariri, yana girma ta wurin karba daga abin da ke kewaye da shi wanda ya ke yi masa

hidimar ransa — iska, hasken rana, da abinci. Abin da wadannan kyautai su ke yi ga dabba

da itace, shi ne Kristi ya ke yi ga wadanda suka amince da shi. Shi ne “Amma Ubangiji za

ya zama madawamin haskenki.” “Gama Ubangiji Allah rana ne da garkuwa kuma.” Ishaya

60:19; Zabura 84:11. “Zan zama kamar raba ga Israila.” “Za ya sabka kamar ruwan sama

bisa sosayayyar chiyawa.” Hosea 14:5; Zaruba 72:6. Shi ne rayayyen ruwa, “Gama gurasar

Allah mai sabkowa daga chikin sama che mai-bada rai kuma ga duniya.” Yohanna 6:33.

Cikin kyauta mafi gaban kwatanci na Dansa, Allah ya kewaye duniya duka da iskar

alheri, tamkar iskar da muka sani mai kewaye duniya. Duk wadanda suka zabi su shaki

wannan iska mai ba da rai za su rayu, sua yi girma zuwa matsayin maza da mata cikin

Kristi Yesu.

33

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Kamar yadda fure ya ke juyawa ga rana, domin hasken rana ya yi taimako wajen dada

ba shi kyau da cikakken fasali, haka kuma sai mu juya ga Ranar Adilci, domin hasken sama

ya haskaka bisam mu, domin halimmu ya yi girma cikin kammannin Kristi.

Daidai abin da Yesu ya koyas ke nan sa’anda ya ce “Ku zamna chikina, ni ma a

chikinku. Kamar yadda reshe ba ya iya bada yaya don kansa ba, sai dai yana zamne chikin

kuringar anab; hakanan kwa ku ba ku iya ba, sai dai kuna zamne chikina . . . gama im ba

tare da ni ba, ba ku iya yin komi ba. Yohanna 15:4, 5. Kuna dogara ga Kristi domin ku yi

zama mai tsarki daidai kamar yadda reshe ya ke dogara ga tushensa domin yin girma da ba

da ‘ya’ya. Im ba tare da Shi ba ba ku da rai. Ba ku da iko ku yi tsayaiya da jaraba, ko ku yi

girma cikin alheri da tsarki. Idan kuka zauna cikinsa za ku yi yabanya. Idan kuna samun

rai daga gareshi ba za ku yi yaushi ba, ko ku rasa ba da ‘ya’ya. Za ku zauna kamar itacen

da aka dasa a bakin kogunan ruwa.

Dayawa suna tsammani dole su yi “kadan daga cikin aikin su kadai. Sun amince da

Kristi domin gafarar zunubi, amma yanzu suna nema su yi zaman kirki ta wurin kokarin

kansu. Amma irin wannan kokari dole ne ya ka sa. Yesu ya ce, “Im ba tare da ni ba ba za

ku iya yin komai ba.” Yin girmammu cikin alheri, farin cikimmu da amfanimmu — duk

ya dogara ga hacfuwar mu da Kristi. Ta wurin shawara da shi ne ko wace rana, ko wace

sa’a — ta wurin zama cikinsa — za mu yi giima cikin alheri. Shi ba farkon bangaskiyamu

ne kadai ba, amma karshen ta ne. Kristi ne farko, da karshe, da ko wane lokaci. Sai ya

kasance tare da mu, ba a farko ko a karshen fagemmu kadai ba, amma a ko wane taki bisa

hanyar. Dauda ya ce, “Na sa Ubangiji a gabana tutur: Da shike yana ga hannun damana ba

zan jijigu ba.” Zabura 16:8.

Kana tambaya, “Yaya zan zauna cikin Kristi?” — Kamar yadda ka karbe shi da farko.

“Tunda shike kuka karbi Kristi Yesu Ubangiji, sai ku yi tafiya a chikinsa hakanan.” Amma

adilina da bangaskiya za shi rayu: Idan kwa ya noke, raina ba shi jin dadinsa ba.

Kolossiyawa 2:6. Ibraniyawa 10:38. Kun ba da kanku ga Allah, ku zama nasa dungum, ku

bauta masa, ku yi masa biyaiya, kum kuma dauki Kristi shi ne Mai-ceton ku. Ku da kanku

ba ku iya biyan bashin zunubanku ko ku sake zuciyarku, amma tun da shi ke kun ba da

kanku ga Allah, kun gaskanta ya yi dukan wannan dominku sabo da Kristi. Ta wurin

bangaskiya kuka zama na Kristi, ta wurin bangaskiya kuma za ku yi girma a cikinsa — ta

wurin bayarwa da karba. Sai ku ba da duka — zuciyarku, hankalinku, bautarku — ku ba

da kanku gareshi domin ku yi biyayya da abin da ya ke bukata; sai kuma ku karbi duka —

Kristi; cikakken dukan albarka, zai zauna cikin zuciyarku, ya zama karfinku, da adilcinku,

da matai- makinku, har abada — domin ya ba ku ikon yin biyaiya.

Ku tsarkake kanku ga Allah da safe; ku mai da wannan aikinku na farko. Bari

addu’arku ta zama, “Ka dauke ni dungum in zama naka, ya Allah. Na sa dukan shiryeshiryenka

a kafafuna. Ka yi amfani da ni yau cikin bauta maka. Ka zauna a cikina, ka sa

kuma dukan ayyukana in aikata su cikinka.” Wannan abu ne da za a yi kullun. Ku ba da

34

Matakai Zuwa Wurin Kristi

duk shirye-shiryenku gareshi, domin a gudana su ko a ki gudana su yadda nufinsa ya ga

dama. Ta wurin yin haka ko wace rana za ku ba da ranku cikin hannun Allah, ta haka kuma

za a fi mulmila rayukanku cikin gurbin Kristi.

Rayuwa cikin Kristi zama ne na hutu. Ba lalai mu ji wani suka cikin rammu wanda

zai sa mu farin ciki farat daya ba, amma dole akwai zaunannen amincewa mai salama.

Begenku ba cikin kanku ya ke ba; cikin Kristi ya ke. An hada rashin karfinku da karfinsa,

jahilcinku kuma an hacfa shi da hikima nasa; kumaman- cinku kuma an hada shi da ikonsa

mai jimrewa. Domin haka ba kanku za ku duba ba, kada ku bar hankali ya dogara ga kanku,

amma ku dubi Kristi. Bari hankali ya zauna bisa kan kauna tasa, da bisa kan jimali da cika

na halinsa, Kristi cikin musun kansa, Kristi cikin kaskancinsa, Kristi cikin sahihancinsa da

tsarkinsa, Kristi cikin kaunarsa mafi gaban kwatanci — wadannan su ne abin da ruhu zai

yi tunani a kansu. Ta wurin kaunarsa ne, da kwaikwayonsa, da dogara gareshi, za a same

ku cikin kamaninsa.

Yesu ya ce, “Ku zauna cilcina.” Wadannan kalmoni suna sifanta hutu, da kafuwa, da

amincewa. Kuma, ya sake kiram mu ya ce, “Ku zo gareni, . . . ni kwa im ba ku hutawa.”

Matta 11:28. Kal- momin mai-zabura ma tunanin da suka furta ke nan, “Ku huta kurum

chikin Ubangiji, ka yi hankuri kana sauraronsa.’’ “Chikin komawa da hutu za ku tsira; da

natsuwa da dogara karfinku za ya tabbata.” Zabura 37:7; Ishaya 30:15. Ba a samun wannan

hutu cikin rashin aiki, gama a cikin kiran da Mai-ceto ya yi an hada alkawarin hutu da aiki.

“Ku dauka ma kanku karkiyata, . . . za ku sami hutawa ga rayukanku.” Matta 11:29. Zuciyar

da ta ke hutawa bisa Kristi za ta yi kwazo da samri cikin yin aiki dominsa.

Sa’anda hankali ya kallafa ga son kai, ya juya daga Kristi, Shi Masomin karfi da rai.

Domin haka kokarin Shaitan ne ko wane lokaci ya kawas da hankali daga Mai-ceto, ta

hakanan ya hana haduwa ko yin shawara da Kristi. Nishadan duniya, al’amuran duniya,

alhinai da bakin ciki, laifofin wacfansu, ko kuwa laifofinku, da kasawarku; zuwa ga duka

ko guda daya daga cikin wacfannan zai nema ya maida hankalinku. Dayawa wadanda su

ke da kuduri na kirki, wacfanda su ke da marmarin su yi zama domin Allah, sai ka ga safai

Shaitan ya bishe su kan tunawa da laifofinsu da rashin karfinsu; ta wajen raba su da Kristi

hakanan kuwa ya ke bege ya ci nasara. Kada ku yarda dabarunsa su bad da ku. Kada mu

maida kanmu ne tsakiya, ko mu yi ta alhini, ko mu ji tsoron cewa ko za a cece mu. Duk

wannan sai ya juyas da ruhu daga Masomin karfinmmu. Ku ba da ajiyar Ruhunku ga Allah,

ku kuwa amince da shi. Ku yi zance da tunani a kan Yesu. Bari tunawa da kai ya bata

cikinsa. Ku jingine dukan shakka, ku sallami tsoronku. Ku ce, tare da Bulus manzo, “Yanzu

kuma ba ni ba ne ina rayuwa, amma Kristi ke rayuwa daga chikina: wannan rai kwa da ni

ke rayuwa chikin jiki yanzu ina rayuwa chikin bangaskiya, bangaskiya wadda ta ke chikin

Dan Allah, wanda ya kamnache ni, ya bada kansa kuma domina.” Galatiyawa 2:20. Ku

huta cikin Allah. Yana ;ya kiyaye abin nan da kuka ba Shi ajiya. Idan kuka bar Shi wanda

35

Matakai Zuwa Wurin Kristi

ya kaunace ku, kuka bar kanku cikin hannunsa, zai, kiyaye ku fiye da mai nasara ta wurin

Shi wanda ya baunace ku din.

Sa’anda Kristi ya dauka wa kansa tabi’ar dan-Adam, ya daura mutunci a jikinsa da

igiyar bauna wadda ba wani ikon da zai iya tsunke ta sai ko da yardan dan-Adam kansa.

Tutur Shaitan zai jarabe mu da nuna mana abubuwa masu kyau domin mu tsinke igiyar nan

da ke tsakanimmu — watau don kammu mu zabi rabuwa da Kristi. A nan ne fa ya kamata

mu lura, mu yi kokari, mu yi addu’a domin kada wani abu ya rude mu har da zai sa mu

zabi wani Ubangiji, domin kuwa a ko wane lokaci a sake mu ke mu yi haka im mun ga

dama. Amma bari mu zura idanummu ga Kristi, Shi kuwa zai kiyaye mu. Duban Yesu zai

hana wani abu ya same mu. Babu abin da zai iya fizge mu daga hannunsa. A cikin dubansa

ko wane lokaci sai “Muna sakuwa zuwa chikin wannan sura daga daraja zuwa daraja,

kamar dai daga wurin Ruhun, watau Ubangiji.&rdquo II Korinthiyawa 3:18.

Ta wurin haka ne almajirai na farko suka samu kamantuwarsu da kaunataccen Maiceto.

Sa’anda wadannan almajirai suka ji kalmo- min Yesu, sun ji a ransu suna da

bukatarsa. Suka neme shi ko v/ace lokaci, a cikin gida, a wajen cin abinci, a cikin lolloki,

ko cikin saura. Suna tare da shi kamar almajirai tare da malami kullun suna karban

koyaswar gaskiya mai tsarki daga lebunansa. Suna dubansa kamar yadda barori su ke

sauraren uban-gidansu, su koyi ayukan da su ke wajibinsu ne. Su wacfannan almajirai

mutane ne “Iliya mutum ne da tabi’a kamar tamu, ya kwa yi addu’a da nachiya, kada a yi

ruwa: kuma shekara uku da wata shidda ba a yi ruwa a kasa ba.” Yakub 5:17. Yaki daya

su ke da shi daidai da mu gaba da zunubi. Alheri daya su ke bukata domin su yi zaman

tsarki.

Ko Yohanna, kaunataccen almajiri, wanda ya fi sauran nuna kamanin Mai-ceto, ba

don tabi’ar kansa ya samu kyaun wannan halin tawali’u ba. A hankali zuciya tasa ta gusa

zuwa ga Kristi har ya manta kuncin rai. Amma da ya gane halin Ba-samaniyin nan, sai ya

ga kasawa tasa, wannan gane nufin hanli nasa kuwa ya sa ya saduda. Ya lura da wadansu

abubuwa da suka kayatad da shi game da halin Dan Allah cikin ma’amilla na zamansa na

duniya. Ya ga a cikin halin Dan Allah akwai karfi amma tare da hakuri; akwai iko amma

hade da taushin zuciya, akwai daukaka amma hade da tawali’u a hankali zuciya tasa ta gusa

zuwa ga Kristi har ya manta da kansa cikin kauna zuwa ga Ubangijinsa. Halin nan nasa na

alfarma da girman kai da kunci ya saduda ga ikon Kristi mai ginawa. Ikon Ruhu Mai-tsarki

mai sake haifuwa ya sabonta zuciya tasa. Ikon kauna na Kristi ya sake halinsa. Wannan shi

ne tabbataccen abin da zai abku cikin haduwa da Yesu. Sa’anda Kristi ya ke zaune cikin

zuciya, duk tabi’a sai ta sake. Ruhun Kristi da kauna tasa su kan tausasa zuciya, su mallaki

ruhu, su cfagad da tunani da nufe-nufe zuwa ga Allah na sama.

Sa’anda Kristi ya hau bisa cikin sama, sanin yana nan bai rabu da masu binsa ba.

Kasancewa ne da ke cikin zuci, cike da haske da kauna. Yesu, Mai-ceto, wanda ya yi yawo,

ya yi tadi tare da su, wanda ya yi wa zukatansu zantattuka na bege da ta’aziya, tun lokacin

36

Matakai Zuwa Wurin Kristi

da sakon salama ya izo bisa lebunansa, ga shi an dauke shidaga garesu zuwa cikin sama,

amon murya tasa kuma ya komo musu sa’ anda girgije na mala’iku suka karbe shi cewa ”

Gashi kwa ina tare da ku kullayaumi har matakar zamani.” Matta 28:20. Ya hau bisa cikin

sama da sifar ‘yan-Adam. Sun sani yana gaban kursuyin Allah, har yanzu kuwa abokinsu

ne da Mai-cetonsu, nufinsa zuwa garesu bai sake ba, ana kuwa lisafta shi da ‘yan-Adam

masu shan wahala har wa yau. Yana mikawa a gaban Allah alhakin jininsa mai daraja, yana

nuna raunin hannayensa da kafafunsa, abin tunawa da tamanin da ya biya domin abin da

ya pansa. Sun sani ya hau bisa cikin sama domin ya shirya musu wurare, kuma sun sani zai

sake dawowa ya dauke su zuwa ga kansa.

Sa’anda suka taru wuri daya, bayan ya rigaya ya hau sama, sun yi himma su mika

roke-rokensu ga Uba cikin sunan Yesu. Cikin ladabi mai yawa suka sunkuya cikin addu’a,

suna maimaita alkawarin da ya ce “Idan kun roki komi ga Uba, zaya ba ku a chikin sunana.

Ku yi roko, za ku karba, domin farinchikinku ya chika.” Yohanna 16:23, 24. Suka dada

mika hannun bangaskiya gaba gaba zuwa sama da wannan roko cewa “Kristi Yesu ne ya

mutu, i kwa, har ya tashi daga matattu, yana hannun damana Allah, yana roko sabili da

mu.” Romawa 8:34. Pentecost kuma ta kawo musu jin kasancewar Mai-ta’aziya, wanda

Kristi ya ambata ‘ ’Gama yana zamne tare da ku zashi kwa zamna a chikinku.” “Yana da

anfani a gareku in tafi: gama idan ban tafi ba, mai-taimakon ba zashi zo wurinku ba; amma

idan na tafi, zan aiko shi a gareku.” Yohanna 14:17; 16:7. Daga nan gaba Kristi zai zama

tutur cikin zukatan ‘ya’yansa ta wurin Ruhun. Hacfuwansa da su ya . . . fi kusa da lokacin

da shi kansa ya ke tare da su. Haske da kauna da ikon Kristi da ke zaune cikin zuciya yana

haskakawa har waje, har sa’anda mutane suka gansu “Suka yi mamaki, suka dauki zato a

kansu da suna tare da Yesu.” Ayukan Manzani 4:13-

Duk abin da Kristi ya ke ga almajiransa na farko, haka nufinsa ya ke zuwa ga

‘ya’yansa a yau, gama a cikin addu’a tasa ta karshe, tare da ‘yan almajiransa kima a kewaye

da shi ya ce ‘Kuma ba domin wadannan kadai ni ke yin addu’a ba, amma domin wadanchan

kuma da ke bada gaskiya gareni ta wurin maganarsu.” Yohanna 17:20.

Yesu ya yi addu’a sabili da mu, ya kuma roka cewa mu zama daya da shi, kamar yadda

cfaya su ke da Shi da Uban. Wanne irin haduwa ne wannan? Maiceto ya yi jawabi a kan

kansa ya ce “Dan ba shi iya yin komi don kansa ba,” Uban da ya ke zamne a chikina yana

yin ayukansa.” Yohanna 5:19; 40:10. Domin haka idan Kristi yana zaune cikin zukatammu

zai yi aiki a cikin mu — “Amma abu daya ni ke yi, ina manta da abubuwan da ke baya, ina

kutsawa zuwa ga wadanda ke gaba.” Filibiyawa 3:13. Za mu yi aiki kamar yadda ya yi, za

mu baiyana hali kamar nasa. Ta hakanan wajen zama a cikinsa da kauna tasa za “Mu yi

girma chikin abu duka zuwa chikinsa, wanda shi ne kai, watau Kristi.” Afisawa 4:15.

37

Matakai Zuwa Wurin Kristi

38

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 9 – Aiki da Zaman Rai

Allah shi ne tushen rai da haske da farin ciki ga dukan halitta. Kamar yadda haske ke

fitowa daga rana, kamar yadda rafukan ruwa su kan fashe kasa daga mabulbula mai rai,

haka albarka ke gudanowa daga wurin Allah zuwa ga dukan halittansa. A kuwa duk inda

ran Allah ya ke cikin zukatan ‘yan-Adam, zai gudana waje zuwa ga wadansu cikin kauna

da albarka.

Farin cikin Mai-cetom mu a cikin dagarwa da pansar ‘yan-Adam fadaddu ya ke. Sabili

da wannan bai mai da ransa abin kauna a gareshi ba, amma ya daure da radadin giciye, ya

raina kuma. Haka mala’iku su ke hidima domin su samowa wacfansu farin zuciya. Wannan

shi ne abin faranta musu zuciya. Abin da wacfansu zukata masu son kai za su ga kamar

hidima ne na kaskanci, yin hidima ga wulakantattu, wadanda ko ta wace hanya, ko ta hali,

ko ta matsayi, daraja tasu ba ta isa ba, wannan shi ne aikin mala’iku marassa zunubi. Halin

Kristi na kaunar ba da kai ya zama hadaya, shi ne ya mamaye samaniya duka, wannan

kuwa shi ne tushen albarkar sama. Wannan shi ne halin da masu bin Kristi ya kamata su

samu, watau aikin da za su yi.

Sa’anda kaunar Kristi ta kafu cikin zuciya, ba za ta boyu ba kamar abu mai kamshi.

kowa da muka zo cikin ma’amala da shi zai ji wannan iko da ke tare da mu. Halin Kristi

cikin zuciya kamar mabulbulan ruwa ya ke cikin hamada, yana bulbulowa domin ya

wartsakad da komai, kuma yana ba wacfanda su ke bakin hallaka himma su sha daga cikin

ruwan rai.

Kauna zuwa ga Yesu za ta baiyana cikin marmarin yin aiki kamar yadda ya yi domin

albarka da daga zaman ‘yan-Adam. Za ta bayas zuwa ga kauna da taushin rai da tausayi

zuwa ga dukan halittan da ke karkashin inuwar Ubammu na sama.

Zaman da Mai-cetommu ya yi a duniyan nan ba zama ne na sauki da yin hidimar kansa

ba, amma da naciya, da himma, da rashin gajiya, ya yi aiki mai tsanani domin ceton ‘yan-

Adam batattu. Tun daga wurin haifuwa tasa a sakarkari zuwa tudun Kalvari ya bi hanyar

kin kai, bai kuwa nemi ya zuke daga ayyuka masu wuya, ko tafiyu masu tsanani, ko ayyuka

masu gajiyaswa ba, ko masu sa a suke Ya ce “Kamar yadda Dan mutum ya zo ba domin a

yi masa bauta ba, amma domin shi bauta ma wadansu, shi bada ransa kuma abin pansar

mutane dayawa.” Matta 20:28. Babban abin da ya kiyaye ke nan cikin zamansa, sauran

abubuwa kuwa ya maishe su baya. Abincinsa ne da abin shansa ya yi nufin Allah ya kuwa

gama aikinsa. Son kai da sa kai a gaba ba su da wuri cikin aikinsa.

Haka ne kuma su wadanda su ka taraiya cikin alherin Kristi za su kasance a shi rye su

yi ko wane irin abu domin su wacfannan da ya mutu domin su su samu ladan daga cikin

kyautan nan na sama. Za su yi iyakacin iyawa tasu su sa duniya ta fi dadin zama garesu

Wannan hali shi ne tabbataccen yabanya na ruhun da ya yi juyawa na gaskiya. Da zuwan

39

Matakai Zuwa Wurin Kristi

dan-Adam wurin Kristi, nan da nan sai a haifi marmari a cikin zuciya tasa na son ya sanas

wa wadansu cewa ya samu aboki mai tamani cikin Yesu. Ba shi yiwuwa a rufe gaskiyar

nan mai cetarwa mai tsarkakewa cikin zuciya kurum. Idan muka saturtar da kammu da

adilcin Kristi, idan kuma muka cika da farin cikin Ruhunsa mai zama a zuci, ba shi yiwuwa

mu rufe bakimmu mu yi shuru. Idan muka dandana muka gani Ubangiji nagari ne, zamu

samu abin da za mu fadi. Kamar Filibus sa’anda ya samu Mai-ceto, za mu kira wadansu su

zo su gan shi. Za mu neni mu nuna musu abubuwa da ke masu jawowa na Kristi da

tabbattattun abubuwan da ido ba ya gani na duniya mai zuwa. Marmari zai tsananta na son

bin gurbin sawayen da Yesu ya taka. Za mu ji tsanantaccen marmari na son wacfanda ke

kewaye da mu su dubi “Dan-Rago na Allah, wanda ya ke dauke da zunubin duniya.”

Kuma, kokarin mu jawo albarka bisa wasu zai komo ya zama albarka a kam mu.

Wannan shi ne nufin Allah da ya ba mu rabo cikin aikata shirin da ya yi domin pansa. Allah

ya ba ‘yan-Adam dama su zama masu taraiya cikin tabi’ar ruhaniya, su kuma sai su hura

wannan albarka zuwa ga sauran ‘yan-uwansu ‘yan-Adam. Wannan shi ne daraja mafi

girma, da farin ciki mafi girma, wanda ya ke yiwuwa ga Allah ya aza bisa kan ‘yan-Adam.

Su wakannan fa da suka zama masu taraiya cikin hidimar kauna ana kawo su su zama

mafiya kusantar Mahallicinsu.

In da ya so, da Allah ya ba da sakon bishara, da sauran dukan hidimar kauna cikin

hannun mala’iku na sama. In da ya so, da ya nemi wata dabara domin ya aikata nufinsa.

Amma sabo da kauna tasa mara iyaka, ya zabi ya maishe mu abokan aiki tare da shi, tare

da Kristi, da kuma tare da mala’iku, domin mu samu rabo cikin albarka, da farin ciki, da

dagarwa mai ruhaniya, wanda su ne ladan wannan hidima na rashin son kai.

An kawo mu cikin tausayi tare da Kristi ta wurin taraiya cikin shan wahala tasa. Ko

wane aiki na ba da kai ya zama baiko domin jin dadin wadansu yana karfafa ruhun yin

kyauta cikin zuciyar mai bayarwa, yana dada hada zumunci ne ama sabili da mu ya zama

matalauci, domin ku zama mawadata ta wurin talaucinsa.” Sai fa mun cika nufin nan na

sama cikin halittammu sa’annan zaman duniya zai zama albarka a gare mu.

Idan za ku tafi ku yi aiki kamar yadda Kristi ya aiyanawa alma¬jiransa, ku ribato

rayuka dominsa, za ku ji bukatar zurfin karuwar sanin abubuwa na ruhaniya, za ku kuma

yunwata da kishirta sabo da adilci. Za ku yi roko tare da Allah, bangaskiyarku kuma za ta

karfafa, rayukanku kuma za su cika cikinsu da ruwan rijiyar ceto Cin karo da tsayaiya da

gwaje-gwaje za su kora ku zuwa ga Littafi Mai-tsarki da addu’a. Za ku yi girma cikin alheri

da sanin Kristi, za ku kuwa karu da wayewar kai.

Tabi’ar yin aiki sabili da wadansu ba game da son kai ba yana ba da zurfi, da kafuwa,

da kyakkyawan hali irin na Kristi, yana kuma kawo salama da farin ciki ga mai irin wannan

halin. Buri su kan cfagu. Babu wuri domin ragwanci ko son kai. Su wadannan da su ke

aikata alherin Kristi za su yi girma su samu yin aiki domin Allah. Za su samu hankula masu

40

Matakai Zuwa Wurin Kristi

ganewa na ruhaniya, da bangaskiya tsayayya, mai yin girma da karuwar iko wajen yin

addu’a. Ruhun Allah mai motsi bisa ruhohinsu ya kan kirawo jituwar ruhu cikin amsawar

tabuwar ruhaniya. Su wacfannan fa da suka maida hankali dungum cikin kokari mara son

kai domin jin dadin wacfansu, babu shakka suna hidimar ceton kansu.

Hanya guda cfaye ce kacfai ta inda za mu bi mu yi girma cikin alheri, ita ce kulawa

cikin aikata ainihim aikin da Kristi ya umurce mu — mu yi iyakacin kokarim mu wajen

taimako da albarkata wacfanda su ke bukatar ta imakon da za mu iya ba su. Motsa jiki

yakan kawo karfi; aiki shi ne matsayin zaman duniya Su wacfannan masu kokari su yi

zaman alheri kawai a ciki bin Kristi, ba su kuwa aikata komai domin Kristi, aniya su ke yi

su yi zaman su na duniya don su ci kawai ba tare da yin aiki ba. Kamar yadda ya ke cikin

halitta haka kuma ya ke cikin ruhaniya zaya jawo masu lalacewa da rubewa. Shi mutumin

da ya ki ya yi amfani da gababuwansa, ba da dacfewa ba zai rasa karfin amfani da su.

Hakanan shi mai bin Kristin wanda ba zai yi amfani da ikon da Allah ya ba shi ba, ba rashin

girma cikin Kristi ne kacfai zai gaza yi ba, amma karfin da ya rigaya ya samu a da zai bace

masa.

Ekkliziyar Kristi itace wakilin Allah domin ceton ‘yan’Adam. Aikinta shi ne ta watsa

Bishara zuwa ga duniya. Wannan aiki ya rigaya ya rataya a wuyan dukan masu bin Kristi.

Ko wane, gwar¬gwadon baiwar da Allah ya ba shi, sai ya cika umurnin Mai-ceto. kaunar

Kristi, wadda aka baiyana mana, ta sa mun zama mabarta ga dukan wad’anda ba su san shi

ba. Allah ya ba mu haske ba domin kammu ne kacfai ba, amma domin mu haskaka masu.

Idan masu bin Kristi suka farka da aikata wajibinsu, za a samu dubbai yau inda da

cfaya ne kawai, don shelar Bishara a kasashen arna. Kuma dukan wadanda ba za su iya yin

wannan aiki don kansu ba, suna iya ba da taimako ta wurin ba da kucfi, da tausayinsu, da

addu’arsu. Kuma da an fi samun himantaccen aiki domin rayuka cikin kasashen masu bin

Kristi.

Ba lalai sai mun tafi kasashen arna ba, ba ma lalai ne mu bar gidajemmu ba, idan

wannan wajib ne a garemu, mu yi aikin Kristi. Za mu iya yi wannan aiki a cikin gidajemmu,

a cikin Ekkliziya, a tsakanin abokammu da abokan cinikinmu.

Yawancin zaman duniya na Mai-ceto a dakin sassaka ya yi su a Nazareth wajen zama

da aiki da hakuri. Mala’iku masu hidima tutur suna tare da Ubangijin rai sa’anda ya ke

yawonsa tsakanin talakawa da ma-aikata, ba tare da an san shi ko ana darajanta shi ba.

Yana cika sakonsa lokacin da ya ke aiki kan sana’a tasa daidai da lokacin da ya ke warkas

da marasa lafiya ko a lokacin da ya ke rafiya bias rakuman ruwa masu hauka a bahar na

Galili. Domin haka komai kaskancin matsayimmu cikin zaman duniya, za mu iya tafiya ko

aiki tare da Yesu.

Manzo ya ce “Bari kowane mutum, inda aka kira shi, shi, zamna nan tare da Allah.”

1 Korinthiyawa 7:3, 4. Mai ciniki ko dan kasuwa zai tafiyad da aikinsa cikin hanyar da za

41

Matakai Zuwa Wurin Kristi

ta daukaka Uban- gijinsa sabo da gaskiya tasa. Idan shi mai bin Kristi ne da gaske, zai

dauki addininsa cikin dukan abin da ya ke yi, ya baiyana wa ‘yan- Adam Ruhun Kristi.

Makaniki ya iya zama wakili mai kwazo, mai aminci, ga Shi wanda ya yi aiki na kaskanci

a tsakankanin duwatsun Galili. Ko wane mutum wanda ya ambaci sunan Kristi sai ya yi

aiki yadda idan wadansu, suka ga ayukansa masu kyau, za ya bishe su su daukaka

Mahallicinsu da Maipansarsu.

Dayawa sun yi wa kansu hujjar kin ba da sadakokinsu sabo da aikin Kristi wai domin

wadansu sun fi su wadata. Akwai tunanin cewa wai sai masu wata baiwa muhimmin ake

bukata su ba da dukan kokarinsu zuwa ga aikin Allah. Wadansu kuma suna tsammani cewa

baiwa ana ba da ita ne ga zababu da aka fi so kawai, sauran jamma’a kuwa ba a bukatar su

samu rabo wajen yin aiki ko wajen samun ladan. Amma ba haka ya ke ba cikin misalin da

aka bayar. Sa’anda Mai-gida ya kira barorinsa, ya ba ko wane aikinsa.

Za mu iya aikata ayyuka na kaskanci cikin dacfin rai “Kamar ga Ubangiji.”

Kolosiyawa 3:23. Idan kaunar Allah tana zuci, za ta fita a fili cikin zamammu. Ba ruwanku

da tunawa da yadda duniya ta ke tsammani a kanku. Muddan zamanku na yau da gobe ya

zama shaida cewa bangaskiyarku tsatstsarka ce, kuma sauran jama’a sun tabbata kuna nufin

ku Sami amfanin su, kokarinku ba zai tafi duka a banza ba.

Komai talauci da kaskanci na almajirin Yesu ya iya zama albarka ga wadansu.

Watakila ba za su gane cewa suna yin wani abin kirki ba amma ta wurin kokarin su cikin

rashin sani za su iya ta da rakuman ruwa na albarka wadanda za su kara fadi da zurfi, kuma

ba shi yiwuwa su san irin albarkar da suka jawo sai ranar lada ta karshe. Ba za su sani ko

su ji cewa suna yin wani babban abu ba. Ba a bukata su gajiyad da kansu da tunanin nasara.

Su dai sai su ci gaba ba tare da hayaniya ba, suna aiki da aminci bisa abin da Allah ya aza

musu, zamansu na duniya kuwa ba zai zama a banza ba. Rayukansu za su ci gaba cikin

kamantuwa da Kristi, ta haka za su iya yin manyan ayuka, su kuma cancanci farin zuciya

na rai mai zuwa.

“Yesu, ka zana shi bisa zuciyata

Cewa kai kadai ne abin bukata.

A iya raba ni da dukan abu,Amma,

dadai, dadai, ba daga gareka ba.’

42

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 10- Sanin Allah

Hanyoyi suna da yawa da Allah ya ke nema ya sanar da kansa garemu kuma ya kawo

mu cikin taraiya da shi. Halitta tana zance da hankulammu ba fasawa. Zuciya budaddiya

za ta gane kauna da daukaka na Allah yadda aka baiyana su cikin aikin kannuwansa. Kunne

mai saurare zai ji ya kuma gane zantattukan Allah ta wurin abubuwan halitta. Ciyawa

algashi, itatuwa masu tsawo, furarruka, gizagizai masu wucewa, ruwan sama, rafaffuka

masu gudu, da dau- kakan sammai, suna zance da zukatammu, suna kirammu mu gane shi

wanda ya halitta su duka.

Mai-cetommu ya daure dukan koyaswa tasa game da abubuwan halitta. Itatuwa,

tsuntsaye, furarruka na saura, tuddai, tekuna, da sararin sama mai jimali, tare da sauran

abubuwan da ke kewaye da zama na yau da gobe, duka a hade su ke da zantattukan gaskiya,

domin a rika tunawa da su ko wane lokaci, komai dawainiyar da mu ke ciki na yau da gobe.

Allah yana so ‘ya’yansa su yaba da halittansa, su kuma yi farin ciki cikin sassaukan

jimali da ya kawata mazaunimmu na duniya. Shi masoyin jimali ne amma fiye da dukan

abu mai kyau na waje da ake gani, yana kaunar kyaun hali. Yana so mu shuka tsarki da

rashin girman kai, kamar jimalin da fure ke bayarwa.

Idan da za mu kasa kunne, sai ayukan halittar Allah su koya mana sosai nassi masu

tamani na biyaiya da amincewa. Tun da ga taurari da su ke tafiyarsu cikin filin sama

shekara kan shekara, har zuwa ga abu mafi kankanta, abubuwan halitta suna biyaiya da

nufin Mahallici. Kuma Allah yana kula da ko wane abu yana kuma agazan dukan abin da

ya halitta. Shi wanda ya ke tallafe da duniya masu yawa fiye da a kirga, Shi ya ke kula da

‘yar tsadda mai raira waka tata ba tare da tsoro ba. Sa’anda ‘yan-Adam suka fita zuwa

wurin hidimarsu na ko yaushe, ko sa’anda su ke yin addu’a, sa’anda suka kwanta da dare,

da sa’anda suka tashi daga barchi da safe, sa’anda mawadaci ya ke buki a fadarsa, ko

sa’anda matalauci ya tara ‘ya’yansa su ci dan abin da suka samu, dukansu Uba na sama

yana lura da su da kauna. Ba hawayen da zai zuba ba tare da sanin Allah ba Kuma babu

murmushin da bai gani ba.

In da za mu gaskanta wannan dungum, da dukan rashin kwan- ciyar rai ya kawu.

Zaman mu ba zai zama da yawan rashin cikar muradimmu ba, domin ko wane abu, babba

ko kankani cikin hannun Allah za mu bar su, wanda yawan abin kulawa ko nauyinsu ba su

dame shi ba. A sa’annan za mu yi farin cikin kwanciyar rai wanda ya zama bakon abu ga

mutane dayawa da dadewa.

Kamar yadda hankulanku su ke murna a kan a abubuwan da suka kawata duniya, ku

tuna da duniya mai zuwa wadda ba za ta san tabon zunubi ko mutuwa ba dadai, inda fuskar

halitta ba za ta kara yafa inuwar la’ana ba. Bari hankalinku ya sifanta mazaunin cetattu, ku

tuna kuma zai fi matukar kyalkyalin da hankalinku, zai iya sifantawa. A cikin baiwan Allah

43

Matakai Zuwa Wurin Kristi

masu yawa daban daban, muna ganin kyallin cfaukakar halittarsa dushi dushi ne kawai. An

rubuta cewa, “Abin da ido baya gani ba, kunne baya ji ba, Baya shiga zuchiyar mutum ba,

dukan iyakar abin da Allah ya shirya ma wadanda ke kamnarsa.” 1 Korinthiyawa 2:9.

Mawaka da mai duba fannin ilmi na halitta suna da abu dayawa da za su ce a kan

halitta, amma mai bin Kristi ne ya ke jin dadin jimali na duniya, domin yana gane aikin

hannuwan Ubansa, yana gani da hankalin zuciyarsa kaunar Allah, a jikin fure, ko ganye ko

itace. Ba wanda zai iya gane dalilin tudu ko kwari, kogi ko teku, im ba ya dube su da kamar

furtawar kaunar Allah ne zuwa ga dan- Adam ba.

Allah yana magana da mu ta wurin shiryayyun ayukansa da ikon Ruhu Mai-tsarki bisa

zuciya. A matsayin da mu ke da abin da ke kewaye da mu, cikin sake-saken da ke abkuwa

a kewaye da mu kullun, za mu iya samun koyaswa masu tamani idan muka bar zukatammu

a bude domin su gane su. Mai-Zabura da ya bincika, ayyukan shiri na Allah ya ce, “Duniya

kuma chike ta ke da rahamar Ubangiji.” Zabura 33:5. ‘ ’Wanda ya ke da hikima duka, za

ya lura da wadannan al’amura, su lura kuma da jiyejiyenkai na Ubangiji.” Zabura 107:43.

Allah yana magana da mu cikin Kalma tasa. A nan ne mu ke ganin baiyanuwar halinsa

a fili, da ma’amillansa da ‘yan-Adam da kuma babban aiki na pansa. A nan aka bucfe a

gabam mu tarihin waliyyai, da Annabawa, da sauran tsarkaka na da. Su mutane ne “da

tabi’a kamar lamu.’’ Yakub 5 :17. Mun ga yadda suka yi fama da katse- hanzari ga burinsu

kamar mu da kuma yadda suka fadi cikin jaraba kamar mu, amma duk da haka suka dauki

karfin zuciya suka kuwa ci nasarta tawurin alherin Allah, cikin ganin hakanan kuwa muna

karfafa cikin kokarinmu ga yin adilci. Sa’anda muka karanta labaran abubuwan da suka

abku garesu, da haske da kauna wanda suka zama abin faranta musu zuciya, da kuma aikin

da suka aikata ta wurin alherin da aka ba su, sai ruhun da ya shiga cikinsu ya su yin haka

ya kunna wutar kwaikwayo mai tsarki a cikin zukatammu, da kuma marmarin mu zama

kamar su wajen hali — mu yi tafiya tare da Allah kamar yadda suka yi.

Yesu ya ambaci Tsofon Alkawari — yaya fa gaskiyar wannan ya ke game da Sabon

Alkawarin — cewa “Su ne fa suna shaida ta.’’ (Yohana 5:39), Shi Maiceto, wanda a cikinsa

ne begen mu na rai na har abada ya tabbata. I, dukan Littafi Mai-tsarki yana ambatar Kristi

ne. Tun daga farkon halitta, — domin “Ba a yi komi ba chikin abin da aka yi, sai ta

wurinsa.” (Yohanna 1:3) — zuwa ga alkawari daga karshe wanda ya ce, “Ga shi, ina zuwa

da samri.” (Ruya ta Yohanna 22:12), muna karanta labarin ayukansa muna kasa kunne ga

murya tasa. Idan kuna so ku san Mai-ceto, ku karanta Littaftafai Masu-tsarki.

Cika dukan zuciya da maganar Allah. Su ne ruwa mai rai, mai kashe kishirwa. Su ne

gurasa mai rai daga sama. Yesu ya ce, “Im ba ku chi naman Dan mutum ba, ku sha jininsa

kuma, ba ku da rai a chikinku ba’’ “Zantattuka wadanda na fada maku ruhu ne, da rai

kuma.’’ Yohanna 6:53, 63. Jikunammmu suna ginuwa daga abin da muka ci da abin da

44

Matakai Zuwa Wurin Kristi

muka sha; kamar yadda ya ke a cikin jiki kuwa, haka ya ke ga ruhu. Abin da mu ke tumani

a kansa shi ne ya ke ba ruhum mu karfi.

Zancen pansa abu ne wanda mala’iku su ke son bincikensa; shi ne zai zama fanni na

ilmi da wakar pansassu cikin dukan tsararraki har abada. Ashe ba abu ne wanda ya cancanci

a duba shi a yi tunam cikin hankali a kansa yanzu ba? Jinkai da kauna mara iyaka na Yesu,

baikon da aka yi sabili da mu, suna bukatar a yi tunani mai zurfi a kansu. Sai mu zauna

bisa kan halin kaunatacen Mai-pansarmu da Matsakancimmu. Sai mu yi tunani a kan aikin

Shi wanda ya zo domin ya ceci mutane daga zunubansu. Idan muna tunanin abubuwa na

sama haka, bangaskiyarmu da kaunar mu za ta yi karfi, addu’okinmmu kuma za su fi

karbuwa ga Allah, domin za su dada garwayuwa da bangaskiya da kauna. Addu’oimmu za

su zama masu ma’ana, kuma za a yi su da kwazo. Za a fi dada samun amincewa da Yesu,

kuma kullum zamu dinga zama cikin sanin ikonsa na ceto har matuka, dukan wacfanda

suka zo ga Allah ta wurinsa.

Idan muna tunani a kan cika na Mai-ceto, za mu yi marmarin mu sake cfugum, za mu

yi marmarin a sabonta mu cikin sifar tsarkinsa. Za mu yunwata mu kishirta a ruhu domin

mu zama kamar shi wanda mu ke yi wa sujada. Gwargwadon tunanim mu a kan Kristi,

gwar- gwadon yadda za mu yi wa wadansu zancensa, mu wakilce shi ga duniya.

Ba domin malamai kadai aka rubata Littafi Mai-tsarki ba, an yi shi domin kowa ne.

Manyan abubuwa na gaskiya da ake bukata domin ceto an nuna su a fili kamar hasken rana

a tsaka; ba kuwa wacfanda za su yi kure har su bace daga hanya sai ko wadanda su ke bin

shawarar kansu maimakon su bi baiyanannen nufi na Allah.

Bai kamata mu karbi shaidar kowa akan abin da Littafi Mai-tsarki ya ke koyaswa ba,

amma sai mu bi cikin zantattukan don kammu. Idan muka bari wadansu suka yi mana

tunanin, kwazon mu da kokarim mu za su tauye. Ikokin hankali za su gajarta sabo da rashin

watsa su a kan abin da ya kamatu su yi tunani a kai har za su rasa ikon da za su iya gane

zurfin ma’ananr Kalmar Allah. Kwakwalwa za ta dacfa fadi idan ta maida hankali wajen

binciken matsalolin da ke cikin Littafi Mai-tsarki, ta jarraba nassi da nassi, da abubuwa na

ruha- niya da wasu abubuwa na ruhaniya.

Babu abin da ya fi karfafa hankali kamar binciken Littattafai masu-tsarki. Ba wani

littafin da ya ke da ikon dagad da tunani, ya wartsakad da kwakwalwa, kamar gaskiyarda

ke cikin Littafi Mai- tsarki. Idan aka binciki Kalmar Allah kamar yadda ya kamata, ‘yan-

Adam za su samu hankali mai fadi, hali mai kyau, da kafaffen nufi wanda ya ke da wuyan

samu a zamani irin wannan.

Amma fa ba a cin ribar kirki idan aka karanta Littafi Mai-tsarki cikin garaje da

gaggawa. Mutum ya iya karanta Littafi Mai-tsarki daga farko har karshen amma ya kasa

ganin jamalinsa, ko ya gane zurfin ma-ana tasa da ke boye a ciki. Idan aka dauki aya guda

kadai aka bi cikinta sosai, aka kuwa gane ma’anarta, da mahadinta cikin shirin ceto, ya fi

45

Matakai Zuwa Wurin Kristi

a karanta surori dayawa ba tare da wani nufi ba, ba a kuma samu wani abin koyo ba. Ka

ajiye Littafi Mai-tsarki tare da kai; idan ka samu dama ka karanta, ka haddace ayoyin. Har

in kana tafiya kan hanya ma ka iya karanta wata aya ka yi tunani a kanta, ka haddace ta.

Ba shi yiwuwa mu samu hikima sai da kulawa da kwazo da bincike tare da addu’a.

Hakika nassosi cikin Littafi Mai-tsarki a fili su ke har ba shi yiwuwa a kasa gane su, amma

akwai wadansu ayoyin da ma’ana tasu ba a sama-sama su ke ba balle a gane su da cewa an

duba. Dole a gwada wani nassi da wani nassin. Dole ne a bincike tare da zurfin tunani da

addu’a. Irin wannan binciken kuwa zai ba da lada mai gwibi. Kamar yadda mai hakar

dukiyar kasa ya kan kai ga jijiyar dalma ko karfe mai tamani a boye can cikin kasa, hakanan

shi mai bicfar Kalmar Allah da naciya kamar wata boyayyar dukiya zai samu sahihiyar

gaskiya mai tamani wadda aka boye ta daga idon mai nema ba tare da lura ba. Maganganu

masu sukan rai, idan aka yi tunanin su a hankali cikin zuci, za su zama kamar rafuffuka

masu gudu daga mabulbulan rai.

Kada a yi binciken Littafi Mai-tsarki ba tare da addu’a ba dadai. Kafin mu fara bucfe

warkokinsa sai mun roki wayewar azanci daga Ruhu Mai-tsarki, za a kuwa bayar. Sa’anda

Natanayilu ya zo wurin Yesu, Mai-ceto ya ce “Duba, ga mutamen Israila na gaske, wanda

ba shi da algus!” Daga ina ka san ni? “Kamin Filibbus ya yi kiran ka, sa’anda kana

kalkashin itachen baure, na ganka.” Yohanna 1:47. 48. Mu ma Yesu zai gam mu a cikin

Iollokin addu’a, idan muka neme shi domin ya haskaka mu, domin mu san abin da shi ke

gaskiya. Mala’iku daga duniyar haske za su kasance tare da wacfannan da su ke neman

koyaswa daga sama cikin tawali’u a zuciyar su.

Ruhu Mai-tsarki yana cfaukaka Mai-ceto yana darajanta shi. Aikinsa ne ya nuna

Kristi, ya nuna tsarkin adilcinsa, da babban ceton da muka samu ta wurinsa. Yesu ya ce a

kan Ruhu Mai-tsarki, “Gama daga chikin nawa za ya karba, ya bayana maku kuma.”

Yohanna 16:14. Ruhun gaskiya Shi ne kadai mai koyaswa na gaskiya ta sama. Ba da daraja

kankanuwa Allah ya ke duban ‘yan-Adam ba tun da ya ba da Dansa ya mutu domin su,

kuma ya nada Ruhu Mai- tsarki ya zama mai koya masu ya zama jagabansu tutur.

46

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 11 – Amfanin Addu’a

Ta wurin halitta da wahayi, ta wurin tanajinsa, da ikon Ruhu Mai-tsarki, Allah ya ke

magana da mu. Amma wacfannan ba su isa ba; ana bukata mu zazzage masa zukatammu.

Idan muna so mu samu rai mai ruhaniya da zafin jiki, dole mu shiga cudaiya da Ubammu

na sama. Tilas sai a jawo hankulam mu zuwa gare Shi, mu yi tunani a kan ayyukansa, da

jiyejiyenkansa, da albarkansa masu yawa; amma wannan kadai ba shi ne taraiya da shi ba.

Idan muna son taraiya da Allah, dole mu samu wani abin da za mu fada masa game da

ainihin zaman mu na duniya.

Addu’a ita ce bude zuciya ga Allah kamar ga aboki. Ba wai don lalai ne mu sanas da

Allah ko mu wane ne ba, amma domin ya yiwu a garemu mu karbe shi. Addu’a ba ta sauko

da Allah zuwa wurin mu amma kai mu sama wurinsa ta ke yi.

Sa’anda Yesu ya ke nan duniya ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a. Ya

umurce su su kai bukace-bukacen su na yau da gobe gaban Allah, kuma su rataya masa

dukan ma’amalansu. Alkawarin da ya yi musu na cewa za a ji roke-rokensu alkawari ne a

gare mu har wa yau.

Yesu da kansa, sa’anda ya ke zaune a tare da yan-Adam addua ya ke yi a kowane

lokaci. Mai-cetommu ya nuna kansa daidai ya ke da mu wajen rashin karfi da bukacebukace

domin ya zama mai roko, mai neman karfi da taimako daga wurin Ubansa, domin

ya samu karfin fita wajen aiki. Shi ne abin misali a garemu cikin komai. Shi cfan-uwa ne

cikin rashin karfimmu, “an jarabce shi ta ko wace hanya, kamar mu”, amma kamar mara

zunubi, tabi’arsa ta yi nesa da zunubi. Ya daure kokawa da addu’a da azabar ruhu cikin

duniya mai zunubi. Tsare mutuncinsa ta sa addu’a ta zama dole ne. Ya samu ta’aziya da

farin zuciya cikin zance da Ubansa. Idan fa Mai-ceton ‘yan-Adam, Dan Allah, ya ji bukatar

addu’a, yaya ‘yan-Adam, masu zunubi, marassa karfi za su ji bukatar addu’a da himma ko

wane lokaci?

Ubammu na sama yana jira ya zuba mana cikakkiyar albarkassa. Halaliyarmu ne mu

sha ruwa yadda mu ke so daga mabulbulan kauna mara iyaka. Abin mamaki ne cewa ba

mu yin addu’a dayawa. Allah a shirye ya ke ya ji addu’ar gaskiya daga mafi kaskanta daga

cikin ‘ya’yansa, amma muna nuna rashin so a fill mu sanar da Allah bukace- bukacem mu.

Me mala’iku na sama za su yi tsammani a kan ‘yan- Adam marassa karfi, marassa taimako,

wadanda za su iya jarabtuwa, ga shi kuwa zuciyar Allah cike ta ke da kauna mara iyaka

tana bidar su, tana shirye ta ba su fiye da abin da za su iya roko, amma duk da haka ba su

yin addu’a dayawa, kuma bangaskiyarsu kadan ce? Mala’iku suna kaunar su yi ruku’u a

gaban Allah, suna kaunar su kasance kusa da shi. Sun dauki taraiya da Allah ya zama

babban abin farin cikin su, amma ‘ya’yan duniya wacfanda suka fi bukatar taimakon da

Allah ne kadai zai bayar, sun nuna kammar sun fi so su yi tafiyarsu ba tare da hasken

Ruhunsa ba, da zama ba tare da shi ba.

47

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Duhun mai muguntar yana kewaye wacfannan da suka wakala yin addu’a. Jarabun da

abokin gaba ya ke yi musu rada cikin kunnu- wansu suna rudin su su yi zunubi, duka

wannan kuwa domin ba su yi anfani da yarjin da Allah ya ba su ba ne cikin ayyana addu’a.

Dom mene ne ‘ya’yan Allah maza da mata za su ji nauyin yin addu’a sa’anda addu’a ita ce

mabudi cikin hannun bangaskiya da za ta bude gidan ajiya na sama, inda aka ajiye taimakon

da ba su da iyaka na Mai-iko duka? Im ba tare da addu’a da tsaro ba fasawa ba, muna cikin

hadarin zama cikin rashin kulawa da karkacewa daga kan hanyar gaskiya. Ko wane lokaci

abokin gaba yana neman ya sa abin tuntube kan hanya zuwa mazaunin jinkai, domin kada

mu samu alheri da ikon tsayaiya da jaraba ta wurin roko da bangaskiya.

Akwai wasu sharuda wancfanda ta wurin su za mu yi begen cewa Allah zai ji ya kuma

karbi addu’o’immu. Daya daga cikin na farkon wacfannan sharadu shi ne mu ji bukatar

taimako daga gareshi. Ya yi alkawari cewa “Gama zan zuba ruwa a bisa wanda ya ke jin

kishi, rafufuka kuma bisa busashiyar kasa.” Ishaya 44:3. Su wadanda su ke yunwata da

kishirta zuwa adilci, wadanda su ke marmarin Allah, su tabbata cewa za a kosad da su.

Dole zuciya ta budu ga ikon Ruhu, im ba haka ba ba za a iya karban albarkar Allah ba.

Babban bukatar mu muhimmi abin mahawara ne, yana kuwa robo sabili da mu da

Iafazi mai girma. Amma sai a nemi Allah ya yi wada- nnan abubuwa domin mu. Ya ce, Ku

roka za a baku. Wanda baya kebe Da nasa ba, amma ya bashe shi domin mu duka, kaka za

ya rasa bamu abu duka kuma tare da shi a yalwache?” Matta 7:7; Romawa 8:32.

Idan muka bar mugu daya tak cikin zukatam mu, ko muka mannewa ko wane irin

zunubin da aka sani, Ubangiji ba zai ji mu ba; amma addu’ar mai tuba da karyayyan ruhu

abin karba ne ko wane lokaci. Idan aka daidaita dukan laifofin da aka sani, za mu iya

gaskanta cewa Allah zai amsa roke-rokemmu. Kirkin mu kawai ba zai koda mu mu ruski

rahamar Allah ba, isar Yesu ne za ta cece mu, jininsa ne zai tsabtace mu, duk da haka muna

da aikin da za mu yi na kiyaye sharudan karba.

Wannan abu game da addu’a kuma shi ne bangaskiya. “Gama mai- zuwa wurin Allah

sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai- sakawa ne ga wadanda ke bidassa.’’

Ibraniyawa 11:6. Yesu ya ce wa almajiransa, “Dukan iyakar abin da ku ke addu’a kuna

roka kuma, ku bada gaskiya kun rigaya kun karba, za ku samu fa.’’ Marku 11:24. Ko muna

daukansa kan magana tasa?

Wannan tabbatarwa yana da fadi, ba shi kuwa da matukan tsawo; Shi kuma wanda ya

yi alkawarin mai aminci ne. Sa’anda ba mu karbi ainihin abubuwan da muka roka ba, a

lokacin da muka roka, duk da haka sai mu gaskanta Allah yana ji, zai kuwa amsa

addu’o’immu. Mu masu kuskure ne, marassa hangen nesa, har wani lokaci mu kan roki

abubuwan da ba za su zama albarka a garemu ba, Ubammu na sama kuwa cikin kauna ya

kan amsa addu’o’immu ta wurin ba mu abin da zai fi mana amfani, abubuwan da za mu so

don kam mu in da tsinkayar mu ta iya hangen abubuwa yadda su ke ta wurin hasken da za

48

Matakai Zuwa Wurin Kristi

mu samu daga sama. Sa’anda muka ga kamar ba a amsa addu’o’immu ba, mu dai sai mu

manne wa alkawarin; gama babu shakka lokacin amsawa zai zo, kuma za mu karbi albarkar

da muka fi bukata. Amma tsayawa kan cewa za a amsa addu’o’immu a daidai hanyar da

muka roka da kuma ainihin abin da muka roka ba daidai ba ne. Hikimar Allah ta fi gaban

ya kure, nagarta tasa kuma ta fi karfin ta hana abubuwa masu kyau ga wacfanda su ke tafiya

sosai. Don haka kada ku ji tsoron amincewa da shi ko ya zamana ba ku ga amsar

addu’o’inku nan da nan ba. Ku dogara kan tabbataccen alkawarinsa da ya ce, “Ku roka, za

a ba ku.” Matta 7:7.

Idan muka shiga cikin yin shawara da shakkokimmu ko tsoracce- tsoracemmu, ko

muka so mu warware ko wane abu wanda ba mu san kansa ba, tun kafin mu samu

bangaskiya, sai rudamu ya dada karuwa da zurfi kawai. Amma idan muka zo ga Allah da

sanin rashin karfim mu da bukatar madogara, kuma da bangaskiya mai tawali’u, mai

amincewa, muka sanas da shi wanda ba shi da iyaka bukatammu, Shi wanda ke ganin

komai na cikin halitta, Shi wanda ya ke mulkin komai, da nufinsa da magana tasa, zai iya,

zai kuma ji kukammu, zai kuwa bar haske ya haskaka zukatammu. Ta wurin addu’a ne ake

kawo mu cikin haduwa da hankalin Madauwamin watakila ba za mu samu wani shaida mai

ban mamaki a lokacin ba cewa fuskar Mai-pansarmu tana sunkuyawa bisa kam mu cikin

tausayi da kauna, amma kuwa lallai haka ne. Ya yiwu ba za mu ji tabawar hannunsa a jikim

mu ba, amma hannuwansa suna bisa kam mu cikin kauna da juyayi mai taushi.

Sa’anda muka zo rokon jinkai da albarka daga wurin Allah, ya kamata mu kasance da

ruhun kauna da gafara cikin zukatam mu. Yaya za mu iya yin addu’a mu ce “Ka gafarta

mana bassussuwan mu, kamar yadda mu kuma mun gafarta ma mabartanmu.” Matta 6:12.

amma mu zauna cikin halin kin yin gafara? Idan muna so a ji addu’o’immu, sai mu

gafartawa wacfansu daidai gwargwadon yadda mu ke begen za a gafarta mana.

Naciya wajen yin addu’a yana cfaya daga cikin sharudan karba Sai mu yi addu’a ko

wane lokaci idan muna so mu yi girma cikin bangaskiya da wayewar kai. Sai mu lizima

cikin addu’a mu ‘ yi tsaro da godiya kuma a cikinta Romawa 12:12; Kolosiyawa 4:2. Bitrus

ya hori masu ba da gaskiya cewa, “Ku yi rai shimfide zuwa ga addu’a.” 1 Bitrus 4:7. Bulus

kuma ya yi umumi cewa “Chikin kowane abu, ta wurin addu’a da roko tare da godiya, ku

bar roke-rokenku su sannu ga Allah.” Filibbiyawa 4:6. “Kuna addu’a chikin Ruhu Maitsarki,

ku tsare kanku chikin kamnar Allah.” Yahuda 20:21. Addu’a ba fasawa shi ne

maganin ruhu da Allah wanda ba ya karyewa, domin rai daga Allah ya dinga gudano zuwa

cikin rayukanmu, daga ram mu kuma sahihanci da tsarki su koma ga Allah.

Akwai dalilin bukatar naciya cikin addu’a; kada ku bari komai ya hana ku. Ku yi

iyakacin kokarinku ku bude hanyar zance tsakanin ruhohinku da Yesu. Ku nemi ko wane

dama da za ku tafi wurin da ake yin addu’a. Duk wadanda su ke ne man zance da Allah da

gaskiya, za a gan su wajen taron addu’a, da amincin aikata wajibinsu, kuma suna himma

49

Matakai Zuwa Wurin Kristi

domin su girbe duk iyakacin albarkan da za su iya samu. Za su gyara daman da suka samu

domin su sa kansu inda za su iya samun haske daga sama.

Ya kamata mu yi addu’a tare da iyalin mu, gaba da komai kuma kada mu bar yin

addu’a ta kadaituwa, gama wannan shi ne cibiyar ruhu. Ba shi yiwuwa ruhu ya yi girma

idan aka bar yin addu’a. Addu’a cikin iyali ko cikin tare kadai bai isa ba. Addu’ar boye

Allah mai jin addu’a ne kadai ke jin ta. Ba kunnen wani da zai ji. A cikin addu’ar boye

ruhu a sake ya ke daga daukewar hankali, abubuwan da ke kewaye da shi, ga kuma

natsuwa. Cikin hankali, amma da himma, za ta isa wurin Allah. Iko ne mai zaki, mai

tsayawa wanda zai fito daga gareshi Mai-gani daga cikin boye, wanda kunnensa a bude su

ke domin ya ji addu’ar da ke tasowa daga zuci. Ta wurin bangaskiya natsatstsiya ruhu ya

ke zance da Allah ya kuma tattara wa kansa haske na sama domin ya ciyad da shi, ya

karfafa shi cikin fada da Shaitan. Allah shi ne hasumiyar kaifim mu.

Ku yi addu’a can cikin boye, bari kuma zukatanku su daga kansu ga Allah a ko wane

lokaci ko cikin tafiya zuwa wajen dawainiya na yau da gobe. Ta haka ne Anuhu ya yi tafiya

tare da Allah. Wadannan addu’o’i na zuci kamar turare mai kamshi su ke a gaban kursiyin

alheri. Shaitan ba zai iya rinjayar shi wannan wanda zuciya tasa ta ke dogara ga Allah ba.

Babu wani lokaci ko wuri wanda za a ce bai yi kyau a roki Allah ba. Babu abin da zai

hana mu daga zukatammu cikin ruhun addu’a mai himma. Cikin jama’a a kan hanya, ko

cikin wani kasafi, za mu iya aikawa da rokom mu zuwa ga Allah domin mu samu bayaswa

daga sama, kamar yadda Nehemiah ya yi sa’anda ya yi rokonsa a gaban Sarki Artaxerxes.

A iya samun kebabben wuri a ko ‘ina domin a yi zance da shi a inda mu ke duka. Sai mu

bar kofar zuciya a bude tutur, kuma mu aika mu gaiyato Yesu ya zo ya zauna ya zama

bakon cikin ruhu.

Ko da a ce a kewaye da mu akwai iskar kazanta, ba lalai sai mun shake ta ba, amma

za mu iya rayuwa cikin sahihiyar iska ta sama. Ya yiwu mu rufe wa miyagun tunai ko wace

kofa ta wurin daga ruhu zuwa gaban Allah cikin addu’a sahihiya. Wadannan da zukatan su

a bude su ke su karbi tallafa da albarkar Allah, za su yi tafiya cikin iska wadda ta fi ta

duniya tsarki, za su kuwa kasance cikin zance da Allah tutur.

Ba lallai sai mun sami wani kwakkwaran tunani kan yadda muka mai da Yesu ba, ko

dada ganewar tamanin hakikatattun al’amura madawami. Jimalin tsarki shi ne zai cika

zuciyar ‘ya’yan Allah, idan ana son haka kuwa sai mu nemi wayewar kai daga sama a kan

abubuwa na sama.

Bari a jawo ruhu waje zuwa sama domin Allah ya ba mu numfashin iskar sama. Za

mu iya kasancewa kusa da shi har zai zamana a cikin ko wane gwaji wanda zai zo mana ba

tare da shiri ba, za mu iya juyawa ga Allah kamar yadda fure ya kan juya ga rana.

50

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Ku ajiye dukan bukace-bukacenku, da farin cikinku, da bakin cikin ku da abubuwan

da suka dame ku a rai, da abubuwan da ku ke ban tsoro, a gaban Allah. Ba za ku iya nawaita

masa ba, ba za ku iya gajiyad da shi ba. Shi wanda ya kididdige gasusuwan kawunanku bai

manta da bukace-bukacen ‘ya’yansa ba. “Ubangiji da shi ke chike da tausayi, mai-jinkai

ne kuma.” Yakub 5:11. Zuciya tasa ta kauna ta kan soku da bakin cikim mu, ko ambata su

muka yi kawai. Ku kai masa dukan abin da ya faskari tunanin ku. Babu abin da ya yi masa

girma domin dauka, gama shi ke rike da duniyoyi. Shi ke da mulki bisa dukan matsalan

halita. Babu wani abin da ya shafi salamar mu wanda ya cika kankanta har da ba zai kula

da shi ba. Babu wata sura cikin abubuwan da suka shafe mu wadda bakinta ya yi yawa har

da ba zai iya karanta ta ba. Babu wata dagulalliyar matsala da ta cika wuya har da ba zai

iya warware ta ba. Babu wani mugun abu da zai samu mafi kankanta daga cikin ‘ya’yansa,

babu wani tashin hankali da zai dami ruhu. ko farin ciki ya karfafa zuciya, ko sahihiyar

addu’a ta fita daga lebuna, wanda Ubammu na sama bai sani ba, ko kuwa wanda bai kula

da su ba. “Yana warkadda masu-karyayyar zuchiya, yana damre miyakunsu.” Zabura

147:3. Dan- gantaka tsakanin Allah da ko wane mai rai daban ya ke, cikakke ne kuma, har

ya zama kamar ba wani mai ran da kaunataccen Dansa bai mutu dominsa sai Shi kadai ba.

Yesu ya ce “Za ku yi roko a chikin sunana: kuma ban che maku, ni yi addu’a ga Uba

domin ku ba, gama Uba da kansa yana kamnarku.” “Ni ne na zabe ku, na sanya ku kuma

domin ku tafi ku bada yaya. . . . domin dukan iyakar abin da za ku roka ga Uba a chikin

sunana, shi ba ku.” Yohanna 16:26, 27; 15:16. Amma a yi addu’a cikin sunan Yesu ya fi

gaban ambaton sunan nan a farko ko a karshen addu’a. Sai a yi addu’a cikin hankali da

ruhu na Yesu, sa’anda mu ke gaskanta alkawaransa, muna dogara ga alherinsa, muna aikata

ayyukansa.

Allah ba ya nufi dukammu mu zama waliyyai, ko sufi ko mu janye kammu dungum

daga duniya mu mayar kan ibada. Zamam mu sai ya zama kamar na Kristi — tsakanin

dutse da taron mutane. Shi wanda ba ya yin komai sai addu’a, ba za a dade ba zai bar yin

addu’a, imma ba haka ba addu’oinsa za su zama maimaitawa ne kawai. Sa’anda yan-Adam

suka tsame kansu daga cudanya da sauran ‘yan-uwansu, suka saukakewa kansu wajibin

mai bin Kristi da daukan giciye, sa’anda suka daina aiki da himma sabo da Ubangiji wanda

ya yi aiki da hikima domin su, lallai kuwayar addu’a ta bace musu, kuma ba su da abin da

zai iza su ga ibada. Sai addu’o’insu su zama don kansu su ke yi da son kai a ciki. Ba za su

iya yin addu’a sabo da bukatar ‘yan-Adam ba ko domin ginin mulkin Kristi, ko rokon

karfin da za su iya yin aikin.

Muna yin hasara sa’anda muka yas da daman cudanya da juna domin mu karfafa juna

cikin hidimar Allah. Gaskiyar Kalmominsa su kan rasa ma’ana tasu ko nauyinsu cikin han

kulammu. Zukatammu sai su daina samun haske ko su kasa farkawa ta wurin ikonsa mai

tsarkakewa, kuma sai mu ragu cikin ruhaniya. Cikin goguwar mu da juna kamar masu bin

Kristi, mu kan yi rashi dayawa sabo da rashin jin tausayin juna. Shi wanda ya je ya boye

51

Matakai Zuwa Wurin Kristi

kansa ba ya cika mutsayin da Allah ke nufinsa da shi ba. Cudanya da juna bisa ga tabi’armu

ta ‘yan-Adam cikin hanyar da ke daidai za su sa mu ji tausayin junan mu, kuma han>. ce

ta ciyad da mu gaba da karfi cikin hidimar Allah.

Inda masu bin Kristi za su yi cudanya da juna, suna zance da juna kan kaunar Allah

da kan gaskiya mai tamani na pansa, sai zukatansu su wartsake kuma su wartsakad da juna.

Ya yiwu kullun mu dada koyon wani abu game da Ubammu na sama, muna cin riban dada

wayewar kai na alherinsa, sa’annan za mu yi marmarin yin zance kan kauna tasa; idan

muna yi haka, zukatammu za su yi tuni, su dacfa karfafa. Idan muna dada tunani da zance

kan Yesu ba kam mu ba, za mu dacfa fin samun kasancewarsa tare da mu.

Idan da za mu yi tunanin Allah a ko wane lokaci kamar yadda mu ke ganin shaidar

kulawa da mu da ya ke yi, za mu kiyaye shi tutur cikin tunanimmu, mu yi farin ciki cikin

zance a kansa da yabonsa. Mu kan yi zance a kan abubuwa na duniya masu wucewa domin

muna kula da su. Mu kan yi zance a kan abokanmu domin muna kaunarsu; farin cikimmu

da bacin ram mu a daure su ke da su. Duk da haka akwai babban dalili mara iyaka da zai

sa mu fi kaunar Allah da abokammu na duniya, ya kamata kuwa ya zama tabi’a a garemmu

mu maishe shi na farko cikin dukan tunanimmu, mu yi zancen alherinsa, mu fadi ikonsa.

Ba a ce wadatattun baiwan da ya yi mana su dauke hankulammu da kaunar mu har da za

mu rasa abin da za mu ba Allah ba, su ne za su rika tuna mana da shi tutur, su daure mu da

igiyoyin kauna da godiya ga Ubangijimmu. Mazaunimmu ya cika kusa da kwarurukan

duniya. Bari mu daga idanummu mu dubi budaddiyar kofa ta mafaka a sama, inda hasken

darajar Allah ke haskakawa bisa fuskar Kristi wanda “Domin wannan yana da iko ya yiwo

cheto ba iyaka domin wadanda ke kusantuwa ga Allah ta wurinsa.” Ibraniyawa 7:25.

Dole mu fi yabon Allah “Da dai mutane suka yarda su yabi Ubangiji domin alherinsa,

Da al’ajibansa da ya ke yi ma yan adam kuma.” Zabura 107:8. Bai kamata dukan ayyukan

ibadarmu su zama na roko ne da karba ba. Kada ko wane lokaci mu rika tunani a kan

bukace-bukacemmu, kada kuma mu tuna da abubuwan da muka karba. Kada mu yi zaton

addu’o’immu sun yi yawa, amma godiyarmu ta yi kadan. Mu masu karban jinkan Allah ne

tutur, amma duk da haka godiyar da mu ke furtawa kacfan ne, yabonsa da mu ke yi kuma

sabili da abin da ya yi mana kadan ne ainun.

A zamanin da Ubangiji ya ce wa ‘ya’yan Isra’ila, sa’anda suka taru domin su yi masa

sujada, “Chan fa zaku chi a gaban Ubangiji Allahnku, za ku yi murna kuma da iyakachin

abin da ku ke sa hannu gareshi, da ku da iyalanku, abin da Ubangiji Allahnka ya albarkache

ka a chiki. Kubawar Shari’a 12:7. Abin da za a yi shi domin darajar Allah sai a yi shi da

dadin rai, da wakokin yabo, da godiya, ba cikin bacin rai da daure fuska ba.

Allahmmu Uba ne mai jinkai. Bai kamata a dubi hidimarsa kamar aiki ne mai bakanta

rai ba. Ya kamata sujada ga Allah da taimakawa cikin yin aikinsa su zama abin dagadda

zuciya. Allah ba ya so ‘ya’yansa, wadanda sabili da su aka shirya ceto mai girma, su aikata

52

Matakai Zuwa Wurin Kristi

kamar cewa shi Ubangida ne mai fitina, mai matsa wa barorinsa. Shi abokinsu ne fiye da

kowa, kuma lokacin da su ke yi masa sujada, yana so ya kasance tare da su, ya albarkace

su, ya yi musu ta’aziya, yana cika zukatansu da farin ciki da kauna. Ubangiji yana so

‘ya’yansa su ta’azantu cikin hidimar sa, su kuma fi samun dadin rai fiye da wahala cikin

hidimarsa. Yana sa wacfanda suka zo yi nasa sujada su koma da tunanin kulawa tasa da

kauna tasa, domin su karfafa cikin dawainiyarsu na yau da gobe, domin su sami alherin yin

gaskiya da aminci cikin dukan abubuwa. Dole mu taru kewaye da giciye. Kristi da Shi

giciyayye shi ne zaya zama abin tunawar mu, abin tadim mu, da abin farin cikim mu. Sai

mu kiyaye cikin tunanimmu ko wace albraka da muka karba daga wurin Allah, kuma idan

muka lura da kauna tasa mai girma, sai mu lamunta mu danka ko wane abu cikin hannun

da aka kafa da kusa bisa giciye domim mu.

Ruhu ya hau sama kusa da aljanna bisa fukafukan yabo. Ana yi wa Allah sujada da

waka da bushe-bushe a can fada ta sama, kuma sa’anda mu ke furta godiyar mu, kwatacin

rundunar sama mu ke yi.

Dukan wanda ya bada hadaya ta godiya yana daukakata.” Zbura 50:23. Bari mu zo

gaban Allah cikin farin ciki mai saduda da “Ban godiya, da muryar rairawa.” Ishaya 51:3.

53

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 12 – Abin da za a yi da Shakka

Dayawa, mu samman su wadanda su ke sabbabi ne cikin zaman masu bin Kristi, wani

lokaci su kan damu da abubuwan da shakka ke kawowa. Akwai abubuwa dayawa a cikin

Littafi. Mai-tsarki wa¬cfanda ba za su iya ba da ma’ana tasu ba, ko kuwa ba su gane su ba,

Shaitan kuwa ya kan yi amfani da wadannan domin ya girgiza bangaskiyarsu cewa Littafi

masu tsarki ru’ya ne daga Allah. Su kan yi tambaya su ce, “Ta yaya zan san hanyar gaskiya?

Idan hakika Litafi Mai-tsarki Maganar Allah ne yaya zan kubuta daga shakkoki?”

Allah bai taba tambayar mu mu gaskanta komai ba ba tare da ba da isashshen shaida

wanda za mu kafa harsashin bangaskiyar bisa kai ba. Kasancewarsa, Halinsa, Gaskiyar

Magana tasa, duk an kafa su da shaida wadda ke magana da hankalimmu, wannan shaida

kuwa a yalwace ya ke. Duk da haka Allah bai kawas da yiwuwar shakka ba. Dole

bangaskiyarmu ta jingina kan shaida, ba nuni ba. Wadanda su ke so su yi shakka suna da

damar yin haka, wadanda kuwa su ke so su san gaskiya za su samu shaida mai yawa inda

za su jingine bangakiyarsu.

Ba shi yiwuwa ga hankalin mamaci ya gane tabi’un ayyukan Madauwami. Ga mai

kaifin hankali, ko ga rikakken masani Allah ba zai zama a nannacfe cikin asiri ba. “Ka iya

binchike har ka tone zurfafan al’amura na Allah? Ka iya binchiken mai-iko duka sosai?

Nisan sa kamar sama; yaya za ka yi? Ya fi Lahira zurfi, me zaka sani?” Ayuba 11:7-8.

Bulus Manzo ya ce, “Ya zurfin wadata na hikimar Allah duk da na saninsa! ina misalin

wuyan binchiken shari’unsa, al’amuransa kuma sun fi gaban a bi sawu!” Romawa 11:33.

Amma ko da shi ke “Hadura da dufu suna kewaye da shi,” “adilchi da shari’a tushen

kursiyinsane.” Zabura 8 97:2. R.V. Za mu iya gane ma’amala da mu, da dalilin da ya sa ya

ke yin haka, domin mu ga kauna mara iyaka da jinkai hade da iko mara iyaka. Za mu iya

gane nufinsa gwargwadon yadda zai yi mana kyau mu sani, amma gaba da wannan sai mu

gaskanta hanu wanda ya ke mai iko duka da zuciya wadda ta ke cike da kauna.

Maganar Allah, kamar tabi’ar Marubucinta na sama, tana da asirai wadanda ba shi

yiwuwa ‘yan-Adam su gane a zancin su. Shigowar zunubi cikin duniya, haifuwar Kristi,

sabon haifuwa, tashi daga matattu, da abubuwa da yawa da ke cikin Littafi Mai-tsraki,

asirai ne wacfanda zurfin su ya fi karfin hankalin dan-Adam ya kwatanta su ko ma ya gane

su. Amma ba mu da wani dalilin da zai sa mu yi shakkar Maganar Allah domin mun kasa

gane asiran ayyukansa. Tutur muna kewaye da asirai cikin halitta kanta wacfanda ba za mu

kai ga gindin azancin su ba. Komai kankantar halitta mai-rai abu ne wanda komai hikimar

malami ba shi da ikon kwatanta ta ko ya ba da dalilinta. A ko ina akwai al’ajiban da suka

fi karfin ganewarmu. To ashe sai mu yi mamaki idan muka ga aikin duniya ta ruhaniya

akwai asiran da ba za mu iya kai ga zurfin azancin su ba? Wuyar abin duka a rataye ya ke

ga rashin karfi da rashin facfi na hankalin dan-Adam. A cikin littattafai masu tsarki, Allah

54

Matakai Zuwa Wurin Kristi

ya ba mu isashshen shaida na sanin cewa tabi’arsa ba-samaniya ce, mu kuwa bai kamata

mu yi shakkar Magana tasa ba, domin ba za mu iya gane dukan asiran shirye-shiryensa ba.

Bitrus manzo ya ce akwai cikin litattafai masu tsarki “wadansu abu masu-wuyan

ganewa a chikinsu, jahilai fa da marasa- tsayawa su kan daguladda azanchinsu, kamar

yadda su ke yi da sauran litattafai, zuwa hallakar kansu.” 2 Bitrus 3:16. Masu shakka sun

tura wuyar azancin Litattafai Masu-tsarki a gaba domin su zama dalilan gaba da Littafi

Masu-tsarki; amma duk da wuyar hakanan sun zama shaida mai karfi na cewa Littafi Maitsarki

daga sama ne aka ba da dai ikon rubuta shi. In da ba wani labarin Allah a cikinsa, sai

abin da za mu iya ganewa nan da nan; idan da dan- Adam zai iya gane girman Allah da

kwarjininsa, da littafi Mai-tsarki bai cfauki shaida ta iko daga sama ba. Wannan jimali da

asiri na abubuwan da ake zancen su ya kamata don kansa ya kunna ban¬gaskiya a zuci

cewa Maganar Allah ne.

Littafi Mai-tsarki yana warwarse gaskiya cikin sauki da daidaitawa bisa ga

bukacebukace da burin zuciyar dan-Adam har wannan ya zama abin mamaki da kayatarwa

ga masana, ga shi kuma yana sa masu tawali’u da biyaiya su gane hanyar ceto. Duk da haka

su wadannan saukakan gaskiya suna karaa da abubuwa masu nauyi, masu kai nesa,

wadanda suka wuce ganewar dan-Adam, domin mu iya yarda da su kawai don Allah ne ya

fade su. Ta haka ne aka shimfida shirin pansa a bude a gare mu, domin ko wane mai rai ya

ga matakan da zai taka cikin tuba zuwa ga Allah da bangaskiya zuwa ga Ubangijimmu

Yesu Kristi, domin a cece mu ta hanyar da Allah ya nufa; duk da haka a karkashin

wacfannan gaskiya da aka gane su a saukake, asirai na nan kwance da su ke su ne boyewar

daraja tasa — asirai da su kan faskari kwakwalwa wajen binciken su, amma suna kunna

wutar zuci cikin ran mai neman gaskiya da sahihanci tare da ladabi da bangaskiya.

Gwargwadon binciken na Litafi Mai-tsarki gwar- gwadon zurfin tabbatarwassa cewa

Maganar Allah mai rai ce, kuma tunanin dan-Adam sai ya yi ruku’u a gaban kwarjini na

ru’ya ta sama.

Yarda da cewa ba za mu iya samun cikakken ganewar gaskiyan Littafi Mai-tsarki ba

yarda ne kawai da cewa hankalin dan-Adam bai isa ya gane rashin iyakar ba, kuma cewa

dan-Adam da gajeren hankalinsa na mutunci, ba zai iya gane nufenufen Mai-iko duka ba.

Domin fa ba za su iya kai ga zurfin dukan asirin ba, masu shakka da kafirai suna kin

yarda da Maganar Allah, kuma ba dukan masu cewa sun gaskanta Litttafi Mai-tsarki suka

tsira daga hadarin wannan ba. Manzo ya ce, “Ku yi lura fa ‘yanuwa kada watakila

mugunyar zuciya ta rashin bangaskiya ta kasance a cikinakowane dayanku da za ku ridda

daga Allah mai-rai:” Ibraniyawa 3:12. Daidai ne a bi cikin Littafi Mai-tsarki da kyau a

kuma yi bicike cikin “Har da zurfafa na Allah.” (1 Korinthiyawa 2:10) gwargwadon yadda

aka baiyana su cikin Littafi. Ko da shi ke “Al’amura na asiri ga Ubangiji Allahnmu suke;

amma wadanda an bayana, a garemu su ke duk da yayanmu har abada.” Kubawar Shari’a

29:29. Amma aikin Shaitan ne ya karkata ikon bincike na hankali. A kan hada fadin rai da

55

Matakai Zuwa Wurin Kristi

tunani kan gaskiya na Littafi Mai-tsarki, har mutane su kan ji rashin hankuri d?. kasawa

idan ba su iya kwatanta ko wace aya bisa ga yadda su ke so ba. Ya zama kaskanci ne a

garesu su yarda da cewa ba su gane kalmomi na huruwa ba. Ba su yarda su yi hankurin jira

har Allah ya baiyana musu gaskiya a lokacin da ya game shi. Suna ji a ransu cewa hikimar

su kawai ba tare da wani taimako ba ya isa ya sa su iya gane Littafi Mai-tsarki, idan kuwa

suka kasa sai su yi musun ikonsa. Gaskiya ne koyaswoyi da yawa da ake tsammani daga

cikin Littafi Mai-tsarki aka same su, basu da tushe daga wurin ta, maimakon haka gaba

suke yi da huruwan Ruhu mai-tsarki. Wadannan abubuwa sun zama abin sa shakka da

rudewa ga mutane dayawa. Amma fa ba za a ce laifin Maganar Allah ne ba, saidai

karkataswa da dan-Adam ya sa.

Idan da zai yiwu halittattu su kai ga cikakken ganewar Allah da ayyukansa, to, idan

suka kai ga wannan matsayi, ba za su dada gano wata sabuwar gaskiya ba, ba za su dada

girma cikin ilmi ba, ko cin gaba na hankali ko zuciya. Allah ba zai zama shi ne mai mulkin

komai ba, kuma idan dan-Adam ya kai ga kurewar ilmi, ba zai kara cin gaba ba. Bari mu

gode wa Allah da shi ke abin ba haka ya ke ba. Allah ba shi da iyaka; a cikinsa “Wanda

am boye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi chikinsa.” Kolosiyawa 2:3. Haka fa, har zuwa

tsararraki, har abada, ‘yan-Adam za su dinga bincike su dinga koyo, ba kuwa za su iya

kwashe dukiyar hikimarsa, da kirkinsa, da ikonsa dungum ba.

Allah ya yi nufi ko a cikin wannan rai gaskiyar Magana tasa ta warwaru ga jama’a

tasa. Hanya cfaya ce kacfai ta inda za a samu sanisa. Ta wurin haskakawar hasken Ruhun

da aka ba da Maganar ta wurinsa kacfai za mu iya kaiwa ga gane Maganar Allah. “Hakanan

kwa al’amuran Allah ba wanda ya sani, sai Ruhun Allah.” 1 Korinthiyawa 2:11. Gama

Ruhu yana binchiken abu duka, i, har da zurfafa na Allah.” 1 Korinthiyawa 2:10.

Kuma alkawarin Mai-ceto ga masu binsa shi ne, ‘ ’Amma sa’anda shi, Ruhu na

gaskiya, ya fito, za ya bishe ku chikin dukan gaskiya, . . . amma dukan iyakar abin da ya

ji, su zaya fadi; za ya bayana maku kuma abin da ke zuwa.” Yohanna 16:13, 14.

Allah ya yi nufi cfan-Adam ya yi amfani da ikonsa na tunani, bi cikin Littafi Maitsarki

kuwa zai karfafa, ya kuma dagad da hankali fiye da yadda ko wane irin bincike zai

iya yi. Amma fa sai mu lura kada mu allahnta tunanimmu wanda ya ke da rashin karfi na

mutunci. Idan ba mu so a dashe mana ganewarmu na litattafai masu tsarki har da ba za mu

iya gane gaskiya mafi sauki ba, dole mu sumu saukin kai da bangaskiya irin ta yaro

kankani,, a shirye domin mu koya, da kuma rokon taimakon Ruhu Mai-tsarki. Ya kamata

sanin iko da hikima na Allah, da sanin gazawar mu na gane girmansa, su cika mu da

tawali’u kuma ya kamata mu bude Magana tasa da kwarjini kamar sa’anda za mu shiga

wurinsa. Idan muka zo ga Littafi Mai- tsarki tilas tunani ya yarda da ikon da ya fi shi, kuma

dole zuciya da kwakwalwa su yi ruku’u ga babba wanda ya ce da kansa Ni Ne.

56

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Akwai abubuwa dayawa da su ke da wuya ko ba a fili ba wadanda Allah zai maishe

su a fili, ko ya saukake su ga wacfanda su ke so su fahimce su. Amma im ba tare da bishewa

na Ruhu Mai-tsarki ba, tutur zai yiwu mu dagulad da nassosi ko mu ba da ma’anarsu ba

daidai ba. Akwai karatun Littafi Mai-tsarki mai yawa wanda ba a samun riba a cikinsa, a

lokaci dayawa ma ya kan zama labari ne. Sa’an — da aka bude Maganar Allah ba tare da

ladabi ba, ba kuwa tare da addu’a ba; sa’anda ba a kallafa tunani ga Allah ba, ko tunani ba

ya cikin muwafaka da nufin Allah, sai hankali ya shiga shakka; kuma shakka ya dacfa karfi.

Sai abokin gaba ya samu iko bisa tunani kuma ya ba da ma’anar da ba daidai ba ne. Duk

sa’ad da ‘yan- Adam ba su neman muwafaka da Allah ko cikin tunani ko cikin aiki, to,

hakika, komai zurfin ilmin karatunsu, yana yiwuwa su yi kure wajen fahimtar littattafi,

kuma akwai hadari wajen yarda da ma’anar da za su bayar. Wadanda su ke dubuwa cikin

litattafai domin su tono rashin jituwa, ba su da ikon ganin cikin abu na ruhaniya. Da

karkataccen ido za su ga dalilan shakka da rashin ban¬gaskiya masu yawa cikin abubuwan

da su ke a fili su ke, masu sauki kuma.

Ko wane irin sake kama aka yi masa sau dayawa za a taras kaunar zunubi shi ne

kwakkwaran daliiin yin shakka. Zuciya mai alfarma mai kaunar zunubi ba ta marhabin da

koyaswa ko kafa iyaka na Maganar Allah, su kuwa wacfanda ba su lamunta su yi biyaiya

da bukace-bukacenta ba, a shirye su ke su yi shakkar ikonta. Idan muna so mu kai ga

gaskiya, dole mu kasance muna da sahihin nufi na son sanin gaskiya, kuma zuciyarmu ta

lamunta ta yi biyaiya da gaskiyar. Kuma dukan wacfanda suka zo binciken litafi Mai- tsarki

da wannan halin za su taras da shaida a yalwace cewa Maganar Allah ce, kuma za su ci

ribar fahimtar gaskiya tasa wadda za ta sa su yi hikima zuwa ceto.

Kristi ya ce, ‘ ’Idan kowane mutum yana da nufin ya aika nufin Allah, shi za ya sani

ko abin da nike koyaswa na Allah ne ko domin kaina ni ke magana.” Yohanna 7:17. R.V.

Maimakon yin tambayoyi ko gardama marassa karfi a kan abubuwan da ba ka fahimta ba,

ka kula da hasken da ya ke haskakawa bisa kanka za ka kuwa karbi haske mafi girma. Ka

aikata ko wane aiki wanda ka fahimta ta wurin alherin Kristi; za ka kuwa samu ikon da za

ka fahimta ka kuma aikata wabanda ka ke shakkar su a yanzu.

Akwai shaidar da ta ke a bude ga kowa — ga mai zurfin ilmi ko ga wanda bai iya

karatu ba — shaida da ake samu daga ma amala na yau da gobe. Allah yana bidar mu mu

tabbatawa kammu hakikanin Magana tasa, gaskiyar alkawarinsa. Yana bidan mu mu

“dandana, mu duba, Ubangiji nagari ne.” Zabura 34:8. Mai makon mu dogara ga cewar

wani, sai mu cfandana don kammu mu. Ya furta, Ko roko, za ku karba.” Yohanna 16:24.

Za a cika alkawaransa. Ba su taba kasawa ba, ba kuwa za su kasa ba dacfai. Kuma cikin

kusatowa ga Yesu, da yin farin ciki cikin cikakkiyar kauna tasa, shakkar mu da duhum mu

zai bace cikin hasken kasancewarsa tare da mu.

Bulus manzo ya ce Allah “Ya same mu daga cikin ikon dufu, ya mai- she mu zuwa

cikin mulkin Da na kamnassa.”Kolossiyawa 1:13 Kuma dukan wanda ya ketare daga

57

Matakai Zuwa Wurin Kristi

mutuwa zuwa rai ya iya ya “sa hatiminsa ga wannan, Allah mai-gaskiya ne.” Yohana 3:33.

Ya iya shaida ya ce “Da ina bukatar taimako sai na samu Yesu. Am biya ko wace bukata,

an kosad da yunwar ruhuna, yan zu kuwa a gareni Littafi Mai-tsarki shi ne baiyanuwar

Kristi . Kana tambayar dom me na kwa ba da gaskiya ga Yesu? — Domin a gareni Shi

Mai-ceto na sama ne. Dom me na ke gaskanta Littafi Mai-tsarki? — Domin na ga muryar

Allah ne ga ruhuna.” Ya yiwu muna da shaida cikin kammu cewa Littafi Mai-tsarki gaskiya

ne, kuma Kristi Dan Allah ne. Mun sani ba tatsuniyoyi da aka tsara su da wayo mai yawa

mu ke bi ba.

Bitrus ya yi wa ‘yan-uwansa galgad’i cewa, “Amma ku yi girma chikin alherin

Ubangijimu Mai-chetonmu Yesu Kristi da saninsa.” II Bitrus 3:18. Sa’anda Jama’ar Allah

su ke girma cikin alheri, tutur za su rika samun budaddiyar fahimtar Managa tasa. Za su ga

sabon haske da jimali cikin gaskiya tata mai tsarki. Wannan ya zama gaskiya a tarihin

Lkklisiya cikin tsararraki duka, haka kuwa zai daure har matuka. “Tafarkin mai-adilchi

yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ke haskakawa gaba gaba har zuwa

chikakkiyar rana.” Misalai 4:18.

Ta wurin bangaskiya za mu iya duban gaba, mu ruski alkawarin Allah domin girman

hankali, kwakwalwar mutunci tana haduwa da ruhaniya, kuma ko wane iko na ruhu ana

kawo shi cikin gogaiya da masomin haske. Sai mu yi farin ciki cewa a sa’annan nan dukan

abin da ya cude mana cikin al’amarin Allah za a faiyace mana shi; abubuwan da su ke da

wuyan ganewa za a baiyana su; kuma inda han kulammu na mutunci suka taras da rudami

da karayen nufe-nufe, za mu ga cikakken muwafaka mai jimali. “Gama yanzu chikin

madubi muke gani a zauranche: amma sa’annan fuska da fuska: yanzu na sani bisa bisa;

amma sa’annan zan sansanche kamar yadda an sansanche ni.” 1 Korinthiyawa 13:12.

58

Matakai Zuwa Wurin Kristi

BABI NA 13 – Yin Farinciki Cikin Ubangiji

An kira ‘ya’yan Allah domin su zama wakilan Kristi, su nuna nagarta da jinkan

Ubangiji. Kamar yadda Yesu ya baiyana mana ainihin gaskiyar halin Uban, haka kuma mu

za mu baiyana Kristi ga duniya wadda ba ta san kauna tasa, mai taushi, mai tausayi, ba.

“Kamar yadda ka aiko ni chikin duniya, haka kuma na aike su chikin duniya.” Ni a

chikinsu, kai kuma chikina, . . . domin duniya ta sani ka aiko ni.” Yohanna 17:18, 23. Bulus

Manzo ya ce wa almajiran Yesu, “Bayanannu ne ku wasikar Kristi.” “Sananniya che,

karantachiya che ga dukan mutane.” 2 Korinthiyawa 3:3, 2. A cikin ko wane daga cikin

‘ya’yansa, Yesu yana aikawa da wasika zuwa ga duniya. Idan kai mai bin Kristi ne, yana

aikawa da wasika ta cikin ka zuwa ga iyalai, kauye, titi da inda ka ke da zama. Yesu, a

zaune cikin ka yana so ya yi magana da zukatan wadanda ba su rigaya sun san shi ba.

Watakila ba su karanta Littafi Mai-tsarki, ko ba su jin muryar da ta ke zance da su ta cikin

warkokinsa, ko ba su ganin kaunar Allah ta cikin ayyukansa. Amma idan kai wakilin Yesu

ne na gaske ya yiwu ta wurin ka a bayas da su zuwa ga fahimtar wani abin nagartassa, a

kuma ribato su domin su yi masa hidima, su kaunace shi.

An ayanna masu bin Kristi su zama kamar masu rike da haske kan hanyar zuwa sama.

Su ne za su sa hasken da suka samu daga Kristi ya haskaka bisa duniya. Sai zaman su da

halin su ya zama daidai yadda ta wurin su wadansu za su samu daidaitaccen fahimta kan

Kristi da hidimarsa.

Idan muna wakiltar Yesu za mu sa hidimarsa ta zama mai kama hankali, kamar yadda

ta ke. Masu bin Kristi da su kan tara bakin ciki da daurin fuska bisa ruhohinsu, su dinga

gunaguni, suna nuna wa sauran ‘ya’yan Adam sifa na karya na Allah da zama na mai bin

Kristi. Suna nunawa kamar Allah ba ya farin ciki ya ga ‘ya’yansa suna murna, cikin yin

haka kuwa suna ba da shaida na karya gaba da Ubammu na sama.

Shaitan ya kan yi murna sa’anda ya iya biyas da ‘ya’yan Allah zuwa cikin rashin

bangaskiya da karaya a zuci. Yana farin ciki ya ga ba mu amincewa da Allah, da shakkar

yarda tasa da ikonsa na cetom mu. Yana so mu ji cikin rammu cewa Allah zai yi mana

lahani ta wurin nasihohinsa. Aikin Shaitan ne ya nuna Allah kamar mara juyayi da tausayi.

Ya kan canja gaskiya game da Allah. Ya kan cika tunani da zace-zace na karya game da

Allah, kuma, mai- makon mu zauna a kan gaskiya game da Ubammu na sama, safai mu

kan kallafa ran mu a kan yadda Shaitan ya nuna Shi cikin karya, har mu ki darajanta Allah

ta wajen kin yarda da shi da yin kunkuni gaba da shi. Tutur Shaitan yana nema ya sa zaman

addini ya yi baki. Yana sa a ga zaman addini abu ne mai wuya da wahalarwa, ta haka fa,

sa’anda mai bin Kristi ya baiyana irin wannan hali a kan addini cikin zamansa, yana goyon

bayan karyar Shaitan ke nan ta wurin rashin bangaskiyarsa.

Da yawa, cikin tafiya kan hanyar zaman duniya, su kan zauna a kan kurakuransu da

kasawa tasu da masifunsu, kuma zukatansu su kan cika da bakin ciki da karayar zuciya.

59

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Sa’anda na ke Turai, wata ‘yar-uwa wadda ta ke yin irin wannan, wadda kuma take cikin

rashin kwanciyar rai, ta yiwo mini wasika tana tambayata im ba ta maganganu na

karfafawa. Kashegari, da dare, bayan na karanta wasikarta, na yi mafarki wai ina cikin wata

gonar fure, kuma sai ga wani kamar mai lura da gonar yana kewayawa da ni ta kan hanyoyin

cikin gonar, ni kuma ina tatsinkan furarruka ina jin dadin kamshinsu. Sai ‘yar-uwata,

wadda ta ke tafiya tare da ni a barayi guda ta jawo hankalina kan wadansu dayayuwa

marasa kyaun gani da suka tsare mata hanya. Ga ta can ta tsaya tana kuka da bacin rai. Ita

ba tana biye da jagaba kan hanya ne ba, amma cikin sarkakiya da kayayyuwa ta ke. Sai

tana fadi da kunkuni a rai wai, “Ashe ba abin tausayi ne ga gonar furen nan mai kyau haka

ta zamma kuwa ta baci da kayayuwa?” Sai jagaban ya ce “Fita sha’anin kayayuwan don

kuwa za su ji maki ciwo. Ke dai tsinki rozis, da su lili da jajjayen kawai.”

Ba wacfansu abubuwa masu dadin tunawa cikin zamanka na duniya? Ba ka taba

samun wacfansu lokatai sa’anda zuciyarka ta kada don farin cikin da Ruhun Allah ya sa

ba? Idan ka duba baya cikin surorin zamanka na duniya, ba ka kan zo kan wadansu shafi

masu dagadda rai ba, Idan ka duba baya cikinsu kuwa ba kakan yi baban tunani ba?

Alkawaran Allah, kamar furanni masu kamshi, ba su yin girma a dama ko hagu da

tafarkinka? Ba za ka bar jamalinsu da dadinsu su cika zuciyarka da farin ciki ba?

Sarkakiyan da kayayuwan sai su ji maka ciwo su bata maka rai kawai, kuma idan su

kawai ka ke tsinkewa kana baiwa wadansu, ashe ba hana wadnda ke kewaye da kai ka ke

yi su yi tafiya cikin hanyar rai, kana kuma rage albarkar Allah da kanka ba?

Ba hikima ba ne a tara tunanin dukan abubuwa marassa dadi da suka wuce cikin zama

na baya — zunubai da masifu — a yi zance a kansu har karayan zuciya ya kewaye mu.

Ruhu wanda ya ke da karaya cike ya ke da duhu, yana rufe hasken Allah waje daga ruhunsa,

yana kuma jefa inuwa kan hanyar wadansu.

Sai mu gode wa Allah sabo da hotunan da ya ba mu kyauta Bari mu tattara wuri daya

tabbatawarsa mai albarka na kauna tasa domin mu rika kallonsu tutur. Dan Allah ya bar

kursiyin Ubansa, ya rufe allanntaka tasa da mutunci, domin ya kwato cdn-Adam daga ikon

Shaitan. Nasara tasa sabili da mu ne, bude sama ga cfan-Adam, baiyanawa idon dan-Adam

farfajiyi inda Allah ya kware daraja tasa; fadaddiyar kabila an cfaga ta daga ramin lalacewa

inda zunubi ya tsunduma ta, aka kawo ta cikin haduwa da Allah madauwami, kuma bayan

mun daure gwaji na sama ta wurin ban¬gaskiya cikin Mai-pansarmu, muka rufe jikimmu

da sutura da adilcin Kristi, daukakkakku zuwa ga kusiyinsa — wadannan su ne hotunan da

Allah ya ke so mu yi tunani a kansu.

Sa’anda ya zama kamar muna shakkar kaunar Allah, muna kin yarda da alkawaransa,

muna kaskanta shi, muna kuma jawo bacin rai ga Ruhu Mai-tsarki. Yaya uwa za ta ji idan

‘ya’yanta suna kuka da ita ko wane lokaci, kamar ba son su da arziki ta ke yi ba, alhali

kuwa duk kokarin zamanta na duniya tattalin su ta ke yi domin ta zama musu jin dad’i da

60

Matakai Zuwa Wurin Kristi

kwanciyar rai? Bisa ga misali a ce suna shakkar kauna tata, wannan zai karya zuciya tata.

Yaya uba ko uwa za su ji idan ya’yansu suka yi musu haka? Kuma yaya Ubanmmu na sama

zai dube mu, idan ba mu yarda da kauna tasa ba, wadda ta sa shi ya ba da tilonsa Dansa

haifaffe domin mu sami rai? Manzo ya rubuta cewa, “Wanda baya kebe Dansa ba, amma

ya bashe shi domin mu duka, kaka za ya rasa ba mu abu duka kuma tare da shi a yalwache?”

Romawa 8:32. Duk da haka guda nawa ne, ta wurin ayyukansu, balle fa da baka, su ke

cewa, “Ubangiji bai yi nufin wannan domina ba. Watakila yana kaunar wacfansu, amma

baya kauna ta?’’ Irin wannan duka yana cutar ruhunku, ko wace kalma ta shakka da za ka

furta, kiran jarabar Shaitan ne, karfafawa ne a cikin ranka ka yi shakka, kuma yana kore

maka mala’iku masu hidima. Sa’anda Shaitan ya jarabce ka, kada ka zabi ka bucfe kofa ga

abin da ya ke facfi, zuciyarka za ta cika da tambaye-tambaye na tawaye. Idan ka yi zancen

abin da ka ji cikin ranka, duk abin da ka furta na wajen shakka ba komowa kanka kadai zai

yi ba, amma zai zama iri da zai tsiro ya ba da ‘ya’ya cikin zaman wadansu, watakila kuwa

ba zai yiwu a kankare abin da maganganunka suka jawo ba. Watakila kai da kanka ka iya

warkewa daga zamani na jaraba ko daga tarkon shaitan, amma watakila wadansu wacfanda

suka janyu ta wurin maganganunka ba za su iya tserewa daga rashin bangaskiyar da ka

furta ba. Muhimmin abu ne mu yi maganar abubuwan da za su ba da karfi na ruhaniya da

rai kadai.

Mala’iku suna kasa kunne su ji irin labarin da za ku kaiwa duniya a kan Ubanku na

sama. Bari dai zancenku ya zama a kan wanda ya ke da rai yana roko dominku a wurin

Uban. Sa’anda ka kama hannun abokinka, bari yabo ga Allah ya kasance a bisa lebunanka

da cikin zuciyarka. Wannan zai jawo hankalinsa zuwa ga Yesu.

Dukan ‘yan-Adam suna shan gwaji, suna da bacin rai masu wuyan dauka, suna da

jarabu masu wuyan a yi musu tsayyayya. Kada ku fadi wahalce-wahalcenku ga yan-uwan

ku ‘yan-Adam, amma ku kai komai ga Allah cikin addu’a. Ku maishe shi doka kada ku

ambata ko magana guda na shakka ko na karya zuciya. Kua iya yin abubuwa masu yawa

domin haskaka zaman wacfansu da karfafa kokarinsu ta wajen maganganu na bege da

dagarwa mai tsarki.

Akwai rayuka dai da yawa masu mazakuta wacfanda su ke fama da matsi na Jaraba,

kusan a shirye su ke su suma cikin kokawa da kansu da kokawa da ikokin mugunta. Kada

ka karya zuciyar irin wannan cikin fadan da ya ke yi mai wuya. Ka karfafa shi da

maganganu na mazakuta, da bege wacfanda za su tura shi gaba cikin tafarkinsa. Ta haka

hasken Kristi ba zai ba da hasken daga gareka ba. “Gama daga chikinmu ba wanda ke

rayuwa ga kansa ba.” Romawa 14:7. Ta wurin kokarimmu ba da sanin mu ba, ya yiwu a

karfafa wadansu, ko a karya zuciyar wacfansu, a kore su daga Kristi daga gaskiya kuma.

Akwai mutane da su ke da kuskuren tunani a kan zama da hali na Kristi. Suna

tsammani ba shi da wani dimin hali na fara’a, kuma suna tsammani shi mai daurarren fuska

61

Matakai Zuwa Wurin Kristi

ne, mai tsanani, wanda ba shi da farin ciki. Ta hanyoyi dayawa duk al’amuran addini an sa

masa launi baki kirin.

Safai a kan ce Yesu ya yi kuka, amma baa taba ji an ce ya yi mur- mushi ba.Hakika

Mai-cetommi mutum ne na yawan bacin rai, ya kuma san bakin ciki, gama ya bude

zuciyatasa ga dukan masifu na ‘yan-Adam. Amma ko da shi ke zamansa na musun kai ne,

Fuska tasa ba ta nuna wata alama ta bakin ciki ko gunaguni ba, amma tutur ta ke cikin

natsuwa mai salama. Zuciya tasa rijiyar mabulbula ne na rai, duk inda ya tafi kuwa yana

dauke da hutawa, da salama, murna da farin ciki.

Mai-cetommu cike ya ke da kwakkwaran nufi da himma, amma dadai ba a taba

ganinsa ya murtuke fuska ba. Zaman wadannan da su ke kwaikwayonsa zai zama cike da

nufi mai himma, za su kasance da rike mutuncin kansu mai nauyi. Za a hana rashin daukan

matsala da himma, babu annishuwa, babu shakiyanci; amma addinin Yesu yana ba da

salama kamar kogi. Ba ya kashe hasken farin ciki, ba ya hana fara’a, ba ya ya dusas da

fuska mai murmucshi. Kristi ya zo ba domin a bauta masa ne ba amma shi kansa ne zai

bauta, idan kuwa kauna tasa tana mulki cikin zuciya, za mu bi gurbin sawunsa.

Idan a cikin rammu muka fi kula da ayyukan rashin nagarta da adilci na wadansu, zai

yi mana wuya mu kaunace su kamar yadda Yesu ya kaunace mu; amma idan muka bar

tunaninmu a kan kauna mai ban al’ajibi da tausayi na Kristi domin mu, wannan nufi zai

gudana zuwa ga wadansu. Ya kamata mu kaunaci juna, mu ba juna girma, kyale kallon

laifuffukan su. Dole mu zama da tawali’u da rashin yarda da kammu. Wannan zai kashe

son kai mai kuntatawa, ya maishe mu dattawa masu hannu sake.

Mai-zabura ya ce “Ka dogara ga Ubangiji, ka yi aikin nagarta; ka zamma a chikin

kasan, ka lizimchi aminchi.” Zabura 37:3. “Ku dogara ga Ubangiji.” Ko wace rana tana da

nata dawainiya, da aikace-aikace, kuma idan muka taru mun faya so mu yi zance a kan

wahalce-wahalcemmu da gwaje-gwajemmu. Dawainiyar da ba su shafe mu ba su kan

kunno kansu, fargaba iri iri, a kan furta rashin kwanciyar rai, har wani zai yi tsammani

cewa ba mu da Mai- ceto, mai tausayi, mai dauna, wadda a shirye ya ke ya ji dukan rokerokemmu,

ya kuma zama mana taimako na yanzu a ko wane lokacin bukata.

Kullum wadansu suna fargaba, suna aron wahala. Kullum alamun kaunar Allah suna

kewaye da su; kullun suna jin dadin baiwatasa, amma su kan manta da wacfannan albarka

na yanzu. Tutur hankalinsu yana zama kan wani abu mara dacfi wanda su ke fargaban zai

abku, ko watakila lallai akwai wata wahala wadda ko da shi ke kankanuwa ce ta kan

makantar da idanunsu daga ganin abubuwa masu yawa da ya kamata a yi godiya a kansu.

Maimakon wahalce- wahlacen da su kan ci karo da su su kora su zuwa ga Allah, wanda shi

ke shi kacfai ne masomin taimakonsu, sai su raba su da shi, domin sun farkad da rashin

kwanciyar rai da kishi.

62

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Mun yi abu mai-kyau kenanan mu zama marasa-bangaskiya haka? Me zai sa mu zama

da rashin bangaskiya da rashin yarda? Yesu aboki- mmu ne; duk samaniya ta kula da zaman

kwanciyar rammu. Bai kamata mu bar damuwa na yau da gobe su tsorata hankulammu ba,

ko su bata mana fuska. Idan muka yarda, ko wane lokaci za mu samu wani abin da zai

cakune mu ya ba mu haushi. Kada mu yarda da rashin kwanciyar rai, wanda zai tsorata mu

ne kawai, ya kare mu amma ba ya taimakon mu ga daukar jarabu.

Ya yiwu ka damu cikin zuciyarka domin watakila al’amarinka zai yi duhu, watakila

kuma hasara wurin ciniki ta zura maka ido; amma kada ka yi karayar zuciya; ka jefa

dawainiyarka ga Allah ka tsaya a natse cikin harka. Ka yi addu’a domin hikima ta bishe

al’amuranka cikin hankali, da haka sai hasara ta kawu. Ka yi iyakacin kokarinka abu nagari

ya fito cikin dukan al’amuranka. Yesu ya yi alka-warin ba da taimakonsa amma fa sai da

kokarin kammu. Sa’anda ka yi bakin kokarinka, kana dogara bisa Mai-cetommu, to sai ka

amshi duk abin da ya samu da harka da farin zuciya.

Ba nufin Allah ne rashin kwanciyar rai ya ami jama’arsa ba. Amma Ubangijin mu ba

ya ludin mu. Ba ya ce mana, “Kada ka damu babu hatsari a kan hanyar ka ba,” ya sani

akwai jarabobi da hatsaroril, sa’an nan yana fita mana a fili. Ba ya shirin ya cire jama’arsa

daga duniyar zunubi da mugunta, amma yana nuna masu mafaka mara-kasawa. Addu’ arsa

domin almajiransa shine, Ba Na yin addu’a Ka dauke su daga cikin duniya ba, amma domin

Ka tsare su daga Mugun.” Ya ce, “A cikin duniya kuma da wahala; amma ka yi farinciki,

Na yi nasara da duniya.” Yohanna 17:15; 16:33.

A chikin wa’azinsa na kan dutse, Kristi ya koya wa almajiransa nassi-nassi masu

daraja game da wajibin bangaskiya ga Allah. Wadannan nassi-nassi kwa an bayar da su

domin a karfafa ‘ya’yan Allah na dukan tsara, gashi kwa sun zo har zamaninmu cike da

koyaswa da kuma ta’aziya. Mai-ceto ya nuna wa mabiyansa tsuntsayen sama yadda suke

wakokinsu na yabo, ba tare da tunanin damuwa ba, gama *’ba sua shibkawa balle su girbe.”

Duk da haka Uba yana cika masu bukatunsu. Mai-ceto yana tambaya, “Ku ba ku fi su daraja

da yawa ba?” Matta 6:26. Babba Mai- bayaswa wa mutum da dabba, yana bude hannunsa

ya bayar wa dukan halittansa. Tsuntsayen sama basu yi nisa da ganinsa ba. Ba ya jefa abinci

a cikin bakunan su, amma Ya kan yi hanyar yadda bukatunsu zasu cika. Dole su tsince

hatsin da ya watsar masu. Dole su shirya shekansu. Dole su ciyad da ‘ya’yansu. Su kan tafi

wurin aikinsu tare da waka gama “Ubanku na cikin sama yana ciyad da su.” Amma “ku ba

ku fi su daraja da yawa ba?” Ku masu hikima, masu sujada mai-tsarki, ba ku fi tsuntsayen

sama daraja da yawa ba? Ko ba Mai-bayar da rai, wanda shike mai-tsaron ranmu, wanda

ya halicce mu cikin sifansa tsatsarka, zai biya mana bukatanmu idan mun bada gaskiya

gare shi ba?

Kristi ya nuna wa alamajiransa furannin jeji, masu girma cikin wadata da haske cikin

daraja wanda Uba ya basu domin ya nuna kaunassa. Ya ce “Ku lura da furannin jeji, yadda

suke girma.” Wadata da rashin alfahari na wadannan furannin sun fi dukan kawan da

63

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Solomon yake da shi. Dukan mafificiyar sutura wadda aikin hannu ya iya yi, ba za a iya

kwatanta shi da kyau da wadatan wadannan furanni wacfanda Allah ya yi ba. Yesu yana

tambaya “Idan fa Allah ya kan yi wa ganyaye sutura haka, abin da ke rayuwa yau, gobe

ana jefawa cikin tanderu, balle ku, ku masu kankantan bangaskiya?” Matta 6:28, 30. Idan

kwa Allah Mai-siffatawa Mai-Tsarki, ya kan ba furanni, wadanda suke lallacewa a cikin

rana cfaya, da launuka masu sha’awa haka, wane irin lura ne ba zai iya yi wa wadanda ya

halicce su cikin siffarsa ba? Wannan nasihan fadakarwa ne ga yawan tunani da shakkar

zuciya mara bangaskiya.

Ubangiji ya gwammace ‘ya’yansa maza da mata su kasance da murna, salama, da

biyayya. Yesu yana cewa “Salama ina bar maku; salamata ni ke ba ku: ba kamar yadda

duniya ke bayaswa ni nike ba ku ba. Kada zuciyar ku ta bace, kada ta ji tsoro kuma”

“Wadannan maganganu nn fada maku domin farin cikina ya zauna cikin ku, domin kuma

farin cikin ku ya cika.’’ Yohanna 14:27; 15:11.

Farin-ciki wanda aka nema daga wurin nufofi na son kai, ba cikin hanyar da ta wajaba

ba. abin muni ne mai kawo bari kuma mara jimawa; ya kan wuche hakan nan ya bar ran

mutum cike da kadaici da bakin-ciki; amma akwai farin cikin da koshiya cikin bautan

Allah; ba a bar Mai-bi ya yi tafiya cikin hanyoyi masu dufu ba; ba a bar shi cikin ladama

da hasara ba. Idan kwa bamu sami shagalin wannan duniya na yanzu ba, muna iya yin

farinciki cikin begen cewa muna da na duniya mai zuwa.

Amma ko a nan ma, Masu-bi zasu iya samun farin-ciki na zama tare da Kristi; suna

iya samun hasken kaunassa, da kuma jin dadin baiyanuwarsa har abada tare da su. Kowace

mataki a cikin rayukanmu tana iya kara kawo mu kusa da Yesu, tana iya bamu ganewa mai

zurfi cikin kaunassa, kuma tana iya kawo mu kusa kusa da gidan albarka na salama. Kada

fa mu jefas da amincinmu, amma mu kasance da tabbatas- wa fiye da da. “Tun da har wa

yau Ubangiji ya taimakemu,” Kuma zaya ci gaba da taimakonmu har zuwa karshe. 1

Samuila 7:12. Bari mu duba taswiran al’amurai, wadanda suke tuna mana da abin da

Ubangiji ya yi domin ya ta’azantad da mu ya kuma cece mu daga hannun mai hallakaswa

. Bari mu rike cikin tunanin mu, dukan jinkan da Allah ya nuna mana, - hawayenmu da ya

share ,dukan azaban da ya kwantar, alhinan da ya dauke, tsoron da ya kora, bukatun da ya

biya, albarkatun da ya watsar, - ta wurin haka yana karfafamu domin dukan abubuwan da

suka rage mana a hanyar hajjinmu.

Lallai ne mu sa zuciya ga abubuwan damuwa a cikin fada mai zuwa, amma muna iya

hangan gaba zuwa ga abin da ke zuwa, kuma mu che, “Har wa yau Ubangiji ya

taimakemu.” “Gwalgwadon tsawon kwan- akinka, gwalgwadon karfin jikinka ne.”

Kubawar Shari’a 33:25. Jarabawan ba zai fi karfin da za a bamu mu danka ba, bari kwa mu

kama aikinmu inda muka same shi, da bangaskiyar cewa, ko mene ne ya faru da mu,za a

bamu karfi gwalgwadon jarabawan.

64

Matakai Zuwa Wurin Kristi

Jim kadan kwa za a bude kyauren samaniya domin a shigad da ’yayan Allah, kuma

daga lebunan Sarki Mai-daukaka, albarka zai zuba cikin kunnuwansu kamar mawadaciyar

waka. “Ku zo, ku masu--albarka na Ubana, ku gaji mulkin da an shirya domin ku tun

kafawar duniya.” Matta 25:34.

Sa’an nan kuwa, za a kubutattu maraba cikin gidan da Yesu ya ke shirya masu. A

chan, abokanansu baza su zama muguntan duniya, makaryata, masu bautan gumaka, mara

tsarki, da marasa bangaskiya amma zasu cudanya da wadanda suka kada Shaitan kuma ta

wurin alheri mai tsarki suka siffata kamilan hankula. Kowache nufin zunubi, ko-wache

rashin kamila da ke damun su a nan, an rigaya an kawas ta wurin jinin Kristi, kuma martaba

da hasken daukakansa, da ya fi hasken rana, an basu. Kuma darajar adalcinsa da kamilcinsa,

yana haskakawa cikin su, fiye da kawan nan na waje. Kamilai ne su a gaban farin kursiyin,

cikin martaba da iko irin na malaiku.

A chikin tunanin gado mai daraja wanda zai zama nasa, “ina kwa abin da mutum zaya

bayas musanyar ransa?” Matta 16:26. Ya yiwu shi matalauci ne, duk da haka yana da

wadata da martaba wanda duniyan nan ba zai iya bashi ba. Ran mutum kubutacce kuma

wakakkiya daga wurin zunubi, tare da dukan darajan ikonta, mikakkiya zuwa ga bautan

Allah, yana da daraja mafi yawa; kuma akwai murna a cikin sama a gaban Allah da

mala’ikunsa masu tsarki domin rai daya wanda aka kubutar, murna wanda ake nunawa

cikin wakar tsatsarkar nasara.

65

Ana jiran ƙarshen komai

Hooray! Your file is uploaded and ready to be published.

Saved successfully!

Ooh no, something went wrong!