11.01.2013 Views

WAIWAYE ADON TAFIYA - IslamHouse.com

WAIWAYE ADON TAFIYA - IslamHouse.com

WAIWAYE ADON TAFIYA - IslamHouse.com

SHOW MORE
SHOW LESS

You also want an ePaper? Increase the reach of your titles

YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.

١

WAIWAYE ADON TAFIYA

(Wannan sako ne zuwa ga shuwagabanni da masanan harkokin yau da kullum na

Turawan yamma, daga dakin taro na girmama hurumin Musulunci wanda a ka yi ka

Kasar Kuwait)

Wanda ya fassara zuwa harshen Hausa:

Abdurrahman Sani Yakubu Zaria

(Jami'ar Musulunci ta Madinah)

ﻢﻴﺣﺮﻟﺍ

٢

ﻦﲪﺮﻟﺍ

ﷲﺍ

ﻢﺴﺑ

GABATARWA

Muna farawa da sunan Allah, Ubangiji Daya, wanda babu

abin bauta bisa cancanta sai Shi, Shi ne Ubangijin dukkan

Annabawa: Ibrahima, da Musa, da Isa, da CikaMakonsu, Annabi

Muhammad, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su daki

daya.

Wasu Malamai da masana harkokin yau da kullun cikin

Musulmi suka rubuta wannan sako, sun taru ne domin duba

hanyar da ta fi dacewa wurin alaka da Turawan yamma, da

kuma duba hanyar magance ta'addanci da suke yiwa Musulmi

da Musulunci, musamman ga shi kullun karuwa abin yake yi, ga

shi masu yin hakan wasu mutane ne, da kuma kungiyoyin

gwamnati da na addini da na 'yan jarida. Ga sako nan zuwa ga

masana harkokin yauda kullum da shuwagabannin addini da na

jama'a saboda wannan abu, muna fada musu cewa: A duk

lokacin da ta'addanci ya yi yawa a kan wata al'umma daga wasu

mutane to dolene ta fara ramuwar gayya, kuma ta ji dalinin da

ya sa hankan ke faruwa, duk da cewa abin da kowa yafi so shi

ne gaba da zalunci su tsaya.

Yau a duniya babu wata al'umma da take gamuwa da

zalunci da kuma mamayar Turawa kamar yadda al'ummar

Musulmi ke gamuwa da shi, kuma a duniyar yau babu wata

al'umma da take gamuwa da izgili da wulankanci game da

hurumominta da addininta, kamar yadda wannan al'umma take

gamuwa da shi, wannan al'umma baza ta karbi wannan al'amari

ba, musammam ita al'umma ce wadda take da sako daga sama,

kuma take da cigaba da tarihi mai asali, kuma ga mutanenta sun

fi daya bisa hudu (25 %) na mutanen duniya. Shi ya sa muka ga

ya wajaba mu jawo hankalin mutane da su waiwaya baya su

kalli abubuwan da suke faruwa, ko a samu a gyara kurakuran da

suke faruwa, daga nan sai tafiya ta yi kyau.

٣

YA ALAKARMU DA TURAWA TAKE YANZU?

Mun sani tun lokacin da musulmi suka fara gogayya da

turawa alakar da take tsakaninsu ta yi tsami, saboda dalilai masu

yawa, daga cikin dalilan: Lalle turawa ba su yin mu'amala da

Musulunci gaba da gaba, koda yaushe suna cikin fargaba da

tsoro, wannan shi ya sa su ka yi kokarin hada kawunansu don su

yaki Musulunci, duk da cewa akwai rashin jituwa kai a

tsakaninsu, daga nan sai Musulunci ya zama babban abokin

gabansu, duk da cewa da sun kasance a rarrabe suna yakar juna,

dukkanmu mun san cewa ba dai-dai ba ne yiwa kowane abu

kudin goro, kuma mun sani cewa a karnonin da suka shude

Amurkawa da sauran Turawan yamma sun yi kokarin rabuwa da

aiboban da ke cikin al'adunsu, wurin mu'amala da wasunsu, sai

dai kash! Yanzu sun manta da wannan al'amari, saboda haka

wannan wasika ba tana magana da musu kiyayya da musulunci

ne kawai ba, tana magana ne da duk wani bature, musamman

masu adalci a cikinsu, kuma mun sani ba duka Turawan suka

taru suka zama daya ba.

MISALAN TA'ADDANCI DA CIN MUTUNCI DA

SUKEWA MUSULMI DA MUSULUNCI.

Lalle muna jan kunnen shuwagabanni Turawan yamma

game da abubuwan da suke ta faruwa, muna kallo a cikin kasa

da shekaru uku an keta huruminmu ba sau daya ba, fara daga

ALKUR'ANI MAI GIRMA, ta yadda suke buka su watsa wasu

litattafai wadan da a zatonsu makwafin Alkur'ani ne, a cikinsu

akwai izgili ga Annabimu da addininmu da akidarmu da

halayenmu da tarihinmu. Bayan haka sai suka kara da cin

mutunci Annabinmu (S.A.W) suna kamanta shi da kamannu

marasa kyau, suna zana hotonsa zane na wulakanci da izgili.

Jaridar kasar "Denmark" ta fara hakan, sai sauran kasashen suka

koya daga wurin ta, wasu wa sa albarka suka yi a cikin aikin.

Daga nan sai ciwon ya kara girmama yayin da "Papa Roma" ya

fito fili ya soki Alku'ani da Manzon Allah (S.W.A) suka irin na

rashin kunya.

Kuma ba mun manta da abin da sojojin Amurka suke yi ba

ne a kurkukun "Abu Guraib" na kasar Iraki, da kuma kurkukun

"Gointanamo" na kasar "cuba" ta inda suke wulakanta Musulmi

٤

da Littafinsu (Alkur'ani). A gefe daya kuma koma yana ganin

abin da ke faruwa a manyan garuruwan Turai na cin zalun

musulmi mazauna wadannan garuruwa. Kuma ba zamu iya

manta abin da ke faruwa Iraki da Afganistan ba, wanda Amurka

ta mamaye, kullum ana kai wa masallatai hari, hakanan kurun,

ko da hujjar wai ana neman masu rike da makamai, wani lokaci

a kashe duk wanda yake cikin masallacin.

Kuma akwai maganganu na kiyayya da shuwagabannisu

suke yawan furtawa, ko abin da marubutansu suke rubutawa, ko

abubuwan da suke watsawa a gidajen Talabijin da radio ko

jaridunsu da mujallu, wadanda suke kamanta Musulmi da

nakasu da ta'addanci.

Lalle shirun da manyaku suke yi a kan wadannan abubuwa

yana bamu tsoro! Mun rasa ina zama sa ku? Wannan shine

'yancin dan adam din? Ko dai rashin 'yanci? Shin kuna

wulakanta Annabawan Allah da suna 'yancin ra'ayi?

SUNA WULAKANTA MANZON ALLAH (S.A.W)!

Duk da cewa akwai al'ummomin da suka yaki Musulmi,

amma duk da haka ba a same su da gadon kiyayya ga Annabin

Musulmi ba, kamar yadda a ka samu kasashe da coci-coci na

turai suna yi masa ba, hakika kiristocin Turai, sun kafa gaba da

Musulmi da Annabinsu gaba na tarihi, har abin ya kai haddin

tunawa juna idan an hadu a coci a lokacin bukukuwan addini.

Wannan abu ya cancanta mutsaya mu duba sababinsa da hanyar

magance shi.

Wai menene ya sa wasu muatane a Turai suke kokarin sai

mun manta da manyanmu kuma abin koyinmu? Lalle ne duk

wanda ya rayuwa ba shi da na gaba, to, tababbe ne shi! Kuma

duk al'ummar da ta manta da tarihinta, to, kamar gini ne babu

asasi, (wadan nan su ne dalilanmu) to, saboda haka ne kuke

walakanta Annabinmu? Lalle mun sani cewa abin da lalatattu a

Turai suke so shi ne mutane su manta tarihinsu, musamman

musulmi, babban misali a kan haka shi ne abin da ke faruwa

yanzu na yiwa Annabawa izgili. To ya kamata su sani cewa

munanan daram dakam wurin tare wa Annabinmu, da ma sauran

Annabawa baki daya, wannan abin ba zai samu karbuwa a wurin

٥

mu ba, wai da sunan 'yancin bayyana ra'ayi, ba zai taba yiwuwa

ba, Musulmi su yarda da dattin tunanin Turawa ba, kamar yadda

suma basu yarda da namu 'yancin dan adam din.

Lalle muna kira da babban murya cewa, masu hankalin

Turai su tsaya su kalli wannan lamari da idon basira, kuma mun

sani a cikin su akwai masu kwadayin duk abin da zai gyara

tarihin su a wurin mutane, ba abin da wasun su suke yi na cin

mutunci mutane ba, musamman Annabawa.

TA'ADDANCI GA MASLLACIN KUDUS (Masallacin duk

annabawa)

Mamaye masallacin Kudus da yin ta'adda gare shi, lalle

yana daga cikin ta'addanci ga murumin musulmi, kuma hakan

yana faruwa da taimakon wasu gwamnatocin Turai ne, da kuma

goyon bayan wasu kungiyoyin addini a can, hakika hakkin

"veto" a majlisan dinkin duniya, ya zama hakkin Yahudawa, su

kadai yake karewa, kuma yake goyon bayan ta'addancin su, da

mamayar su ga "Palastine" da masallacin Kudus, wanda har

gobe baza mu taba barin musu shi ba! Kuma muna sake

tambayar masu hankali cikin Turawa, wai menene kuka yi wurin

magance zalucin da a ke yiwa Musulmi a "Palastine", da keta

huruminsu, da kuma hana musu hakkokinsu.

Abin a kwai tukka da warwara, kullum suna kiran

musulmi da su zo su yi "Democracy" (dimukradiyya) lokacin da

Falasdinawa suka zabi hukumar da suke so ta mulke su, sai ga

shi sun fito fili suna fada da hakan. Lalle shirun da manyansu

suke yi akan hakan, to abin kunya ne a goshin duk wanda yake

da'awar 'yanci da dimukradiyya a duk duniya. Saboda haka

muke kira gare su da su yi kokari wajen share wannan abin

kunyan da yake tare da su, wurin hada kai da masu adalci, kuma

masu kare hakkin dan adam na gaskiya, masu kokarin sai sun ga

an baiwa kowa hakkinsa.

IZGILI GA HIJABIN MACE MUSULMA.

'Yancin kai yana da goyon baya a dimukradiyyar Turai,

kamar yadda suke shela koda yaushe, saboda haka mace tana da

hakkin sanya abin da take so, idan dai bai sabawa al'adun

mutanen kwarai ba, sai dai abin mamaki shi ne, an sami wasu

٦

suna walakanta hijabi da mace mai hijabin, wanda wannan shi

ne ainihin tikka da warwara, kullum suna kokarin yada

dimukradiyya, amma wannan ya sabawa abin kira a kai, kuma

babu wata kungiyar kare hhakkin mata ta duniya da ta sa baki

warin abin da yake faruwa. Shin 'yancin fita tsirara shine 'yanci

kuma za a kare shi, amma 'yancin kamun kai da kunya ana

yakan shi?!

Ya kamata masu kokarin yada hakkin dan amdam na Turai

su yi kokarin tsarewa mutum asalinsa da al'adansa ne, ba yakan

su ba, ta ya suna kallo ana yakan Musulmi mazauna can. Wurin

zabar kayan da suke so? Ko sun manta da abin da suka gada

daga addinin su da al'adun su ne? har yanzu ana samun wasu

matan turawa masu kunya suna sa kayan mutunci, wanda yana

kama da hijabin Musulmi, kamar matan kauye, da matan da

suka rike addini. Shin idan su sun saki wadannan al'adu, sai ya

zama dole mu ma sai mun saki na mu? Hakika muna kyamar

yaki da ake yi da kamun kai, kuma wannan bai kamata a ce shi

ne sakamakon wayewa da cigaba ba, shin wai hijabi shi ne ya

zama alamar kama kai da a ke yaka a Tirai? Hakika dokokin da

ake kafawa saboda hakkin mace saboda tasa hijabin Musulunci,

to a mafi yawan kasashe Turai a na kafa su ne domin daga baya

a hanata sa hijabin; wai wannan duk saboda gaba da Musulunci

ne, kama yadda ya bayyana kwanannan? Ko saboda gaba

dakamun kai ne? ko saboda 'yan iskan gari su ji dadi? Ga

tambayoyi suna bukatar amsa daga wurin masu tunani a Turai,

kuma wajibi ne su bayyana tukka da warrar da take cikin

wannan lamari.

YAKAR TUNANI.

Hakika manyansu da shuwagabannin addininsu sun fito fili

su tuhumci Musulunci da tuhunce-tuhumce da baban-daban a

kwanannan, kamar: "Lalle Mususlunci bai wasu ba sai da tilasci

da takobi" ko kuma "ba a amfani da hankali a cikinsa" ko kuma

"Lalle Musulunci addinin ci baya da ta'addanci ne" da sauran su,

wannan sako ba zai maida hankali warin karyata wadannan

tuhumce-tuhumcen ba, sai dai za mu yi bayani cewa lalle

wadannan tuhumce-tuhumcen ba su dacewa da yadda a ke

٧

muhawara a ilmance, sun yi kama ne da kokarin yakan tunani da

wasu kungiyoyi masu karfi a Amurka suke yi don kokarin

canzawa Musunci riga.

Mun yarda cewa Musulunci ya watsu ta hanyar jihadi "fi

sabilil lah", da hanyar Da'awa cikin kwanciyar hankali, kuma ko

wata daula tana bukatar karfi wurin kare tushenta da abubuwan

da ta mallaka. Dalilin haka abin da a ke kira yaki mai adalci

"just war" shi ne cocin Turai ya kafu a kai kua ya yarda da shi,

kuma da shi 'yan ba ruwan mu da addini na Turai suke yin abin

da suke so a duniya, to na saboda me za a tsangwami

Musulunci? Alhali kun sani kuma tarihi ya tabbatar cewa

"Indonesia" da "philipis" da "Malasia" da wasu daga kasashen

Afrika ba sojan da kafarsa ta taka wadannan kasashe, to ta yaya

wadannan miliyoyin mutane suka shiga Musulunci? Tambayar

da ya kamata mu yi a nan ita ce: me ya sa har yanzu Musulunci

yake watsuwa a duniyi? Musamman a turai? Su ma takobin ne?

Sam, tasirin da ya ke yi ne a zuciyar duk mau hankali.

Amma amfani da hankali a cikin Musulunci kuwa, shimfidar da

zamu yi anan ita ce: Hakika tarihi ya tabbatar da cewa Turawa

su ne ba suka watsar da hankali a bayansu, wasu kuma suke

wauta masa, wato imma a yi wannan, ko a aikata kishiyarsa, a

dai-dai wannan lokaci kuwa, Musuluci adalci yake yi game da

amfani da hankali, da amfani da shi warin yiwa dan adam

hidimar da ta kamata, wai me ne ya sa wasu shuwabannin addini

a turai suke sukan Musulunci ta bangaren hankali? Saboda kin

gaskiya ne da boye nakasun da yake tare da su? Ko domin su

taya 'yan baruwan mu da addi yaki da Musulunci?

Lalle muna kira ga shuwagabanin addininsu, da su yi

muraji'ar akidunsu musamman akidar Uluhiyya, a lokacin za su

san tikka da warwarar da take cikin akidarsu, wanda rashin

amfani da hankali ya jawo musu. Hatta boren da a ka yi musu

gaban da suke yi da hankali da ilimi ya jawo musu, kuma shi ya

sa kin addini ya mamaye kasashen su.

Amma abin da ya watsu a turai na tuhumar Musulmi da

Musulunci da abin da suka sawa suna ta'addanci, to, tuhuma ce

ta zalunci, bata da asasi a tarihi balle a sarari, al'ummar Musulmi

da a ka sani da rahama da kyautatawa. Lalle muna kiran turai da

٨

su yi kokari su bar abin da suka gada na gaba da Musulunci tun

lokacin da suka yaki Musulmi da sunan yakin salib (yakin

kiristanci) wannan shi ne asalin ta'addanci, kuma duk wanda

yake kiran mu 'yan ta'adda a yau, to shi ne babban dan ta'addan

da ya kashe kuma yake kashe moliyoyin 'yan adam, yakin

duniya na daya da na biyu Musulmi suna da hannu wurin tada

su?

Lalle masu tunani a Musulmi za su iya lura da canjin da ya faru

daga wasu masu gaba da Musulunci daga yaki da Musulmi zuwa

yaki da Musulunci, kuma daga kokarin canza Musulmi zuwa

kokarin canza Musulunci. Muna fada musu cewa lalle

Musulunci baya bukatar kwaskwarima kamar yadda suka yiwa

addinin su, Musulunci an san shi addini ne kammalalle kuma

har yanzu yana watsuwa ba tare da canza wani abu a cikinsa ba.

Hakika zumudi ya debi wasu shuwagabanni turai wurin neman

wasu kyara-kyare a Musulunci, addinin da ba su san kome a

cikinsa ba, kawai abin da suka sani game da shi, shi ne lalle shi

wani addini ne da ya sabawa kiristancinsu na zamani, wanda ya

cakuda da lebralancin turai domin ya zama wani sabon addini,

wanda dole ne duk wanda ya saba masa ya yi kokarin kyara

tafiyarsa don ta yi dai-dai da wannan sabon addinin.

Lalle mu mun sani cewa addininmu da babu wanda ya isa

ya ce zai iya canza wani abu a cikinsa, ya isa ya zama maganin

duk wata mushkilar da take damun turai, shi ya sa wasu suke

kikarin rabuwa da Musulunci rabuwa ta karshe, kuma zamar

Musulunci ba a canza kome a cikinsa ba ya na karyata abin da

wasu suke zato cewa sune karshen tarihi.

Lalle mu muna kin duk wani kokarin hana al'ummarmu

damar ta gina tunaninta yadda take so, a lokaci daya kuma muna

bayyana cewa lalle mun yarda da leka al'adun wasu da daukan

mai amfani a ciki, kuma muna bayyana cewa lalle tunanin

turawa wurin akidunsu da dokokinsu da al'adunsu ba karbabbe

ba ne a duniyance, kuma ba mai tsarki ba ne. kuma duk wani

kokarin sa shi ya zama haka, ba zai yi amfani ba. Lalle Musulmi

sun sani cewa yakin da turai suke yida Musulunci, da sunan

yakin tunani ba wani abu ba ne face tsoron cigaban Musulunci,

wanda zai hanasu mamaye ko'ina.

٩

Abin da kuke kira yakin tinani, abu ne da bamu yarda da

shi ba, kuma ba za mu bar kare mutuncin addininmu ba, saboda

mun lura cewa filin yakin tunani shi ne filin al'ummarmu, amma

yakinin da muke da shi ya sanya bamu tsoron wani abu zai iya

girgiza abin da muki yi imani da shi, kuma zamu iya bayyana ko

gyara abin da ya batawa turai tunaninsu a cikin akidunsu, da

suransu.

YA MUKE FAHIMTAR TA'ADANCIN DA SUKE YIWA

HURUMINMU?

Daga abin da shuwagabanninsu suke fadi, ko wasunsu

suke rubutawa zamu iya fahimtar cewa lalle yakin da suke yi da

Musuluncin ba aikin Mutun daya ba ne, ko kuma ramuwar

gayya saboda wani abu da a ka yi musu, wani shiri ne da a ka

zauna aka shirya domin a takura musulmi a duniya, kuma shi ne

ya fito fili a cikin maganar shugaban Amurka " J. W. Bush"

yayin da ya ce: "wannan yaki da yake yi yakin addinin ne"

wanda daga baya ake cewa yaki da ta'addanci, a Iraki da

Afganistan da wasu wuraren da dama. Kuma shi ne maganar

faraministan Italiya "sifo" ya yin da tuhunci Musulunci da

tuhuma ta zalunci, kuma ya dauki Musulunci wai addini ne na ci

baya, kuma ya manta aikin Musulunci a tarihi mai tsawo.

"Adviser" Jamus ma ya fadi irin wannan magana, har yana

cewa: "baza a bar Musulunci ya firgita ciganban turai ba"

A nan tambaya zata zowa mutum cewa: shin mene suke

nufi da wannan cin mutunci da ba ya karewa? Idan domin

'yancin ra'ayi ne, to me ya sa ba bu hawa kan sauran addinai

kama addinin mutanen Indiya da Yahudawa da Budanci da

sauran su? Musulunci kawai a ke yaka, wannan sh ne ya ke

karyata abin da suke fada koda yaushe. Shin ko abin da ya faru

kwanannan shi ne dalilin wannan yaki? Lalle ba za mu yarda da

wannan maganar ba; saboda yakin da suke yi da Musulunci yana

nan tun kafin wannan abin da ya faru suka tuhumi wa su

Musulmi da ta'addanci.

Wasu masana lamuran yau da kullum daga Musulmi suna

ganin abin da ke faruwa yanzu na yaki da Musulunci da

ta'addanci a kan huruminsa dalilinsa shi ne: ganin turai

١٠

Musulunci ya fara maida karfinsa da ya rasa kuma ya fara

farkawa daga barcinsa, saboda ya cigaba da aikinsa na kyara dan

adam da jiyar da shi dadi. Kuma abokin rige-rige wurin cigaba

da tunani.

Lalle muna ba maganar kungiyar yafiya a addini na kasar

"Canada"mahimmanci yayin da su ka ce yawan Musulmi a

duniya a shekarar 2003 biliyon 1,226 19 % na mutanen duniya a

wancan lokacin, kuma suka tabbatar cewa addinin Musulunci

shi ne addinin da masu shigansa suke karuwa, a lokacin da

sauran addinan suke raguwa, kuma kungiyar ta kara da cewa

nan da shekara ta 2023 Musulunci shi zai zama addinin farko a

duniya, shin wannan magana ita ce ta sanya tsoron da ya ke

cikin zukatanku ya dawo? Muna tambaya?

Har ila yau muna ganin tikka da warwara game da sha'anin

turai, kullum suna maganar 'yanci da dimukradiyya amma a

lokaci daya suna hana Musulunci 'yancinsa a kasashensu,

saboda kar Musulmi su dauki addininsu abin bi a cikin harkokin

rayuwar yau da kullum. Kuma suna zuga wasu su cutar da su

har a cikin gudajensu, da kuma kokarin yin musu mulkin

mallaka.

Lalle mun lura cewa gaban da wasu shuwagabanni da

sauran mutanen turai suke yi da Musulunci ta gidajen sadarwa

suna ganinsa dai-dai ne, kuma bakin shuwagabanninsu da

gidajen sadarwarsu daya wurin gaba da Musulunci.

Kuma wannan yakin da gidajen sadarwan suke yi ya haifar

da wata matsala mai girma, ita ce hana wasu shiga addinin Allah

Madaukakin Sarki. Kuma masana addinin kiristanci a cikinsu

suna da hannu cikin wannan yaki, wurin boye hakikanin

Musulunci, da kuma aibanta shi, da kokarin kore mutane daga

gare shi, da kuma boye bisharar da a ka yi na zuwan Annabi

Muhammad (S.A.W) a cikin Attaura da Linjila.

Kuma akwai wani abu, shi ne yakan wasu rubuce-rubuce

da wasu masu adalci a cikinsu suke yi, idan sun yiwa Musulunci

adalci, sai ka ga a na kai musu farmaki da karfi, wanda zai ba ka

tabbas cewa akwai wasu jama'a a turai maslaharsu ita ce su

nunawa 'yan'uwansu aibun Musulunci da Musulmai.

١١

A KARSHE:

Lalle tattaunawa tsakanin al'ummomi yana da

mahimmanci, musamman idan za a yi shi akan ka'ida saboda a

samu zuwa hakika, kuma a samu tsayar da ta'addanci babu gaira

babu dalili, kuma muna tabbatar musu da cewa fahimtar juna zai

yiwu, idan za a lizimci adalci.

Lalle cigaban turai a yau baya nuna cewa daga wurin su

abin yake, a a, cikaban al'ummomi suka tara a wuri daya (daga

ciki har akwai Musulmi) sai dai yanzu suna kokarin ninawa

dunuya a su kadai ke da shi, kuma suna hana Musulmi duk wani

abun da zai sa su su cigaba, sai su shagala da fadace-fadacen da

su suke kunna su. (su kuma sai su yi gaba)

Tuntuben da muke samu wurin cigaba da kere-kere saboba

wasu dalilai, ya sha bamban da abin da muke kai a da, kuma

wannan tuntuben ba ya nuna wai an barmu a baya, a wurin

cigaba da halaye masu kyau, mun mallaki abu mai yawa na daga

al'adu da halaye masu kyau, da mabubbugan shiriya da haske,

kuma ba zai yuwu mu yi wasa da su ba, ko mu bar kiran mutane

zuwa ga wannan hasken.

Muna kiran ku da ku sake waiwaya baya game da finkarfin

da kuke yiwa mutane cikin al'adunsu, kuma muna kara fadawa

manyansu, su lizimci adalci game da Musulunci da al'adunsa

masu girma, da kuma aikin da yakewa dan adam tun da har

yanzu.

Zai iya yiwuwa halin da muke samu kanmu a ciki yanzu

mawuyacin hali ne, amma tushen akidarmu da shari'armu da

halayenmu har yanzu masu kyau ne, kuma sun dace da duk wani

zamani ko wani wuri. Idan muna ganin turai sun cigaba a zahiri,

amma tushen cigaban na su ba shi da amfani ga dan adam kome

zawon zamani, muna kara fada muku cewa duk da cewa akwai

wasu aiboba a tare da mu a halin yanzun, amma duk da haka ba

zai sa mu kasa ganin mahimmanci al'dunmu da addininmu ga

dan adam, kuma muna kiranku da babban murya kuma manyan

turai, da ku masu yakin Musulunci a madadin sauran mutane,

muna son ku kiyaye wadannan abubuwa kamar haka:

NA DAYA: Ku bar zaluntar mu, da yi mana shishshigi a

lamurranmu, ko yi mana ta'addanci kan huruminmu, saboda

١٢

wadannan abubuwa zasu cutar da ku ta bangaren kasuwancinku

a kasashenmu, kuma hakan ba zai yiwu ba sai kun yiwa kanku

adalci.

NA BIYU: Muna kiran ku da ku taya mu fada da abin da 'yan

jarida suke bazawa na batunci a kanmu, ko taba Alkur'aninmu,

ko Manzonmu (S.A.W) amma idan sun cigaba da hakan, to

muna zamu dauki mataki akan abin.

NA UKU: Ku yi kokari wurin karantar sabubban da suka sa

tsamin alaka tsakaninmu, maimakon kokarin mamaye mu da

bangaren siyasa da kasuwanci da harkan soji, kuma ku tsaya ku

fahinci sakon da a ka aiko Annabi Muhammad (S.A.W) kuma

ku bude zukatanku ku fahinci Musuluncinmu cewa ya dace da

duk duniya, kuma ku fahinci hakikanin addininmu da al'adunmu

fafin ku yake mu, ko ku tare mutane wurin karban sa.

NA HUDU: Lalle shuwagabannin turai su yi kokin gyra aibobin

da suke cikin al'adunsu na yanzu kafin su ce zasu gyara na wasu:

hakika turai suna bukatar gyara da gaske, wannan ya fi da

wannan kokarin da suke yi wurin sai sun canza duniyar

Musulmi. Lalle ne idan ba hakan suka yi ba, to suna dab da su

fada wani rami mai zurfi wanda zasu kasa fitowa, idan dai sun

ce zasu cigaba da zaluci, saboda duk wadannan aibobin zasu

koma kansu ne su da masu taimaka musu su hallaka su. Lalle

muna kira zuwa ga shuwagabanninsu su yi kokin gyara halin da

kasashensu suke ciki, don su koma su bi hanyar Manzonnin

Allah, kuma su gimama su dukkan su, cira da amincin Allah su

tabbata a gare su, kuma su rinka taimako wadan da basu da laifi,

kuma su hana zalunci da cutarwa, aduk duniya ba a turai ba

kawai. Kuma muna sake kiran su da su gyra abin da ya shafi

aure da iyali da kamun kai, kafin su ce zasu gyra mu, kuma su

kare mutum daga ta'addancin kamfanoni da 'yan jari hujja, kuma

su girmama al'adun mutane kafin su kalli ribar da zasu ci, kuma

a yi kokari a dawo da kimar Malamai da karatu a duniya. Lalle

wannan abu ne da lokaci ya yi da a fara aikata shi, saboda rashin

addini yana kawo rushewar kome a duniya.

NA BIYAR: Wajibi ne turai su nemi afwa game da wulakancin

da suka yiwa Musulunci, haka kuma su nemi afwa game da duk

wani laifi da suka yiwa Musulmi lokacin mulkin mallaka da

١٣

kafin wannan lokacin da bayansa, kuma wajibi ne su san inda

zasu yi amfani da karfi a duniyar da al'adu sun sha bamban.

Amma sakonmu ga wanda ya dage sai ya yaki Musulunci

shi ne, lalle bai bar watsuwa ba saboda yakin da a ke yi ba shi

tun da, haka kuma ba zai bar yaduwa ba har sai Allah ya nade

kasarSa da wadan da suke kanta, kuma lalle wannan al'umma

zata iya dawowa da kaefinta bayan ta yi rauni, kamar yadda

kowa ya sani a tarihance

Mu kuma ba zamu takaita a kare huruninmu da addininmu

kawai ba, zamu mai da hankali wurin tunawa masu gaba da dan

adam asiri, kuma da sannu mutanen turai zasu gane cewa abin

da masu gaba da Musulunci suke yi cutar da turai yake yi fiye

da yadda yake cutar da Musulmi, kuma zai haranta musu fa'idan

tuwa da mutum biliyon daya da kwata, kuma suna da karfi

wurin yin ciniki a dunuya, kuma suma sun mallaki abubuwa

masu waya da ake takama da su a duniya. Kuma sun daurawa

kansu nauyin wanzar da adalci a duniya.

Lalle bude ido game da abin da turai ke da shi warin

cigaba baya nufin mutaru mu zama iri daya da su, mu bama son

bin turai rididi, ko waninsu, duk da haka bamu hana anfawa da

kere-kerensu ba, da amfanuwa da juna.

Lalle muna kira zuwa ga shuwagabannisu da su karanci

hakikanin Musulunci da Musulmi, dalilinmu a nan shi ne fadin

Allah Madaukakin Sarki, kuma da shi zamu rife wannan sako:

ﺎﺌﯿ ﺷ ﮫﺑ كﺮﺸﻧﻻو

ﷲا ﻻإ ﺪﺒﻌﻧ ﻻأ ﻢﻜﻨﯿﺑو ﺎﻨﻨﯿﺑ ءاﻮﺳ ﺔﻤﻠﻛ ﻰﻟإ اﻮﻟﺎﻌﺗ بﺎﺘﻜﻟا ﻞھأ ﺎﯾ ﻞﻗ"

لآ)"

نﻮﻤﻠﺴ ﻣ ﺎ ﻧﺄﺑ وﺪﮭ ﺷا اﻮ ﻟﻮﻘﻓ اﻮ ﻟﻮﺗ نﺈ ﻓ ﷲا نود ﻦ ﻣ ﺎﺑﺎﺑرأ ﺎﻀﻌﺑ ﺎﻨﻀﻌﺑ ﺬﺨﺘﯾ ﻻو

( ٦٤ ناﺮﻤﻋ

Ma'ana: Ya ku mazuwa littafi! Ku taho zuwa wata kalma wadda

zamu yi dai-dai da ku, kar mu bautawa kowa sai Allah, kuma ba

za mu hada shi da wani abu ba,

kuma sashinmu ba zai riki sashi iyayen gida ba Allah ba, to idan

suka bada baya, to ku fadi lalle mu mun shaida lalle mu

Musulmi ne. (Al Imran 64)

Hooray! Your file is uploaded and ready to be published.

Saved successfully!

Ooh no, something went wrong!