11.01.2013 Views

مﻮﻴﻟا ﻢﻜﻴﻠﻋ ﺐﻳﺮﺜﺗ ﻻ

مﻮﻴﻟا ﻢﻜﻴﻠﻋ ﺐﻳﺮﺜﺗ ﻻ

مﻮﻴﻟا ﻢﻜﻴﻠﻋ ﺐﻳﺮﺜﺗ ﻻ

SHOW MORE
SHOW LESS

You also want an ePaper? Increase the reach of your titles

YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.

JAWABI WAJEN BIKIN AURE

A yau, mun hadu a walimar auren Dr. Zahoor da amaryar sa Asma Rizvi. Ina taya

ku murna da sauran jama'ar da suka hallara a wannan wuri. A koda yaushe

muna fatan irin wannan haduwa wadda zata tattara abokai da 'yan uwa da kuma

abokan aiki daga kasashe da kuma addinai dabam-daban, domin ba karamin jin

dadi bane kasancewar mu a wannan wuri, musulunci ya tsara ko kuma ya maida

irin wadannan shagulgula su kasance masu ma'anar gaske.

Su dai Musulmi, mabiya tsari irin na Annabin Rahma Muhammad (sallallahu alaihi

wa sallam), kan fadakar da sabin ma'aurata, da kuma wadanda suka yi auren tun

tuni da ma masu son su yi aure nan gaba bisa hakkokin su ko kuma nauyin da ke

rataye a wuyan su. A na yin wannan ne kuwa domin ita rayuwar aure tana da

muhimmancin kwarai a wurin Allah SWT. Kai in muka yi dubi sosai cikin Al-

Qur'ani Mai Girma zamu ga cewa Allah SWT ya yi bayanin rayuwar aure da fadi

fiye da duk sauran nau'o'in ibada (bayan tauhidi). Nagartacciyar rayuwar iyali ita

ke gina al'umma ta gari, wannan kuma shi zai samar da nagartacciyar rayuwa a

cikin al'umma.

Da farko muna godiya ga Allah SWT wanda shine ya halatta aure.

Allah SWT ya fadi cewa :

�ﺎﻔﻴﻌﺿ نﺎﺴﻧﻹا ﻖﻠﺧ و�

Ma'ana: "Kuma an halitta mutum yana mai rauni" (An-Nisa: 28).

Idan aka ce a rayuwa kowa ya tsaya shi kadai (babu aure) har abada abin da

wuya ta bangarori da dama. Allah SWT bai kirkiri rayuwar aure kawai ba, amma

ya ma kwadaitar damu yi aure da a kan kari, domin shine hanya nagartacciya

tabbatacciyar da zamu iya kare rauni irin na dan Adam. Ta wannan hanya ne

mutane biyu daban da suka fito daga wuri daban za su amince wa junan su ta

hanyar soyayya da mutunta juna su zauna tare. Allah SWT da ya halatta yin aure

bai bar mu kara zube ba, ya bayyana yadda za a cimma nasara a rayuwar aure

kamar yadda ya fada a Suratur-Rum aya ta 21:

ةدﻮﻣ ﻢﻜﻨﻴﺑ ﻞﻌﺟ و ﺎﻬﻴﻟإ اﻮﻨﻜﺴﺘﻟ ﺎﺟاوزأ ﻢﻜﺴﻔﻧأ ﻦﻣ ﻢﻜﻟ ﻖﻠﺧ نأ ﻪﺗﺎﻳﺁ ﻦﻣ و

. نوﺮﻜﻔﺘﻳ مﻮﻘﻟ تﺎﻳﻵ ﻚﻟاذ ﻲﻓ نإ ﺔﻤﺣر و

Ma'ana:

"Yana daga ayoyin sa (Allah SWT): (shine yadda) ya halitta maku matan aure

daga kan ku domin ku sami natsuwa daga gare su kuma ya sanya soyayya da

rahama a tsakanin ku, hakika a cikin wannan akwai ayoyi ga (mutane) masu

tunani"

A nan manufar yin aure shine samun kwanciyar hankali da jin dadi da darajta

juna.

Wannan zaman lafiya ba zai samu ba sai ta hanyar soyayya ta hakika tsakanin

ma'aurata, daga kowa ne daya daga cikinsu zuwa dayan, ba wai daga bangare

daya kawai ba. A wannan ayar da ta gabata, kalmomi guda biyu an yi amfani da

su tare da juna domin bayyana wannan soyayya ta hakika a tsakanin ma'aurata.

Ta farko ita ce 'mawaddah' dayar kuma itace 'Rahmah', duka suna nufin soyayya,

malamai sun yin bayanin mawaddah ita ce soyayya dake wanzuwa a tsakanin

ma'aurata lokacin da suke a halin samartakarsu ko a lokacin farko na aurensu,

suna sha'awar junansu. Rahama ita ce so da jin-kai da mutunta juna da ke

wanzuwa bayan da ma'aurata suka tsufa. Duk da cewa ma'auratan na iya samun

aiwatar da abubuwan biyu lokaci guda a tsawon rayuwar aurensu.

A yanzu, ina son zan yi bayanin hakkokin ma'aurata. Muna da hakkoki iri biyu,

akwai hakkoki na mu'amala ta fuskar kasuwanci, wanda ake zaunawa a tsara

ka'idoji wanda idan aka sami wata matsala ana iya zuwa kotu domin a waware

matsalar, wanda yake da gaskiya a bashi wanda kuma yayi rashin-gaskiya ko cinamana

a hukunta shi. Akwai kumda hakkoki a tsakanin iyaye da 'ya'yan su, miji a

kan matar shi, mata a kan mijin ta, sa'annan hakkokin 'yan-uwa. Wadannan duka

basu cika sai idan akwai soyayya, kauna, biyayya, tausayi da sanin-ya-kamata. A

duk fadin duniya babu wani tsarin doka ko wani ma'auni da zai tantance mizanin

da zai gwada yadda wani zai nuna soyayyarsa da kauna da sanin-ya kamatar sa.

A mutum na iya yin wadannan abubuwa da aka zayyana a baya ta hanyar tsoron

Allah da ranar karshe. Wannan ne ya sanya mason tsira Muhammad (sallallahu

alaihi wa sallam) yake huduba yana cewa "ku ji tsoron Allah".

Ku ji tsoron Allah a dukkkan al'amuran ku, wannan ita ma tunatarwa ce , tunda

wadansu ayoyin Al'qur'ani mai girma suna fassara wasu ne. manzon Allah SAW

yana kasanecewa yana bayanin aya ta farko a cikin Suratun- nisa'I:

ﺎ�ﻬﺟوز ﺎﻬﻨﻣ ﻖﻠﺧ و ةﺪﺣاو ﺲﻔﻧ ﻦﻣ ﻢﻜﻘﻠﺧ يﺬﻟا ﻢﻜﺑر اﻮﻘﺘﻟا سﺎﻨﻟا ﺎﻬﻳأ ﺎﻳ

نإ مﺎ�ﺣرﻷاو

ﻪ�ﺑ نﻮﻟءﺎ�ﺴﺗ يﺬﻟا ﷲا اﻮﻘﺘﻟا و ءﺎﺴﻧ و اﺮﻴﺜآ ﻻﺎﺟر ﺎﻤﻬﻨﻣ ﺚﺑ و

Ma'ana:

ﺎﺒﻴﻗر ﻢﻜﻴﻠﻋ نﺎآ ﷲا

Ya ku mutane ku bi uban-gijin ku da takawa, (wannan) da ya halitta ku daga rai

guda (daya), kuma ya halicci matarsa (shi rayin) daga gare shi, kuma ya halicci

maza da mata masu yawa daga gare su. Ku ji tsoron Allah SWT wanda kuke

rokon juna da sunansa (ku kuma ji tsoron Allah cikin hakkin) zumunta

tsakaninku). Allah SWT ya kasance Mai tsaro ne a kanku.

Me ya sa zamu ji tsoron Allah? Amsar wannan tambaya ita ce : shine ya halicce

mu kuma rayuwar mu duka a hannun shi take. Allah ya fada a cikin Suratul-Insan

aya ta 1 cewa :

ارﻮآﺬﻣ ﺎﺌﻴﺷ ﻦﻜﻳ ﻢﻟ ﺮهﺪﻟا ﻦﻣ ﻦﻴﺣ

نﺎﺴﻧﻹا ﻰﻠﻋ ﻰﺗأ ﻞه

Ma'ana :

«Lallai ne wani tsawon lokaci ya kasancewa dan Adam (wadda a cikin

shi) bai kasance wani abin ambato ba»

Idan ya kasance mutum shekararsa ashirin da haihuwa, waye zai san shi shekara

ashirin da biyar da suka wuce. Hatta iyayensa ma basu san shi ba, Allah SWT

shine ya halicce shi.

Allah SWT ba mahalicci ne ba kadai, duk wani abu da muka ci da kuma wanda

muka samu shi ne ya bamu, anan duk wata biyyaya da girmamawa ga Allah ta ke

SWT, ba shi da abokin tarayya .

Da Allah ya ga dama, da ya halicce mu ta hanyoyi dabam-daban, amma sai ya

halicce mu ta hanyar mutum daya (Adam) domin ya nuna mana ya kuma tunatar

da mu cewa mu fa al'uma daya ne, a nan wadanda su ka kasance a wannan

faffadar al'ummar ya kasance dole su nunawa junan su soyayya da kauna da

mutunta juna. Anan musulunci yana koya mana 'yan uwantaka. Babu wani addini

da ya nuna 'yan uwantaka da juna kamar addinin musulunci.

A nan za mu yi bayanin matsayin ma'aurata da hakkokin da ke rataye a kan su ta

hanyar Al-Kur'ani mai girma da hadisan Annabin rahma, Muhammad (sallallahu

alaihi wa sallam).

Allah SWT ya ce a cikin suratun-Nisa'I aya ta 34:

Ma'ana : «Maza sune shuwagabanni akan mata»

ءﺎﺴﻨﻟا ﻰﻠﻋ نﻮﻣاﻮﻗ لﺎﺟﺮﻟا �

Wannan ayar wani lokaci ana yi mata rashin fahimta saboda ana mantawa da

wasu ayoyin da suka yi bayani akan aure. Misali anan ba a ce ba maza su zama

masu tsauri, saboda an basu iko akan matan su, Allah SWT cewa yayi

«ku zauna da su (matan ku) a cikin kyautatawa».

Dole mu zauna da matan mu cikin kyautatawa da mutuntawa. Allah SWT ya fada

a cikin Suratul Baqara aya ta 233 cewa:

�روﺎﺸﺗو

ﺎﻤﻬﻨﻣ ضاﺮﺗ ﻦﻋ�

«… a kan yardatayya daga garesu da shawartar juna", kaga ke nan Allah

yana umartarmu da tuntubar matanmu a harkokin gida da zamantakewar iyali.

Shawarwari a musulunci suna da matukar muhimmanci, don haka wajibi ne mu yi

amfani da ita a sha'anin iyalin mu. Babu bambancin hakkoki a takanin na-miji da

mace. Allah SWT ya fada a cikin a cikin suratul Baqara aya ta 228

�ﻦﻬﻴﻠﻋ

يﺬﻟا ﻞﺜﻣ ﻦﻬﻟ و�

«(Mata) suna da hakki a kan ku irin wanda kuma kuke da shi akan su»

Kowa yana da matsayinsa, na-miji shi ya kamata yayi ayyuka irin na maza, haka

nan mace ita ya fi cancanta ta yi ayyuka irin na mace. Yaya ko za a ce wanda ya

halicce mu bai san wadannan hakkoki ba, alhali kuwa shi ne ya shimfida su?

Don haka muna ganin na-miji shi ne shugaba ga matarsa, kuma shi ne mai

jibintar al'amuranta, amma ya rika yin shawara da ita kuma ya rika mutunta ta a

ko da yaushe. Na miji na iya fadawa rikici in ya yi gurgun hukunci, domin abin na

iya komowa kansa. Don haka za a kama shi da laifi a nan duniya da kuma ranar

gobe kiyama.

Na yi gargadi da jawo hankali ga mazaje, a yanzu kuma zamu ga mataye.

Wacece mace ta gari? Allah SWT ya fada a suratun Nisa'I aya ta 34 cewa:

ﷲا ﻆﻔﺣ ﺎﻤﺑ ﺐﻴﻐﻠﻟ تﺎﻈﻓﺎﺣ تﺎﺘﻧﺎﻗ تﺎﺤﻟﺎﺼﻟﺎﻓ�

Ma'ana; Mata na-gari masu da'a ne (ga Allah da kuma mazajensu), masu tsare

kan su ne a lokacin da mijin su baya nan (kuma suna tsare masu dukiyoyin su).

A nan dukiya ana nufin kaddarorinsa da kuma 'ya'yansa. A nan tarbiyyar 'ya'ya

tana da matukar muhimmaci kuma wanda yake da wahala. Allah yace zai

taimakawa dukkan macen da ta sauke wannan nauyi matukar tayi kokari. Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) yayi bayani wannan aya cewa " mace tagari

ita ce wacce idan mijin ta ya gan ta za ta faranta masa rai, idan ya yi mata

umarnin sai ta yi masa biyayya idan kuma baya nana sai ta kare kanta da kuma

dukiyoyinsa".

Sha'anin rayuwa ba ya yiyuwa sai an sami gargada. To idan ya kasance an sami

sabani (tsakanin mata da miji) sai Allah SWT ya ce :

�ىﻮﻘﺘﻠﻟ

بﺮﻗأ اﻮﻔﻌﺗ نأ و�

Ma'ana : >

Idan ka yafe ai ba asara kayi ba, sai ka ci nasara, saboda haka kada ku kasance

masu wulakanci ga junan ku, kada ku kasance masu zargin juna, Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya fadawa sahabbansa cewa: "Kada ku

zagi iyayen ku" sahabbai suka ce ta yaya zamu zagi iyayen mu ? sai manzon

Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yace idan ka zagi iyayen wani shima sai ya zagi

naka.

Saboda gudun irin wannan fito-na-fito Al-Qur'ani mai girma ya nuna mana cewa

mu yafe kuma kada mu manta da kyautatawa da kuma godewa juna. Allah SWT

yace :

�ﻢﻜﻨﻴﺑ

ﻞﻀﻔﻟا اوﻮﺴﻨﺗﻻو�

Ma'ana :

Kada ku manta da falala a tsakanin ku>>

Allah SWT ya wasafta mutunta juna tsakanin ma'aurata a cikin Suratul Baqarah

ayah ta 187:

�ﻦﻬﻟ

سﺎﺒﻟ ﻢﺘﻧأو ﻢﻜﻟ سﺎﺒﻟ ﻦه�

Ma'ana: "Su (matanku) tufafi ne a gare ku, kuma tufafi ne a gare su". Allah ya yi

amfani da wani misali mai kyau don bayanin wannan dangantaka.

To a nan zan tambaye ku.. meye amfanin tufafi ? yana kare mu daga zafin rana,

sanyi, kura, da dai sauran su, a nan ma'aurata kariya ne ga junan su kuma

garkuwa ne ga juna. Tufafi suna kare mana illa daga muhimman wurare a jikin

mu, haka nan ma'aurata za su kare illoli da matsalolin juna ba wai kawai a tafi a

fallasa wajen 'yan uwa da abokai ga matsalar abokin zama ba.

Tufafi suna karawa mutum kyau da kawa ta jan hankali, haka nan ma ma'aurata

ke karawa junan su kyau da kawa, su yi ado wanda ya amsa sunansa domin

juna, amma ba a yi ado saboda zuwa wajen biki ko suna ba. Misali ba a son maza

su yi shiga ta banza maras ma'ana a gidan su, haka nan kuma mata. Ana so

kuma halayen kowa daga cikinsu su zama tamkar madubi ne na halayen

danuwansa. Misali idan mace bata da halayya ta gari to fa tana gwada irin

halayyar mijinta ne, haka nan kuma shi ma mijin.

Abu na kusa da na karshe, su tufafi sune kusa da jiki fiye da komai, haka nan

ma'aurata suna kusa da junan su fiye da kowa, sun san sirrin junan su. Don

haka lallai su kare sirrin junan su, ba daidai bane mace ta kasance

kusancinta da 'yan uwanta ya fi kusancinta da mijinta, ko kuma miji ya

kasance kusancinsa da 'yan uwansa ya fi kusancinsa ta matarsa. Babu

wata kalma a wani littafi a duk duniya banda Al-Qur'ani mai girma wanda yayi

kammalallen bayani akan hakkokin ma'aurata kamar wannan ayar :

Ma'ana :

" Su (matan ku) tufafi ne a gare ku, kuma tufafi ne a gare su"

�ﻦﻬﻟ

سﺎﺒﻟ ﻢﺘﻧأ و ﻢﻜﻟ سﺎﺒﻟ ﻦه�

Ina addu'a ga Allah SWT ya shiryar damu mu gane mu yi amfani da abinda muka

ji a rayuwar mu, ina yiwa ango da amarya fatan Alheri, kuma ina taya su murna

da iyayen su da 'yan uwan su da abokan su.

Allah SWT ya ce a Suratul Hashri :

GAISUWA A MUSULUNCI

ﺰ�ﻳﺰﻌﻟا ﻦﻤﻴ�ﻬﻤﻟا ﻦﻣﺆ�ﻤﻟا مﻼ�ﺴﻟا سوﺪ�ﻘﻟا ﻚ�ﻠﻤﻟا ﻮ�ه ﻻإ ﻪ�ﻟإ ﻵ يﺬ�ﻟا ﷲا ﻮه

�نﻮآﺮﺸﻳ

ﺎﻤﻋ ﷲا نﺎﺤﺒﺳ ﺮﺒﻜﺘﻤﻟا

رﺎﺒﺠﻟا

Ma'ana :

A wannan ayar, kalmar 'As-Salam' tana daya daga cikin sunayen Allah

madaukaka (Asma'ullahil Husna), za mu yi kokari mu fahimci ma'anarta, dalilai

da kuma amfanin kalmar salam.

Kafin bayyanar musulunci, larabawa sun kasance suna gaishe da junan su da

kalmar "Allah ya barka" sai musulunci ya kawo sabuwar gaisuwa: Assalamu

Alaikum" , ma'ana: ina fata ka kasance cikin tsari daga dukkan wani bakin-ciki

kon kunci, wahalhalu da kuma tsiya. Ibnul Arabi yace (Ahkamul Qur'an) "ita

kalmar as salam tana daya daga siffofin Allah kuma tana nufin Allah shine mai

tsaron ka .

Wannan gaisuwa ta musulunci ta fin irin gaisuwar soyayya wadda wadansu

kasashe ke amfani da ita saboda wadannan dalilai:-

1) Ba wai kawai an ambaci soyayya bane kadai,a'a, an bayyana manufar

soyayyar ne a yanayin addu'a, ana fatan ka tsaru daga bakin-ciki, wannan

addu'ar bata rayuwar ba ce kadai kamar yadda larabawa ke fadi, a'a rayuwar

wadata wadda take ita ce mafificiya.

2) Kuma tana tunatar da mu cewa mu dogara ga Allah SWT babu wanda zai cutar

da mu ko ya amfanar da mu sai Allah ya yarda. Haka nan wata irin ibada wadda

take tunatar da musulmi Allah.

3) Ka sani idan wani yayi maka addu'ar ka kasance cikin salama, yana

tabbatarwa da yin alkawalin cewa ka tsira daga hannun shi da kuma harshen shi,

kuma zai mutunta ka da daratta ka da mutunta ka.

A cikin littafin Ahkamul qur'an, Ibnul Arabi ya ce " ka san ko menene 'salam'? mai

maganar ya na sanarwar cewa ka tsira kwata-kwata daga duk wata cutarwa daga

gare ni.

A takaice, 'Salam' ita ce :-

i) Tunawa da Allah.

ii) Tunatarwa

iii) bayyana soyayya a tsakanin musulmi

iv) addu'a madaukakiya.

v) hakikan da sanarwar cewa ka tsira daga hannaye na da kuma harshe na.

Hadisi yayi bayani gaba-daya:-

"Musulmi na gari shine wanda baya cutar da wani musulmi da hannun shi ko da

harshen shi".

Idan muka fahimci wannan Hadisin kadai ya isa ya shiryar da al'ummar musulm.

Shi ne ya sa Annabi Muhammadu (sallallahu alaihi wa sallam) yake jaddada

muhimmancin yin sallama a tsakanin kuma ya kuma kira ta mafificiya a cikin

ayyuka na gari da kuke yi.

A karbo Hadisi daga Abu hurairah RA ya ce : Manzon Allah (sallallahu alaihi wa

sallam) ya ce " Ba za ku shiga aljanna ba sai kun zamo muminai, ba kuma za ku

zamo muminai ba har sai kun so junan ku, bari in fada maku wani abu wanda

idan ku ka yi shi zai kara soyayya a tsakanin ku: ku yawaita yin sallama ga

mutumin da ka sani da ma wanda ba ka sanin ba."

Abdullahi bn Umar ya ce: wani mutum ya tambayi Manzon Allah (sallallahu alaihi

wa sallam) wadanne ayyuka ne su ka fi a musulunci? Sai Manzon Allah (sallallahu

alaihi wa sallam) ya ba amsa mashi da cewa : Ka ciyar da mutane abinci sannan

ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba."

Abdullahi bn Mas'ud ya ce: Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce "

Kalmar 'Salam' tana daya daga cikin sunayen Allah wanda ya saukar a duniya son

haka mu yawaita yin sallama". Idan wani ya yiwa wani sallama darajar shi ta

karu a wurin Allah, idan a taron jama'a babu wanda ya amsa mashi sallama, to

wata halitta wadda ta fi su (wato mala'iku) za ta amsa mashi sallamar.

Abu hurairah ya ce : Babban marowaci shine wanda yake yin rowa wajen yin

sallama.

A cikin Alqur'ani mai girma, suraun Nisa'I aya ta 86, Allah SWT ya ce :

Ma'ana :

A nan Allah SWT yace ku amsa sallama kamar yadda aka yi ko kuma da wasu

kalmomi wadanda suka fi wannan. Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya

nuna wannan kamar yadda ya zo a ibnu Jareer da Ibn abi Haatim cewa: wata

rana Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yana zaune tare da sahabban shi sai

wani mutum ya zo ya ce "Assalamu alaikum" sai Manzon Allah (sallallahu alaihi

wa sallam) ya amsa mashi kamar haka : wa alaikumus salaam wa rahmatullahi",

sai wani mutum na biyu ya zo ya ce " Assalmu alaikum wa rahmatullah" sai

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya amsa mashi kamar haka : wa

alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakatuhu", nan take sai wani mutum na

uku ya zo ya ce : Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh" sai Mnzon

Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya amsa ma shi da cewa : "wa alaika". Mutumin

na uku ya ce ya Manzon Allah da suka gaishe ka a takaiace ka amsa masu da

kalmomi wadanda suka fi, ni kuma na gaishe ka da cikakkiyar gaisuwa na yi

mamaki da ka amsa mani da takaitacciya ka ce ' wa alaika'! Manzon Allah

(sallallahu alaihi wa sallam) ya amsa cewar : baka bar wani wuri da za a yi kari

ba. Wannan ne ya say a maida maka sallama domin in cika ka'idar da Allah ya

tsara a Alqur'ani.

A takaice anan mayar da sallama a cikin matakan nan guda uku sunnah ce ko

kuma muce hanya ce ta Annabi Muhammadu (sallallahu alaihi wa sallam). An

kayyade yin sallama a wannan matakai guda uku domin ta zama takaitaccen sako

bai I don bayani ba.

A wannan aya Allah SWT yayi amfani da karkarfan karshe ba tare da bayyana

maudhu'I ba.

A nan Alqur'ani mai girma ya koya mana yadda ake amsa sallama, a fakaice yana

umurtar mu da mu yi sallama ga junan mu, wannan yana nuna mana ya zamana

halayya da al'adar mu, kuma yau da kullum muminai su rika gaishe da juna da

sallama, kamar yadda aka ambata a baya wanda ya fara yin sallama shine wanda

yake kusa da Allah SWT. Hassan Albsri ya ce yin sallama ba wajibi bane amma

amsa ta wajibi ne.

Ya zo a cikin Almuwatta na Al imam Malik wanda aka samo daga Tufail bin Ubayy

bin Ka'b cewa Abdullah bn Umar ya kasance yana zuwa kasuwa domin yayi

sallama ga mutane ba don ya sayo ko ya sayar da komai ba, domin ya fahimci

amfanin fara yin sallama.

A karshe, aya ta 86 a cikin suratun Nisa'I, Allah SWT ya ce " Allah ya na lissafe da

komai"

A nan kuma, fara yi da kuma amsa sallama duk an shigo da su do haka mu so

mu fara yin sallama kuma mu amsa sallama domin mu kyautatawa Allah SWT

kuma mu sanya soyayya a tsakanin mu.

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya fadakar da cewa;-

- wanda yake akan abin hawa ya yiwa wanda yake a kasa sallama.

- wanda yake tafiya ya yiwa wanda yake zaune.

- mutane kadan su yiwa mutane wadanda suke da yawa sallama.

- wanda zai tafi ya yiwa wanda su ke tsaye sallama.

- idan za ka bar gida ko shiga gida ka yi sallama ko da babu kowa, domin

mala'iku za su amsa.

-idan kuna yawan haduwa ku yawaita yin sallama.

HALIN DA BA A AMSA SALLAMA

- a lokacin da ka ke yin sallah, idan har ka amsa sallama to sallar ka ta abaci.

- mai huduba, mutumin da ke karatun Alqur'ani, ko kiran sallah ko tada iqama,

ko koyar da littafan musulunci.

- ko kana zaune a dakin wanka.

Allah SWT yayi bayanin falalar yin sallama a suratul An'aam aya ta 54.

A nan Allah yana ilmantar da Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) a

kan muhimmancin wadanda suke talakawa wadanda suke a koda yaushe tare da

shi, koda yake masu arzikin daga cikin wadanda ba suyi imani ba sun so Manzon

Allah ya kori wadannan matalauta domin masu arziki su kasance taer da shi.

Allah SWT ya umarci Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yayi wa wadannan

talakawa muminai Magana ya ce 'Assalamu alaikum'da zaran sun zo, wannan

kuma tana nufin abu biyu: na farko ya isar da gaisuwar Allah a gare su, kuma

wani abu na girmamawa da mutuntawa ga mutanen da suke talakawa kuma

musulmai na gari, wannan zai kara karfafa zuciyar su da imanin su. Abu na biyu

zai isar masu da labari mai dadi cewa da ikon Allah za su kasance cikin jin dadi,

salama da kuma aminci ko da kuwa sun aikata wasu kusakura.

Ya Allah SWT ka bamu ikon yin gaisuwa cikin tafarki na musulunci a halin

rayuwar mu, wajen yin wannan ka sanya soyayya da hadin kai a tsakanin mu,

Ameen.

TAQAWA

Allah SWT ya ce a cikin suratu Aal Imran, aya ta 133:

Ma'ana :

a gaba sai Allah ya yayi bayani akan wadanda su ke a imani na gaskiya, sai yace

Ma'ana :

Bari mu fahmci menene Taqwa.. Taqwa tana da matakai guda uku : idan mutum

ya tsare kan shi daga kafirci da kuma hada Allah da wani a wurin bauta, wannan

shine musulmin na gari, a nan duk wanda yayi imani mumini ne koda kuwa yana

aikata zunubi. Wanda duk ya nisanta kanshi daga abinda Allah SWT da Manzon

shi (sallallahu alaihi wa sallam) su ka yi hani, to wannan yana da kololuwar

Taqawa. A karshe, idan mutum yana son Allah ya so shi a ko yaushe, wannan ma

ya na da kololuwar Taqawa. Allah yayi bayani a cikin suratu Aal Imran, aya ta

102 cewa:

Ma'ana :

Allah SWT ya yi bayanin alamomin musulmi na gari: sune su ke ciyarwa ta

hanyar Allah, a misali idan suna da Naira dubu suna iya bayar da mafi kankanta

(Naira daya), ciyarwa ta hanyar Allah shine tsarin rayuwar su,

Allah zai cire su daga kangi saboda wannan kyaukyawan aiki. Har-ila-yau, mutum

wanda ya ke son taimakon jama'a ba zai handame dukiyaer mutane ba, ya fi son

ya yi wa mutane abu mai kyau. A'isha RA ta taba bayar da kwayar dabino daya

sadaka tun da bara da komai.wasu mutanen kirki suna bada albasa daya sadaka.

Annbi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce " ka kare kanka daga wuta

koda kwaya daya ne, kada ka bar mabukaci ya tafi hannhn shi haka nan.. ka

bashi ko da takon akuya ne idan shin kadai ya rage.

An yi bayani a cikin At-tafseer Al-Kabeer na Al imam Ar raazi cewa wata rana

Annabi Muhammadu (sallallahu alaihi wa sallam) yayi kira mutane su bada

sadaka, sai wadan su suka kawo zinare da azurfa, wani ya kawo sanhon dabino

ya ce bani da sauran wani abu , wani mutum ya ce wa Annabi (sallallahu alaihi

wa sallam) ba ni da abin da zan bada sadaka! Yace na bada sadaka da imani na,

idan har wani ya ci mani mutunci ko ya ba ta mani rai tko ba znn yi hushi ba". A

nan mun gain ko da talakawa suna ciyarwa da dan abinda ke garesu son su

taimakawa wasu a lokacin Annabi (sallallahu alaihi wa sallam).

A wannan ayar ba a kayyade ciyarwa ba. Yin abu domin Allah ba ana nufin kadai

yin amfani da dukiya ba, har ma da lokacin ka da basirar da Allah ya baka. Akwai

wata hikima da aka ce muminai suna ciyarwa a huce (a lokacin da suke a

yalwace), saboda yawancin mutane suna mantawa da Allah a lokacin da suke a

cikin yalwa. Sun mance da Allah saboda suna damuwa da abubuwan da suka

sanya a gaba.

Wani baitin waka da aka yi da yaren 'Urdu' yana cewa:

' Kada ka dauki mutum mai ilmi ne wanda yake mantawa da Allah idan yana cikin

samu, baya jin tsoron Allah idan ran shi ya ba ci'.

Allah SWT ya ce alama ta biyu ta muminai na gari ita ce suna kamewa daga bacin

ran su. Na uku ba wai kawai suna kamewa daga bacin-ran su ba, har-wa-yau su

na yafewa wanda ya bata masu rai har cikin zuciyar su, kuma suna kyautatawa

mutane 'yan uwan su. A wajen bayanin wannan ayar Al Imam Al baihaqi RA ya

kawo wani al'amari da ya afku cewa : wani lokaci Ali bn Ahussain RTA yana yin

alwala wani bawan shi ya na zubo mashi ruwa a hannun shi da wani mazubi,

wannan mazubin ruwa sai ya kubuce daga hannun bawan nan ya fada a kan Ali

sai bawan ya fahinci ran shi ya baci a fuskar Ali, bawan nan yana da wayo sai ya

rika karanta ayar nan a hankali- a- hankali ya karanta cewa muminai na gari

sune masu boye hushin su, sai Ali ya hadiye bacin ran shi, da bawan ya karanta

cewa sune masu yafewa idan an yi masu laifi sai Ali ya ce na yafe maka, da ya

karanta cewa Allah ya na son maso kyautatawa sai Ali ya ce na 'yanta ka!.

Yafewa wanda yayi maka wani laifi yana da sakamako babba a ranar tashin

kiyama. Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce Allah SWT zai yi kira ranar

tashin kiyama : wanda duk ke da wani a warin Allah ya tashi tsaye, a wannan

babu wanda zai mike sai masu yafewa wanda suka cuce su ko azabtar da su.

Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya sake cewa " wanda duk ke son

wata katafariyar fada a aljannar firdausi to yayi wadannan abubuwa:-

- Ya yafewa wanda ya azabtar da shi.

- Yayi kyauta ga wanda bai taba baka komai ba.

- Kada ya guji wanda da niyya ya yanke hulda da su.

Ba wai ba ya cikin tsari a tunatar da musulmi su rika musayar kyauta a tsakanin

su ba, ya kamata wannan ya kasance hali ne a gare su ba wai su takaice wata

rana kamar yadda arna ke yi a bukin kirsimeti da wasu shagulgula ba.

A nan Allah SWT yana nuna mana da kyau yadda za mu zauna da manyan

makiyan mu- suratu Fussilat aya ta 34.

Ma'ana :

Wata rana wani mutum ya ci zarafin Abu Hanifa RA, sai Abu Hanifa bai ce da shi

komai ba, sai ya je gida ya tattaro kyaututtuka ya baiwa wannan mutum ya gode

mashi yadda ya yi mashi ya ce " kayi mani alfarma da ka dauki ayyukan ka masu

kyau ka sanya cikin nawa sakamakon ta yadda ka ci mani fuska"

Allah SWT har-wa-yau ya ce , suratu Al Imraan aya ra 135-136 ya kara bada

haske a yadda muminai su ke :

Ma'ana :

Ka sani da cewa :

Gafara Allah SWT ta zarce shiga aljanna a wannan ayar, yana a fili karara shiga

aljanna yana cikin gafara da rahmar Allah SWT. Bai takaita ba a kan ayyukan mu

na sha'awa, ka sani matsayin aljanna ya fi duniya da sammai idan aka hada baki

daya. Kuma wata ma'anar wannan ayar shine girman aljanna ya fi sammai da

ﷲا

kassai da duk abinda ke ciki. Muna iya mamakin aljanna yaya tsawonta yake tun

a koda yaushe tsawao ya fi fadi. A karshe, wannan ayar tana nufin cewa aljanna

an tanade ta ne saboda muminai na gari, kamar yadda wasu sannannun

malaman musulunci suka fada cewa aljanna tana gaba da saman bakwai rayukan

wadanda suka yi shahada tuni suna cikin dausayin aljanna.

Allah SWT muna rokon ka ka bamu matsayi irin na muminai na gari, Ameen.

MUNAFUKAI

A farkon Al qurni mai girma, Allah SWT ya rarraba wannan al'umma zuwa kashi

uku, akwai mumunai, akwai kafirai, sa'annan akwai munafukai. Allah SWT yayi

bayani takaitacce a kan mumunai, kafirai kuma yayi baynin su a aya daya,

sa'annan yayi bayani mai tsawo akan munafukai saboda sune suka fi kowa hadari

a cikin al'umma. Ya dace mu fahimci halayen su da kuma makomar su.

Ya kamata a san cewa wannan karkasawa da aka yi wa al'uma an yi ta ne bisa

gwargwadon imanin mutane da kuma aikin su ba tare da lura da launi su ba, ko

kuma inda suka fito, ko yaren su, kasar su ko kuma yankin da suka fito ba.

Bari mu dubi halayyar munafukai kamar yadda aka siffanta su a aya ta 8 da ta 9

a cikin suratul Baqarah :

Ma'ana :

ka sani cewa duk da suna ikirarin sun yi imani da Allah da ranar lahira, to amma

babu maganar imani da annabcin Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam). Wannan shine aikin yahudawa a wancan lokaci. Don haka, duk wani

imani ba tare da imani da manzancin Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam) ba to ba karbabbe ne ba. Sun yi hasara, kuma ba su san aibnda suke yi

ba.

Ma'ana :

A nan, karya ba karamin zunubi ce ba, tana iya maida mumini ya koma munafiki.

Allah SWT ya bayyan karya tare da bautar gumaka a Alqur'ani mai girma:

Ma'ana :

Allah SWT yayi bayanin ababe guda uku da ke nuna munafukai; Baqarah, aya ta

11 da 12:

Ma'ana:

Na biyu, Allah SWT ya ce a aya ta 13 a suratul Baqarah;

Ma'ana :

A nan a bayyane yake cewa, jarrabawar imani na gaskiya shine kayi imani kamar

yadda sahabban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) suka yi. Allah SWT

yana girmama sahabban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) shine ya tsara

matakan da za a jarraba imani na gaskiya. Har-wa-yau, Allah SWT ya karrama

sahabbai a farkon ayar inda ya ce " munafukai suna kokarin su yaudari Allah da

wadanda suka yi imani (wato sahabbai)"

Allah SWT yayi bayanin mataki na uku dake nuna munafukai kamar haka:

Baqarah, aya 14,15,16:

Ma'ana:

نوءﺰﻬﺘ��ﺴﻣ

Ma'ana :

Akwai abubuwa da dama da ya kamata ayi bayanin su a nan, mun gani cewa

maza da mata wadanda suka yi imani an dauke su a matsayin daya a ladar da

za su samu saboda aikin su. Akwai haske a gaban su saboda an basu sakamakon

su a hannun dama. Al'ada ne ka sami fitila a gaban wanda ya ke a halin tafiya,

wannan haske dake gaban su ya sakamakon aiyukan su na gari.

Akwai Hadisai da dama daga bakin Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)

wadanda suka yi bayani akan hakan.

An karbo daga Anas RTA ya ce Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yayi

albishir ga wanda suke zuwa masallaci cikin duhu cewa za su sami wani irin haske

a ranar tashin kiyama. (Ibn Maajah ne ya ruwaito shi)

An karbo daga Ibn Umar cewa Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce "

wadanda suke yin sallah a akan lokacin ta a koda yaushe za su sami sakamakon

wani irin haske na shiriya a ranar tashin alkiyama, wadanda ba sa aikata hakan

ba za su wannan haske ba, za su kasance tare da Qaruna, da Hamana da

Fir'auna. ( Ahmad ya ruwaito shi a cikin Al Musnad)

An karbo daga Abu Sa'id cewa Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce "

duk wanda ya karanta Suratul Kahfi a ranar Juma'a zai sami haske na shiriya a

ranar tashin kiyama wanda zai tashin tun daga kafar sa har zuwa Aljanna". (At

tabarani ne ya ruwaito shi)

An karbo daga Abu Hurairah RA cewa Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)

ya ce " duk wanda ya karanta aya daya ta Al qur'ani za ta kasance mashi haske

na shiriya a ranar tashin alkiyama (Al imam Ahmad ne ya ruwaito shi)

An karbo daga Abu Hurairah RA cewa Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)

ya ce " duk wanda ya rokar mani aminci da salama zai sami haske a kan Siradi a

ranar lahira"

Haka nan ma duk wani aiki mai kyau zai zama haske ga muminai. Sabanin halin

da muminai suke a ciki a ranar lahira, Allah ya bayyana halin da munafukai za su

kasance a ciki. Allah SWT ya ce (suratul Hadeed, aya ta 13,14,15.

ﺬ�ﺧﺆﻳ ﻻ مﻮﻴﻟﺎ�ﻓ روﺮ�ﻐﻟا ﷲﺎ�ﺑ ﻢآﺮ�ﻏ و ﷲاﺮ�ﻣأ ءﺂ�ﺟ ﻰ�ﺘﺣ ﻲﻧﺎ�ﻣﻷا ﻢﻜﺗﺮﻏو ﻢﺘﺒﺗراو

ﺮﻴﺼﻤﻟا ﺲﺌﺑ و ﻢآﻻﻮﻣ ﻲه رﺎﻨﻟا ﻢآ ىوﺄﻣ اوﺮﻔآ ﻦﻳﺬﻟا ﻦﻣ ﻻ و ﺔﻳﺪﻓ ﻢﻜﻨﻣ >>

Ma'ana :

A ranar tashin kiyama munfukai maza d mata za su cewa mumunai ku jira mu

domin mu yi amfani da hasken ku, sai su ce da su ku koma ku samo haske. Za yi

bango tsakanin muminai da munafukai, a cikin wannan bango rahma ce ta Allah,

a bayan shi kuma azaba ce. Munafukaii za su cewa muminai (da karfi) " shin ba

mu kasance tare da ku (a duniya) ba? Sai muminai su ce " kwarai da gaske! Sai

dai ku kun fitini kawunan ku, kun yi shakku, kun gurace-guracen rayuwa sun

rude ku har sai da lamarin Allah ya zo, kuma mai rudarwa ya rude ku. Don haka

a yau ba za a karbi fansa daga gare ku ba, kuma ba za a karba daga wanda suka

kafircewa Allah ba, makomar ku ita ce wuta, ita ta fi dacewa da ku, makoma ta

munana.>>

Kamar yadda Ibn Katheer yace dukkan muminai da minafukai za a basu haske a

ranar tashin kiyama idan zasu tsallake siradi. Hasken munafukai za a bushe shi. A

cikin wannan hali zai masu ba'a ne kamar yadda suke yin ba'a da bayin da suke

yi ma shi biyayya. Allah SWT yace (suratul Baqarah aya ta 15)

Ma'ana :

Allah yana yi masu ba'a zai bar su a cikin batan su a dimauce >>

Ka sani cewa munafukai an ba su haske ne domin sun taba yin aiki na gari don su

yi riya (don a gani)

Muna iya yanke cewa aiki na kwarai yana iya kaiwa a kasance da dawwamamen

haske. Munafukai kuma za a yi masu izgili a ranar tashin kiyama. Ibn Katheer ya

ruwaito wani Hadisi mai tsawo inda aka ce mumunai za su sami hasken dai dai da

ayyukan su, wasu zasu sami haske kamar tsauni, wasu kamar tsawon iccen

goriba, wasu kuma kamar hasken kamar tsawon mutum.

Allah SWT ya ce a cikin suratul Hadeed aya ta 17

Ma'ana :

A nan Allah SWT yana tunatar da nu cewa zai raya kasa idan ta mutu kum zai

raya zukatan munafukai idan sun yi tuba na gaskiya, ina rokon Allah ya sa mu

zama musulmi na kwarai ya kuma ba mu haske na shiriya na dun-dun-dun a

ranar tashin kiyama.

BARZAKHU

Barzkhu wani lokaci ne tsakanin mutuwa a duniya da ranar da za a tayar da

mutane a ranar tashin alkiyama. Ba mu san ba abinda ke faruwa a wannan lokaci

sai dai za mu iya sani daga wadansu ayoyi na alqur'ani mai girma da Hadisan

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), misali Allah SWT ya ce a cikin suratul

An'am aya ta 93:

Ma'ana:

Ma'ana :

A nan ya nuna cewa mutanen fir'auna an jefa su cikin wuta yayin da aka nutsar

da su a a cikin ruwa, wannan ya nuna cewa akwai azabtarwa tun daga lokacin

mutuwa. Yana da ban-sha'awa ka fahimci cewa an ambaci azabar wuta tare da

nutsarwa a cikin ruwa. Al imam Ar raazi y ace " wannan hujja ce mai karfi akan

cewa akwai azabar barzkhu da kuma 'kabari" yayi nuni cewa kalmar "fa" a cikin

wannan ayar anyi amfani da ita ne don nuna cewa azabar wutar ta faru ne da

gaggawa bayan nutsewa a rowan, kuma wannan azabar ba ana nufin ita ce

azabar ranar tashin alkiyama ba.

Allah SWT ya ce a suratu Gaafir (aya ta 45-46) :

Ma'ana :

Wannan ayar tana nuna mana cewa akwai azaba a kabari ga wandanda suka

kafirce da kuma azabar da zata same bayan an yanke hukunci ranar tashin

alkiyama.

Abdullah dan Mas'ud yayi bayanin wannan ayar cewa rayukan mutanen fir'auna

za a kawo su kamar bakaken tsuntsaye safiya da marece zuwa wuta ana fada

masu "wannan shine karshen makomar ku"

Allah SWT ya ce a suratul Takathur (aya ta 1,2,3,4):

A karshe, Allah SWT ya fada a cikin Alqur'ani mai girma cewa: Duk wanda ya

manta dani to zan sanya rayuwar shi cikin kunci kuma zamu tashe shi a makaho

a ranar tashin kiyama "

Ibn Mas'ud RA da Abu Sa'id Al khudri RA sun ce ma'anar sanya rayuwar shi cikin

kunci na nufin azabar kabari. Haka kuma Abu Hurairah RA yace: Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce "abinda ake nufi da wannan shine

Allah SWT zai aiko macizai casa'in da tara (99) a kabarin wanda ya kafirce,

macijin zai dingi sarin shi har zuwa ranar tashin kiyama.

Me zai faru ga ran Dan Adam idan ya mutu?

An karbo daga Abu Hurairah cewa Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam) ya ce " idan ran mumini ya rabu da gangan jikin shi, Mala'iku buyu za su

dauke shi zuwa sama, sai Mala'ikun nan su ce " ran mumini ya zo daga duniya

sai su ce "Allah yayi ma gafara da jikin da ka yi amfani da shi", sai a gabatar da

wannan ran ga Allah SWT sai Allah SWT ya ce " ku sanya wannan ran a Sidratul

muntaha sai ranar tashin kiyama". Idan kuma aka zare ran kafiri daga gangan

jikin shi, sai Mala'iku su ce " mummunan rai ya zo daga duniya, sai Mala'iku su

rika tsine mashi, wurin da yake kuma sai ya dume da wari, Allah SWT sai ya bada

umurni a ajiye wannan ran a Sijjeen, Sijjeen wani wuri ne inda za a ajiye ran

kafirai.

Annabin rahama, Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya sanya rigar shi ya

rufe hancin shi ya na bayyana warin ran kafirai.

Akwai Hadisai da dama da suka nuna yadda zaman kabari ya ke.

An samo daga Anas RA ya ce : Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam)

yace "idan aka sanya mutum a kabari bayan mutuwar shi, idan 'yan uwan shi da

abokan shi sun bar makabartar zai rinka jin karar tafiyar su da sauran jama'a.

Mala'iku biyu za su zowa mutum a kabarin shi, Mala'ikun sai su tayar da shi

zaune sai su tambaye shi wadanan tambayoyi :-

Me ka sani game da Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ? Mumini sai ya

amsa : Na tabbata shi bawan Allah ne kuma manzon Allah ne. Sai Mala'kun su ce

mashi da baka yarda ba da makomar ka wutar jahannama ce, duba ka gani Allah

SWT ya canza ta da Aljanna, duba kuma ka gani. Har-wa-yau, Mala'iku za su

tambayi munafukai da kafirai : me kuka sani game da Muhammadu (sallallahu

alaihi wa sallam)? Sai su amsa : ni ban san komai ba ina fadar abinda mutane

suke fadi. Sai Mala'iku suce masu baka taba gwada yin imani da shi ba ko bin

wanda suka yi imani dashi. Sai Mala'ika ya buge shi da sandar karfe, zai yi kara

mai tsanani wanda duk wani abu mai rai zai ji shi banda aljanu da mutane. (

Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi)

Asma'u diyar Abubakar tace : wata rana Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam) ya yi huduba ga mutane yayi bayanin yadda azbar kabari take, da fadin

haka sai muminai suka yi ta kuka, wurin duk ya rude da kuka. (Bukhari ne ya

ruwaito shi)

Ibn Abbas RA yace Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya yi addu'a

kamar ayar Alqur'ani mai girma yace " Ya Allah ina neman tsarin ka daga azabar

wuta, da kuma azabar kabari da jarrabar rayuwa da jarrabar mutuwa, da

jarrabar Dajjal". (Muslim ne ya ruwaito shi)

Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) yace " karanta Suratul Mulk akai-a-kai

zai tsare mutum daga azabar kabari.(Tirmizi ne ya ruwaito shi)

Ina rokon Allah ya kare ni da mai karatu da mai sauraron wannan takaitaccen

bayani daga azabar wuta, kabari da kuma Dajjal, Ameen.

TASHIN KIYAMA

Yana da wuya kafiri ya amince cewa Allah SWT zai tayar da shi bayan mutuwar

shi a ranar tashi alkiyama. Suratul Waqi'ah (aya ta 47da 48) ta yi bayani :

Ma'ana :

daya. Tun da Allah SWT zai iya halittar mutune mabanbanta da junan su, me zai

hana iya tayar da matattu ya maida rayayyu?

A cikin suratun Nazi'aat (aya ta 27-28) Allah SWT ya kara fayyace hakan a

fili:

Allah SWT ya na yi mana bayani cewa yana da wuya ayi ginin sama ba tare da

wani matokari ba. Da za mu yi kokarin gano wani kuskure ko matsala a yadda

aka halicci sama, ba za mu iya ganowa ba, idanuwan mu har sun gaji ba tare da

mun gano wata matsala ko kuskure ba. To idan har Allah SWT zai halicci sama da

irin wannan tsarin da muke gani a kowane lokaci, menene abin wuya idan zai

tayar da mutum bayan ya mutu?

Allah SWT ya ce a cikin Suratur Rum (aya ta 50)

Dubi yadda alamomin rahmar Allah su ke, yadda yake rayar da kasa bayan

mutuwar ta. Lallai wanda yayi haka zai tayar da matacce, lallai shi mai iko ne a

kan komai>>

Wannan lamari an fayyace shi a bayyane a suratu Fussilat (aya ta 39):

Wannan wata muhimmiyar hujja ce ta yau da kullum wadda samari da tsofaffi da

masu arziki da talakawa, masu ilmin da jahilai ke gani. Ruwa yana sauka da iznin

Allah SWT, sai fako ya farfado a hankali ya samar da tsirrai da za su tashi akan

wannan fako. Wannan mashahurin al'amari mai ban mamaki yana nan har ma a

kewaye da gidajen mu mutane na duba kurum ba tare da suna dubar abinda ke

faruwa ba. Waye yake farfado da kasar nan? Mun manta waye yake bubbugo

tsirran nan har suke fitowa daga cikin fakon.

Duk wanda ya dubi wadannan ayoyi na Allah SWT da idon basira, ba zai sami

wata shakka ba a cikin zuciyar shi akan cewa Allah SWT zai tayar da mu a ranar

sakamako bayan mun mutu mun koma turbaya da kuma kasusuwa.

Akwai wadan su abubuwa guda biyu masu ban sha'awa da suka faru da aka

bayyana su a cikin Suratul Baqarah domin shiriyar mu. Da farko mu duba aya ta

259:

MA'ANA DA MANUFAR GASKIYA DA RIKION AMANA A MUSULUNCI

Allah SWT ya ce a Surat An Nisa'i (aya ta 58)

Masu masu tsare amana (da aka basu) da kuma alkawullan su. Sune masu

tsayuwa a kan shaida ta gaskiya. Sune masu dawwama akan yin Sallolin su.

Wadannan sune wadanda za a karrama su a gidan aljanna.>>

A nan, cika alkawali dayai yake da yin Sallah ingantacciya.

Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) har-ila-yau yace

ﺔﻧﺎﻣأ ﺲﻟﺎﺠﻤﻟا

" Haduwar mutane a wani wurin zama amana ne a tsakanin su" don haka duk

abinda aka fadi a wurin tarukan mutane baya kamata a fade shi ga wasu na waje.

Har-wa-yau, Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce " Duk wanda aka nemi

shawarar shi kamar an bashi rikon Amana ne, don haka lallai ne ya bayar da

shawara ta gari, kada yana kan sani ya bayar da mummunar shawara, yin haka

cin amana ne. haka kuma idan wani ya sanar da kai wanin sirrin shi kada ka

sanar da kowa ba tare da izinin shi ba.

Bari mu duba mu ga yadda sahabban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)

suka dauki wannan al'amari. Ka rike a kan ka cewa sahabban Manzon Allah

(sallallahu alaihi wa sallam) mutane ne kamar mu kuma su na iya yin kuskure

kamar kowa. A cikin Suratul Anfal, aya ta 27 Allah ya yi bayanin wani lamari, inda

ya ce:

daga wannan sansani ? sai Abu Lubabah ya sa yatsar shi a wuyan shi yana nuni

da cewa za a sare ma su kawuna ne. wannan wani sirri ne tsakanin Manzon Allah

da Abu Lubabah. Bayan da Abu Lubabah ya fahimci ya tafka kuskure sai ya ji ba

dadi, duk hankalin shi ya tashi, sai ya je ya daure kan shi a jikin wata itaciya.

Yana a cikin wannan hali har kwana bakwai, ya ce ba zai kwance kan shi ba sai

an karbi tubar shi haka nan ya zauna ba ci ba sha. Sa'adda Annabi Muhammad

(sallallahu alaihi wa sallam) ya sami wannan labari sai ya ce " da dai ya zo kaitsaye

gare ni in roka mashi gafara, amma yanzu ya bar lamarin shi ga Allah ya

jira har sai Allah ya karbi tubar shi. Bayan kwana bakwai aka yi wa Annbi

(sallallahu alaihi wa sallam) wahayin cewa an karbi tubar Abu lubabah. Wasu

dangin shi suka rugo su kwance shi, Abu Lubabah yace ya gwammace ya tsaya

har sai Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya kwance shi da hannun

Shi mai albarka, don ya nuna kwata-kwata an karbi tubar shi.

Wannan ya nuna mana cin-amana ba karamin al'amari bane a wajen sahabban

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), suna daukar wannan tsatstsauran

mataki ne don su nuna jimamin su. A yanzu haka, akwai wani ginshiki a

masallacin Madina ya mayi ainihin itaciyar da Abu Lubabah ya daure kan shi a

jikin ta. Mutane da yawa suna zuwa kusa da wanna ginshiki suna rokon Allah ya

yafe masu zunubban su kamar yadda Abu Lubabah yayi,\.

Kuma muna iya ganin cewa : Lokacin da Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ya

mayarwa da Uthman bn Talha da makullan dakin Allah, a kudance ba wata daraja

gare su ba, idan da za a sai da su, ba wani abu bane illa tsofaffin karafa, amma

ba karamin matsayi ne ba a ce mutum ya kasance mai dawainiya da dakin Allah.

Amana a nan ana nufin dora wata dawainiya. Muna iya yankewa da cewar duk

wata gwamnati ko kungiya amana ce. Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam) ya ce " idan wani shugaba ya dora wasu a wani mukami saboda 'yan

uwantaka, ko abuta ko kuma wadanda aka dora basu cancanta ya rike wannan

mukami ba, to tsinuwar Allah ta tabbata a kan wannan shugaba, sallar su kuma

ba za a karba ba, a karshe kuma za a jefa su wutar Jahannama.

Kamar yadda aka ruwaito a cikin littafin Bukhari, Annabi Muhammad (sallallahu

alaihi wa sallam) ya ce

" idan aka jingina abu ga wadanda ba su cancanta ba ku saurari tashin kiyama."

Za mu iya karawa da cewar: babu abinda zai hana matsaloli a irin wannan

gwamanti ko kungiya in har aka kauce daga dokokin Alkur'ani da Hadisin Manzon

Allah (sallallahu alaihi wa sallam).

Za mu kara lura da cewa amana babbban nauyi ne wanda lallai ne a sauke shi,

idan a ka ci amana mumman sakamako zai afku, a misali, wani lokaci Abu Zarr

RA ya roki Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ba shi wani mukami

babba kamar yadda aka ruwaito a 'Muslim' , sai Manzon Allah (sallallahu alaihi wa

sallam) ya ce :

> ma'ana su

wadannan sun tsira.

Kamar a aya ta biyu inda Allah SWT ya ke cewa "Idan za ku yi hukunci tsakanin

mutane,kuyi hukunci da adalci" wannan umarni ba a kan shuwagabanni kadai ya

ke ba har ma a kan kowane mahaluki. A nan kowa dole ne a yi mashi adalci a

Musulunci, babu wannan dan uwa ne ko aboki, Musulmi ko wanda ba Musulmi ba,

dan kasa ko bako, kowa lallai ne a dauke shi abu daya bisa adalci.

Yana da kyau mu lura, Allah SWT ya fara ambaton amana sa'annan ya umarce

mu da mu yi adalci, ke nan ya nuna mana adalci baya tabbata sai an dauki wanda

suka cancanta a dora su a kan hakkokin jama'a. A halin yanzu abinda aka rasa ke

nan a wasu gwamnatoci da kungiyoyi har ma da masallatai da makarantun

Islamiyyah. Matukar dai ba a yi abinda ya dace ba, to matsaloli ba za a iya

magance su ba a gwamnatocin nan.

Alqur'ani mai girma ya yi Allah-wadai da akidar nan ta bayar da mukami a

ma'aikatun da hukomomin gwamanti a kan yawan jama'a ko jihohi ko kuma lardi.

Alqur'ani ya ce wannan ba wata dama ba ce ta wani, wannan amana ce ga Allah,

za a bada ta ne ga wanda kadai ya dace ya kuma cancanta. Alqur'ani mai girma

ya fayyace a wata cewa: (qawiyyun ameen) ma'ana sai ya cancanta ko da yana

da gaskiya da rikon addini, wadannan matakai sai sun gamsar. Kumaya bayyana

karara kamar yadda ta kasance a kan annabi Musa a lokacin da ya sami wasu

yara 'yan mata suna rike da shanun su kusa da rijiya. Annabi Musa ya lura

mutane suna zuwa wurin rijiyar da shanun suna jawo ruwa su basu su sha su

tafi,sukuma wadannan 'yan mata suna nan a rike da shanun su tsawon lokaci.

Annabi Musa ya tambaye su " ko me ke faruwa?" sai 'yan matan nan suka amsa

mashi "mu baban mu tsoho ne,kuma mu ba za mu iya jawo ruwa daga cikin rijiya

ba, muna zuwa da shanun mu ne wurin rijiya idan kowa ya tafi sai shanun mu su

sha abinda yayi saura. Annabi Musa AS ya jawo masu ruwa shanun su suka sha

suka koshi, sai 'yan matan nan suka koma gida suka roki baban su da ya dauki

Annabi Musa aiki, domin sun same shi ya cancanta, yana da karfi, gashi kuma da

kyakykyawan hali. Wannan sune hanyoyin da za a dora amana.

A nan, ka'idoji da za a bi wajen bada mukaman gwamnati da hukomomi sune:-

1. Allah SWT shi kadai ne shugaba duk wata gwamnati wakilai ne na Allah ta'ala.

Duk wani iko yana kasa da na Allah ne shi kadai.

2. Ayyukan gwamnati ba za a karkasa su a kan yawan mutane ko yankuna sai dai

wadanda suka dace suka cancanta sune kadai za a rarrabawa mukamai.

3. Tun da mutane wakilai ne na Allah SWTdole ne su bi dokokin Allah a bisa

dukkan lamurra.

4. Idan wani rashin jituwa ya afku, a yi adalci ba tare da nuna kabilanci ba ko

yare ko launin fata ko akida ta addini.

A karshe, mun sani a lokacin Hijirar Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) daga

Makka zuwa Madina ya bar Ali a kan gadon shi kuma ya umarce shi da ya mayar

da duk wani abin amana ga masu. A wannan lokaci ne fa dukkan kabilu suka

hada karfi da karfe suka zagaye gidan Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) don su

kashe shi kai-tsaye. Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya nuna

kyakykyawan hali ya tabbatar duk an mayar da kayan amana ga masu su har da

wandanda suka nuna mashi mummunar gaba an mayar masu ta kowane hali.

Allah SWTmuna rokon ka ka bamu ikon rikon amana da alkawulla, ameen.

KADDARA DA RABO

Yana da wuya mutane su yarda da cewa rayuwa da mutuwa duka suna hannun

Allah SWT. Akwai tsayayyen lokaci wanda babu wanda ya isa ya canza shi ta

kowace hanya. Allah SWT ya shiryar da mu a kan kaddara da rabo a cikin

Alqur'ani mai girma, Suratul Baqarah, aya ta 246-247 :

A nan, muna iya ganin cewa: Allah SWT ya tace wadanda suka yi imani na hakika

da wadanda suke masu rauni ta hanyar kogi, kadan da suka yi imani ba wai sun

tunatar da 'yan uwan su bane akan ikon Allah kadai, a'a, har-ila-u' sun nuna

kaskantar da kana su ga Allah SWT ta hanyar yin addu'a a cikin lokaci, don haka,

ba a yarda ba mutum ya yi alfahari da imanin shi ko wani kokarin shi. An

ayyana sakamakon biyayya da mika wuya da karfin halin da suka yi a aya ta

251 ta suratul Baqarah:

Yana da ban mamaki, mu gani an yi amfani da wannan kalma 'kadan' sau uku,

da farko kadan ne suka mika wuya lokacin da aka wajabta masu yaki, kuma

kadan ne basu sha ruwan kogi ba, a cikin kadan da suka rage wasu daga cikin su

su ki yarda su yi yaki da Jalut da rundunar shi mai karfi. A karshe, yan kadan ne

daga cikin masu cikakken imani a cikin kaddara da rabo suka lamarin(yakin).

Allah SWT ya saka masu ba wai da nasara kadai ba, a'a, har ma da karfin mulki

ya kuma sanar da su hanyoyi masu yawa na hikima. Allah SWT ya fada a cikin

Alqur'ani mai girma: Al Baqarah aya ta 269

Khalid bn Al Walid RA, sanannen sahabin Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) ne,

Khalid yayi yakoki da yawa wanda har ya kasance babu wani a cikin jikin shi

wanda babu tabon rauni. Yana son ya mutu Shahidi. Daga karshe ya mutu a kan

gadon shi a gidan shi. Kun gani, rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke shi

kadai.

A nan, yana da kyau mu sami cikakken imani a kan kaddara da raboda umarnin

Allah SWT- cin nasara zai kasance a gare ka. Ya Allah ka kara mana imani a kan

kaddara da rabo, Amin.

ABUTA DA WANDA BA MUSULMI BA

Allah SWT ya ce a cikin suratu Aal Imran, aya ta 28:

Dangantaka ta uku ita ce nuna halayya ta gari ga wasu, ita kuma ana kiran ta

(MUDAARAAT), ita ma an yarda a yi ta har ga kafirai ma. Alal misali lallai ne ka

kyautatawa kafirai idan suka kawo maka ziyara. An yarda Musulmai su nuna

halayya ta gari domin su ceci kan su daga sharrin kafirai. Wannan shine ake nufi

a cikin Suratu Al Imran aya ta 28:

Sai dai idan kun ji tsoron hadari ko cutarwa daga gare su""

Dangantaka ta hudu shine ta fuskar kasuwanci, masana'antu ko aiki, wannan ana

kiran shi 'MU'AMALAT' an bada dama ayi da kafirai har idan ba zai cutar da

Musulmi ba, kuma an bada dama a nemi aiki a wajen wanda ba Musulmi ba ko

kuma ka yi aiki a wata masana'antar shi. Har-wa-yau, an bada dama a yi

kasuwanci da kafirai sai dai ba a yarda a sayaar masu da makamai ba idan suna

yaki da Musulmi.

Wannan kyakykyawar halayya Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya

nuna ta. Misali lokacin da aka sami fari a Makka, ya taimake su duk kuwa da

cewa sune suka kore shi daga gidan shi. Har-wa-yau, lokacin da ci Makka da yaki,

mutanen Makka sun yi tsammanin Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) zai kashe

su ne ko ya mayar da su bayi ko ya wasashe dukiyoyin su da kadarorin su. Sun

damu matuka suna sauraren hukuncin da Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) zai

yanke a jawabin da zai yi mai dimbin tarih. Sai Annabi (sallallahu alaihi wa

sallam) ya fara jawabin sa yana cewa da kafirai:

مﻮﻴﻟا ﻢﻜﻴﻠﻋ ﺐﻳﺮﺜﺗ ﻻ

"Yau babu sauran zargi a gare ku a kan komai kuma babu wanda zai tsangwame

ku". Babu wani a tarihin Dan Adam da zai iya nuna irin wannan kyakykyawan

haliga abokan gaba. Sakamakon nuna wannan kyaukyawan hali ne mutanen

Makka dubbai suka karbi Musulunci.

Har-wa-yau, Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya bar wakilan

kabilar Banu Thaqeef su zauna a masallacin shi duk da kasancewar su ba

Musulmin ba, ya nuna karimci da mutuntawa.

Khalifa Umar RA ya kasance yana ba kafirai tallafi daga baitil malin gwamnati.

Muna riko da wadannan misalai a cikin ran mu. Sai mu sake duba wadansu

ayoyin Alqur'ani mai girma mu ji abinda su ke cewa akan dangantakar muminai

da kafirai. Allah SWT ya ce a cikin suratul Mumtahanah, aya ta 1:

Ya ku wadanda kuka yi imani! Kada ku riki makiyi na kuma makiyin ku (kafirai) a

matsayin masoya, kuna nuna kauna a gare su>>

A karshen wannan ayar, Allah SWT ya ce, Suratul Mumtahanah aya ta 1:

ﻞ�ﺿ ﺪ�ﻘﻓ ﻢﻜﻨ�ﻣ ﻪ�ﻠﻌﻔﺑ ﻦ�ﻣ و ﻢﺘ�ﻴﻔﺧأ ﺂ�ﻣ و ﻢﺘ�ﻨﻠﻋأ ﺂ�ﻤﺑ ﻢﻠﻋأ ﺎﻧأ و ةدﻮﻤﻟﺎﺑ ﻢﻬﻨﻴﻟإ نوﺮﺴﺗ

ﻞﻴﺒﺴﻟا ءاﻮﺳ>>

A cikin Suratul Ma'idah, aya ta 51, Allah SWT ya ce :

Haka nan kuma Allah ya fada a cikin suratul Mujadala, aya ta 22:

wanda ya cutar da wani kafirin amana da ke zaune a kasar Musulmi nine mai bi

mashi hakki kuma zan yi nasara ".

Har-wa-yau, Ali RA ya ruwaito Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yace " Allah

SWT

Ya yi hani a ci mutuncin wanda ba Musulmi ba dake zaune tare da Musulmi>>

Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce zan yi rook a madadin kafiri

a ranar tashi alkiyama wadanda aka cuta ko kuma aka tauye masu wata dama,

ko kuma aka takura su ko aka karbe masu wani abu ba tare da hakki ba.

To dangantaka tsakanin Musulmi da kafirai dangantaka ce ta adalci, mutuntawa

da kuma ka'idoji.

Ian rokon Allah ya taimake mu mu zauna kamar yadda aka tsara a kur'ani da

kyakykyawan misali daga Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) da

sahabban shi.

HALAL DA HARAAM A MUSULUNCI

A cikin Al qur'ani mai girma, Suratul Baqarah, aya ta 188, Allah SWT

Ya ce :

Dalilin saukar wannan ayar shine an same shi a cikin littafin 'Ruhul Ma'ani' kamar

haka:

Wasu sahabban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) su biyu sun yi rigima

dangane da wani fili sai suka kawo kara gaban Manzon Allah (sallallahu alaihi wa

sallam). Wanda yake ikirarin cewa filin na shi ne, ba shi da shaida zai nuna na shi

ne. Sai Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ya tambayi dayan "ko ka

iya rantsewa da Allah cewa wannan wuri na ka ne ? sai ya amsawa Annabi

(sallallahu alaihi wa sallam), sai ya karanta

aya ta 77 a cikin Suratu Aal Imran a matsayin tunatarwa.

" Lallai wadanda ke bayar da alkawalin Allah da rantse-rantsen su, (a maimakon

su) a basu wani dan abin duniya, lallai wadannan ba su da rabo a lahira kuma,

Allah ba zai yi Magana da su ba ranar kiyama kuma kuma ba zai tsarkake su ba,

kuma akwai azaba mai radadi a gare su>>.

Wanda ya ke mallakar wannan fili a wannan lokaci ya saurari wannan ayar sai ya

ki yarda yayi rantsuwa, sai ya ji tsoro ya na shakku, filin nan kuwa na shi ne

kuma baya son ya kasance mai asara ranar tashin kiyama. Nan take Annabi

(sallallahu alaihi wa sallam) ya mayar da fili ga mai abin.

Ka sani wannan ayar an saukar da ita ne ta hana wasu tauye dukiyoyi ta

mummunar hanya. Haka nan kuma gabatar da kara na karya da rantsuwa ta

karya da bada shaida ta karya dukkan su haram ne. a farkon ayar an yi amfani

da kalmar (bainakum), a nan yana da ban sha'awa yadda Allah SWT ke koya

mana cewa kaci kayan wasu zai baiwa wasu kwarin gwiwa kai ma su ci kayan ka.

Misali, wani ya hada madara da ruwa sai wani kuma ya sayar da rubabbun kaya

marmari, sai wani kum aya sayar da rubabben dabino. Dukkan su suna cin

dukiyar wani ba tare da son ran shi ba. A gaskiya, har ta kai yanayin da kowa

yake cin dukiyar shi ba bisa ka'ida ba, kuma babu mahalukin da yayi nasara. Abu

na biyu yana koya mana idan ka sa wasu suka yi asarar dukiyar su, suna jin zafi

kamar yadda kai ma kake jin zafi idan kayi asarar ta ka dukiyar. A nan, ka kiyaye

dukiyar kowa tamkar taka wajen kula da ita.

Um Salama RA ta ruwaito daga Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yace "

Ni mutum ne kamar ku, kuna kawo rigingimun ku zuwa gare ni, kuma watakila

wani ya fi abokin rigimar shi iya bayani da dadin-baki, wannan na iya ja na in ba

shi gaskiya. Ku sani cewa sanin hakikanin gaskiya hannun Allah SWT yake shi

kadai, idan abu ba mallakar ku bane kada ku karba, saboda abinda nake ba ku a

wajen wannan shari'ar ba kome bane illa gungumen wuta"

A nan muna iya yanke hukunci cewa babu wata kotu, ko da kotun Manzon Allah

(sallallahu alaihi wa sallam) ce ba za iya maida haram ya zama halal ba ko ta

maida halal haram.

A wata fadar kuma a cikin Surtul Baqarah, aya ta 168, Allah SWT yace :

A wata ayar mai kama da wannan a cikin Suratun Nahl aya 51 Allah SWT ya ce :

A ciki wadannan ayoyi guda biyu, an yi amfani kalmomi guda biyu, 'Halal' da

kuma 'Dayyeb'. Halal ana nufin abinda aka yarda a yi ba ba tare da wani hani ko

iyakancewa ba. Dayyeb kuma abinda ake nufin abin Halal kana son shi ko kana

da sha'ar ka ci.

A nan, muna iya hakikance cewa ayyuka na gari ba za su samu ba sai mun ci

abinda yake Dayyeb. Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) yayi

bayanin wannan ayar, ya jaddada cewa ba an saukar da wannan ayar bane ga

annabawa kadai, har ma da mabiyan su. Manzon Allah (sallallahu alaihi wa

sallam) yace addua'ar wanda yaci Haram ba karbabbiy ba ce. Ya kara da cewa

mutane da dama suna bada kokari wajen bautar Allah kuma su mike hannayen

suna cewa ya Allah! Ya Allah! Ka karbi addu'ar mu amma idan abin cin su Haram

ne abin shan su Haram ne tufafin su Haram ne yaya za a yi a karbi addu'ar su?

Muslim ne ya ruwaito shi.

Akwai Hadisai da dama daga Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) wadanda

suka fayyace tsakanin Halal da Haram.

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce "wanda suka ci Halal suka bi

tafarkin Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam), sannan ba su zalunci

kowa ba, za su shiga Aljanna" Sahabbai suka ce "ya Annabi (sallallahu alaihi wa

sallam) wannan abu ai ya zama rowan dare ga mabiya a yanzu" Sai Manzon Allah

(sallallahu alaihi wa sallam) ya ce "Akwai mutane da za su a nan gaba da wannan

hanya".

Abdullahi Bn Umar RA ya ce Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) yace "idan

kana da halaye guda hudu sun ishe ka ka shiga Aljanna ko da baka sami komai

ba a duniya 1) ka tsare alkawali.2) ka fadi gaskiya. 3) ka kyautatawa mutane. 4)

ka ci abu na Halal.

Wani lokaci Sa'ad Bn abi Waqqas RA ya roki Manzon Allah (sallallahu alaihi wa

sallam) ya roka mashi Allah idan yayi addu'a ta zama karbabbiya, sai Manzon

Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce mashi " ya kai Sa'ad, kaci abinda yake

Halal da Dayyib ne Allah SWT zai karbi dukkan ddu'ar ka kuma ka zama wanda

ake karbar addu'ar shi".

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya kara da cewa "Na rantse da Allah

SWT wanda rayuwa ta take a gare shi, idan mutum ya ci mafi kankantar abu na

Haram duk wani aikin shi ba za a karba ba har tsawon kwana arba'in. Idan jikin

shi ya ginu da haram to babu abinda ya cacance shi sai wutar jahannam.

Mu'az bn Jabal RA ya ce Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) ya ce " Idan

aka tara mu ranar tashin kiyama, babu wanda zai bar wurin shi sai ya amsa

wadannan tambayoyi guda biyar :

1. Yaya ya gudanar da rayuwar shi.

2. Yaya ya gudanar da kuruciyar shi.

3. Yaya ya sami abinci shi.

4. Yaya ya kashe abinda yake samu.

5. Yaya ya tafiyar da ilmin da yake samu.

An karbo daga Abdullahi Bn Mas'ud RA yace Manzon Allah (sallallahu alaihi wa

sallam) yace " Na rantse da Allah wanda rayuwa ta take a hannun shi, wani ba

zai zama cikakken Musulmi ba sai zuciyar shi da harshen shi sun kasance

Musumi, kama makwabtan shi sun tsira daga duk sharrin shi. Idan mutum ya

mallaki dukiya ta Haram idan ya bada sadaka ba za a karba ba, idan kuma ya

batar da ita babu albarka a ciki, idan kuma ya barwa magadan shi ya bar masu

abinda zai kai su zuwa wuta, Allah SWT baya kankare mummunan aiki da wani

mummunan, Allah ya na kankare mummunan aiki da mai kyau ne.

Abadullahi bn Umar yace Manzon Allah SAW ya yiwa wasu gungun masu hijira

jawabi cewa: Ina neman tsarin Allah kuma ina fata abubuwa biyar ba za su

kasance ba a tsakanin ku:

1. Idan munanan halaye suka yawaita a cikin mutane, ko kin hanuwa daga

abinda Allah ya haramta, ko yin shiga mai bayyana tsiraici, Allah zai saukar masu

da bala'I da cututtuka wanda kakannin su ma basu taba jin labarin su ba.

2. Idan mutane suna tauye ma'auni (suna cin hakkin wadansu) kamar yadda

mutanen Annabi Shu'aib su ka yi,to Allah zai saukar da fari da kunci rayuwa da

wahalhalu da azzaluman shuwagabanni a gare su.

3. Idan kuma basu bada Zakka za a dauke masu ruwan sama daga nan sai su

fada talauci da bala'i.

4.Idan suka kauce daga tafarkin Allah SWT da Manzon shi SAW makiya daga wani

bangare za su zo su wasashe dukiyon su da karfi.

5.Idan kuma jami'an gwamnati ko shuwagabanni ba su zartar da wani abu kamar

yadda Allah SWT ya shirya a cikin Alqur'ani mai girma sai Allah ya saka gaba a

tsakanin su sai su yi ta rigingimu a tsakanin su." (Muslim ne ya ruwaito shi)

Ya Allah ka kare mu daga dukkan sabo. A bayyane yake cewa dukkan wasu

abubuwa ba su kawo haduwar-kan Musulmi, hadin-kai zai samu ne kawai ta

hanyoyi wadanda suke na Halal ne.

Yana da ban-sha'awa aya ta 188 a cikin Suratul Baqarah (wadda ta gabata) ta zo

ne bayan cikakkun dokoki da ka'idojin azumi ne a inda aka yi haramta cin wasu

abubuwa na halala har zuwa wani kayydajjen lokaci. Don haka, yin manufar yin

azumi ita ce domin ya sanya da'a da koyon kamun-kai wajen amfani da

abubuwan da suke na halal ne. wannan koyarwa da kamun-kai da dangana yana

da amfani kwarai. Ta hanyar wannan koyarwa mutum ya barranta kwata-kwata

daga abubuwan da suke na haram ne. karin bayani, duk wanda zai yi buda baki

yayi da abinda yake na halal ne. Idan abincin haram ne yayi buda-baki da shi

Allah SWT baya karbar wannan azumi.

Daga karshe, hanyoyi na halal da haram sune wanda Allah SWT ya bayyana. Duk

wasu tarurruka na duniya da kulla yarjejeniya ba zai warware wannan matsala

ba, tunda kowa kokarin shi shine ya kare kan shi. Haka kuma yarjejeniya da aka

kulla da nufin matsawa wani ko ko wata kasa akwai son zuciya ne a ciki don haka

babu wata hujja mai karfi a ciki. dokokin Allah su ne na gaskiya a ko wane lokaci.

Kamar yadda aka fada a baya, Allah SWT ya fayyace halal da haram, ba a barsu

a karkashin hukuncin wani annabi na wani lokaci ba. Tsarin Allah shine wanda ba

kuskure a ciki shi.

Ya Allahka bamu ikon mu tsaya a kan halal, ka kare mu daga fadawa cikin

iyakokin na haram da kuma abubuwa masu rikitarwa.

SURATUL FATIHA

Suratul Fatiha ita ce Sura ta farko a jerin Surorin Al qur'ani mai girma, tana da

muhimmanci kwarai saboda dalilai masu yawa:

1. Ita ce sura ta farko wadda a dunkule a ka saukarwa Manzon Allah SAW ita,

shine ya sa ake kiran ta 'Fatihatul Kitab'

2. Har-wa-yau, ana kiranta 'Ummul Kitab' kuma 'Ummul Qur'an'. Abu Hurairah,

RA yace Manzon Allah SAW yace " na rantse da ubangiji wanda rayuw ta take a

hannun shi, babu makamanciyar wannan surar a littafan da aka saukar, har ma a

cikn Al qur'ani". Muslim da Tirmizhi ne suka ruwaito shi.

3. Anas RA yace Manzon Allah SAW yace " A cikin duk surorin da ke cikin

Alqur'ani Suratul Fatiha ita ce babba.

4. Wanna sura har-wa-yau, ana kiran ta 'Sura ash ashifa'' (sura mai warkarwa)

A yanzu za mu yi kokari mu fahimci ma'anar wannan sura da kadan-kadan.

Al hamdu lillah na nufin dukkan wani irin yabo ya tabbata ga Allah SWT shi kadai.

Ba yabo da godiya ga Allah SWT bane kawai, a'a, har ma akwai ma'anar kadaita

Allah a cikin ta, don haka manufa ko dalilin yin yabo an gina shi ne a cikin ta.

Wannan misali ne na farko na fasahar magana ta Alqur'ani.

" Lallai dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Mahaliccin kowa da komi"

A nan, farkon ginshikin da aka kafa Musulunci shine "imani", an gina shi a kan

wannan takaitacciyar kalma.

Har-wa-yau, 'Alhamdu lillahi rabbil aalamiin' shi ma dalili ne na dukkan wani irin

yabo yana ga Allah shi kadai. Ma'ana, Allah SWT shine Mahalicci, Majibincin mu,

Mataimakin dukkan duniya wacce aka sani da wadda ba a sani ba, ta kowace

hanya

Bari mu ga yadda yayain bayanin halittar shi a cikin Al qur'ani mai girma. A

misali, Allah SWT ya ce a cikin Alqur'ani, Suratat az Zaariyaat aya ta 47,48,49:

wadannan ayoyi da Allah SWT ya yi bayanin su a wurare da yawa a cikin Alqur'ani

mai girma shekaru aru-aru da suka wuce. Sai Allah SWT yace a cikin Suratul

Waaqi'ah aya ta 68-73.

" Shin ba ku ganin rowan da kuke sha ? shin kune kuke saukar da shi daga gizagizai

ko kuma mune masu saukar da shi? Da mun so sai mu sanya shi ya zama

mai zartsi (wanda bashi da amfani). To me ya sa kuma ba za ku godewa Allah

ba?

Shin ba ku ganin wutar da kuke kunnawa? Shin kune ku ka yi itatuwan ta (wanda

a ke tada wuta da su) ko kuma mu ne masu yin su? Mu ne mu ka sanya ta

(wutar) ta zama abin jin dadi ga masu yawo a cikin daji>>.

Ka sani wannan ayar tana tunatar damu game da wutar lahira. A nan duniya,

Allah SWT ya bamu ikon amfani da wuta domin jin dadin mu har ma mu yi girkegirken

mu.

Sai kuma Allah SWT ya yi Magana akan halittar Dan Adam a cikin Surat Al insan,

aya ta 1,2,3, y ace:

Shi mutum kamar wata mu'ujizar duniya yake. Da wasu bangarori suke iki da

junan su a cikin kwanciyar hankali. Wannan babbar alama ce ta mahalicci. Shine

ya sa Allah SWT ya ce a cikin Alqur'ani mai girma :

Wannan ya bamu takaitaccen bayanin halittu na Allah SWT. Yanzu bari mu duba

ma'anar 'Ar Rahman' da 'Ar Raheem'. Dukkan wadannan kalmomi am tsamo su

ne daga tushe daya shine 'Ar Rahmah'.

'Ar Rahamaan' tana nufin: rahama tun daga farko har karshe, wannan kalma ce

da bata da jam'i, kuma 'AlRahaman' za a iya amfani da ita ne ga Allah SWT kadai.

'Ar Raheem' shine: cikakkiyar ko dawwamammiyar rahama. Wannan kalmar ana

iya amfani da ita ga mutum ma. Misali Allah SWT siffanta Annabi SAW da cewa:

ﻢﻴﺣر فوؤر

Ma'ana :Mai matukar tausayi da kuma dawwamammiyar rahma ga wanda suka yi

imani.

Na ukku sai mu ce Allah SWT shine sarki a ranar hisabi.wannan yana bukatar

sharhi na kashin kan shi. Aya ta gaba ita ce :

ﻦﻴﻌﺘﺴﻧ كﺎﻳإ و ﺪﺒﻌﻧ كﺎﻳإ

"Kai kadi muke bautawa kuma daga gare ka kadai mu ke neman taimako (a kan

dukkan komi)."

A nan, dukkan wani irin yabo ga Allah SWT wanda ya halicce mu kafin yanzu, a

yanzu kuma yayi mana cikkakkiyar rahama, a nan gaba kuma shi kadai ne mai

cikakken mulki a ranar sakamako. Idan haka ne don me ba za mu ce "shi kadai

muke bautawa kuma shi kadai muke neman taimako a gare shi ba". Wannan ayar

ana kiran ta zuciyar Suratul Fatiha. Yabo ne ga Allah SWT kuma addu'a ce ta

neman taimakon Allah SWT.

Abu na gaba sai mu fara da addu'a, muna rokon Allah ya shiryar damu a kan

hanya madaidiciya. Kalmar "shiriya" tana bukatar bayani. Allah SWT ya na bada

shiriyar shi ta hanyoyi guda uku. Allah SWT ya bada shiriya ga dukkan ababen

halittar shi kamar yadda ya zo a bangarori da dama na Alqur'ani mai girma.

Misali, Allah ya ce a Surat Al Isra' aya ta 44 :

Sammai bakwai da kasa da duk abinda ke cikin su suna yin tasbhi gare shi (Allah

SWT), babu wani abu face yana tasbihi da godiyar shi (Allah SWT) sai dai ku

(mutane) ba ku fahimtar tasbihin su. Lallai shi ya kasance mai matukar hakuri ne

kuma mai yawwan gafara>>

Dubi bakin iyakar mu. Lallai Allah SWT ya bada shiriya ga bishiyoyi, taurari, har

ma duwatsu.

Har-wa-yau, Allah SWT ya kara cewa a cikin Surat An Nuor, aya ta 41:

Shin baku ganin duk abin da ke cikin sammai da kasa duk su na tasbihi ga Allah

SWT, har ma da tsuntsaye su na masu shawagi da fuka-fukan su. Allah ya san

addu'ar ko wanne daga cikin su da kuma tasbihin da yake yi wa Allah SWT. Lallai

Allah Masani ne da abinda su ke aikatawa.

Har-wa-yau, Allah SWT ya ce a cikin Surat Al A'la, aya ta1-3:

" Yi tasbihi da sunan Ubangijin ka, wannan da yayi halitta kuma ya daidaita

halittar, wannan da ya tsara halittar shi kuma ya shiryar da su"

a nan, komi yana da hanyar shiriyar da zai bi. Misali, kunne ba zai iya amfani ba

wajen gani, haka kuma idanu wajen ji. Wannan ne ya sa Allah SWT ya ce a cikin

Surat Maryam

" Babu abinda ya ke cikin sammai ko kasa face bawa ne ga Allah "

Abu na biyu, Allah SWT ya na bayar da shiriyar shi ta hanyar Manzannin Shi da

littafan Shi.

Na ukku : Allah SWT yana bada shiriyar Shi kai tsaye ga zababun bayin Shi.

Daga cikin dukka alheran da Allah SWT yayi wa ababen halittar Shi abu mafi

girma shine bada shiriya a gare su. Ba don wannan shiriyar ba to da an rasa

dukkan halittu da kuma dukkan tsarin ya ruguje. Yanzu ke nan za mu iya

tabbatar da cewa Allah SWT akwai wani nau'i na shirya da yayi ga dukkan komi.

Me ya sa muke rokon Allah ya shiryar da mu akan hanya madaidaiciya? Haka

kuma manzannin Shi hakika suna kan hanya madaidaiciya, me ya sanya

wadannan Manzannin suke ta rokon Allah ya shiryar da su hanya madaidaiciya?

Amsar wannan tambaya shine: Allah SWT zai iya kara shiriyar Shi a kan kowa,

don haka babu wanda zai dauki kan shi a matsayin wanda ya wuce wannan

larurar. A misali, Allah SWT ya cewa Annabi Muhammad SAW lokacin da yake

bayanin fa'idojin cin Makka da yaki a cikin Suratul Fath:

" Daya daga cikin fa'idojin shine a shiryar da ku hanya madaidaiciya"

A hakika, dukkan Annabawa suna yin kokari daga wannan babban matakai zuwa

ga babban mataki na shiriya daga Allah SWT

ﻢﻬﻴﻠﻋ ﺖﻤﻌﻧأ ﻦﻳﺬﻟا طاﺮﺻ

"Siratal lazina an'amta alaihim"

Addu'a ce mai mai matukar ban-mamaki, tana cewa " ka nuna manar hanyar

wadanda ka yi wa ni'ima"

An yi cikakken bayanin wannan jimla a cikin Surat an Nisa' :

" wanda duk ya bi umarnin Allah SWT Annabi Muhammad SAW to hakika

wadannan suna tare da wadanda Allah SWT yayi wa ni'ima, daga cikin Annabawa,

masu gaskiya, shahidai da kuma mutanen kirki"

ka sani fa ba muna cewa " ka nuna mana hanya madaidaiciya ta Annabawa ko

hanya madaidaiciya da aka yi bayanin ta a Alqur'ani. Alal- hakika, Allah SWT yana

nuna mana cewa mu nemi ita wannan daidaitacciyar hanya a bisa shiryarwar

alqur'ani mai girma a tawagar mutanen kirki wanda ake samun su kowane

zamani.

Manzon Allah SAW ya taba cewa sahaban shi " Al'umma za ta karkasu kashi

sabai'in, amma kashi daya ne zai kasance a kan hanya madaidaiciya" sahabbai

suka tabaye shi "wadanne ne ?" sai Manzon Allahj SAW ya amsa " sune wadanda

suka bi hanya ta da kuma hanyar saddhabban na". A nan, bin tafarki na mutanen

kirki yana da amfani. Wani baiti da aka yi da yaren Urdu ya na cewa:

" Ayyukan kwas suna bayar da sanin kalmomi ne kadai, amma malami mai

koyarwa shi yake gyara matsayin mutum".

Wadansu musulmi suna bin suna bin bayanan Alqur'ani wajen neman shiriya

amma sai su manta da mutanen kirkin da ke kewaye da su, sun manta Allah

SWT ya turo Manzon shi a matsayin malami mai koyarw. Hatta fasahohi na

rayuwar duniya kamar ta ilmin likita koyarwa ta hanyar takardu kadai ba ta

wadatarwa, tana bukatar malami.

Wadan su musulman kuma suna bayar da hankalin su kadai a kan mutanen kirki

na zamanin su wajen neman shiriya su kauda kai daga Al qur'ani mai girma. A

nan sai matsala ta shiga tsakanin wadannan bangarori. A hakika, muna bukatar

koyarwa ta Al qur'ani da tafarkin salihan mutane wadanda ke a cikin ko wane

nau'I na mutane. Shine yasa Allah SWT ya ke nuni wajen wadannan mutane

wajen neman hanya madaidaiciya wajen neman shiriya.

A karshe, muna rokon Allah SWT kada ya sanya mu a kan hanyar wadand yayi

fushi da su, hanyar wadanda karkace. Wannan ana nuni ne ga Yahudawa da

kiristoci. An samo daga Abu Hurairah RA a cikin 'Muslim' cewa Manzon Allah SAW

ya ce " Allah SWT ya ce na raba salla tsakani na da bawa na gida biyu, ina bashi

duk abinda ya ke so.

IDAN MUTUM YA CE SAI ALLAH YACE

* Alhamdu lillahi rabbil alamin bawa na ya gode mani.

* Ar Rahmanir rahim Bawa na ya yabe ni.

* Maliki yaumid din Bawa na yayi bayanin karfi na

* Iyyaka na'budu wa iyyaka nasta'in Wannan tsakanin bawa na ne

da ni.

Farkon wannan ayar yabo ne ga Allah SWT bangare na biyu kuma addu'a

* Ihdinas siraatal mustaqim Bawa na zai sami duk abinda

ya roka.

A nan, Suratul Fatiha yabo ne ga Allah kuma addu'a ce madaukakiya zuwa ga

hanya madaidaiciya. Ya Allah SWT ka gwada mana ka bamu ikon bin wannan

hanya madaidaiciya har lokacin mutuwar mu. Amin.

Muna godiya ga Allah SWT da ya koyar da mu yadda za mu yabe shi, yadda za

mu roke shi da kuma abinda zamu roke Shi. Allah SWT ya koya mana yadda za

mu yabe shi cewa : "Al hamdu lillahi Rabbil aalamin". Wannan shine zai kasance

gaisuwar 'yan aljanna kamar yadda a cikin Alqur'ani Allah SWT ya bamu alfarmar

mu yi amfani da wannan kalmar a nan duniya. Lallai Allah SWT mai rahma ne ga

bayin Shi masu biyayya. Babban abinda ya fi dacewa shine mu rufe wannan

bayani da cewa ' Al hamdu lillahi Rabbil aalamin'.

ISRA'I DA MI'RAJI

Allah SWT yace a suratul Isra'i :

" Tsarki ya tabbata ga Wanda ya dauki bawan Shi da dare daga masallacin

harami ya zuwa masallacin masallaci mafi nisa (Kudus)wanda muka yi albarka a

gare shi, domin mu nuna mashi ayoyin mu, lallai shi Allah mai ji ne kuma mai

gani ne"

Wannan tafiya da Annaci SAW yayi ta kasu gida biyu. Na farko shine tafiya daga

Makka zuwa Kudus, ana kiran ta 'isra'i'. bangare na biyu kuma shine daga

masallacin Kudus zuwa sama, wanann kuma shine 'Mi'raji'. Ya kamata mu dubi

dalilan da suka sanya yin wannan tafiya domin mu fahimci Isra'i da Mi'raji.

Akwai abubuwan da suka faru shekara daya da rabi kafin tafiyar. Da farko kafirai

sun kara matsa kaimi wajen takurawa da muzgunawar da suke yiwa musulmi. A

wannan lokaci musulmi ba a basu damar su yi yaki ba a kowane irin hali suke.

Allah SWT yayi umarni a cikin Suratul Baqarah aya ta 109:

"Ku yafe ku kauda kai har sai umarnin Allah ya zo"

kuma ya faru a lokacin da kawun Manzon Allah SAW, Abu Talib wani babban karo

ne ga Annabi SAW daga kafirai, wannan shine ma ya sa kafirai suka kara

tsandare. Kuma bayan rasuwar Abu Talib, matar Annabi SAW Khadija ta rasu, sai

abubuwa suka cabewa Manzon Allah SAW. A cikin wannan yanayi sai Annabi SAW

yayi shawarar komawa Ta'if ya ci gaba da yada musulunci. Ya tsammaci goyon

baya daga shuwagabannin wannan gari, tunda dangi ne na mahaifiyar shi.

Wadannan shuwagabanni su ka ko-in-kula da Annabi SAW lokacin da ya sauka a

garin. Daga karshe ma si suka turo mashi yara suna jifar shi har suka ji mashi

rauni kwarai sai da ta kai takalmin shi ya cika da jini da yake kwarara daga kan

shi, sai ya fake a wani lambu a bayan garin. Mai lambun ya tausaya mashi ya

korar mashi yaran. A nan sai Mala'ika ya zo mashi ya ce da shi " ya Muhammad

hakika mutanen wannan gari azzalumai ne, idan kana so zamu birkice wannan

gari mu lalata shi baki daya. Annabi SAW ya ce ni na zo ne domin rahma ga kowa

ba domin azaba ba. Ina fata mutanen wannan gari nan gaba za su gane gaskiya.

Saboda munanan abubuwa da suka faru a wannan shekara shine ya sa ake kiran

ta " Shekarar bakin-ciki".

lokacin da Annabi Muhammad SAW ya dawo Makka sai aka hana shi shiga, domin

yanzu sun dauke shi ba mazaunin Makka ba, sai bayan da aka yi shawarwari

sa'annan aka kyale shi ya shiga amma da sharadin ba zai sake yiwa kowa wa'azi

ba a Makka, Annabi SAW yana wa'azi ne kadai a wajen wasu taruka ko wasu

ukukuwa a wajen Makka. Wannan ya nuna mawuyacin hali da matukar hakuri

da karfin hali na Annabi SAW. Allah SWT ya bashi lada mai yawa saboda tsananin

hakurin shi ya dauke shi zuwa wannan tafiya ta Isra'i da Mi'raji.

Bari mu bayyana yadda Isra'i ya ke. Mala'ika Jibril ya zo masallacin Makka, ya

umarci Annabi SAW da yayi alwalla da ruwan zam zam. Ya dauki Annabi SAW

akan wani doki mai sauri, ana kiran shi Buraqa daga masallacin Makka zuwa

masallacin kudus. Annabi SAW ya yi sallah raka'a biyu, sai Mala'ika Jibril ya bashi

kofi biyu, daya na madara daya kuma na giya, sai Annabi SAW ya karbi na

madara, sai Mala'ika yace "ka zabi abinda yake tabbatacce kuma mai kyau, ka

sami shiriya ta gari , haka kuma al'ummar ka, da ka zabi giya da al'ummar ka

sun karkace. Mun sani cewa giya ita ke kai al'umma ga tabarbarewa, kuma ana

kiran ta

Uwar zunubbai. Don haka, musulunci an gina shine akan tsafta/tsarki, gaskiya da

kuma kyautatawa.

Bayan nan sai Mi'raaj. Mala'ika Jibril ya dauki Annabi Muhammad SAW akan

Buraqa suka yi sama, suka je sammai da-ban-da-ban. A can ne Annabi SAW ya

sadu da sadu da Annabi Adam a sama ta farko, Annabi Yahaya da Annabi Isa a

sama ta biyu, Annabi Yuosuf a sama ta uku, Annabi Anaq a sama ta hudu,

Annabi Haaroun a sama ta biyar, Annabi Musa a sama ta shidda, Annabi

Ibraheem a sama ta bakwai. Annabi Muhammad SAW ya yi sallama ga dukkan

wadannan shuwagabanni namu.

A wani wurin Annabi SAW ya ga Mala'ika Malik mai tsaron wuta. Annabi SAW ya

roki Mala'ika Jibril ya bar shi ya ga yadda wuta take, Mala'ika Malik ya daga wuta

Annabi Muhammad SAW ya wata irin wuta wadda za ta iya cinye komi. An

nunawa Annabi Muhammad SAW misalin irin azabar da dake yiwa wadanda suka

aikat zunubai.

Ya ga wadansu mutane leben su kamar an rakumi kuma suna da dunkulen wuta

a hannuwan su, ya gan su su na sanya wannan dunkulen wuta a bakin su, sai

kuma dunkulen wutar ya fito daga duburar su. Mala'ika Jibril yayi bayanin cewa

wadannan su ne maciya amana da a ka damka a hannun su.

Ya gani SAW wadan su mutane masu katon ciki sa'annan mahaukatan rakumma

masu jin kishi suna tattaka su, a ka yi wa Annabi Muhammad SAW bayanin cewa

wadannan sune masu cin kudin riba (kudin ruwa)

Ya ga wadan su mutane wadanda ke da abinci mai kyau da kuma abincin marar

kyau gurbatacce a ajye kusa da su, amma suna cin abincin marar kyau

maimakon wanda yake mai kyau din. Aka fada mashi cewa wadannan sune masu

gujewa matan su na halal.

Sa'annan ya ga wasu mata wanda aka rataye su da nonon su, aka fada mashi

cewa wadannan su ne suke cin amanar mazajen su.

A wanann tafiya, Annabi Muhammad SAW ya zarce saman bakwai inda babu wani

Mala'ika da ya taba zuwa. A nan ne Annabi Muhammad SAW ya ga ayoyin Allah a

wannan wuri mai daraja. Allah yayi bayani a cikin Suratun Najm aya ta 17-18 :

ىﺮﺒﻜﻟا ﻪﺑر تﺎﻳاء ﻦﻣ ﺁر ﺪﻘﻟ , ﻰﻐﻃ ﺎﻣ و ﺮﺼﺒﻟا غاز ﺎﻣ

wannan ya nuna matsayin nutsuwa da kamun kai na Annabi SAW. Ya ga abinda

ya kamata ya gani, har tsawon lokacin da ya ke son gani. Bai yi wani doki da

kagara ba a lokacin da yana kallon kudurar Allah da kuma iradar Shi.

Wajen wannan kusantaka da Allah an bashi abubuwa guda uku.

An fadawa Annabi Muhammad SAW cewa duk wanda yayi kalmar shahada

sahihiya zai shiga Aljanna.

Annabi Muhammad SAW ya karbi ayoyi biyu na karshe na Suratul Baqrah.

Da farko an bashi salloli guda hamsin a rana daya, aka rage su zuwa biyar

rangwame na musamman da aka yiwa al-umar sa. Kuma za su sami ladar salla

hamsin idan suka yi guda biyar. Allah SWT yana kyautatawa al'umar Annabi

Muhammad SAW.

Annabi Muhammad SAW yace :

ﻦﻣﺆﻤﻟا جاﺮﻌﻣ ةﻼﺼﻟا

" Sallah ita ce mi'rajin Mumini" ita ce dangantaka ta kusa tsakanin Ubangiji da

bawan shi.

Bayan da Annabi SAW ya karbi wannan sako sai ya sauko zuwa ga masallacin

Kudus, sauran Annabawa suma suka zo, annabi Muhammad SAW ya jagorance su

suka yi salla. Ya nuna cewa sakonnin manzanni Allah duk daya ne kuma ya nuna

ya nuna fifikon Annabi Muhammad SAW a kan sauran manzanni.

Daga nan sai mala'ika Jibril ya maido Annabi Muhammad SAW zuwa Makka a

cikin dare daya. A lokacin da kafirai suka sami labarin tafiyar Annabi Muhammad

SAW daga Makka zuwa Kudus zuwa sama ta bakwai duk a dare daya sai suka

maida maganar abin dariya. Sai kafiran suka samin sayyidina Abubakr suka ce da

shi " ka ji abinda abokin ka yake ikirari da shi na tafiya a cikin dare? Sai Abubakr

RA ya tambaya " lallai manzon Allah shi ne ya fadi hakan?" sai kafiran suka ce

lallai shi ya fadi, sai Abubakr ya ce lalllai ikirarin shi gaskiya ne. Tun daga nan

Annabi Muhammad SAW yake kiran Abubakr 'As siddiq'.

Aya ta farko a cikin Surat al Isra' tana karantar da mu abubuwa da yawa, misali,

Allah SWT yana amfani da kalmar 'Abd' ko bawan Allah mai biyayya wajen

ambaton Manzon Allah SAW a maimakon ya kira shi da duk wani suna. Wannan

yana nuna duk da ya kai matukar kusanci da Allah SWT amma yana nan a

matsayin bawa mai biyayya, ba wai tsara ne na Allah ba ko ta wane bangare. A

nan ana nuna maka kada mu hada Allah da kowa a wurin bauta kamar yadda

wasu mabiya littafai ke yi.

Har-wa-yau, wannan tafiya an yi ta ne da amfani da gangan jiki da kuma zuciyar

Manzon Allah SAW saboda an yi anfani da wannan kalma ' Al abd'. A wannan

ayar, kalmar 'Al abd' ta kunshi gangan jiki da kuma rai ba wai daya daga cikin su

ba. Kuma ayar ta nuna mana mu so masallacin Kudus wanda Allah ya albarkaci

dukkan kasar da ke kewaye da shi.

Dadin-dadawa, kalmar 'Lailan' da ta zo a cikin ayar ta na nufin bangaren dare.

Allah mai ji ne kuma mai gani ne, ya ji addu'ar Annabi SAW kuma ya ga hakurin

shi sai ya saka mashi da wannan tafiyar mai girma ta Isra'i da Mi'raaji wadda

take nufin cewa daga karshe shine zai ci nasara.

I na rokon Allah SWT ya bamu ikon fahimtar ainihin manufar Isra'i da Mi'raaji,

Ameen.

YAKIN BADAR

Ba a umarci musulmi ba da su yi yaki tsawon zaman su shekara goma sha uku a

Makka ko da kuwa ana muzguna masu ko an fitar da su daga gidajen su. Bayan

hijrar Manzon Allah SAW daga Makka zuwa Madina ya shirya dangantaka da

wadanda ba musulmi ba a matsayin yarjejeniya kuma ya kafa daular Musulunci.

A tarihin addinin Musulunci, yakin badar shine na farko wanda kafirai sun ninka

musulmi yawa har sau uku. Rundunar musulmi ta kunshi mutum 313, rakumma

70, dawaki 2 da takubba 8. Annabi Muhammad SAW sun hau rakumi daya da shi

da Abu Lubabah RA da Ali, kamar yadda su ma sauran su ka yi. Su kuma kafirai

sun kunshi sojoji 1000 da makaman su, rakumi 700, dawaki 100.

Za mu yi bayanin abubuwan da suka faru kafin lokacin yakin da lokacin yakin da

kuma bayan yakin domin mu sami koyami daga wannan yakin.

Kafin yakin, Annabi Muhammad SAW ya damu matuka, ya roki Allah SWT cewa

idan aka cinye wadannan musulmin da yaki to da kyar za a samin sauran

musulmi wanda za su daukaka kalmar Allah SWT. Wannan lamari an yi bayanin

shi a cikin Surat Al anfal, aya ta 9-10:

ﷲا ﻪ�ﻠﻌﺟ ﺎ�ﻣو , ﻦﻴﻓدﺮ�ﻣ ﺔ�ﻜﺋﻼﻤﻟا ﻦﻣ ﻒﻟﺄﺑ ﻢآﺪﻤﻣ ﻲﻧأ ﻢﻜﻟ بﺎﺠﺘﺳﺎﻓ ﻢﻜﺑر نﻮﺜﻴﻐﺘﺴﺗ ذإ

ﻢﻴﻜﺣ ﺰﻳﺰﻋ ﷲا نإ , ﷲا ﺪﻨﻋ ﻦﻣ ﻻإ ﺮﺼﻨﻟا ﺎﻣو ﻢﻜﺑﻮﻠﻗ ﻪﺑ ﻢﻜﺑﻮﻠﻗ ﻦﺌﻤﻄﺘﻟو ىﺮﺸﺑ ﻻإ

(ka tuna) lokacin da kuke neman taimakon Ubangijin ku, sai ya amsa maku da

cewa "Zan agaza maku da mala'iku dubu wanda za su ci gaba da zuwa wasu

bayan wasu har sai an kammala yakin, Allah SWT yana yin haka ne don ya baku

kyakykyawan albshir kuma zuciyar ku ta sami nutsuwa da zuwan wadannan

mala'iku. Nasara ba daga kowa take ba face daga Allah shi kadai. Lallai Allah

mabuwayi ne kuma mai matukar hikima".

Allah SWT yana bada sanarwa zai kawo gudun-mawar mala'iku ne domin ya ba

muminai bayyanannar hujja domin zuciyar su ta wadatu. Allah SWT yana cewa

kada ku yi tsammanin wannan taimako daga mala'iku yake. Hakika nasara daga

Allah take shi kadai, kuma shine ya turo da wadannan mala'iku.

An umarci mala'iku su yi abubuwa da yawa. Allah SWT ya fada a cikin Suratul

Anfaal, aya ta 12:

اوﺮ�ﻔآ ﻦﻳﺬ�ﻟا بﻮ�ﻠﻗ ﻲﻓ ﻲﻘﻟﺄﺳ اﻮﻨﻣاء ﻦﻳﺬﻟااﻮﺘﺒﺜﻓ ﻢﻜﻌﻣ ﻲﻧأ ﺔﻜﺋﻼﻤﻟا ﻰﻟإ ﻚﺑر ﻲﺣﻮﻳ ذإ

نﺎﻨﺑ ﻞآ ﻢﻬﻨﻣ اﻮﺑﺮﺿاو قﺎﻨﻋﻷا قﻮﻓ اﻮﺑﺮﺿﺎﻓ ﺐﻋﺮﻟا

(ka tuna) lokacin da uban gijin ka yayi wahayi ga mala'iku cewa ina tare da ku,

don haka kuj tabbatar da wadanda suka yi imani. Da sannu zan jefa tsoro a cikin

zukan kafirai. Ku sare kawunan da yatsun kafirai".

Mun ji daga wannan ayar mala'iku ba wai sun karfafi zuciya da kuma duga-dugan

musulmi ba, har ma sun shiga yakin . Abu Dawoud hanafi da Suhail bn Haneef

sun ce " mun kasance muna nuna kafiraia da takubban mu sai su fadi kasa tun

kafin takubban mu su isa gare su. Hakika wadannan mala'iku su ke wannan aiki.

Aya ta 50 a ciki Suratul Anfal ta kara bayyana yadda abin ya faru :

باﺬ�ﻋ اﻮﻗوذ و ﻢهرﺎﺑدأ و ﻢﻬهﻮﺟو نﻮﺑﺮﻀﻳ ﺔﻜﺋﻼﻤﻟا اوﺮﻔآ ﻦﻳﺬﻟا ﻰﻓﻮﺘﻳ ذإ ىﺮﺗ ﻮﻟو

ﻖﻳﺮﺤﻟا

Da za ka ga yadda mala'iku ke daukar ran kafirai, suna dukan fuskokin su da

bayan su (su na cewa) ku dandani azabar wuta"

Wanan ayar tana nuan mana idan mala'iku za su dauki ran kafiri daga jikin shi

suna azabtar da shi ta hanayr bugon shi a fuska da kuma bayan shi da sandar

karfe mai zafi. Allah SWA ya kara da cewa a cikin Suratul Anfal, aya ta 51:

"wannan (azabar) an yi maku ita ne saboda ayyukan da kuka yi wa kan ku,

kuma lallai Allah ba mai zaluttar bayin shi ne ba"

Har-wa-yau, a aya ta 14 Suratul Anfal, Allah SWT yace ku dandani azabe yanzu,

akwai azaba babba a ranar tashin al kiyama. Mun hakikance cewa 'sakraatul

maut' ko kuma lokacin mutuwa lokaci ne mai tsanani ga kafirai, ana azabtar da

su saboda sun ki Allah SWT da manzon Shi. Duk wanda ya ki Allah da manzon

Shi to Allah mai tsananin azaba ne.

Akwai wadansu abubuwan mamaki da suka faru kafin yakin. Misali Annabi

Muhammad SAW ya yi mafarki kafin yakin, kamar yadda aka yi bayani a Suratul

Anfal, ay ta 43:

ﷲا ﻦ�ﻜﻟو ﺮ�ﻣﻷا ﻲ�ﻓ ﻢﺘﻋزﺎﻨﺘﻟ و ﻢﺘﻠﺸﻔﻟ اﺮﻴﺜآ ﻢﻬآارأ ﻮﻟو ﻼﻴﻠﻗ ﻚﻣﺎﻨﻣ ﻲﻓ ﷲا ﻢﻬﻜﻳﺮﻳ ذإ

روﺪﺼﻟا تاﺬﺑ ﻢﻴﻠﻋ ﻪﻧإ ﻢﻠﺳ

Allah ya nuna maka abokan gaba kadan a mafarkin ka, da ya nuna maka yawan

su da kun tsorata kuma da kun yi jayayya a tsakanin ku dangane da lamarin, sai

Allah SWT ya kare ku daga samun rashin jituwa. Allah ya san abubuwan da suke

a zukatan ku"

Koda yake abokan gaba suna da yawa, Allah SWT ya nunawa Annabi su a

mafarkin shi. Da Allah ya nuna mashi makiyan da yawa Annabi Muhammad

SAWda ya shawarci sahabban shi da kuma ya jawao mummunan sabani gare su.

Rashi jituwa ba ya da kyau a koda yaushe, kuma sabani a filin daga ba karamin

bala'I ba ne, Allah sai ya kare musulmi daga wannan bala'in cikin hikima.

Har-wa-yau, wani abin mamaki ya kara faruwa a lokacin yakin kamar yadda Allah

SWT ya bayyana a Surat Al Anfal, aya ta 44:

نﺎ��آ اﺮ��ﻣأ ﷲا ﻲ��ﻀﻘﻴﻟ ﻢﻬﻴ��ﻋأ ﻲ��ﻓ ﻢ��ﻜﻠﻠﻘﻳ و ﻼﻴ��ﻠﻗ ﻢﻜﻨ��ﻴﻋأ ﻲ��ﻓ

رﻮﻣﻷا ﻊﺟﺮﺗ ﷲا ﻰﻟإ وﻻﻮﻌﻔﻣ

ﻢﺘ��ﻴﻘﺘﻟا ذإ ﻮ��ﻤﻜﻳﺮﻳ ذإو

" A lokacin yakin, mummunai sun ga abokan gaba kadan, haka nan abokan gabar

sun ga mummunai kadan, saboda Allah ya yanke abinda zai afku, dukkan

al'amura za a maida su ne ga Allah>>

muminai sun ga abin mamaki nan a filin daga, sun ga abokan gaba kadan sai

suka sami kwarin-gwiwa. Hikimar da ta sa kafirai suka ga muminai kadan shi ne

don kafiran su matso kusa a azabtar da su a filin daga.

Wani abin sha'awa ya faru a lokacin yakin: Shaidan ya zo a siffar Suraqah bn

Malik shugaban kabilar Banu bakr shigo cikin kafirai, ya yaudari kafirai ya nuna

yana tare da su ya rika zuga su yana cewa " Duk duniya babu mai iya murkushe

ku, ni ma mai taimakon ku ne. yayin da shaidan ya ga banagarorin biyu sun

fuskanci juna sai ya tsere ya na cewa " Ni babu ruwa na da ku, lallai ni ina ganin

abinda ba ku gani (mala'iku), ni mai tsoron Allah ne, lallai Allah mai tsananin

azaba ne wannan an yi bayanin shi a Suratul anfal.

Musulmi sun ci wannan yaki sai Allah SWT ya ce da su a cikin Suratul Anfal

ﻪ�ﻨﻣ نﻮ�ﻨﻣﺆﻤﻟا ﻲ�ﻠﺒﻴﻟو ﻰﻣر ﷲا ﻦﻜﻟو ﺖﻴﻣر ذإ ﺖﻴﻣر ﺎﻣو , ﻢﻬﻠﺘﻗ ﷲا ﻦﻜﻟو ﻢهﻮﻠﺘﻘﺗ ﻢﻠﻓ

ﻢﻴﻠﻋ ﻊﻴﻤﺳ ﷲا نإ

ﺎﻨﺴﺣ ءﻼﺑ

" Ku musulmi ba kune ku ka kashe su ba, Allah ne ya kashe su. Kuma kai

(Muhammad SAW) a lokacin da ka jefe su ba kai ne ka same su ba, Allah ne ya

same su. Lallai Allah mai ji ne kuma mai gani ne"

Allah yana cewa Annabi Muhammad SAW da sahabban sa, kada su yi alfahari don

sun ci nasara a yakin. Nasara tana zuwa ne daga Allah kadai. Allah yana tuna

mana yayin da Annabi Muhammad SAW ya dauki kasa da duwatsu a hannun shi

ya watsawa abokan gaba sai ta koma guguwa. Wannan guguwa ta shiga cikin

idanun abokan gaba kuma ta sanya dole suka tsere, kamar yadda kasar nan da

ya jimka ta canza zuwa guguwa da ikon Allah, haka nan ma cin nasarar ya zo ne

da ikon Allah SWT.

Kusa da karshen yakin, sai musulmi suka kasa kan su uku, kashi daya su ka bi

kafarai da suka tsere don kada su dawo, kashi na biyu kuma suka debi

kayayyakin da aka zubar a filin daga, wadannan musulmi da suke talakawa ne

sun yi matukar farin ciki da wannan kayayyakin abokan gaba da suke mawadata,

kashi na uku kuma suka tsaya tare da Annabi Muhammad SAW domin kada wasu

kafirai suyi sumame su far mashi. To akwai matsala babba da ta faru a wajen

yadda za a raba ganimar. Wannan kashin da syuka tattara kayan suna ikirarin na

su ne, domin su ne suka tattara. Kashi na farko su ka ce sai dai a raba da su,

domin sune suka kawo damar da aka tattara kayan. Kashi na uku suma suke ce

ai suna da kaso domin sune suka yi aiki mafi muhimmanci na kare Annabi

Muhammad SAW.

Kamar yadda aka samo daga Ubbadah Bn As Saamit ya ce " an sami matukar

rashin jituwa a tsakanin su har ta kai sun fara aibanta juna. A lokacin babu wani

umarni ta yadda za a raba wanan ganima. Al'ummai da suka shude ba a basu

damar su yi amfani da ganima ba, sai dai su tara su a wuri daya, idan wata wuta

ta zo ta kona su to alama ce ta cewa an karbi wannan jihadi na su.

Allah SWT ya saukar da cikakken bayani ga Annabi Muhammad SAW akan yadda

za a kasafta wannan ganima a cikin Suratul Anfal. Sa'adda sahabban manzon

Allah SAW suka sami labarin wannan shiriya sai dukkan sabanin da suka samu ya

gushe. Sai dukkan ganimar aka raba ta ga dukkan wadanda suka halarcin yakin

kamar yadda Allah SWT ya tsara. Wannan rahama ce daga Allah SWT ga al'umar

Annabi Muhammad SAW da ya basu alfarma da kuma matsayin yin amfani da

dukiyar ganima. Kuma ya koya mana yadda sahabban Annabi Muhammad SAW

suke a hade suna gaggawar bin umarnin Allah SWT.

Kamar yadda wasu masana tarihi da ba musulmi ba su ka fadi, yakin Badar shine

yaki mafi muhimmanci a tarihin dan Adam baki daya, wannan kuma shine ya

samar da dawwamammen tasiri ga tarihin dan Adam.

Mun bi abubuwan mamaki da suka faru a yakin Badar ta yadda taimakon Allah ya

zowa musulmi da suka mika wuya.

Wani mawakin Urdu ya ce " Idan da za ku kawo yanayi irin na Badar da mala'iku

sun sake saukowa sahu-sahu sun kawo maku taimako.

Ina rokon Allah SWT ya taimake mu mu bi tafarkin Annabi Muhammad SAW da

sahabban shi, Ya kuma bamu nasara kamar yadda ya basu a yakin Badar, Amin.

MU'UJIZOZI TARA NA ANNABI MUSA AS

Mutane a zamanin annabi Musa AS ba tare da wata tababa ba suke amincewa da

al'amura na tsafi. Allah SWT ya ba annabi Musa mu'ujizozi guda tara domin ya

gamsar da mutanen shi akan samuwar Allah SWT da kuma cikar ikon Shi. Biyu

daga cikin wadannan mu'ujizozi sanannu ne, sauran bakwai din kuwa ana

mancewa da su.

Kafin mu shiga mu fara bayani a kan wannan al'murra, za mu banbance tsakanin

mu'ujiza da tsafi.

Mu'ujiza wata irin baiwa ce ta musamman wanda wani mahaluki ba zai iya yin ta

ba. Allah SWT yana bad wannan damar ta hannun zababun manzannin Shi.

Sauran alamomin mu'ujiza sune :

Mutumen dake nuna mu'ujiza a koda yaushe mutane ne masu halaye masu

kyawu, kuma ba su nuna mu'ujiza domin su yi wasa da mutane.

Annabawa suna gwada mu'ujiza wadda Allah SWT ya basu, umarni nuna

mu'ujiza yana ga Allah SWT Shin kadai.

Mu'ujiza tana gwadawa karara cewa akwai wani mai iko da ya sanya wannan

abubuwa suke faruwa.

Zababbun manzannin basu ikirarin cewa wannan mu'ujiza saboda wata baiwar

suce ta musamman. Sun yi imani cewa Allah SWT ya yarda wannan ta kasance

domin ya gwada cewa Allah na nan da ikon Shi.

Ba yaudara bace da ake yiwa yan kallo wadda za su gani a matsayin wani abu da

ya wuce tunanin su.

Mu'ujiza kowa ma yana iya kallon ta ba wani sashe ba na yan kallo kadai kamar

yadda tsafi yake.

Annabawa basu gwada alfahari da wannan baiwa da Allah ya basu.

Annabawa basu rokon a basu lada ko kudi ko kuma su yi wani suna.

A bangare guda, tsafi siddabaru ne wanda wasu mutane da ke da mummunan

hali suke aikatawa. Rayuwar su duka bata da kyawu. Su kuwa annabawa ko da

makiyan su sun amince cewa su mutanen kirki ne.

Tsafi wani siddabaru ne a fili wanda ke iya kuskurewa nan-da-nan. A dayan

hannu, mu'ujiza wani al'amari ne na Allah. A misali, Allah SWT ya ce da Annabi

Muhammad SAW

ﻰﻣر ﻦﻜﻤﻟو ﺖﻴﻣر ذإ ﺖﻴﻣر ﺎﻣو

" Ba kai ka yi jifa (da jimkin kasa) ba a yakin Badar, Allah ne yayi (jifar), suratul

anfal 17.

Wannan jimkin kasa a hannu ya koma gagarumar guguwa da umarnin Allah,

wannan ya rikitar da abokan gaba. Wannan guguwa ita ta kawo murkushewar

kafirai daga musulmi yan kadan.

Tsafi mafi yawa ana yin shine domin kudi ko suna.

Ana yin tsafi domin a kawo matsala a tsakanin mutane har ma tsakanin miji da

mata. Yana kawo burgewa, amma idan aka sami akasi yana zamewa hadarin

gaske.

Yanzu zamu koma a kan karamomin annabi Musa AS. Duk lokacin da annabi

Musa AS ya fiddo hannu daga cikin mayafin shi sai ka gan fari kal, kuma ba tare

da wata cuta ba.

Fir'auna, shugaba na wannan lokacin sai ya tattara matsafa na kasar shi, ya

shirya wata gasa tsakanin su da annabi Musa AS. Matsafan su ka tambayi annabi

Musa AS mu zamu fara gwada tsafin mu ko kuma kai za ka fara gwada naka, sai

annabi Musa AS yace " ku fara"

Matsafan nan suka jefa igiya a kasa sai ta zamewa yan kallo macizai. Sai annabi

Musa AS ya jefa sandar shi a kasa. Ba wai sandar ta koma maciji bane kawai, a'a,

har ma sai da ta cinye igiyoyin matsafan nan wanda wannan shi ya kawo faduwar

fir'auna.

Gamsuwa da wannan karamomi guda biyu ya sa wasu da suka dade a cikin kafirci

suka musulunta.

Fir'auna ya cewa wadannan wanda suka musulunta:

نﻮﺒﻠﻘﻨﻣ ﺎﻨﺑر ﻰﻟإ ﺎﻧإ ﺁﻮﻟﺎﻗ , ﻦﻴﻌﻤﺟأ ﻢﻜﻨﺒﻠﺻﻷ ﻢﺛو فﻼﺧ ﻦﻣ ﻢﻜﻠﺟرأ و ﻢﻜﻳﺪﻳأ ﻦﻌﻄﻗﻷ

" Zan sassare maku hannuwa da kafafu da-ban-da-ban, sai musulman suka ce "

Ba damuwa! Ai daman za mu mutu mu koma ga Allah"

Sai wadannan sababbin shiga musulunci suka yi kyakykyawar addu'a. suratul

A'raaf, aya ta 126:

ﻦﻴﻤﻠﺴﻣ ﺎﻨﻓﻮﺗ و اﺮﺒﺻ ﺎﻨﻴﻠﻋ غﺮﻓأ ﺂﻨﺑر

" Ya Allah ka kara mana hakuri, kuma ka dauki ran mu muna musulmi"

annabi Musa AS ya kwashe shekara ashirin yana wa'azi ga kafirai na Masar.

Kafirai sun karya alkawarin su daya bayan daya, suka ci gaba da muzgunawa da

azabtar da wanda suka yi Imani. Allah SWT ya aiko da ayoyi wadanda za su

farkar da Fir'auna da mutanen shi, wadannan ayoyi an yi bayanin su a takaice a

nan kasa:

mutanen Fir'auna sun fuskanci fari na tsawon shekaru babu kayan lambu.

Fir'auna da mutanen shi suka yiwa annabi Musa AS alkawali :idan Ubangijin shi

ya ye masu wannan wahala za su bi tafarkin Allah SWT. Annabi Musa AS yayi

addu'a wannan fari da rashin kayan lambu ya gushe, amma kafirai suka karya

alkawarin su suka ce sai ta wuce wani dan lokaci.

Allah SWT ya aikio masu da ambaliyar ruwa domin ya ladabtar da su. Kafirai suka

yi alkawarin cewa da zarar ya tsaya za su karbi musulunci. annabi Musa AS ya yi

addu'a Allah ya tsaida ruwan. Wannan ruwa mai yaaewa sai ya kasance an sami

amfani mai kyau. Ganin wannan amfanin gona yayi kyau kwarai sai kafirai suka ji

hankalin su ya kwanta, don haka, ba su canza komai ba a kan alkawarin da su ka

yiwa annabi Musa AS.

Allah SWT ya aiko da fara ta zo ta cinye abincin da yake a tsaye. A haka amfanin

gonar da ya sanya kafirai murna, yanzu a kan idon su ya bace. Har-wa-yau, su ka

rokon annabi Musa AS ya roka masu Allah ya raba su da wannan bala'i. suka ce

wa annabi Musa AS " Wannan karon dai ba za mu karya alkawarin mu ba. annabi

Musa AS ya yi roko ga Allah, sai ba a sake ganin fara ba, amfani ya farfardo. D di

mutanen nan suka suka ga suna da abinci dankare da gidajen su, har-wa-yau, sai

suka manta da alkawalin su.

A lokacin na gaba si Allah ya aiko masu da kwari suna cinye abincin da aka boye,

kuma suka sake zuwa wajen annabi Musa AS da dai alkawalin da suka saba.

annabi Musa AS ya yi hakuri ya sake yin addu'a aka cire masu ladabtarwar da aka

yi masu. Sai suka ji ai suna da abinci mai yawa da zasu dafa su ci su more

rayuwa, ba su bukatar Allah SWT sam.

Allah SWT ya azabtar da su ta hanyar aiko da kwaddi a wannan kasar. Kwaduna a

ko ina, a gidaje, a tukunyar abinci, a dakin ajiyar abinci, da kuma cikin ruwan da

za su sha. Kafirai su ka yi kuka babu mataimaki. Sai suka rokin annabi Musa AS

yayi addu'a sun yi alkawalin za su musulunta da zaran sun fita daga cikin wannan

matsala. Annabi Musa AS mai zuicya mai tausayi yayi addu'a Allah ya cire

kwadunan. Har-wa-yau, kafirai suka sake karya alkawalin su, sai ma suka kara

bijirewa, sai suka ce lalli Musa shahararren matsafi ne".

Allah SWT ya sake turo masu wani bala'in na jini. Idan suka dauko ruwa daga

rijiya sai ya koma jini. Duk wani abincin su ya cika da jini. Idan suka yi kokarin

yin girkin abinci sai sai ya koma jini. Abin mamaki, mabiya annabi Musa AS su an

kebe su daga wannan, yana faruwa ne kadai a gidajen kafira. Bugo da kari, idan

kafiri ya roko ruwa daga gidan mumini, sai ya koma jini da zaran za su yi amfani

dashi.

Sai mutanen Fir'auna su ka hanzarto zuwa wajen annabi Musa AS da suka karya

bayan da aka raba su da akubar, shine yasa Allah ya ce :

"su masu girman kai ne kuma manyan masu laifin ne a ko wane lokaci"

Yanzu kafirai suka hadu da wata irin annoba ta agana. A kiyasi, mutane 70,000

ne suka mutu. Kuma suka sake rokon annabi Musa AS yayi masu addu'a. babu

makawa, wannan lokaci za su bi tafarkin Allah SWT idan aka kauda masu wanna

bakin-ciki.

Ba wai sun karya sun karya alkawalin su ba ne kadai, har-wa-yau, suna zargin

wannan bala'i nasu ya faru ne a dalilin kasancewar annabi Musa a cikin su, sai

suka fidda annabi Musa AS da mutanen shi daga gidajen su, suka bisu don su

kashe su. Lokacin da musulmi suka je bakin teku, Allah SWT ya raba teku domin

su, suka wuce salim-alim. Fir'auna da mutanen shi cikin fushi suka bisu sai ruwa

ya cinye su.

Sun yi bayani cewa farin da aka ayi da kuma karanci kayan lambu sai da ya

kwashe shekara bakwai. Sauran horon sun dauki sati guda guda, kuam sun sami

sati uku a tsakanin su. Duk wannan tunatarwa ba ta taimake su ba su fito daga

cikin duhun kin yin imani.

Wannan an yi bayanin shi a cikin Suratul A'raaf, aya ra 130-133.

ﻢﻬﺗءﺂ��ﺟد اذﺈ��ﻓ , نﻮ��ﻌﺟﺮﻳ ﻢ��ﻬﻠﻌﻟ تاﺮ��ﻤﺜﻟا ﻦ��ﻣ ﺺ��ﻘﻧ و ﻦﻴﻨ��ﺴﻟﺎﺑ نﻮ��ﻋﺮﻓ لﺁ ﺂﻧﺬ��ﺧأ ﺪ��ﻘﻟو

ﻢهﺮﺋﺎ�ﻃ ﺎ�ﻤﻧإ ﻵأ , ﻪ�ﻌﻣ ﻦ�ﻣو ﻰ�ﺳﻮﻤﺑ اوﺮ�ﻴﻄﻳ ﺔﺒﻴ�ﺼﻣ ﻢﻬﺒ�ﺼﺗ نإو ﻩﺬ�ه ﺎﻨﻟاﻮﻟﺎﻗ ﺔﻨﺴﺤﻟا

ﺎ�ﻤﻓ ﺎ�ﻬﺑ ﺎﻧﺮﺤ�ﺴﺘﻟ ﺔ�ﻳاء ﻦ�ﻣ ﻪ�ﺑ ﺎ�ﻨﺗﺄﺗ ﺎ�ﻤﻬﻣ اﻮﻟﺎ�ﻗ و نﻮ�ﻤﻠﻌﻳ ﻻ ﻢهﺮﺜآأ ﻦﻜﻟو ﷲا ﺪﻨﻋ

تﻼ��ﺼﻔﻣ تﺎ��ﻳاء مﺪ��ﻟاو ﻞ��ﻤﻘﻟا و داﺮ��ﺠﻟاو نﺎ��ﻓﻮﻄﻟا

ﻢﻬﻴ��ﻠﻋ ﺎﻨﻠ��ﺳرﺄﻓ , ﻦﻴﻨﻣﺆ��ﻤﺑ ﻚ��ﻟ ﻦ��ﺤﻧ

ﻦﻴﻣﺮﺠﻣ ﺎﻣﻮﻗ اﻮﻧﺎآو ضرﻷا ﻲﻓ اوﺮﺒﻜﺘﺳﺎﻓ>>

Hakika, azabtar da mutanen Fir'auna ta hanyar shekarun fari da karancin 'ya'yan

itatuwa da fatan za su dawo ga Allah"

Amma idan wani abu mai kyau ya zo masu sai su ce "wannan shine namu", idan

wani abin sharri ya same su sai su danganta shi da Musa da da mutanen shi. Ka

sani! Sharrin da ya ke bibiyar su daga wurin Allah yake, amma da yawa daga

cikin su ba su san haka ba"

Suka ce (wa annabi Musa AS) duk wani wata aya da zaka zo mana da ita don ka

tsafe mu da ita to mu fa ba za mu yi imani da kai ba"

Sai muka aiko masu da ambaliyar ruwa da fara, da kwarkwata da kwaduna da

jini, a matsayin ayoyi, amma sai su ka kasance masu girman kai suka kasance

'yan ta'adda "

A kan wannan, muna iya yanke hukunci / samun fa'idoji daga wannan bayani. :

* Mutane nan-da-nan suke mantawa da Allah SWT idan suna cikin wadata duk da

cewa ya kamata kwanciyar hankali ta kasance karin godiya ga Allah SWT. Abin

takaici, mafi yawan mu abin ba haka yake ba. Misali, duk da yadda aka bamu

kayan more rayuwa da jin dadi, amma kadan ne daga cikin mu suke zuwa

masallaci a koda yaushe.

* Allah yana son ya gwada shiriya har ga masu aikata zunubai ko da yaushe.

* Allah SWT ya na ya yafe zunubai a ko da yaushe.

* Annabawa suna da wani irin hakuri da sanin ya-kamata, shine ya sa Allah SWT

ya zabe su.

Wadanda suka sami shiriya sai su dauka cewa sun yi sa'a kuma su godewa Allah

SWT.

Muma akwai wata mu'ujiza a tare da mu wadda bata karewa- shine Al qur'ani mai

girma. Sai mu bi shiriyar Al qur'ani ko mun sami nasara a rayuwar mu da kuma

gobe kiyama.

Ina rokon Allah ya kara rahma a gare mu.

RANAR HISABI

Sa'adda annabi muhammad SAW ya fara wa'azin addinin musulunci a Makka,

sakon shi ya kunshi abubuwa uku kamar haka:

1. Babu wani abin bautawa sai Allah SWT shi kadai. Kada ka hada Allah da

komai ta ko wace hanya. Mutanen Makka ba su damu da su bautawa Allah shi

kadai ba, sun fi so su hada shi da wani. A saboda haka ba su iya su yi wa manzon

Allah SAW gardama da tsanani ba wajen kare ra'ayin su.

2. Annabi Muhammad SAW ya ce " Ni manzon Allah ne ". mutanen Makka basa

so su yarda da haka amma babu dama suce ba gaskiya ya ke fada ba, tunda

mutanen sun san shi da cewa shi "Ameen" ne, wato amintacce. Don haka

mutanen Makka ba su iya musunta wannan sabon aike

3. Annabi Muhammad SAW yace akwai wata rana da za ta zo, kuma mutane za

a saka ma su da abinda suka aikata. Za a basu lada ko kuma a yi masu azaba

gwargwadon ayyukan su a ranar hisabi. Wannan shine ya ba mutanen Makka

dama su karyata wannan sabon aike. Mutanen Makka suka ce da annabi

Muhammad SAW, suratul Waqi'ah aya ta 47-48 :

نﻮﻟوﻷا ﺎﻧءﺎﺑﺁ وأ , نﻮﺛﻮﻌﺒﻤﻟ ﺎﻧإء ﺎﻣﺎﻈﻋ و ﺎﺑاﺮﺗ

نﺎآ اذإء نﻮﻟﻮﻘﻳ اﻮﻧﺎآ و

(kafirai) suna cewa "shin yanzu idan mun zama kasa da kasusuwa za a tayar da

mu, har ma da kakannin mu suma (za a tada su)?.

Mutanen Makka ba wai suna wannan magana ba ne kawai, har ma su na kiran

annabi muhammad SAW mahaukaci. Allah SWT ya basu amsa a suratul Waqi'ah,

aya ta 49-56:

ﻢ���ﻜﻧإ ﻢ���ﺛ مﻮ���ﻤﻠﻌﻣ مﻮ���ﻳ تﺎ���ﻘﻴﻣ ﻰ���ﻟإ نﻮ���ﻋﻮﻤﺠﻤﻟ

ﻦﻳﺮ���ﺧﻵا و ﻦﻴ���ﻟوﻷا نإ ﻞ���ﻗ

نﻮ�ﻄﺒﻟا ﺎ�ﻬﻨﻣ نﻮﺌﻟﺎ�ﻤﻓ مﻮ�ﻗز ﻦﻣ ﺮﺠﺷ ﻦﻣ نﻮﻠآﻵ نﻮﺑﺬﻜﻤﻟا نﻮﻟﺎﻀﻟاﺎﻬﻳأ

ﻦﻳﺪﻟا مﻮﻳ ﻢﻬﻟﺰﻧ اﺬه ﻢﻴﻬﻟا بﺮﺷ نﻮﺑرﺎﺸﻓ ﻢﻴﻤﺤﻟا

ﻦﻣ ﻪﻴﻠﻋ نﻮﺑرﺎﺸﻓ >>

ta 'Zakkuum'. Za ku cika ciki da ita. Za ku sha tafasashshen ruwa. Irin shan

rakumma. Wannan shine masaukin su a ranar sakamako>>.

Kalmar 'Nuzul' na nufin abinda za a sauke su da shi da zarar sun iso. Kuma

kalmar 'Nuzulu hum' tana nufin farkon abinda za a yi masu. Abinda zai biyo baya

ya fi tsanani.

Mutanen Makka kuma sun ce, Suratul Mulk, aya ta 25:

ﻦﻴﻗدﺎﺻ ﻢﺘﻨآ نإ ﺪﻋﻮﻟا اﺬه ﻰﺘﻣ نﻮﻟﻮﻘﻳو

Kuma suna cewa yaushe ne wannan rana (da ake yi mana alkawali) za ta zo?

Idan abinda kake fadi gaskiya ne?.

Allah SWT ya basu amsa a aya ta 26:

ﻦﻴﺒﻣ ﺮﻳﺬﻧ ﺎﻧأ ﺂﻤﻧإ و ﷲا ﺪﻨﻋ ﻢﻠﻌﻟا ﺎﻤﻧإ لﺎﻗ

(ya Muhammad)! Ka ce da su " ilmin wannan rana ya kadaita ne a wurin Allah. Ni

kawai mai gargadi ne">>.

Mutanen Makka suna tambayar ranar hisabi da wasa ko da yaushe. A cikin

Suratun Naba'i, aya ta 4-5 Allah SWT ya ce :

نﻮﻤﻠﻌﺗ فﻮﺳ ﻼآ ﻢﺛ

نﻮﻤﻠﻌﺗ فﻮﺳ ﻼآ

A na nufin cewa za ku sani game da ita a lokacin mutuwa da ake kira 'sakratul

maut' a Barzakhu, (wanda lokaci ne tsakanin mutuwa da ranar hisabi) kuma

lallai za ku san ta idan kuka fuskanci ranar a lokacin hisabi.>>

A wani lokaci Allah SWT yana bada takaitacciyar amsa domin mu gane ba wani

abu bane mai wuya wajen Allah SWT ya kawo wannan ranar hisabi. Surat an

Naba', aya ta 6-16 tana cewa :

و , ﺎﺗﺎﺒ�ﺳ ﻢﻜﻣﻮ�ﻧ ﺎ�ﻨﻠﻌﺟ و , ﺎ�ﺟاوزأ ﻢآﺎﻨﻘﻠﺧ و , ادﺎﺗوأ لﺎﺒﺠﻟا و , ادﺎﻬﻣ ضرﻷا ﻞﻌﺠﻧ ﻢﻟا

ﻦ��ﻣ ﺎ��ﻨﻟﺰﻧأ و , اداﺪ��ﺷ ﺎﻌﺒ��ﺳ ﻢﻜﻗﻮ��ﻓ ﺎ��ﻨﻴﻨﺑو , ﺎ��ﺷﺎﻌﻣ رﺎ��ﻬﻟا ﺎ��ﻨﻠﻌﺟ و , ﺎ��ﺳﺎﺒﻟ ﻞ��ﻴﻠﻟا ﺎ��ﻨﻠﻌﺟ

ﺎﻓﺎﻔﻟأ تﺎﻨﺟو , ﺎﺗﺎﺒﻧ و ﺎﺒﺣ ﻪﺑ جﺮﺨﻨﻟ , ﺎﺟدﺎﺠﺛ ءﺂﻣ تاﺮﺼﻌﻤﻟا,

A nan, Allah SWT yace idan zai yi duk wadanna abubuwa da ya bayyana,mai zai

hana ya iya kawo ranar hisabi? A misali, ya samar mana da barci wanda zamu

sami cikakken hutu, ko da wani yana son ya kauce mashi (yin barcin) sai ya zo a

cikin rahamar Allah SWT. Bayan wannan barcin, mutum zai tashi cikin karazan da

karfi. Idan Allah SWT zai ba mutum wannan haka nan daga wannan al'uma zuwa

wata al'umar, me zai hana ya iya kawo ranar hisabi? Duk wannan misalai suna

bukatar irin wannan bayanin. Za mu takaita domin mu yi bayanin wasu abubuwa

na ranar hisabi.

Annabi muhammad SAW ya kawo mana albishir da kuma gargadin azabar ranar

hisabi ga wadanda basu bi shiriyar Allah SWT ba. Musulmi sun amince da ranar

hisabi ko da ba su ganta ba. Allah SWT cikin rahmar shi ya yi bayanin irin

abubuwan da za su wakana a ranar hisabi saboda fahimtar mu da shiryuwar mu.

Da farko, bari mu ji yadda aljanna take. Allah SWT a cikin Surat Al Tur, aya ta

17-20 ya ce :

اﻮ�ﻠآ , ﻢﻴ�ﺤﺠﻟا باﺬﻋ ﻢﻬﺑر ﻢهﺎﻗوو , ﻢﻬﺑر ﻢهﺎﺗﺁ ﺂﻤﺑ ﻦﻴﻬآﺎﻓ ﻢﻴﻌﻧ و تﺎﻨﺟ ﻲﻓ ﻦﻴﻘﺘﻤﻟا نإ

ﻦﻴﻋ رﻮﺤﺑ ﻢهﺎﻨﺟوزو ﺔﻓﻮﻔﺼﻣ رﺮﺳ ﻰﻠﻋ ﻲﻨﺌﻜﺘﻣ , نﻮﻠﻤﻌﺗ ﻢﺘﻨآ ﺎﻤﺑ ﺎﺌﻴﻨه اﻮﺑﺮﺷاو

Hakika masu tsoron Allah za su kasance a cikin lambu (Al janna) suna masu farin

ciki da abinda Ubangijin su ya basu, kuma Ubangijin su ya tsare daga azabar

wuta. (za a ce dasu) ku ci, ku sha, ko koshi saboda abinda kuka kasance kuna

aikatawa. Suna masu kishingida a kan gadaje na daraja wanda aka shirya su.

Kuma mun aura masu 'yan mata masu kyawun idanu>>

Har-wa-yau, a cikin suratul Haaqqah yana cewa :

Allah SWT ya sake bayani a kan mutanen da ke zaune a gidan aljanna a cikin

Suratu Yasin, aya ta 55-58 :

abinda suka bukata. Za a gaishe su da kalmar 'Salam' daga Ubangiji mai jinkai.>>

kamar yadda wannan aya ta nuna, idan mutanen gidan aljanna suka sami

kowane irin karimci daga wurin Allah SWT, Allah zai tambaye su " Ya ku bayi na

masu biyayya me kuma kuke so ?" 'Yan aljanna sai su ce " Ya Allah mun gode

maka, mun sami komi" Allah SWT sai ya ce dasu "Bari in baku wani abu wanda

duk ya fi karimcin da kuka samu". A wannan lokaci sai a girmama su cikin jin

dadi su ga Allah SWT kuma Allah SWT sai ya gaishe su da 'salam'.

Har-wa-yau, Allah SWT ya yi bayanin abubuwan da za su faru a ranar hisabi da

azabar da za a yi wa wadanda suka fandare. Misali, a cikin Surat al Mulk, aya ta

6-10 Allah SWT ya ce:

ﺮﻴﺼﻤﻟا ﺲﺌﺑ و ﻢﻨﻬﺟ باﺬﻋ ﻢﻬﺑﺮﺑ اوﺮﻔآ ﻦﻳﺬﻠﻟ و,

MATSAYI DA HAKKOKIN NA-MIJI DA MACE A MUSULUNCI

Allah SWT ya ce a cikin surat An Nisa'i aya t a32:

" kada ku yi gurin samun abinda Allah SWT ya fifita sashen ku a akan sashe da

shi. Maza suna da ladar abinda suka yi, (haka nan ma) mata suna da ladar

abinda suka yi. Allah masani da dukkan komi".

Wajibi ne fahimtar wannan ayar don sanin ka'idoji da hakkokin mazaje da mataye

a musulunci. Dalilin da suka sanya aka saukar da wannan ayar yana da bansha'awa.

Ummu Salama RA matar annabi Muhammad SAW ta tambayi annabi

SAW " tunda mata suna samun rabin abinda maza suke samu a gado, ke nan za a

bamu rabin ladar ayyukan mu na gari idan aka kwatanta da maza?" ba wai tana

so ta kawo rudani a kan abinda ake ba maza bane, a'a, ta yi tambayar ne saboda

ta sami ilmi. Wadansu mata ma cewa su ke dama a ce su maza ne da sun shiga

jihadi domin su sami lada a wurin Allah SWT.

Duk amsoshin wadannan tambayoyi suna kumshe ne a cikin wannan aya. Allah

SWT yana cewa da Ummu Salama da daukacin musulmi, kada su kwaikwayi wasu

da Alla SWT ya daukaka su a kan su. Bari mu kara kawo misali. Allah SWT ya

halicci wasu gajeru, wasu dogaye, wasu kuma masu kyawun gaske. Idan Allah

SWT ya sa wani mutum abin sha'awa ba zai iya kame kan shi ba, sai ma ya kara

samun damar tafka sabo. Amma sai Allah ya kare shi daga yin sabo ta kin maida

shi mai kyau. Wadansu mutane kuma talakawa ne, wadansu kuwa samun duniyar

su kadan ne. Allah ya sani idan ya maida su masu arziki ko wani matsayi na

duniya wanda ya fi nasu, da ba za su yi adalci ba. Haka nan Allah SWT ya zabi

wani fili domin ayi masallaci a cikin garin. Wannan fili ya fi duk sauran wani fili da

yake a cikin garin daraja. Mana yin sallah (tahiyyatyl masjid) duk lokacin da

muka shiga masallacin don mu nuna girmamawar muga wannan sama da duk

sauran wuraren da ke cikin garin. Za mu yi mamakin yadda Allah SWT ya zabi

birnin Makka a cikin hamada aka gina dakin Allah, wanda shine wuri mafi daraja a

nan duniya. A nan muna iya cewa Allah SWT shine masani, akwai hikima wajen

sanya wani abu ya dara wani wanda ya zarce fahimtar mu. Fifiko tsakanin wani

da wani ba wani abu bane na son kai kuma abu ne da ya wuce iyawar mu. Allah

SWT yana bada baiwar sa ne ga wanda ya so. Kuma Allah SWT ya fifita wasu

manzanni a kan wasu ta hanyoyi da dama. Allah SWT yace a cikin Surat Al

Baqarah, aya ta 253:

"Mun fifita wasu manzannin akan wasu".

Da wannan takaitaccen bayani, a bayyane yake cewa duk abinda Allah SWT ya

bamu sai mu yi farin cikin da shi. Idan mace aka bata matsayi irin na na-miji ba

za ta iya cika wannan matsayi ba kamar yadda ya kamata. Allah SWT ya amsawa

Umm Salama RTA da sauran mata babu rabin lada ga mata idan aka kwatanta da

maza. Maza da mata za a basu lada dai-dai a bisa ayyukan su masu kyau. Ayoyi

da dama a cikin Al qur'ani mai girma sun yi bayanin hakan. Misali, Allah SWT

yace a Surat Gaafir ko Mu'min, aya ta 40:

" Duk wanda ya aikata aiki na-gari na-miji ne ko mace, wadannan sune za su

shiga aljanna ana azurta su a cikin ta ba tare da lissafi ba"

Fitattun mata kamar Umm Ammarah Al ansariyya da Asma' Bint Umais, da sun

nuna damuwar su ga annabi Muhammad SAW kamar yadda ya zo a cikin 'Tirmizi',

sun ce yaya mafi yawan lokaci Allah SWT ya na maganar maza kai tsaye, muna

tunanin anya mata ma suna da irin wadannan alkawulla. Sai Allah SWT ya saukar

da a cikin Surat Al Ahzaab, aya ta 35:

"hakika musulmai maza da musulmai mata, masu imani maza da masu imani

mata, maza da mata masu tawali'u, maza da mata masu gaskiya, maza da mata

masu hakuri, maza da mata masu yin sadaka, maza da mata masu yin azumi,

maza da mata masu kare al'aurar su (daga zina), maza da mata masu ambaton

Allah, Allah yayi masu tanadin gafara da lada mai girma".

A nan, mata suna da dama daya da lada kamar maza a musulunci. Mutane suna

aikata laifuffuka da zunubbai a lokacin da basu bi wannan shiriyar ta Allah ba.

Wadansu suna yin sata domin suma su yi arziki, wasu ma sai su kashe wasu

domin su mallake dukiyar su. Shiriyar Allah ta tafiyar da irin wannan tunani na

Hassada da hali na ta'addanci. Da mutane suna farin ciki da kuma wadatuwa da

abinda Allah ya basu da basu aikata ta'addanci ba. Muna sane cewa wasu

mutanen masu arziki ne sosai, wadansu kuma suna da tarin ilmi da gaske kuma

sun yi fice. An yarje mana mu roki Allah ya bamu wannan ta hanyar rahmar Shi.

Zai bamu idan yana da kyau a gare mu, tunda Ya san komi.

Idan muka fahimci ayar da ta gabata, da cikin sauki zamu ji dadin sanin hakkokin

dake a kan maza da kuma mata a musulnci. Kamar yadda ya zo a cikin Surat An

Nisa', ya ta 34:

" Maza sune masu karewa da kuma jibintar mata, saboda Allah ya fifita dayan

sashen akan dayan, saboda (su maza) suna ciyarwa daga dukiyoyin su (domin su

dauki dawainiyar matan). Saboda haka, mace ta gari itace mai biyayya ga Allah

da kuma mijin ta, kuma tana tsarewa idan mijin ta baya nan abinda Allah ya

umarce ta ta tsare, (misali, mutuncin su da kuma dukiyoyin mijin su)".

A nan ba ana nufin ba maza su kasance masu kama-karya akan mata.

Za mu kawo wadansu ayoyi a alqur'ani mai girma domin mu gane ma'anar ta.

Allah SWT yace a aya ta 19 a surat An Nisa':

" Ku zauna da su a cikin kyautatawa"

Haka kuma a Surat Al Baqarah, aya ta 228, Allah SWT yace :

"Mata suna da hakki a kan maza kamar yadda su ma maza suke da hakkin a kan

mata.

A aya ta 233 a Surat Al baqarah, Allah SWT ya ce:

"Ku shawarci matan ku a kan abubuwan da suka jibinci rayuwar gidan ku"

Tuntuba abu ne mai matukar muhimmancia rayuwar musulmi.

A bisa ga haka, mazaje ba wai kawai za su shawarci matan su bane, su ma zauna

da su a mutunce kuma su ba su damar su. Bayan sun yi wannan abu mai

muhimmanci sai su rinka yanke shawara daya. Hakika, maza sune su ke daukar

babban nauyi, idan su ka yi son-kai ko suka yi abinda bai dace ba to zai dawo

masu a rayuwar su ta gobe kiyama. A wata fadar kuma su maza sune masu

hakkoki da Karin jibintar al'amura. Idan aka maida mace kamar na-miji, ba za tai

ya jibintar wadansu al'amura masu wahala ba. A nan mata ba za su so su

kasance kamar maza ba, haka nan kuma maza. Kowa Allah ya bashi matsayin da

ya dace da shi. Na-miji zai gudanar da hakkokin shi ta hanyar da ta fi dacewa

haka nan ma mace za ta gudanar da na ta.

Bari mu fahinci hikimar baiwa mace rabin abinda na-miji ke samu a gado. Dun

abinda mace ta samu na ta ne, tana da damar ajiye shi don karon kan ta, ba ma

za ta kashe ko kwabo domin gudanar da wani sha'ani na gidan ta ba. Idan ita

daya ce (ba ta da aure) mahaifin ta zai dauki nauyin rayuwar ta, idan kuma

matar aure ce mijin ta ne zai jibinci al'amuran ta kome arzikin ta. Idan kuma

bazawara ce tana da 'ya'ya ko kuma a'a sai ta koma wajen mahaifin ta ya dauki

dawainiyar ta idan ya zama tilas. A koda yaushe dai, akwai namiji da zai taimake

ta. Idan kuma namiji ya karbi ninkin abinda mace ta samu ba zai ajiye domin kan

shi ba, dole ya kasha shi saboda iyalan shi, matar shi ko 'ya'yan shi da kuma

sauran dangi. Akan haka muna iya cewa mace tafi namiji cin moriyar gadon duk

da cewa ta samu rabin gadon ne idan aka kwatanta na namiji. Wannan shine

fifikon da mata suka samu a musulunci.

Yana da muhimmanci mu duba yadda rayuwar mata ta kasance kafin zuwan

musulunci. Laarabawa sun kasance suna binne 'ya'yan su mata da ran su, kuma

ana daure gashin mace a jikin rakumi a sanya rakumin ya ruga. Wannan shine

rayuwar larabawa a wancan lokacin. Mata a wannan zamanin ba a barin su su

sami wani abin kirkia gado. Musulunci ba wai kawai ya baiwa mata dama daya

ne, a'a, ya ma ba su damar mallaka da kuma cin gado.

Za mu kuma duba alamomin mace ta gari. Allah SWT ya ce a cikin Al qur'ani a

cikin Surat An Nisa', aya ta 34:

"Mace ta gari itace mai biyayya ga Allah da kuma mijin ta, kuma tana tsarewa

idan mijin ta baya nan abinda Allah ya umarce ta ta tsare, (misali, mutuncin su

da kuma dukiyoyin mijin ta)".

Annabi Muhammad SAW ya ce mace ta gari ita ce wadda idan miinta ya gan ta

sai hankalin shi ya kwanta, idan ya umar ce ta sai ta yi mashi biyayya, kuma tana

tsare kan ta da kuma dukiyar sa idan baya nan.

A nan, mace ta gari dole ne ta bi dokokin dokokin Allah, kuma su yarda a zuciyar

su da dokokin da ya sanya ma su na yin biyayya ga mazan su a matsayin

shuwagabannin su a kan komi. Kuma an umarce su da su tsare kan su daga

shaidan wanda karara makiyin mu ne, kuma su kare dukiyoyi. Bai kamata su kai

wata ziyara sai da izinin mijin su. Har-wa-yau, dole ne su tsare muhimman

kadarorin mijin su kamar 'ya'ya. A kuma wata fadar dole ne su ilmantar da

tarbiyyantar da 'ya'yan ta fuskar musuluncin su, cusa masu kyakykyawan hali.

Wadannan abubuwa suna da nauyi kwarai. Allah yayi alkawali a wannan ayar

cewa zai taimake su ya tallafa masu domin su sauke wannan matukar sun yi

gaskiya wajen neman yin hakan.

Musulunci ya tsara yadda za ladabtar da mata a cikin Surat An Nisa', aya ta 34,

Allah SWT ya ce :

"wadannan matan da kuke tsoron bijirewar su, sai ku yi masu nasiha sannan ku

kaurace masu a wajen kwanciya, daga karshe ku buge su. Amma idan sun dawo

da biyayya, kada ku nuna masu fushin ku. Lallai Allah shine madaukaki mai

girma".

A nan, muna ganin hanyoyin da za a bi a gyara al'amurra a kowane mataki. Da

farko za a bi hanyar shawarwari na cikin gida sannan kuma sai shawrwari daga

waje. A bin takaici, musulmi a fadin duniya sun kauda kai daga wadannan

muhimman matakai, sun bari sai da matsaloli su ka taru sun wuce a yi maganin

su. Musulmi su na jin tsoron ace suna da matsala ta wajen sanin halayyar

mutane, don haka sai suke gujewa neman shawarwari. Gaskiya ne kowane irin

mutum yana bukatar shawarar wani a rayuwar shi. Ina rokon mu da mubi

wadannan hanyoyi da aka tsara da kyau da kuma sanin ya-kamata a duk lokacin

da wata matsala ta taso.

Abu na biyu, ku kaurace masu daga gadaje. Wannan ba yana nufin a matsawa

mace ta bar gida ba, haka nan kuma, mace kada kawai don karn kan ta tafi gida

saboda wannan sabani. Kamar yadda wasu malamai su ka ce : kada su raba

dakin kwanciya, an unmarce su kawai su kauracewa juna a akan gado. Hikimar

yin haka shine: yin hakan abu ne da ke da wuyar daurewa. Wannan mawuyacin

hali yana iya canja masu ra'ayi su koma yadda suke.

Abu na uku ; an anincewa na-miji ya bugi matar shi domin ya ladabtar da ita. Ba

wai ana nufin ya ware damtse ya naushe ta a ido ko a fuska ko a wasu bangarori

na jikin ta ba. Kamar yadda wasu suka ce : ka dan buge ta da buroshin gugar

hakori ko kuma wani abu ba mai nauyi ba ka ladabtar da ita.

Annabi Muhammad SAW yace " Namiji na kirki ba zai ladabtar da matar shi ba da

duka"

Muna iya sani cewa babu wani annabi da yake bugon matar shi, har da annabi Lut

AS.

Annabi Muhammad SAW ya ce wanda suke kyautatawa matan su za su kasance

kusa da ni a cikin aljanna.

Allah ya bamu shawara " Idan suka dawo suna bin umarnin ku kar ku yi

maganganu gatsai-gatsai gare su, wannan zai tunatar da su rashi jituwa ta baya.

Na miji an sake bashi umarni daga Allah SWT kada ya manta Allah SWT shine

babba kuma madaukaki. Shine ya maida shi shugaba a kan matar shi kuma

namiji zai kasance mai kididdiga a kan ayyukan ayyukan shi gare shi. Saboda

haka, dole ya yi mata adalci a kan wadannan matakai.

Allah SWT ya sake cewa a cikin surat An Nisa', aya ta 35:

Idan kuna jin tsoron sabani a tsakanin su (miji da mata) ku sanya masu sulhu a

tsakanin su, daya daga dangin shi daya kuma daga dangin ta, idan suna nufin

gyara Allah zai daidaita tsakanin su ma'auratan. Hakika Allah ya kasance masani,

ya san komi da komi".

A nan, idan sabani ya abku tsakanin miji da matar shi kuma ba a warware shi ba,

sai mu sanya masu sulhu a tsakanin daya daga kowane bangare. A nan Allah yayi

kyakykyawan alkawali. Allah ya ce idan dukkan su suka kawo shiriya a tsakanin

su Allah zai tabbatar da haka tunda abinda ke a zuciyar kowa. Malamai su ka ce

"wannan Magana tana tana nufin miji da matar har ma da masu shiga tsakani na

dukkan bangarorin. A nan idan dukkan su hudun suna neman gyara a kan

wanann ma'ala to Allah yayi alkawalin zai kawo ta, tunda shi masani ne game da

niyyar mu.

Musulunci kuma ya bada dama bai daya ga namiji da kuma mace kuma ya tsara

wasu hanyoyi da za a bi idan sabani ya abku. Kwata-kwata ba daidai bane kace

mata su kasance gaba –gaba a kan gida. Maza da mata kowanne an shata mashi

matsayin shi wanda ko wanne zai iya. Mata sun iya cin gado kuma su ajiye

abinda su ka samu har abada.

Sahabban Annabi Muhammad SAW suna tsammanin mata an basu dama da yawa

kuma an daga matsayin su na kafin zuwan Musulunci. Suna ganin wadansu da

aka basu a janye. A nan suka yi ta tambayar Annabi Muhammad SAW akai-akai

dangane da wahayi a kan damar da aka ba mata. Allah yace a cikin Surat An

Nisa' aya ta 127:

" sun tambaye ka game da ka'idojin sharia dangane da mata. Allah ya umarce ka

a akan dagane da su da abinda aka karanta maku a cikin littafi dangane da

marayun 'yan mata wanda baku ba bangare daga gado wanda kuke son ku aura,

kuma dangane da yaran da aka zalunta kuma ku tsaya tsayin daka akan yin

adalci ga marayu. Duk abinda kuka yi mai kyau Allah har abada yana sane da shi.

A wata fadar, dama daya da daukakar darajar mata tana nan daram har abada a

addinin Musulunci.

Ina rokon Allah ya sa mu bi wannan umarni ta fuskar iyalin mu domin mu

daukaka matsayin al'umar Musulmi, Amin.

ZATO, SA-IDO DA GULMA

Allah SWT ya ce a cikin suratul Hujuraat aya ta 12:

" Ya ku wanda kuka yi imani ku daina zargi (zato) domin zargi laifin ne , kada ku

rinka sa-ido, kada ku yi gulma a tsakanin ku, dayan ku yana son ya ci naman dan

uwan shi da ya mutu? Ba za ku so ba , to ku ji tsoron Allah. Hakika Allah shine

mai karbar tuba mai jin-kai".

A nan, Allah SWT yana koya mana mutunta juna da kuma zamantakewa a

ayyukan mu na yau da kullum. Za mu bisu daya bayan daya mu fara da zargi.

Akwai zargi mai kyau da zargi marar kyau. Imam Abubakr Jassas ya kasa zargi

gida hudu, kamar yadda yayi bayani a littafin shi ' Ahakamul qur'an'

Wadannan matakai guda hudu sune : haram, wajib, mustahab, da mubah.

Zargin da ba a yarda da shi ba shine mutum ya dinga cewa a ranshi " Allah zai

azabtar da shi, Allah zai yi mashi akuba, yanke tsammani aka n rahama da jin

kan Allah SWT. Manzon Allah SAW yace:

"Ka sanya kyakykyawan fata wurin Uban gijin ka har ranar mutuwar ka"

A Hadisi Kudusi kuma, Allah SWT yace " ina yi wa bawa na a yadda ya sanya

tsammani a gare ni. Misali zato wanda yake wajibi shine baka san al kibla ba,

kuma babu wanda zai nuna maka a nan an baka dama ka yi amfani da abinda

kake zaton daidai ne.

Misali, zato na mustahabbi shine ka sa kyakykyawan tsammani ga kowane

Musulmi. A nan an amince ka yi taka tsan tsan wajen huldayya ta yau da kullum

ba tare da daukar wani barawo ko dan ta'adda haka nan kawai ba.

Misali zato da aka amince shine idan kana kokanton baka cika raka'a uku ko hudu

a salla an amince a amince ka yi amfani da abinda kake zato dai dai ne a zuciyar

ka. Sauran zato haramun ne a musulunci.

A yanzu bari mu duba sa-ido, ba a yarda ba kayi bincike kuma ka fallasa asirin

wasu ko kuma ka ji idan wani idan yana boyewa ko kuma yana fakewa yana barci

kamar sa-ido ne ga wadansu. Amma idan akwai kyaukyawa zato, wadansu zasu

cutar da wani Musulm, wannan bincike ne ko sanya ido an yarda.

Zamu kuma bada misalign gulma. Manzo SAW yace " Gulma itace yin zancen

wani wanda idan yaji ba zai ji dadi ba.

A nan ba a yarda ba ka yi zancen wani a bayan idon shi, ko da kuwa abinda ka ce

din gaskiya ne. idan kuma ba gaskiya ba ne, ya zamana babban zunubi wanda

ake kira Buhtan (zargin karya).

Yana da kyau mu sani idan ka sami kuskuran wasu ko yin maganganu gatsegatse

ko kuma muzanta wani a na kiran shi ' Lamz', a cikin Al qur'ani mai girma,

Allah SWT yace a cikin Surat Al Hujraat, aya ta 11:

" kar ku muzanta junan ku".

A na nufin idan ka sami kuskure a wajen wasu suma zasu juyo su sami kuskure

a kan ka.

Abin sha'awa ga wannan ayar shine samun wasu da laifi kamar samun laifin ne

ga kan ka. kamar yadda Allah yace

ﻢﻜﺴﻔﻧأ اﻮﻠﺘﻘﺗ ﻻو

" kada ku kashe junan ku".

Idan ka kashe wasu, kai ma za su yi kokari su kashe ka. Allah SWT ya ce a cikin

Alqur'ani mai girma, Surat al Humazah 1:

ةﺰﻤﻟ ةﺰﻤه ﻞﻜﻟ ﻞﻳو

" Bone ya tabbata ga mai aune, mai zune (mai rada) "

Bahadar Shah Zafar yace " Idan ban san kai na ba sai in dinga ganin kuskure a

wajen wasu, idan kuma na duba kai na, ban ga mutumi wanda ya fi ni muni ba".

A aya ta 12 ta Surat al Huraat, Allah SWT ya bayyana karara bata sunan wani

Musulmi bayan idon shi kamar cin naman dan uwan ka ne da ya mutu, wanda

kowa ba ya kauna.

Wannan shine mummunan zunubi ka sani idan mutum yana nan zai kare kan shi

ko da yake ba kowa yake da kwarin gwiwar da zai kare kan shi ba a wannan hali,

idan kuma aka bata mashi suna a bayan idon shi batancin yayi tsanani na

dundundun ne. Allah SWT ya yi bayanin wannan zunde a wani yanayi da ko wane

Musulmi zai kyamaci wannan mummunan laifi.

Zunde ba ana yin shi da harshe bane kawai, ana yi kuma da ido, hannu da sauran

kyafuce-kyaufuce, misali kwaikwayon wani gurgu domin bakanta shi. Manzon

Allah SAW yace " zunde yin zina laifi", kuma an sami Karin bayani daga Manzon

Allah kamar yadda Abu Sa'id da Jabir suka ce, a Timizi " Allah SWT yana

gafartawa wanda yayi zina idan ya tuba, kuma Allah SWT ba zai yafewa wanda

yayi gulma ba da dan uwan shi har sai wanda a ka yi da shi ya yafe mashi". A

wani lokaci Manzon Allah SAW ya nuna wadansu kabarurruka guda biyu yace da

sahabban Sa " Dukkan wadannan mutanen ana yi masu azaba a cikin kabari,

daya daga cikin su yana gulma da mutane, dayan kuma baya kiyayewa yana

fantsama fitsari a jikin shi da tufafin shi. Shine ya sa wani lokaci Manzon Allah

SAW yace wa matar shi A'isha RA " Kibi a hankali da abinda kike kira da karamin

zunubi", suna iya kawo mummunar azaba a kabari. A lokacin Mi'raji Annabi SAW

ya ga wasu mutane wanda farautan su na jan karfe ne suna kartar fuskokin su da

kirjin su, Manzon Allah SAW ya tambayi Mala'ika Jibrilu labarin su, Mala'ika Jibrilu

ya amsa mashi " Ana azabtar da su domin suan cin naman mutane a rayuwar su,

sun kasance suna gulma da bata sunayen mutane.

An karbo daga Abu Huraira cewa Manzon Allah SAW yace " Kashe musulmi haka

nan ko kwace dukiyar wasu ko bata sunan wani dan uwa Musullmi an haramta shi

kwata kwata a Musulunci". (Muslim ne ya ruwaito).

Har wa yau, an karbo daga Abu huraira cewa Manzon Allah SAW yace " wanda

bai bar yin karya ba, Allah bai damu da kin cin abincin shi ba da sauran su a

lokacin azumi.

Imam Ghazali ya rubuta a cikin Ihya'u ulumid din cewa wani mutum ya kasance

yana gulma da Hassan basri sai Hassan Basri ya aiko mashi da dabino kyauta, da

ya sami labarin wannan zunde, Hasan basri kuma ya aika mashi da wannan

sakon " Yin gulma da kake yi da ni, kana dauko ayyukan ka na alheri zuwa gare

ni, sai wannan dabino bai cancanci abin kirkin da kake yi mani ba, ina fata zaka

amshi wannan muhimmiyar kyauta.

Ka sani fa yin gulma da yaro ko mahaukaci ko kafiri da yake zaune a kasar

Musulmi ba a yarda da shi ba.

Abubuwa wadanda ba a dauke su ba a zunde ba :-

1. Ka yi koke a kan azzalumin shugaba domin wanda yake da hakki ya ladabtar

da azzalumin shugaba.

2. Ka yi koke ga uba ko miji akan dan shi ko matar shi, wanda shine zai iya gyara

masu rayuwar su.

3. ka yi bayani cikakke ta yadda za a sami fatawa.

4. ka yi bayani ka ceto Musulmi kada a cutar da shi ta fuskar addini.

5. a yi bayani ta yadda za a sami kwararriyar tuntuba.

6. ka yi bayanin manya-manyan zunubbai ga mutum da ya ke aikata wannan

zunubbai a fili karara, kuma kayi alfahari da yin hakan.

Ka sani fa manufa a nan bisa wannan abubuwan da aka bayyana a sama shine

anbaton da aka yi an yi shi ne domin wani mashahurin abu da ake nufi ba domin

a dankwafe ko bata sunan wasu ba da niya ko kuma haka nan kawai.

Har way au, sauraren gulma dai dai yake da yin gulma da wani. Mafi kyau shine

ka bar wajen da ake yi.

Cin naman wani tuyewa ne ga damar Allah SWT da damar mutane. Domin haka

dole da farko, ka nemi gafara ga wanda kayi wa, tunda Allah ba zai gafarta maka

ba sai wanda ka yi da shi ya gafarta mak. Idan wanda aka yiwa ya mutu ko kuma

ba a san inda yake ba, to a nan sai a biya diyya.

An karbo daga Anas cewa Manzon Allah SAW yace " Diyyar cin naman wani shine

ka roki Allah gafara cewa " Ya Allah ka yafe mani zunubai na da nashi".

Ina rokon Allah SWT ya kare mu daga aikata mummunan zato da sa-ido da gulma

(zunde), Amin.

BABBA DA KARAMIN ZUNUBI

Allah SWT ya ce a cikin Surat An Nisa', aya ta 31:

" Idan kuka bar babban zunubi wanda aka hane ku da aikatawa zamu barranta ku

daga kananan zunubai, mu sanya ku a kykykyawan mushiga, watau aljanna".

A bayyane yake daga wannan aya akwai zunubi iri biyu, karami da babba, kuma

a yake alkawalin Allah SWT, idan mutum ya guji aikata manyan zunubai, zai yafe

mashi kananan zunubai . muna sane wajibi ne mu aikata Fardh (abubuwan da

suka wajabta a kan mu) kamar Salla, Zakka da azumi kamar yadda ya dace,

kuma muna masu kauracewa babban zunubi. Barin ayyukan nan da aka wajabta

to shima babban zunubi ne. A nan idan mutum ya aikata manyan zunubbai Allah

SWT zai yafe mashi kananan zunuban shi.

Menene zunubi?

Duk abinda aka aikata sabanin yadda Allah ya ce ko umarnin Allah wannan shine

zunubi, a nan babu karamin zunubi ko babban zunubi, saboda haka, idan ana

yawaita kananan zunubai ba tare da wata damuwa ba zi zamana babban zunubi.

Wani malami yayi bayanin matsalar kananan zunubai da babban zunubi a

wadannan misalai. Yace ka kaddara harbin mu'ujizar kunama da babbar kunama,

kuma ka kaddara konewa daga mu'ujizar wuta da konewa daga konewa daga

giwar wuta. Dukkan su suna da zafi amma illar da babbar za ta yi ya fi matsala.

Kuma dukkan zunuban nan suna da illa amma babban zunubi yafi ta'adi akan

karamin zunubi. Muhammad Bn Ka'ab Karazi ya ce " Mafi kyawun bautar Allah

mutum ya bar dukkan zunubbai ". Allah SWT baya karbar Sallar mutum da

kullum sauran ibadu matukar wannan mutum baya barin aikata zunubbai. Haka

nan kuma Fudhail Bn Ayyadh ya ce " idan mutum ya kasance yana daukar zunubi

karami wadannnan zunubai za su kasance manya a idon Allah SWT".

Annabi Muhammad SAW yace " idan mummuni ya aikata zunubi sai ya kasance

wani bakin digo a zuciyar shi, idan ya tuba sai wannan bakin digo ya bace, idan

kuma bai tuba ba sai wanann digon yayi ta girma har ya mamaye zuciyar. Allah

SWT ya bayyana a cikin Alqur'ani mai girma a cikin Surat Al Mutaffifin, aya ta 14

A aha! Ba haka ba abinda su ka kasance suna aikatawa yayi tsatsa a zukatan su".

Idan zuciyar ta kasance cike da tsatsa babu wata shiriya ko fadakarwa da zata

ratsa zuciyar irin wadannan mutane, don haka, ba za su ba za su amfana da

tunatarwa ta Alqur'ani ba. Alqur'ani ya karfafa wannan magana da dama cewa shi

Alqur'ani fadakarwa ne ga masu tsoron Allah da wankakkiyar zuciya wadda zata

karbi shiriya.

Bari mu fassara zunubi a haske da shiryarwa ta Alqur'ani da Sunna. Kamar yadda

wadansu malamai duk wani zunubi wanda ALqu'rani ya fadi hukuncin wanda ya

aikata shi ko tsinuwar Allah da aka fadi, ko gargadin wutar Jahannama wadannan

an dauke su manyan zunubbai. Kamar yadda aka yi bayani a baya duk wani

karamin zunubi da aka aikata ba tare da nuna wata damuwa ba, a bayyane

karara yana iya kasancewa babban zunubi. Wani ya fadawa Ibn Abbas cewa

manyan zunubai guda bakwi ne. sai Iban Abbas ya amsa mashi da cewa ba

bakwai bane gara ma dari bakwai ne. Imam Ibn Hajjar Meccy RA yayi bayani a

tsare jerin manyan bayanai da cikakken bayani a cikin littafin sa KITABUZ

ZAWAJIR ya lissafa dari hudu da sittin da takwas manyan zunubbai. Tare da

kebance wurin kin biyayya da umarnin Allah SWT.

Yaya za a yafe karamin zunnubi ? misali yafe karamin zunubi an yi bayanin shi a

Hadisi : Idan mutum ya yi alwalla, ya wanke bangarori na jikin shi, zunubin da

aka aikata a bangaren jikin an wanke shi, kamar yadda busashshen ganye zai

fado daga kan bushiya idan iskya kada. Misali idan muka kurkure baki zunubin da

muka aikata da harshen mu an wanke shi, idan muka wanke kafafun mu, zunubin

da muka aikata da taimakon kafar mu an wanke shi. Idan mutum ya tafi zuwa

masallaci bayan yayi alwalla bayan yayi alwalla duk takin da yayi ya zama diyyar

kananan zunubban shi. Shi babban zunubi ba a wanke shi ta hanyar alwalla ko

kuma yin salla kadai, wanke babban zunubi yana faruwa ne ta hanyar tuba na

gaskiya. Tuba ya kunshi abubuwa guda uku. Da farko mutum sai ya mutunta ya

kuma tabbatar da aikata zunubin. Na biyu sai ya hakikance cewa ba zai sake

aikata wannan laifi ba. Na uku sai yayi nadama sannan ya roki gafara. A nan,

idan yana yin salla kuma yana azumi kana kuma ya sa kan shi a cikin babban

zunubi, to Allah SWT ba zai yafe mashi manyan zunubai da kanana. Annabi

Muhammad SWA ya fadi manya-manyan zunubbai da dama a kan wani yanayi da

lokaci. Saboda haka, malamai sun yi ittifaqi ba a sanya wani kiyasi a kan dukkan

manyan zunubbai. Annabi Muhammad yace " Bari in sanar da ku manyan

laifuffuka guda uku: hada Allah da wani, kin biyayya ga mahaifa da kuma shaidar

zur. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Wani ya tambayi Annabi Muhammad SAW game da manyan zunubbai, ya amsa

mashi da " Kada ka hada Allah SWT da wani". Sai ya sake tambayar shi " sai

wane?", Annabi Muhammad SAW ya ce " kada ka kashe dan ka domin gudun

dawainiyar ciyar da yaron da abinci". Sai ya sake tambayar shi " wane zunubi

babba ne gaba? Sai Annabi Muhammad SAW ya ce " ka yi zina da matar

makwabcin ka. Kamar yadda ka sani, zina babban zunubi ce, makwabcin ka yana

da hakki ka kare iyalin shi. Saboda haka, zina da matar makwbcin ka laifi guda

biyu ne. (Bukhari da Muslim)

Annabi Muhammad SAW ya ce " Zunubi ne babba mutum ya zagi mahaifin shi",

Sahabbai suka ce " yaya za a yi mutum ya zagi mahaifan shi"? Annabi

Muhammad SAW yace " Idan ka zagi iyayen wani to shima zai zagi naka iyayen.

Saboda haka, zagin iyayen wani tamkar kana zagin naka iyayen ne.

Annabi Muhammad SAW yace " hada Allah SWT da wani, kashe wani haka nan,

cin dukiyar maraya, cin riba, gudu daga fagen fama, ka zargi mace mummuna,

kin biyayya ga mahaifa, da kin girmama dakin Allah SWT dukkan wadannan

zunubai ne manya.

Annabi Muhammad SAW ya ce idan wani ya zargi wani ba da hakkin shi domin

kawai ya muzguna mashi ko kuma ya yanke kauna daga rahmar Allah SWT ko kin

bin shari'ar rabon gado, wannan suma zunubbai ne manya. Kamar yadda aka

samu daga wani Hadisin hada salla guda biyu ba tare da abinda addin ya shimfida

ba, wannan ma babban zunubi ne. Ya zama dole mutum ya rika yin sallah a kan

lokacin ta.

Wani lokaci, Annabi Muhammad SAW yace " Wannan mutum ya halaka! Har sau

uku. Abu Zarr ya tambaya wanene wannan ? Annabi Muhammad SAW ya amsa :

Mutum mai alfahari wanda zai saki tufafin shi su rika jan kasa, mutum da zai

ciyar domin Allah SWT sannan ya rika fadawa mutane abinda ya yi, mutumen da

ya ke tsoho sannan yana yin zina, mutumen da ya ke rike da babban mukami

sannan yake cin amana, mutumen da yake alfahari domin Allah ya bashi 'ya'ya,

ko wanda yake biyayya ga wani Imam domin samun duniya. (Muslim)

Annabi Muhammad SAW yace " wadannan mutane ba su shiga aljana : wanda

yake sha giya, da wanda baya biyayya ga mahaifan shi, da wanda ya kauracewa

dangin shi ba tare da dalili ba, wanda yake tunatar da mutane abin da yayi na

kyautatawa. Da wanda yake bokanci da wanda ba ya kokarin ya hana iyalan shi

aikata wadansu abubuwa marasa kyau."

Annabi Muhammad SAW yace mutumin da yake cin naman dan uwan shi ba zai

shiga aljanna ba.

Sahihaan.

Ina rokon Allah SWT ya yafe mana zunubban mu manya da kanana, ya sany mu

bi tafarkin Alqur'ani da Hadisi,Amin.

IKIRARIN MABIYA LITATTAFAI

Babban abin alheri da Allah SWT ya yiwa Yan Adam shine sanya su akan hanyar

shiriya. Matukar babu shiriya mutane za su dimauce su fada halaka ta hanyoyi da

dama. Yahudawa da kiristoci Allah SWT ya basu baiwa ta samun shiriya ta

gaskiya, amma mafi yawa daga cikin su sun yi fatali da wanna muhimmiyar dama

da suka samu. Bari mu ga yadda suka nuna halayya da wannan shiriyar da

Allah SWT, Surat Al Baqarah, aya 135:

" sun ce ka zama bayahude ko kirista ko sami hanya madaidaiciya ! kace da su "

mu mun bi addinin Ibraheem AS madaidaici kuma ba ya tare da wanda suka hada

bautar Allah da wanin sa".

A nan, mun gani yahudawa da kiristoci suna ikirarin su mabiyan. Annabi ibrahim

AS amma ikirarin karya ne tunda Annabi Ibrahim AS bai taba hada Allah SWT da

wani ba.

Aya ta 40, a Suratul Baqarah Allah SWT ya ce :

" Ko kace ku da Ibraheem, Isma'il, da Ishaq, Ya'qub da Al asbad su yahudawa ko

kirista. Kace kun fi sani ne ko kuma Allah mafi cancanta ya sani (cewa dukkan su

Musulmai ne), to wanne ne ba akan dai dai ba ga wanda ya biyo samun tabbaci

daga Allah ? ko Allah bai san abinda san abinda suke yi ba?"

Allah SWT ya bayyana wannan tabbaci wanda ma'abuta littafi su ka sami, wanda

a bayyane suka sami shaida, ba gara a aya ta 146 v yace :

" Wadanda suka baiwa littafai (yahudawa da kiristoci) sun gane shi (Muhammad

SAW) kamar yadda suke gane dan su, amma wasu bangare daga cikin su sun

boye gaskiya duk da sun san ta (shima alamomin Muhammad SAW wanda aka

rubuta a cikin littafin su).

Karara masu ilmi daga cikin malaman su sun boye gaskiya da gangan saboda son

samun duniya, duk da haka da yawa daga cikin ikirarin su mai rauni ne. A misali,

ma'abuta littafai sun ce ; Suratul Baqarah, aya 111;

" (sun ce) Babu wanda zai shiga aljanna sai dai wanda ya ke bayahude

ko nasara, wannan abinda suke so ke nan. Kace da su (ya Muhammad)

ku kawo hujjojin idan kun kasance kuna da gaskiya."

Har wa yau, sun sake ikirarin, Suratul Baqarah, aya ta 150:

" Su yahudawa suka ce: wuta (watau lahira a ranar tashin kiyama) ba za ta taba

su ba sai na wasu 'yan kwanaki! Kace da su (ya Muahmmad) kun yi alkawali ne

da Allah wanda (kuma) Allah ba zai taba alkawalin su ba? Ko kun fadi wani abu

game da Allah wanda ku baku sani ba."

Ikirarin ma'abuta littafi bai iya rike ruwa, kuma zai sanya wani ya fada kogin

tunanin gaskiya ko dibar wannan Magana, shine Allah SWT ya ce a cikin Suratu

Aal Imran, aya ta 65:

" ya ku ma'abuta littafi (yahudawa da kiristoci) me yasa kuke yin jayayya akan

Ibrahim bayan At Taura da Linjila ba a saukar da su ba sai bayan shi? Ko ba ku

da hankali ne ?"

ِAllah SWT ya sake cewa a suratu Al Imran , aya ta 68 :

" Hakika , akin mutane wanda yafi can canta suyi ikirarin Ibrahim sune mutanen

suka bishi, da Annabin sa Muhammadu SAW da wadanda suke yi imani, Allah

shine mai kariya da taimakon mummunai."

Wannan kinaya ta wadan nan mutane ma abuta littatafai ya kai awani

mastayi sai Allah ya sake cewa a suratul Al Imran aya ta 72 " Wadansu bangare

na cikin mutane ma'abuta littafi sun ce ku yarda dasa saifya wanda aka saukowa

mummunai (musulmi) ku yi watsi da karshen rana domin su juya baya"

A wata aya ta 78, Surat Aal Imran:

"hakika a cikin su akwai wadanda suka bata littafi idan (idan suna karantawa)

domin ka yi tsammanin daga littafin su ya ke amma b adaga littafin ya ke ba, sai

su ce wannnan daga Allah SWT ne, amma ba daga Allah ya ke ba. Sun yi wa

Allah karya duk da sun sani."

Allah SWT ya bawa Annabi Muhammad SAW hakuri saboda ya na kokari da

gaskiya, a sanya ma'abuta littafi akan hanya madaidaiciya.

Allah SWT yace a cikin Baqarah, aya ta 75-77 :

" Kana tsammanin za su bada gaskiya da addinin ka duk da wasu daga cikin su

(yahudawa) suna sauraron kalmomin Allah, suna sane suke jirkita ta bayan sun

fahimce ta. Idan (yahudawa) suka iske wadanda suka bada gaskiya sai suce " Mu

mun yi imani", idan kuma suka hadu da junan su sai su ce " Mu (yahudawa) yaya

za mu sanar da su ne abinda Allah ya saukar mana (yahudawa) game da

Alamomi da ingancin Annabi SAW wanda aka rubuta a (At Tauarh), da musulmi

sun yi jayayya da ita dangane da ita a gaban Allah, (yahudawa) suka ce baku

sani ba? "

Yanzu yahudawa suna sane da cewa Allah SWT ya san abinda suka boye da

abinda suke bayyanawa.

Shine Allah SWT yace a aya ta 79:

" Tir da wanda suke rubuta littafi da hannun su, sai suce wannan daga Allah ne, a

saye shi da arha! Tir da su da abinda suka rubuta da hannun su, tir da su da

abinda suka karu da shi"

Daga karshe Allah SWT ya gayyace su zuwa ga hanya madaidaiciya a aya ta 64

Surat Al Imran:

" ka ce yaku ma'abuta littafi (yahudawa da kiristoci) ku zo mu yi magana tsakani

na da ku, kada mu bautawa kowa sai Allah, kada mu hada Allah da wani, kada

mu dauki kowa uban giji sai Allah."

Ya na da ban sha'awa ma'buta littafi ba su kasance daya ba, kamar yadda Allah

ya ce a aya ta 75 a cikin surat Aal Imran:

" A cikin ma'abuta littafi (yahudawa da kiristoci) akwai wanda idan a ka bashi

amanar Qintar a shirye ya ke ya mayar, kuma a cikin su akwai wanda idan aka

bashi kwabo na azurfa ba zai biya ba sai an yi fama, saboda sun ce babu laifi

gare mu idan mun ci amana, kuma idan muka ci kayan jahilai, amma suna fadar

karya da Allah bayan sun sani"

a aya ta 113-114, Al Qur'ani ya furta cewa ba dukkan su daya suke ba, wadansu

daga cikin su sun kasance a hanya ta daidai, suna karanta ayoyin Allaha a cikin

dare kuma suna yin Salla, sun yi imani da Allah da ranar karshe, suna umarni da

kyakykyawan aiki da bin tafarki.wadannan suna daga cikin mutanen kirki".

Ina rokon Allah ya nunawa ma'abuta littafi hanyar shiriya ta gaskiya, wadda ita

ce tun farko aka saukar masu da ita, wadda kuma ba ta da banbanci da Alqur'ani.

WATAN SHA'ABAN

Musulmi suna shagulgula a wani dare a cikin watan sha'aban, a wurare da ban

da ban a fadin duniya, ana kiran wannan dare 'SHAB-BARAH' ko kuma

'LAYLLATUL BARA' dare ne muhimmi. Akwai wadansu sanannun al'adu da imani

ga Musulmi dangane da wannan dare wanda bashi da wani mahalli ko gurbi a

Musulunci. Misalai sune kamar haka:-

1. wadansu Musulmi sun yi imani cewa rayukan wadanda suka mutu suna dawo

masu a wannan rana. Suna daddafa abinci masu dadi rarrabawa mutane. Kwata

kwata wannan ba Musulunci bane. Duk Musulmi na kwarai ba zai bautawa wanda

ya mutu ba sai dai yayi mashi addu'a.

2. A wani camfin kuma, wadansu Musulmi sun ce shawarar a halitta rai da

mutuwa, Allah SWT ya yanke shawarar yin haka ne a sha biyar ga watan

Sha'abaan (15 th Sha'abaan). Gaskiya ne Allah SWT ya yanke shawarar yin rai da

mutuwa, amma fa ya yi hakan ne tun ma kafin a yi halittar mu.

3. Wani shaci-fadin zance kuma shine wai akwai wata itaciya wadda aka rubuta

sunayen kowane mahaluki a bisa ganyayyakin ta. A wanann dare na ake girgiza

ta ganyaye za su fado, su gwada wadanda za su mutu.

4. Wata al'ada kuma maras kyau wadda ake yi a wannan dare shine: mutane

suna yin wasan wuta. Allah kadai ya san bisa ko wane dalilin suke yin ta. Amma

wannan yana kasancewa saboda cudanya da wadansu al'adu na addinan Hindu da

kuma Budah. Mun kasance a cikin wannan al'ada shekaru da shekar, kuma mun ji

dadin aikata wannan mummumar al'ada, kuma bamu damuwa muje wajen

masana daga ciki mu mu gano gaskiyar al'amarin.

Manzon Allah SAW yace " zan bar maku abu guda biyu a baya na sune Alqur'ani

da Hadisi, matukar kuka rike su ba za ku karkace ba. To a nan tambaya ta hakika

: menene matsayin Alqur'ni da Sunna a kan wannan dare na Sha'aban ?

Babu inda aka gwada wannan rana ko a kafa hujja a kan ta a cikin Alqur'ani mai

girma sai dai kadan daga cikin masu Tafsirai sun an'anbace a cikin aya ta 3-4 a

cikin Surat Ad Dukhaan Allah SWT ya ce :

" Mun saukar da shi a cikin dare mai albarka, lallai mun kasance masu gargadi. A

wannan dare ake raba ko wane irin umarni".

Yawancin masu Tafsiri sun yi imani cewa wannan aya tana nufin LAILATUL

QADARI ko dare mai albarka wanda yake a cikin watan Ramdhaan. Kamar yadda

muka gani a fassara, Allah SWT yace an saukar a cikin dare mai albarka, Allah

SWT ya sake cewa a ciki Suratul Al Qadri aya ta 1:

" Na saukar da Shi a dare mai albarka". Daga karshe, Allah SWT ya ce a cikin

Suratul Baqarah, aya ta 185 :

" Na saukar da Al Qur'ani a cikin watan Ramadhan."

A nan ayar da ke a Surat Ad Dukhan tana nufin Lailatul qadri ne ba wai tsakiyar

Sha'aban ba.

A cikin littaifin shi ' At Targhib wat Targhib', al Imam Ibn Al Munzir ya kawo

Hadisai goma sha hudu daga Manzon Allah SAW a kan watan Sha'aban, ga wasu

daga cikin su:-

Manzon Allah SAW ya ce " Ku bada muhimmanci na musamman ga watan

Sha'abaan, saboda yana zuwa kaifn watan Ramadhaan". Watan Ramadhan wata

ne mai tsarki wanda aka saukar da Alqur'an. A watan Ramadhan ne Musulmi su

ke yin azumi. Ka shiryawa zuwan watan Ramadhan a cikin watan Sha'aban. Misali

kuyi kowane irin shiryeye kafin muhimmin bako ya zo, haka nan ka yi shiryeshirye

a cikin watan Sha'aban domin zuwan wata mai alfarma watan Ramdhan.

A wani Hadisin kuma, Manzon Allah SAW yana yawaita yin Azumi a cikin watan

Sha'abaan. A'isha RA tace " Annabin Muhammad SAW yana yawaita yin Azumi a

watan Sha'aban. Wani lokaci sai ya yi ta yi kamar ba zai tsallake kwana ba. A

wadansu lokuttan ba zai yi azumi mai tsawo ba a cikin watan Sha'ban, wannan

yana nuna mana wannan azumin na ganin dama ne domin neman Karin falala.

A wani Hadisin kuma, Manzon Allah SAW ya ce " Allah SWT yana bada wata dama

ga ababen halittar shi da dare. Me ake nufi da wannan? Allah yana kara bada

dama ga ababen halittar shi su tuba, su kyautata halayen su da rayuwar su. Allah

SWT yace " Akwai wanda ya ke son gafara in gafarta mashi? Akwai wanda yake

son taimako in taimake shi? Akwai wanda yake cikin kunci yake rook na in yaye

mashi kuncin?

A nan kofa a bude take ga mai son taimakon Allah musamman a watan Sha'aban.

A wani Hadisin kuma, Manzon Allah SAW yace " ku ziyarci kabarurruka cikin

watan Sha'aban, yana da muhimmanci kuma cikakkiyar tunatarwa ce ". Manzo

SAW ya kara da cewa " Idan wani bai sami wani darasi akan rayuwa da ranar

karshe a wajen ziyarar kabari ba, wannan bashi da wani rabo na samun shiriya ta

gaskiya.

Ina rokon Allah SWT ya shiryar damu a kan hanyar Al Qur'ani da Sunnah, kuma

ya sanya mu a kan hanya ta gaskiya, Ameen.

LAILATUL QADAR

Allah SWT yace a cikin Al Qur'ani a cikin Surat Al Qadar, aya ta 1-5:

" Mun saukar da Al Qur'ani a cikin dare mai albarka. Dare mai albarka yafi

watanni dubu. A wannan dare ne Mala'ika Jibrilu da sauran Mala'iku suke sauka

da izini Allah SWT da umarni. Shi wanan daer amince ne cikin sa har gari ya

waye"

kamar yaddad yazo a wannan surah, Allah SWT ya saukar da Al Qur'ani a cikin

dare mai alabarka. Sani kuma an saukarwa Annabi Muhammad SAW da Alqur'ani

a cikin shekara ashirin da uku, kadan kadan. Hakika, abin tambaya anan shine

me ya sanar da kai cewa an saukar da Alqur'ani a cikin dare mai albarka ?

Yana nufin cewa an sauko da Alqur'ni daga wata muhimmiyar ma'adana ta Allah

wadda ake kira LAUHUL MAHFUZ zuwa duniya a cikin dare mai albarka. Kuma

yana nufin cewa wahayi ma farko da aka yi wa Annabki Muhammad SAW a kogon

Hira' an yi shi ne a cikin LAILATUL KADAR dare mai albarka. Yana da ban sha'awa

mu gane cewa wannnan sura ita ce ta gamo da suratul Alaq, tana nunawa wahayi

na farko an yi shi ne a dare mai albarka.

Me kadar take nufi ? Kadar yana nufin mai daraja, mai karfi. Me ya maida

wannan dare mai girma? Saukar da Al Qur'ani da aka yi a wannan dare shine ya

maida shi mai daraaja da girma.

Haka nan kuma, mutum da ba shi da wata daraja sai ya zama mai daraja mai

farga da Allah idan yayi bauta a wannan dare.

Abu na biyu da ake nufi da KADAR shine Kaddara, ko da yake Allah SWT ya yanke

hukunci tun ma kafin a halicce mu, amma abubuwan da za a yi a wannan shekara

an damkawa Mala'iku domin a zartar a wannan dare. Kamar yadda wadansu

malamai su ka ce., kadan daga cikin ayoyin Surat Addukhan suna nufin wannan

dar kuma suna tabbatar da wannan Magana. Allah SWT ya ce a cikin Surat Ad

Dukhan aya ta 1-4 :

" Wannan littafi yana warware abubuwa da bayyan. Mun saukar da wannan Al

Qur'ani a dare mai albark. Hakika, muna gargadin mutane. A wannan dare

abubuwa masu faruwa a bayyane suke (kamar mutuwa da haihuwa).

Wadansu malamai suna ganin wannan ayoyi na suratud Dukhan suna nufin watan

Sha'aban. Sun ce yanke hukunci an yi shi ne a watan Sha'aba an baiwa Mala'iku

su zartar a cikin wannan dare mai girma. Allah SWT shi ya san dai dai.

A gaba, sai Allah SWT yace wannan dare mai girma yafi dare dubu. Me ake nufi

da wannan? Larabawa wannan lokacin sun dauki dubu wani abu mai yawa. Ana

nufin yin bauta a wannan dare yafi darare masu yawa.

Watanni dubu dai dai ne da shekara tamanin da uku ko da hudu, larabawa su na

ganin mutumen da ya shekara tamanin ya zama cikakkiyar ibada ko mai yawan

ibada tunda ya kasance mai ibada tsawon rayuwar shi. Amma yin ibada a cikin

wanna dare ya fi yin ibada na sama da shekara tamanin.

Har wa yau, Ibn Abi Hatim ya ruwaito daga Mujahid cewa : Annabi Muhammad

SAW ya baiwa sahabban shi labarin wani mutum daga cikin Bani Isra'ila wanda

yake ta yin bauta har tsawon shekara tamanin ba yankewa. Haka nan kuma Ibn

Jarir ya ruwaito daga Mujahid cewa Ananbi Muhammad SAW ya ce " Wani mutum

daga cikin Bani Isra'aila ya kasance yana yin ibada cikin dare kuma yana fita yaki

don daukaka kalmar Allah da rana. Yayi wannan har tsawon shekara tamanin

babu yankewa. Allah SWT yana cewa al'umar Annabi Muhammad SAW cewa yin

ibada a wannan dare yafi ibadar wannan Bani Isra'aila ta shekara tamanin. Don

haka, dare mai albarka wata muhimmiyar dama ce ta al'umar Annabi Muhammad

SAW kuma kyauta ce ta musamman daga Allah zuwa Annabi Muhammad SAW da

mabiyan Shi. Wannan ya gwada yadda Allah SWT ya ke son Annabi Muhammad

SAW da mabiyan wannan Annabin, koda yake mabiyan Annabawa na farko an

wajabta masu yin azumi amma al'ummar Annabi Muhammad SAW aka ba

kebantacciyar daraja ta samin mai albarka a cikin watan azumi.

A daren lailatul kadar, Malai'aka Jibril da wasu Mala'iku wanda suke a Sidratul

Muntaha suke saukowa a doron kasa su yi roko na musamman ga Allah ga

wadanda suke tunawa da Allah a zaune suke ko a tsaye. Dare mai albarka na

lailatul kadar dare ne na aminci da kyautatawa. Wannan yanayi na aminci yana

tabbata har wayewar gari. Wadansu mutane suna kasancewa suna ganin

wadansu ababen mamaki a wannan dare. Wadanda ma basu ga wani abin

mamaki ba sun sami nasu rabon su a wanna dare mai albarka.

A yaushe ne wannan dare Allah SWT ya ce a cikin Alqur'ani, suratul Baqrah, aya

ta 135:

" Mun saukar da Al qur'ani a cikin watan Ramadhan"

a cikin Surat Al Qadar aya ta 1 Allah yace :

" Mun saukar da Al Qur'ani a cikin dare mai albarka".

A nan dare mai albarka ya kasance a wani lokaci a watan Ramdhan. Akwai

Hadisai na Annabi Muhammad SAW da dama da suka yi bayanin hakan kamar

yadda ya zo a Bukhari.

A'isha RA tace Annabi SAW yace " ku dubi daren Lailatul qadar a kwanaki goma

na karshe na watan Ramadhan.

Kuma ya zo a Muslim daga dan Umar cewa Annabi Muhammad SAW yace " kubi

dare a lokaci a kwananki na mara a kwanaki goma na karshen watan Ramdhan".

Mutane da dama sun amince da daren 27 na watan Ramdhan. Ba a tantance shi

ba saboda mu sami Karin rahma wurin Allah SWT mu nemi wannan dare mu yi

tsaye wajen tunawa da Allah SWT. Wannan rahma ce ta Allah SWT a gare mu.

Wani lokaci muna rayawa wannan dalili ne Allah SWT ya saukar da AlQur'ani mai

girma a cikin dare ba da rana ba. Allah SWT shine masani. Har wa yau, muna iya

cewa dare lokaci ne na aminci kuma lokaci ne na nutsuwa, kuma mun fi

kasancewa cikin kamun-kai da nutsuwa kamar yadda Allah SWT yace a cikin

Surat Al Muzzammil aya ta 6:

" A cikin dare yanayin ya fi kuma kalmomi suna a kai tsaye"

A wata fadar, kalmomi sun fi kasancewa da gaske da tasiri a cikin dare yanayin

kuma yafi shudewa.

Mun sani kuma dare kamar yadda wadansu manazarta suka ce yana nufin duhu

kararre da babu. Idan gari ya waye komi sai ya kasance a bayyane. Lokacin da

aka saukar da Al Qur'ani al'uma suna ciki duhu Al Qur'ni ya sauya wannan duhu

zuwa ga haske. Wannan ita ce saukakkiyar hanyar shiriya ta Al Qur'ani wanda ya

banbanta tsakanin abinda yake na daidai da wanda ba na daidai ba. Allah SWT ya

ce a cikin Surat al Baqarah, aya ta 185:

" Al Qur'ani shiriya ce ga mutane bayyananniyar hujjar shriya da za ta banbance

tsakanin abinda yake (dai dai da wanda ba daidai ba)".

Ka sani ba wai shiriya ba ga larabawa kawai, ko wadanda suka yi imani kadai

bane amma ga dukkanin al'umma. Allah SWT yace a Al Qur'ani:

" Allah SWT ya saukar da Al Qur'ani ga bayan shi masu biyayya masoya bay.

Wannan shiirya tana fitar da mutane daga cikin duhu ta sanya su a cikin haske.

Allah SWT hakika mai tausayi ne mai rahma ga ababen halitta".

Ka sani cikin duk alfarmar da Allah SWT ya yiwa al'umma babbar alfarma ita ce

ya ba su shiriya. Hakika idan babu wannan shiriya mutane za su kasance a cikin

hasara a cikin duhu.

A karshe, A'isha RA ta tambayi Annabi Muhammad SAW " me zan yi idan na ga

dare mai albarka?". Annabi Muhammad SAW sai yace yi wannan addua'r :

Allahumma innka Afuwwun tuhibbul Afwa fa'afu anna".

" Ya Allah kai mai gafara ne kuma son gafara, ka gafarta mana".

Ya Allah muna rokon ka ka amshi wannan daaan kokari ka gafarta min da

wadanda suke karantawa da masu sauraren wannan bayani amin.

AL'UMMAR MUSULMI DA KE ZAUNE A MADINA

Musulmi da suke zaune a birnin Madina a lokacin Annabi Muhammad SAW za a

kasu su gida biyu : Yan Hijira (Muhajirun) sai 'yan gari (Ansar). Halayen

wadannan rukuni na al'umma an yi bayanin shi a a cikin Surat Al Hashr aya ta.

Allah SWT yace :

" (Akwai rabo a cikin wannan ganima) ga talakawa masu Hijira wadanda aka kore

su daga gidajen su da dukiyoyin su, suna neman yardar Allah da kuma kyautata

mashi da taimakon Allah (shine taimakon Addinin Shi) da manzon Shi, wannan

hakika su ne masu gaskiya ( a cikin abinda suka ce)".

Wadannan 'yan Hijira sun kasance ana ta gana masu akuba a Makkah, shine ya

tilasta su su yi hijira zuwa Madina. Kafirai suka mamaye kayayyaki da kadarorin

wadannan ma su hijira. Shine ya sanya Al Qur'ani mai girma yake kiran 'yan

Hijira Faqeer watau talakawa kwarai. A mafi yawan lokaci mafi yawan su basu da

ba su da abinda za su ci, ya kasance suna daura dutse a cikin su. Wadansu kuma

sai su haka rami su zauna a ciki domin su kare kan su daga sanyi.

Hali na biyu na wadanna Muhajirun shine dalilin da yasa suka bar gidajen su ba

domin wani abin duniya ba. Hakika shine domin samun soyuwa a wurin Allah SWT

a nan duniya da kuma samun rahmar Allah a gobe kiyama.

Hali na uku na masu Hijira domin taimakon Allah SWT da Manzon Shi SAW. A

nan taimakawa Allah yana nufin taimakawa wajen yada addinin Allah SWT. Sun yi

mashahuriyar sadaukar da rayuwa domin cin nasarar wadannan ababe guda biyu.

Hali na hudu na muhajirun shine su masu gaskiya ne a wajen maganganun su da

huldayyar su. Sun tsaya akan dugadugan su a kan shaidawar da suka yi Allah

SWT da Manzon Shi SAW a lokacin da suka shiga Musulunci. Allah SWT ya Fada a

wannan ayar cewa dukkan Muhajirun masu gaskiya ne . a nan kayi batanci a kan

su wannan kin yin biyayya ne ga fadar Allah SWT.

A aya ta gaba, Allah SWT yayi bayanin halayen Ansar Suratul Hashr aya ta 9:

" Da su wadana kafin su, suna da gidaje kuma suka yi imani suna son wadanda

suka yi Hijira zuwa wajen su, ba su da bakin –ciki a ran su akan abinda aka basu

da wadanda aka ba muhimmanci akan duk kuwa da suma mabukata ne. Duk

wanda ya tsira daga bin son zuciyar shi, wadannan sune masu samun nasara".

Yana da ban-sha'awa ka sani cewa Imam Malik ya dauki birnin Madina mai daraja

a matsayin birni mafi mafi albarka da daraja a fadin duniya, saboda shi wannan

birni an mamaye shi ne ta hanyar iman. Duk wadansu sauran birane har ma da

Makka an mamaye su ne ta hanyar yaki. Allah SWT yace :

" Hakika nasara ta farko ta Ansar shine sun tashi ne daga gari mai girma, wanda

ya bada mafaka ga Manzon Allah da mabiyan shi".

Abu na biyu, su Ansar basu dauki wadannan yan Hijira su zame masu matsala ba,

sun karba ne da hannu bibbiyu kuma sun nuna masu soyayya ta gaskiya. Saboda

wannan soyayya ne Ansar suka raba dukiyoyi da gidajen su da su. Ansar wanda

yake da mace fiye da guda, sai ya saki matar shi guda domin ta auri dan gudun

hijirar nan (Muhajirun). Ta wannan hanya , Ansar zai gabatar da Muhajir dan

uwan shi ga matan shi sai ya bashi dama ya zabi wadda ya ke so. Sai ya kasance

a wannan lokaci sanya hijabi ba a saukar da shi ba.

Hali na uku na Ansar shine da zuciya daya suke karbar duk abinda Manzon Allah

SAW ya baiwa Muhajirun. Misali lokacin da Musulmi suka sami galaba a akan

Banun Nadheer da Banu Qainuqa', an sami dukiyoyi ba tare da an yi wani yaki

ba. Annabi Muhammad SAW ya rarraba wanann kaya ga kashi biyar wanda aka

fadi a cikin Al Qur'ani mai girma. Annabi Muhammad SAW ya tamabayi Thabit bn

Qais ya tattar dukkan Ansar. Annabi Muhammad SAW ya yi masu jawabi kuma ya

yaba masu da halin su abin koyi wanda suka yi wa Muhajirun. Annabi Muhammad

SAW ya kawo shawarwari guda biyu dangane da rarraba kayan da aka samu ,

yace " idan na rarraba kayan ga Ansar da Muhajirun, a wannan hali to Muhajirun

za su dinga kasancewa a gidajen Ansar. Amma idan na rarraba kayan nan ga

Muhajirun za su kasance sun bar gidajen Ansar sun tafiyar da rayuwar su ta cin

gashin kan su. Shuwagabannin Ansar Sa'ad Bn Ubbadah da Sa'ad Bn Mu'az suka

ce ka rarrabawa masu hijirah su kadai kuma su ci gaba da zama a gidajen mu.

Allah SWT ya ji dadin wannan abu da Ansar suka yi kuma ya saukar da aya yana

cewa Ansar ba su sami wani rashin jin dadi ba a ransu wajen bayar da wannan

manyan kadarori. Ansar su yi hakan ne tamkar su ba su bukatar waddannan

kayayyaki .

Sai ya kasance, wadannan kayayyaki Annabi Muhammad SAW ya rarrabawa

Muhajirun har wadansu mutane daga cikin Ansaar wadanda ked a tsananin

bukata Sahal Bn Haneef da Abu Dujanah.

Halayya ta hudu ta Ansar shine sun fi son su biya bukatar Ansar sama da su biya

bukatun kan su.

Qurtabi RA yayi baayanin abubuwan da suka rika faruwa a tsakanin masu Hijira

da Ansar. Wadannan abubuwa sune aka yi bayanin nan saboda suna da

muhimmanci saboda rayuwar al'umma.

Abu Hurairh RA ya ruwaito cewa wani lokaci wani mutum ya zo wajen Annabi

Muhammad SAW yace " ina jin matsananciyar yunwa har ta kai ni ga wani

matsayi bana iya daurewa". Annabi Muhammad SAW ya tambayi matan shi ko

akwai abinci? Suka ce babu kome sai ruwa. Annabi Muhammad SAW ya ce wa

sahabban shi wa zai dauki nauyin wannan dan uwa yau da dare? Wani Ansar ya

dauki wannan dan uwa zuwa gidan shi, sai ya tambayi matar shi ta kawo abinci,

sai ta amsa mashi " abincin ma ba zai ishi yaran su ba". Sai Ansar ya cewa matar

ta shimfidar da yaran su yi barci. Yace ta kawo abincin kuma ta kasha fitila, zan

yi kamar ina cin abincin da bakon, ba zai sani ba tunda cikin duhu ne. bakon yaci

abincin, sai suka koma wajen Manzon Allah SAW kashe gari. Annabi Muhammad

SAW ya taya wannan Ansar murna, yace " Allah ya ji dadin karimcin da ka yi jiya

da dare.

Abdullah Bn Umar ya ruwaito cewa wani mutum ya aikawa wani dan uwa Musulmi

kyautar naman akuya, sai wannan shima ya aikawa wani dan uwa Musulmi tunda

yana ganin shi ya fi shi bukata, na uku shima ya aikawa mutum na hudu sai da ta

tabi hannun mutum bakwai, har daga karshe ta koma hannun wanda ya fara

badawa. Wannan an yi bayanin shi a kushari. Akwai wata riwaya irin ta

daga Anas kamar yadda a ka yi bayani a Tha'labi

A'isha RA tace wani almajiri yazo gidan ta yana bara, to biredi daya ya rage a

gidan ta. A'isha ta umarci bawan ta ya ba wannan almajiri biredin nan, sai bawan

yake mamakin ta yaya A'isha za ta yi buda baki a wannan yammaci. A'isha RA ta

nace akan sai an baiwa almajirin biredin. To sai ya kasance da yamma sai aka

aikowa Aisha dafaffen naman akuya. Aisha RA ta kira baiwar ta zo su ci.

Nasa'i ya ruwaito cewa wani lokaci Abdullahi Bn Umar RA ya kasance baya da

lafiya kuma yana son ya ci inabi. A nan aka sayo mashi inabi. Kwatsam sai

almajiri ya zo, sai Bn Umar ya baiwa wannan alajiri wannan inabin. Wani daga

cikin bakin Bn Umar ya je ya sayo wannan inabin daga wajen wannan almajirin

ay kawowa Bn Umar, sai wannan almajirin ya sake dawowa, Bn Umar ya sake

baiwa wannan almajiri wannan inabin, wannan almajiri ya sake sayo wannan

inabi ya kawowa Bn Umar, yana tsammanin wannan inabi an sayo shi ne daga

kasuwa , da ya san haka da ba zai ci ba inabin a karo na uku.

Ibn Mubarak ya fada a cikin Musnad nashi cewa wani lokaci Khalifa Umar ya aikin

bawan shi da dinari dari hudu wajen Abu Ubaida Bn Jarrah. Umar ya umarci

bawan da ya lura da yadda zai yi da wannan kudi. Bawan nan ya fadawa Umar

cewa Abu Ubada ya rarraba dukkan kudin ga masu bukata. Haka nan kuma Umar

ya aikawa Mu'az Bn Jabal dinar dari hudu ta hannun bawan shi kuma ya umarce

shi da ya lura da yadda zai yi da wannan kudi. Bawan nan ya dawo ya fadawa

Umar cewa Mu'az Bn Jabal ya rarraba wannan kudin ga masu bukata, da sauran

dinar biyu suka yi saura matar Mu'az ta ce " ni ma mabukaciya ce, a bani", sai

Mu'az ya ragowar dinari biyu. Khalifa Umar RA ya cewa bawan shi " Yan uwa na

kamar su daya a halin su ".

Huzaifa Adawi ya ruwaito : na tafi neman kawu na a yakin Yarmouk ina rike da

ruwa ga wadanda suke da sauran rai. Na sami kawu ya kusa mutuwa. Na ba shi

rowan da nake dauke da shi, sai ya ji wani dan uwa yana kuka kusa da shi, kawu

na ya ki shan rowan matsa in kaiwa wannan dan uwan. Shi na biyu sai ya ji

kukan wani dan uwa na uku, sai ya umarce ni in yi sauri in kaiwa wannan na uku.

A haka sai da na kai kan mutum na bakwai, a lokacin da na kai kan mutum na

bakwai har ya riga ya cika, na hamzarta wurin kawu na, shi ma har ya riga ya

rasu.

Allah SWT ya kasa al'ummar Annabi Muhammad SAW kashi uku : masu hihira,

Ansar, da kuma sauran al'mmah. Allah SWT yayi bayani nagartar Muhajirum da

Ansar a cikin Al Qurani. Har way au, yayi bayanin nagarta daya ta sauran

al'umma. Wannan kashi na uku dole su kasance suna yabawa sahabban Manzon

Allah SAW ba wai don sun kasance ba sun banbanta saboda irin imanin su ba,

amma sai saboda imani yazo mana ne ta hannun su. A nan su wadannan rukuni

na uku, su kasance suna yi wa sahabban Annabi Muhammad SAW addu'a, kada

kuma su dauki wata kiyayya a ran su a kan sahabban Annabi Muhammad SAW.

Aya ta 10 a suratul Hashri addu'a ce mai kyau:

" da wadanda suka zo bayan su, ya Allah ka yafe mana da yan uwan mu da suka

zarce mu imani, kada ka sanya a cikin ran mu wata kiyayya akan wadanda suka

yi imani. Ya Allah hakika kana da cikakkken jin-kai, mai rahama".

Mus'ab Bn Sa'id yace muna iya kasancewa kadai a cikin wannan rukuni idan

muka sami halayen da aka zayyana a sama.

Qurtubi ya tsamo a cikin wannan aya cewa wajibi ne mu kasance muna mutunta

sahabban Annabi Muhammad SAW. Imam Malik yace " musulmi bashi da wani

kaso a kowace ganima idan ba shi da kyakykyawar alaka ta mutunci da sahabban

Annabi Muhammad SAW".

Abdullah Bn Abbas yace " Allah SWT yayi umarni ga daukacin musulmi su yi

addu'a ga sahabban Annabi Muhammad SAW. Allah ya sani, za su sami sabani a

tsakanin su, kuma za su yi fada a tsakanin su, duk da haka mu kyautata

tsammani ga sahabban Annabi Muhammad SAW.

An karbo daga A'isha RA daga Annabi Muhammad SAW yace : al'ummar shi ba za

su wargaje ba idan basu zagi wadanda suka shude gabanin su ba.

Abdullahi Bn Umar RA yace idan ka gamu da wani wanda yake la'antar sahabban

Annabi Muhammad SAW sai kawai kace " Uban giji Allah ya la'anci wanda yake

mafi muni daga gare ku". A wannan hali Allah SWT sai yayi maganin shi.

Awwam Bn Jush'ab yace" na sami Musulman farko suna tunatar da saura akan

baiwar sahabban Annabi Muhammad SAW, su kara soyayya a gare su, su kauce

fadar sabani da rigingimu tsakanin sahabbai, saboda ba za su kasance kanana

suna zargin sahabban Annabi Muhammad SAW.

Ya Allah mu yabo da kirki irin na sahabban Annabi Muhammad SAW domin mu

kasance cikin rukuni na uku mu sami cin nasara a rayuwa da rayuwa ta ranar

karshe. Amen.

JARRABAWAR DA AKA YIWA ANNABI IBRAHIM AS

Aya ta 124 a suratul Baqarah, Allah SWT yace:

" Da Allah SWT ya jarraba Annabi Ibrahim AS, Annabi Ibrahim AS ya ci

jarrabawar. Allah SWT yace da shi " zan maida kai shugaban duka al'uma".

Annabi Ibrahim AS yace ya Allah wannan alkwali har da yara suma ! Allah SWT

ya bada amsa "I" amma banda wanda suka fandare".

Tambaya da yawa ta zo a rai, ko menene ya sa Allah SWT zai jarraba wani,

wanda kuma shi masani ne a kan komi? Yaya yanayin wannan jarrabar take?

Menene sakamako wannan jarabawar ? idan akwai ko yaya? Za mu amsa wannan

tambayoyi daya bayan daya.

Dalilin wannan jarrabawa ba wai domin a bada wani maki bane, ci ko faduwa.

Dalilin wannan yana nuna da kalmar 'Rab' a wannnan ayar. Allah SWT ya zabi

wannan kalma domin kan shi, kuma amfanin wannan jarrabawa domin sanya

mutum akan wani a kan wani ruhu da kuma koyar da shi a kan mataki na

kokkoliya. Waka a Urdhu ta ce :

Kai meke kada kaji tsoron iska da ya kiye maka, wannan zai kai ka sama da

kokkoliya. A nan wahala tana koyar da mutum ya kai babban matsayi.

Mun sani cewa Allah SWT yana fada mana sakamakon jarrabawar Ibrahim AS,

yana cewa ya cika wanna jarrabawa. Wannan yana nufin Ibrahim AS ya fada da

kyakykyawar sifa cewa " Ibrahim AS wanda ya aika alkawalin shi". A aya ta 37 a

surat An Najm.

A anan, sai mu yanke cewa Ibrahim AS ya ci dukkan jarrabawar shi. A bisa

wannan sakamako ne Allah SWT yace dashi " Zan maida kai shugaban dukkan

talikai". Annabi Ibrahim AS yayi farin ciki amma kuma yana tunanin bayan shi.

Allah SWT yace " Hakika akwai shuwagabannin talikai daga zuriyar ka sai dai

wadanda suka fandare.

A nan mutanen littafi ba su kasance shuwagabanni ba tunda sun hada Allah da

wanin sa.

Yanzu za mu yi bayanin jarrabawar da aka Annabi Ibrahim AS. Za mu fara da

lokacin da yake yare da iyayen shi da mutanen su. Ya same su suna bautar

gumaka wanda suke sassakawa da hannun su. Annabi Ibrahim AS yayi jawabi ga

wadannan gumaka kamar yadda bayani ya zo a suratus Saffat aya ta 91-98:

" sai ya juya ga gumakan ya ce " ba za ku ci (abubuwan da ake kawo maka ba)?

Menene ya same ku da ba za ku yi Magana ba? Sai ya juya gaba gare su yana

bugon (su) da (hannun shi)na dama. Sai masu bautar gumakan suka juyo gare

shi a gaggauce. Yace da su " kuna bautawa abinda ku da (kan ku) kuka sassaka?

" bayan da Allah ya halicce ku da kuma abinda ku ke yi". Sai suka ce " ku gina

mashi wani gini (wannan gini tamkar wurin narka karfe), ku jefa shi cikin wuta

mai kuna". Sai suka shirya wannan makarkashiya a kan shi, sai muka maishe shi

kaskantattu".

Annabi Ibrahim AS yace " Hasbunallahu wa ni'mal wakilu". "Allah SWT shine ya

isa ya kare ni shine mai jibinta ta".

Allah SWT ya umarci wannan giwat wutar ta kasance mai sanyi ba mai cutarwa

ba ga Annabi Ibrahim AS.

A yanzu Annabi Ibrahim AS dole ya bar mahaifin sa da mutanen shi da abinda

suke bautawa. Sai ya tafi Syria da matar shi. Wannan al'amari ma an yi bayanin

shi a suratus Saffaat aya ta 99-100 :

" (Annabi Ibrahim AS) ya ce " na bi hanyar Allah SWT wanda shine hakikan

wanda zai shiryar dani. Ya Uban-giji ka ba ni 'ya'ya daga masu adalci".

Daga nan ne malamai suka ce sunna ce ta kowane Annabi yayi aure ya sami yaya

ma su shiriya, saboda su kasance sun ci gaba da aikin Allah SWT. Misali kuma

shine na Annabi Zakariyya' AS, aya ta 38 Surat Aal Imaran:

" A lokacin da Zakariyya ya rokin Uban-gijin shi : Ya Uban-giji ka bani daga gare

ka 'ya'ya na gari. Hakika kai mai jin roko ne".

to dole ne mu yi addu'a ga Allah SWT ya bamu 'ya'ya na gari salihai.

Allah SWT ya baiwa Annabi Ibrahim AS shiryayyen da wanda zai gwada wata irin

mu'ujiza ta yin hakuri da kamun-kai. Hajara matar Annabi Ibrahim AS ta haifai da

Isma'il AS.

Allah SWT ya umurci Jibril ya dauki Annabi Ibrahim AS da matar shi da kuma

jaririn su wani waje ana kiran shi Makka a yanzu. An umarci Annabi Ibrahim AS

da ya koma Syria da zaran sun je wajen. Ruhin mika wuya ga umarnin Allah ya yi

girma a zuciyar Annabi Ibrahim AS, nan da nan ya kama hanya zuwa Syria. Sai

matar shi tace " ina za ka tafi ka bar mu nan inda babu wasu gidaje ba ruwa ba

ciyayi? Duk da haka bai amsa mata ba. Daga karshe tace " ko Allah ya kai ka

haka?" Annabi Ibrahim AS ya amsa "I". Sai tace " ba koma wanda ya tura ka zai

jibinci al'amarin mu".

Da Annabi Ibrahim AS yaje akan dutse sai ya juyo yayi addu'a " ya Allah SWT na

ajiye iyalai ba a wajen da babu alamar tsirrai ko kadan! Ka basu abinda za su

rayu domin su yi sallah domin su kasance sun mika wuya a gare ka".

Yana da ban sha'awa muga yadda annabawa suke daidaitawa tsakanin hakkin

Allah SWT da hakkin mutane.A wani hannun kuma ' Sufaye' suna tsunduma ne

wajen cika hakkin Allah SWT kawai.

Wannan ita ce babbar jarabawa ga dukkan iyalan Annabi Ibrahim AS . Hajara ta

sami jaririn ta yana kuka a bashi ruwa sai ta ruga kan wani tsauni tana neman

ruwa, sai ta je bata samo ba, ta ruga da gudu wajen yaron da yake kuka. Sai ta

sake rugawa a kan wani dutsen da ake kira 'MARWAH' ta gani ko ta sami ruwa.

Nan ma bata samu ba. Hajara sai da tayi zarya sau bakwai tsakanin safa da

Marwa ta neman rowan da zata bai wa dan ta. A yayin da ta dawo wajen wannan

zarya sau bakwai, sai ta sami dan ta yana buga kafar shi a kasa. Abin mamaki,

sai ta sami ruwa yana bulbulowa daga wurin wanda da yanzu ake kira ZAM ZAM.

Har yanzu wannan ruwa yana nan yaan kwararowa yana amfanar al'umma.

Annabi Ibrahim AS ya kasance yana ziyartar iyalin shi lokaci zuwa lokaci. Da dan

shi Isma'il ya kai saurayi, Annabi Ibrahim AS yace da shi " ya kai da na na gani a

mafarki zan yi layya da kai me kake gani game da wannan?". Wannan ya gwada

mana yadda uba zai yi Magana da dan shi. Annabi Ibrahim AS yayi mashi

cikakken bayani ya jira ya saurari abinda zai ce. Wannan ya bar faffadar Magana

ta nasiha idan ya kama. Wannan kuma ya jarraba irin matsayin mika wuya ga

Allah SWT na dan shi, kuma ya sake gwada mana wannan shine lokacin da da

yake taimakon iyayen shi, ko wadanne iyaye a kagare suke suna jiran wannan

lokaci. Allah SWT ya umarci Annabi Ibrahim AS yayi hadaya da dan sa a halin

kuruciyar shi. Wannan ma babbar jarrabawa ce ga iyalan Annabi Ibrahim AS.

Amsar da dan yayi tana da ban-al'ajabi. Yace " ya kai baba na, ka ci gaba da

abinda aka umurce ka".

Wannan saurayin yaro karara ya fahimci cewa ko da mafarkin Annabi kamar

wahayi ne daga Allah SWT kuma umarni daga Allah SWT. Kuma Isma'il ya kara

da cewa " In sha Allah za ka same ni daga cikin masu hakuri". Wannan amsar

tana da darasi da yawa a kan mu. Abu na farko mu rika sanya In sha Allah a cikin

zantuttukan mu, kamar yadda a gwada mana mu yi a cikin suratul Kahf da suratu

Noun. Abu na biyu Isma'il ya gane cewa akwai mutane kafin wadanda suke da

matsananciyar dangana. Maimakon ya cika baki game da hakurin shi sai ya

kaskantar da kan shi ya ce " da yardar Allah za ka same ni a cikin masu hakuri.

Uba da dan sa tare sai suka tafi wani wuri da ake kira Mina. A kan hanyar su

shedan yayi kokari ya hana uban, si yace " mafarkin ne kadai ka yi me ya sa za

ka yanka dan ka a kuruciyar shi?" Annabi Ibrahim AS ya dauki duwatsu ya jefi

Shaidan ya kore shi. Sai Shaidan ya dawo yana jawo hankalin Isma'il da

mahaifiyar shi. Suma suka dauki duwatsu suka rika jifar shi suka kore shi da

karfin imanin su.

Da da uba a shirye suke da yin hadaya. Maganganu masu cin rai suka afku a

tsakanin su. Da ya cewa uban shi wadannnan abubuwa :-

* Ya baba na ka daure hannu na da kafa ta domin kada in yi ta tsalle.

* Ka wasa wukar ta yi kaifi domin ka yi saurin yanka makogaro na, domin rai na

yayi saurin fita, mutuwa tana da wuya kwarai.

* Ka janye tufafi daga jini na domin kada lada ta ta ragu kuma uwa ta hankalin

ta kada ya tashi idan ta ga jinin.

* Ka yi sallama ga uwa ta, ka bata riga ta, wannan zai iya kwantar mata da

hankalin ta.

Annabi Ibrahim AS ya saurari wannan jawabi mai tada hankali daga bakin dan

shi, amma Annabi Ibrahim AS bai karaya ba. Sai yace ga dan shi " Ya kai da na

kana da taimako wajen aiwatar da aikin Allah SWT.

Wannan bayani ya zo a Surat As Saffat aya ta 103-107 :

" Lokacin da dukkan suka mika wuya ga Allah SWT, Annabi Ibrahim ya kwantar

da dan shi a kan fuskar shi. Allah ya kirawo Ibahim " ya Ibrahim ! ka cika

wahayin abinda ka gani a mafarki. Muna bayar da lada ga aiki mai kyau irin

wannan. Hakika wannan bayyananniyar jarrabawa ce. Mun sauya maka da

babbar hadaya".

Rago aka bayar a maimakon Isma'il AS. Allah SWT ya shaidar Annabi Ibrahim AS

kuma ya umarci duk wadanda za su zo bayan shi su girmama shi. Allah SWT ba

kawia ya ceto Isma'il bane, kuma ba shi wani da Isaac. Dukkan su mashahuran

Annabawan Allah ne.

Allah SWT yana son mika wuya irin na kowane daya daga cikin iyalan Ibrahim AS

sosai ya sanya shi ya zamo alama ga sauran baya su mayar da ita bangaren aikin

Hajji.

Ya Allah SWT ka bamu kwarin gwiwa da zuciyar mika wuya ta bin Allah kamar ta

iyalin Annabi Ibrahim, Amin.

MARYAM

Kafin kirsimati, ko lokacin kirsimati ko bayan kirsimati, muna jin maganganu da

yawa game da Maryam (Mary) daga kiristoci. Za ka ga an baje kolin kamannin

Maryam a coci-coci da wuraren ciniki da wake-wake da dama. Wannan tana

kawowa Musulmi da yawan su rudani. Ya kamata mu san ko wacece wannan

Maryam din (Mary). Yana da ban-sha'awa mu juyo mu dubi yarintar ta, yadda ta

tashi, kuruciyar ta, da kasancewar ta cikakkiyar mutum ta haske da shiriyarwar

ta a Al Qur'ani. Yadda Maryam ta dauki ciki da hanyar da ta haifi mashahurin da

(Jesus) Isa AS. Yana daga ayoyin Allah SWT ga ababen halitta. Abinda ya faru da

haihuwar Maryam an yi bayanin sa a cikin Surat Aal Imran aya ta 35-36:

Yayin da mahaifiyar Maryam take tsammanin haihuwa sai ta ce " Ya Allah":

" Na damka wannan da nake dauke da shi a ciki na domin yayi dawainiya domin

ka, ka amsa ka san sahihancin abinda na ce kuma kana jin duk abinda muke

cewa".

" Sa'annan da ta haifi jaririyar ta (Maryam) sai tace " Ya Ubangiji! Na haifi diya

mace. Allah shine ya fi cancantar ya san abinda ta haifa, kuma na-miji ba kamar

mace bane, kuma na sanya mata suna Maryam. Ina neman kariya daga gare ka

Allah domin ta da 'ya'yan ta daga shaidan wulakantacce".

Lokacin da mahaifiyar Maryam ta haihu ta yi mamakin abinda ta haifa yarinya ce.

Wannan wani abu ne da kowa ya amince; yaro na-miji shine ke iya daawiniya a

masallaci. Duk da haka ta sanyawa wannan yarinya suna 'MARYAM', kuma tayi

roko ga Allah " Na damka ta da 'ya'yan ta karkarshin kariya ta Allah daga shaidan

wulakantacce. Sai kuma abinda ya wanzu a haihuwar wannan jaririya (Maryam),

an kara bayani. A wannan surah Allah SWT yace:

" Hakika, yarinya ba kamar yaro ta ke ba". A wata fadar, kuma yarinya za ta

zama ta da ban daga yaro. Kuma yazo hakika daga wannan ayar uwa tana da

dama ta sanyawa dan ta suna kamar yadda uba yake. A wata fadar kuma ba

dama bace ta uba ya sanyawa dan shi suna. A gaske dama ta mace da namiji

daya take a musulunci. Sai dai kawai dawainiyar da zai yi ya banbanta, wannan

dawainiya Allah ya sanya ta shine ya fi cancantar sanin abinda abin halittar sa zai

iya.

Allah SWT ya kuma kawo bayanin yadda wannan yarinya ta tashi a Surat Aal

Imran aya ta 37:

" Allah SWT ya karbi wannan yarinya ta hanya wace take mafificiya, kuma ya

rayar da ita akan tafarkin mafifici, ya damka ta a bisa kulawar Zakariyya'. Duk

lokacin da Zakariyya' ya je wajen ta a masallaci sai ya gani tana da abnci ( da

dama na kowane irin yanayi) sai ya ce ya Maryam! Daga ina kika kika kawo

maki? Sai ta ce daga Allah, yana bayarwa da dama ga wanda yake so". Wannan

ne yasa Zakariyya yaga ya dace ya roki Allah SWT ya bashi da, tunda bashi da da

ga shi kuma tsufa ya zo mashi. Ya gane cewa tunda Allah SWT zai samarwa

wannan yarinya abinci na kowane irin yanayi da yawa, to zai iya bashi da duk

kuwa da tsufan shi. Addu'ar shi an yi bayanin ta a Surat Aal Imran aya ta 38:

" Sai Zakariyya yayi addu'a ga Allah yace " Ya Ubangiji na, ka bani da wana yake

salihi, hakika kai mai jin addu'a ne".

Yana da ban sha'awa an sa a Musulnci mutum yayi aure ba domin kawai ka haifi

'ya'ya ba, har ka tarbiyyantar da su su kasance salhai a bisa tafarkin addinin

Musulunci da koyarwar sa. Shine dalilin da ya sanya Annabawa kamar su

Zakariyya da Ibrahim AS suka yi addu'a a basu 'ya'ya a lokacin da suke tsofaffi,

saboda 'ya'ya na gari domin su ci gaba da aikin Allah SWT ko bayan mutuwar su.

Allah SWT ya karbi wannan addu'a ta Zakariyya kamar yadda aka yi bayani a aya

ta 39, Surat Aal Imran:

" Sai Mala'ika ya kira Zakariyya a yayin da yake addu'a a masallaci. Allah yana yi

maka albishir da da ana kiran shi 'YAHYA' wanda zai zo ya jaddada kalmomin

Allah. Yahya zai kasance mai matsayi a wajen Ubangiji kuma Annabi jaddada

gaskiya".

Muna iya ganin cewa addu'ar mutum tana iya kasancewa karbabbiya wajen Allah

SWT idan yana sallah a masallaci. Allah SWT yana gwadawa mutane na kowane

karni tunda zai iya ba Zakariyya da lokacin da ya tsufa tukuf. Haka nan kuma

yana iya baiwa Maryam duk da cewa babu wani mahaluki da ya taba taba ta.

Zakariyya yace da Allah SWT, suratu Aal Imran, aya ta 40-41:

" Sai ya ce " ya Allah yaya zan yi in sami da bayan da tsufa ya baibaye ni kuma

mata ta bakararra ce?" Mala'ka ya ce " haka yake, Allah yana yin abinda ya so".

Zakariyya ya ce " ya Allah ka bani wata alama". Mala'ika yace " alamar ka itace;

ba za ka iya magana da kowane irin mahaluki ba, sai bayan kwana uku, sai dai

da nuni. A wannan lokaci kayi tasbihi ga Allah safiya da marece".

Bari kuma mu ga yadda Musulmi suke daukar Maryam a lokacin da ta kasance

cikakkiyar mutum. Allah SWT ya ce a cikin Surat Aal Imran aya ta 42-43:

" Da mala'aka ya cewa Maryam Allah ya zabe ki, ya tsarkake ki daga (bata) ya

zabe ki sama da dukkan mata da ke a doron kasa da kuma aljannu. Ya Maryam!

Ki kasance mai biyayya ga Ubangijin ki, ki kame kan ki, kiyi sujada tare da wanda

suke yin sujuda wajen bauta".

Mun gane cewa idan Allah ya kara ma kyauta ya kamata ya kamata ya kara mika

wuya ta wajen yin salloli. Umunin yin sujuda ya gwada cewa an fi son ayi salla a

cikin jam'i. Mala'ika sai ya kara cewa Maryam, Aal Imran aya ta 45-46:

" (tuna) Yayin da Mala'ika ya ce " Ya Maryam ! hakika Allah ya yi maki

kyakykyawan albishir da da daga gare shi, sunan shi Isa dan Maryam. Amintacce

a nan duniya da kuma lahira, daya daga wadanda suke da kusanci da Allah SWT.

Wannan yaro zai yi magana da mutane a cikin dan-goyon shi. Idan kuma ya kai

munzalin cikakken mutum zai kasance daga cikin masu gaskiya".

Maryam sai ta cika da mamaki, sai ta ce : Aal Imran, aya ta 47:

" ta ce " Ya Allah ! yaya za a ayi in sami da bayan da babu mahalukin da ya taba

ni" sai ya ce " haka yake ! wajen Allah, yana halittara abinda ya ga dam, idan

yace da abu ya zama sai ya zama".

A nan, haihuwar Isa an yi ta ne kawai da kalmar Allah SWT wanda aka samu

tabbaci daga Yahya AS. Karin dadawa, a bayyane yake karara haihuwar Isa AS ta

faru ne inda babu mahalukin da ya taba taba Maryam.

Al Qur'ani yayi bayanin yadda Maryam ta dauki ciki da tayi da kanta lokacin da

tana da ciki. Suratu Maryam Allah SWT ya ce , aya ta 16-26 :

" An yi bayani a cikin littafi (Al Qur'ani) Maryam. Lokacin da ta fita daga mutanen

ta, zuwa wani dakin da ke dubar gabas, ta zama ta kaurace daga gare su. Sai

muka turo mata Ruhin Mu (Mala'ika) ya zo mata tamkar wani mutum. Sai ta ce

dubi ! ina neman tsari wajen mai rahma daga gare ka idan kana tsoron Allah".

Mala'ika yace " Ni kawai manzo ne na Allah, za a baki da wanda yake salihi".

Maryam tace " yaya za a yi in sami da tunda babu mutumin da ya taba taba ni,

kuma ban kasance ba mai tsarki ba". Mala'ika yace " Allah ya ce abu ne mai sauki

gare shi, haka zai kasance tunda abinda ya nufa ke nan. Allah zai maida shi wata

alama ga mutane da jin-kan shi. Maryam ta tafi wani waje mai nisa. Lokacin da

ciwon nakuda ya kai ta a gindin wani dabino, sai ta ce " Kash, na gwammace ma

in mutu a kan wannan in kasance wani abinda za a manta da shi". Sai wani yayi

magana ta kasan ta yace " kada ki damu! Allah ya sanya a kasar ki. Ki

girgiza gindin itaciyar nan nunannun dabino za su fado maki, ki ci ki sha ki

kwantar da hankalin ki. Idan kika gamu da wani mutum, ki ce " ina yin azumi ne

ba zan yi zance da kowane mutum ba".

Mun ji an ce Maryam ta girgiza itaciyar dabino ta sami nunannun dabino. Wannan

yana koya mana mu yi bakin kokarin mu mu sami na kan mu. Wannan kokari ba

wai kin yarda da Allah ne ba.

Bayan kwana arba'in, Maryam ta koma ga mutanen ta da dan ta a hannun ta.

Yadda al'amarin ya kasance tsakanin ta da mutanen ta an yi bayanin shi a Surat

Maryam aya ta 27-32:

" Sai ta kawo shi zuwa ga mutanen ta tana dauke da shi, sai su ka ce "Ya Maryam

kin zo da abin mamaki. Ya ke yar uwar Haruon, baban ki ba mugun mutum ne ba

haka nan babar ki ba karuwa bace". Sai ta nuna shi, sai suka ce to yaya zamu yi

magana da wanda ke cikin magoyi yaro karami". Sai Isa yace " ku sani ni bawan

Allah ne, ya bani littafi, ya nada ni Annabi, ya albarkace ni a duk inda na ke, ya

umarce ni in yi salla da bayar da zakka in har ina da rai. Allah ya umar ce ni da in

yi biyayya gare ta wadda ta haife ni, bai maida ni ba mai girman kai maras

albarka".

A abinda aka gutsuro, kalma ta farko wanda Isa yayi shine 'bawan Allah', don

haka, bai kasance ba abokin tarayya a kowane lokaci. Abu na biyu sallah zakka

dole ga kowace irin alu'mma dole mutane su cika wannan umarni idan har sun

kasance rayayyu.

Mun ga Maryam tana jaririya, yadda ta tashi, kasancewar ta cikakkiyar mace,ta

kuma uwa. Akwai almomi na shiryiwa ga Allah SWT ga wadanda suke neman

yardar Allah. Maryam tana da banbanci da Maryam wacce kiristoci suke

gwadawa.

Allah SWT ka tsare daga kowace iri shirka, mai sai mu bayi masu biyayya, Amin.

WASIYYAR ANNABI MUHAMMAD SAW ( KASHI NA FARKO)

Allah SWT ya ce a cikin Surat al An'am aya ta 151:

" ka ce zo, zan karanta maku abinda Ubangijin ku ya haramta a kan ku : kada ku

hada shi da wani, kuma ku kyautatawa mahaifan ku, kada ku kashe 'ya'yan ku

saboda talauci, mu ke ciyar da su (yaran) da ku, kada ku kusanci abubuwa

marasa kyau ko a bayyane ko a boye. Kada ku kashe rai wadda Allah SWT ya

haramta (tsare) sai da gaskiya, da wannan ne ya umarce ku ko kun fahimta.

Wannan ya umarce ku ko da kun fahimta".

Wannan aya da ayoyi biyu bayan ta sun yi amfani da kalmar wasiyya sau ukku a

wata fadar kuma Allah SWT yana umartar mu ko jaddada mana mu bi wadannan

ka'aidoji.

An fada a cikin tafsin Ibn Katheer cewa Abdullah Bn Mas'ud RA yace idan wani

yana so ya ga wasiyyar Annabi Muhammad SAW da hatimi a jiki to ya karanta

wadannan ayoyi wadanda ya barwa al'umar shi.

Haka nan ya rubuta cewa Ubaadah Bn As Samit RA ya ruwaito cewa Annabi SAW

ya taba yi wa sahabbai bayani cewa kowa zai yi mashi alkawali akan wadannan

ayoyi guda uku. Annabi SAW ya kara da cewa duk wanda ya cika alkawalin ladar

shi tabbatacciya ce a wurin Allah.

A wannan ayoyi abubuwa daban daban an kira su HARAM. Ta yadda Al Quar'ani

ya fiti abin yana gayyato tunda yana umarni ne ya fara da kalma zo. Barin in fada

maka kamar wani yana gayyatar wani daga wani wuri mai tsawo domin ya daga

mai saurare na sama da gaba sama can. Ya ce " bari fada maku abinda Allah SWT

ya haramta maku". Yana jaddadawa kada ka aikata haram a kan ka. Bayan

wannan bayani na bai-daya, ko wace haram an bayyana ta da ban.

- Abu na farko, kada ka hada Allah da wani. Ana yin shirka ta bangarori da dama.

- hada Allah da wani kamar yadda yahudawa da kiristoci su ke yi.

- Duk da yadda cewa Allah SWT yana yin komi amma ka dauka cin ma wata

nasara akan rayuwa bisa wasu abubuwa na harkoki.

- Ka yi addu'a amma kada ka sare.

- Ka ciyar domin Allah SWT domin samun wani matsayi.

Annabi Muhammad SAW yace " babu abinda zai cutar da ku ba tare da yardar

Allah ba SWT.

Shirka an fara ambaton ta saboda ita ce mafi girman laifi, Allah SWT baya yafe ta

har abada.

Ubbada Bn Samit da Abu Darda' sun ce Annabi Muhammad SAW

Yace " kada ka hada Allah da wani ko da za a rataye ka ko kuma za a kona ka da

ran ka".

Na gaba, an yi mana umarni mu kyautatawa iyayen mu. Yana da ban-sha'awada

an ce " kada ku ki biyayya ga iyayen ku". Amma fuskanta ta Al Qur'ani yana da

ban sha'awa. Allah SWT yace ba wai ku yi biyayya amma ku kyautata masu

domin su ji dadin ku. Allah SWT ya kara cewa :

" Ku kasance masu biyayya gare su".

Allah ya sake cewa: " Ubangijin ku ya yanke wannan shawara domin kada ku

bautawa wani ba shi ba, kuma ku kyautatawa iyayen ku".

A cikin Surat Lukman aya ta 14, Allah SWT ya ce " ku gode mani da iyayen ku,

saboda za ku dawo gare ni".

A wata fadar kuma, Allah SWT yace idan baka gode mashi ba kuma iyayen ka za

a azabtar da kai idan ka koma gare sh. A dukkan wadannan ayoyi, hakkin iyaye

an sanya shi bayan hakkin Allah SWT. Hakkin iyaye yana da muhimmanci a

wurin Allah.

Abdullah Bn Masuud RA ya ce na tambayi Annabi SAW " wane aiki ya fi ?" sai ya

amsa mani " yin sallah cikin lokaci". Sai na tambaye shi "sai me?" yace

"kyautatawa iyaye". Na tambaye shi " Sai me ?" ya ce " kayi yaki ta hanyar Allah

SWT. (Saheehan)

Abu Hurairah RA ya ruwaito cewa wata rana Annabi Muhammad SAW

Ya ce har sau ukku " Ya halaka", sahabbai suka tambaya " Ya manzon Allah

wanene ya halaka? Sai ya ce wanda duk ya riski iyayen shi sun tsufa amma bai

shiga aljanna ba.

Wanna yana nufin idan wani yayi dawayiniya da iyayen shi cikin kwanciyar

hankali, an yiwa wannan mutumen alkawalin shiga aljanna.

A gaba, Allah SWT ya yi bayanin damar 'ya'ya. Allah SWT yana umartar mu kada

mu kashe 'ya'yan mu domin jin tsoron talauci. Allah SWT zai ba su kamar yadda

ya ke baku. A cikin Surat Al Isra', Allah SWT ya ce : " Muna bayar gare su da

kuma ".

A nan ana gwadawa 'ya'ya wadanda suke masu rauni wadanda suke basu iya

daukar dawainiyar kan su sun fi dacewa a basu fiye da ku. Haka nan Allah SWT

yana budawa gare ku domin su, su wata rahama ce a gare ku, don haka wata

larura ba ce. Subhanallah.

Dubi yadda iri zai girma ya zama itace ya rika samar da 'ya'ya, iyaye ba su yin

wani abu da zai girma, Allah ne ya ke yi. Ta wannan hanya ne Allah zai samar

maku da kyauta wanda babu iyaka ta hanyoyi da ba ku sani ba. Idan ba mu

baiwa diyan mu ba ilmi da tarbiyya ta addinin Musulunci ba mun kashe su.

Saboda Alqur'ani yana kiran irin wadannan mutanen matattu wanda bai ba bin

Allah SWT muhimmanci ba. A nan wadanda suka kauda kai daga baiwa diyan su

ilmi da tarbiyya ta addinin Musulunci suke da hakkin kashe diyan su. Kisa kisa na

rashin bin shiriya ya fi kisa domin wani abin duniya. Zunuban da diya suka aikata

saboda rashin bin tafarkin shiriya kwata kwata ya lalata masu rayuwa.

Allah SWT ya umarce mu kada mu kusanci abubuwa wadanda basu da kyau a

bayyane ne ko a boye. Abubuwa na bayyane suna nufin da harshe ne ko hannu

ko kafa da dai ire-iren su. Abubuwa na boye suna nufin bakin-ciki, muguwar

sha'awa, rashin godiya da rashin hakuri. Har wa yau, ayyuka na bayyane suna

nufin kamar dubar mace da mugun tunani, taba ta da hannu ko yin Magana da ita

da mugun nufi. Kuma abubuwa na boye suna nufin yin wani abu a suturce domin

aikata abubuwan da aka ambata a sama. Annabi Muhammad SAW ya hane mu

kada mu yi kutse abinda bamu da tabbas ko gonar da ba tamu ba zai kai mu ga

halaka.

Annabi Muhammad SAW ya ce:

Duk wanda yayi shawagi a wuraren da aka haramta mashi, yana iya kasancewa

ya shiga wannan .

Allah SWT yana umartar mu kada mu kashe wanda aka haramta mana mu kashe.

Abdullah Bn Mas'uud ya karbo daga Annabi Muhammad SAW yace " ba a yarda

ba a kashe daya daga cikin Musulmi sai a bisa wadannan dalilai:

· Mutum mai aure da ya aikata zina.

· Wanda ya kashe wani haka nan.

· Wanda yayi ridda bayan ya karbi musulunci.

Bukhari da Muslim.

Halifa Usman RA ya tunatar da mutanen da mutanen da suka zo kashe shi

wannan Hadisi.

Haka nan kuma kashe wanda ba musulmi ba haka nan kawai ba a yarda ba a

Musulunci.

Abu Hurairah ya karbo daga Annabi Muhammad SAW yace " Duk wani wanda ya

kashe wanda ba Musulmi ba a kasar Musulmi ya karya alkawarin Allah SWT. Duk

wanda ya karya alkawarin Allah bai zai ji kamshin aljanna ba duk kuwa da ana jin

shi tafiyar shekara ashirin.

Wannan shine umarnin Allah SWT gare mu.

Ina rokon Allah ya bamu ikon bin wannan umarni kuma bisu kamar yadda ya

dace, Ameen.

WASIYYAR ANNABI MUHAMMAD SAW ( KASHI NA biyu)

Allah SWT a cikin surat Al an'am aya ta 152-153 ya ce:

Kada ku kusanci dukiyar maraya sai adi da abinda ya ke mai kyau, har sai ya

balaga. Ku bayar da cikakken awo da cikakken ma'auni cikin adalci. Kada mu yi

harajin da ya zarce iyaka. Idan ka yi Magana ka yi adalci a kan ta ko da ba a bisa

son ran mutane ba. Kuma ku cika alkawalin Allah. Shine ya umarce ku ko da kun

tuna shi. Allah SWT ya sake umarta cewa : wannan ita ce mikakkiyar hanya ka

bita kada ka bi sauran hanyoyi ko ka yaudare daga hanayar sa. Allah ya yi maku

haka don ku yi imani.

Da farko, an umarce mu kada muci kayan maraya dake a ajiye a wajen mu, mu

ba su dukiyar su idan sun mallaki hankalin su. Kamar yadda Imam Abu Haneefa

yace mu dakata har sai maraya ya kai munzalin da zai iya jibintar al'amarin shi.

Kuma mu mayar masu kafin marayan ya kai shekara 25, sai dai idan ba shi da

cikakken hankali. Wadansu malaman kuma suka ce a mayar da dukiyar a kotu

ita kuma ta nada wani amintaccen mutum ya kula da ita.

Allah SWT ya ce : " idan shekarun maraya sun kai kuma yana kuma yana jibintar

al'amuran shi to ku bashi dukiyar shi".

A nan muna iya yanke hukuncin cewa cikar shekaru bai isa ba, amma karfin

jibintar al'amura yana da muhimmanci. Allah SWT ya sake cewa : " wadanda

suke cin dukiyar maraya suna cika cikin su da wuta ne".

A nan, Allah SWT har wa yau ya umarce mu da mu bayar da cikakken awo da

cika ma'auni. Mutanen Annabi Shu'aib an dirkake su ne saboda kin bin wannan

umarni. Akwai gargadi mai tsanani a cikin Al Qu'rani mai girma a kan wadanda su

ke tauye ma'auni. Ka sani fa kin yin adalci a kan aikin ka shima tauye ma'auni ne.

A nan mutum yayi kokari iyakar iyawar shi, duk abinda ya wuce iyawar shi ba

matsalar shi bace. Sa'id Bn Qais ya ji da ga Annabi Muhammad SAW cewa " auna

kuma ka kara abinda yafi".

Abu Dawoud da Tirmidhi

Jaber yaji daga Annabi Muhammad SAW yace " jikan kan ya kasance a kan

mutumin da yake da sassauakar zuciya a wurin cininki kuma yana bada kadan da

ya zarce abinda ake bukata, da kuma mai saye wanda yake da sassaukar zuciya

wanda zai karba koda ya gaza kadan".

Bukhari.

A gaba, Allah SWT ya umarce mu idan za mu yi Magana mu fadi gaskiya ko da

kuwa ga 'yan uwan mu ne na kusa. Annabi Muhammad SAW ya ce shaidar zur

kamar hada Allah da wani ne " har sai da ya maimaita sau uku sa'annan ya

karanta wannan ayar:

Ka tsare kan ka daga bautar gumaka da shaidar zur da hada Allah da wani"

Abu Dawoud da Ibn Majah

Burraida ya ruwaito cewa Annabi Muhammad SAW ya ce " alkalai iri uku ne, daya

zai shiga aljanna sauran biyun kuma za su shiga wuta. Wanda yayi bincike akan

abinda aka kawo gaban shi a kan koyarwar Islama yayi kokari ya gano gaskiya

kuma ya zartar da hukunci na gaskiya zai shiga aljanna. Wanda kuma ya gano

gaskiya ta hanyar sani da bincike amma kuma sai ya yi hukunci ba daidai ba zai

shiga wuta. Haka kuma wanda ba shi da ilmi ko yin bincike da ya dace a kan

al'amarin kuma ya yanke hukunci cikin rashin sani shine zai shiga wuta.

Al Qur'ni ya shiryar da mu akan yin shaida : " ka fadi gaskiya da a kan ka ne ko

iyayen ka ko yan uwan ka".

Musulunci yana da cikakkiayar da'a. Allah SWT ya ce :

" Zamantakewa kada ta hane ku daga shaida ta gaskiya da zartar da abu kamar

yadda ya ke".

A nan an shawarce mu bi a sannu ko da a huldayyar mu ta yau da kullum ce, da

hirar bai kamata ba mu yi karya, yi da wani ko kuma mu fadi abinda zai cutar da

wani ko jawowa wasu asarar kudaden su.

Allah SWT ya umarce mu mu cika alkawali. Allah SWT ya ce a cikin surat Al

Baqarah aya ta 177:

" Ma su imani na gaske suna cika alkawali idan sun yi".

Yana da ban-sha'awa mu sani cewa wannan ayar ta na cewa ya kamata ya zame

hali na wadanda suka yi imani su cika alkawali tunda wadanda ba su yi ba imani

kan cika alkawalin su.

Haka nan kuma Allah SWT ya ce a cikin Surat Al Ma'arij aya ta 32:

Alamar muminai na gaskiya shine :

" Suna da rikon amana da alkawali".

A karshe Allah SWT ya na ce mana wannan ita ce mikakkiyar hanya ta don haka

ku bi ta, kada ku bi sauran hanyoyi tunda za su kawar da ku daga hanyar Allah.

Abdullahi dan Mas'uud RA ya ruwaito cewa : wani lokaci Annabi Muhammad SAW

ya zana wani mikakken layi ya ce " wannan ita ce hanyar Allah SWT. Sai ya sake

zana wadansu layika a jikin wannan ya ce "Wadannan su ne 'Subul', shaidan yana

a dukkan wadannan layuka yana kokarin ya kawadda mutane daga hanyar Allah

SWT. Annabi Muhammad SAW sai ya karanta aya daga cikin Surat Al An'am

kamar yadda aka yanko daga farko.

Za mu takaice ta kuma mu yi cikakken lura a kan wadannan ayoyi guda uku na

surat Al An'am.

Aya ta farko: ya yi bayani akan rukunnai guda biyar :-

· Kada ka hada Allah SWT da wani.

· Yin biyayya ga mahaifa.

· Kada ku kashe diyan ku.

· Ku tsare daga munan dabi'u.

· Kada ku kashe wani da gangan.

Sai Allah SWT ya ce " saboda ko kun fahimta". Tunda wadannan ba a dauka ba

wani mummunan abu kafin zuwan Musulunci. Allah SWT yana bamu shawara mu

bar wadannan dabi'u na jahiliyya, ku koma cikin hankalin ku.

Aya ta biyu, tana bayanin akan rukunai guda hudu :

· Kada ku ci kayan maraya.

· Kuyi awo daidai.

· Ka fadi kuma ka tsaya a kan gaskiya.

· Ka cika alkwali.

Wadanna abubuwa hakikanin gaskiya ne kowa zai iya ganin kyawun su. Mafi

yawancin mu ba mu da wadannan abubuwa ba. Maganin wannan rashin damuwa

shine tunatarwa, shine a karkashin wannan aya Allah SWT ya ce :" ko da wannan

shiriya ta zame maku tunatarwa".

Aya ta uku.

Aya ta uku an ce mu bi hanya madaidaiciya mu guji sauran hanyoyi. Wannan ba

ya samuwa sai ana tuna Allah SWT kuma ana kokarin cikakken imani. Kuma a

cikin wadannan ayoyi akwai rukunai guda goma. Wadannan ayoyi guda uku sana

da muhimmaci. Ka'bul Ahbar RA shi bayahude ne masanin At Taurah. Ya ce

bayan ya karbi Musulunci : " At Taurah ta fara da wadannan rukunnai guda goma

wadanda aka ambata a cikin Al Qur'ani a cikin wadannan ayoyi guda uku.

Wadannan su ne rukunnai guda goma da aka saukarwa Annabi Musa AS.

Abdullahi dan Abbas RTA ya ce "wadannan sune bayyanannen wahayi wanda aka

ambata a cikin Surat Aal Imran. Har wa yau, duk wasu tsare-tsare tun daga kan

Annabi Adam AS zuwa Annabi Muhammad SAW duka sun kunshi wadannan

rukunai guda goma babu inda aka goge su a kowace irin Shari'a.

A tafsirin Ibn Katheer an tuwaito daga Abdullah Bn Mas'ud RA cewa idan wani

yana son ya ga wasiyyar Annabi Muhammad SAW an danbara hatimi a jikin ta to

ya karanta wadannan ayoyi guda uku na Surat Al An'am.

Haka kuma Hakam yayi bayanin ta kamar yadda aka ruwaitodaga Ubbadah Bn

Samit cewa wata rana Annabi SAW ya yiwa sahabban shi Bayani yace " wa zai yi

mani alkawali akan wadannan ayoyi?" sai ya karanta wadannan ayoyi guda uku

na suratul An'am, daga nan sai yace " duk wanda ya cika alkawalin shi ya

tabbatar da ladar shi a wajen Allah SWT.

Ina rokon Allah SWT ya bamu ikon bin wasiyyar Annabi Muhammad SAW.

CIYARWA TA HANYAR ALLAH (SWT)

Ciyarwa ta hanyar Allah yana daga cikin halayya mai muhimmanci ta wadanda

suka yi imani na gaskiya. Allah SWT bai umarce mu ba kawai har ma ya

kwadaitar da mu ta haya mai kyau. Misali, Allah SWT yace a ciki Surat Al

Baqarah aya ta 265:

" Kamanni wadanda suke ciyarwa a dukiyoyin su domin neman yardar Allah da

kuma tabbatar da kawunan su, kamar lambu ne wanda yake a jigawa idan ruwa

ya sauka a kan shi sai ya samar da 'ya'yan itace launi biyu, idan kuma ruwa bai

sauka a kan shi ba ko da yayyafi ma ya isa. Allah yana ganin abinda kuke yi".

Yana da sauki ka yi Magana a kan ciyarwa domin Allah, amma yana bukatar

karfin hali kafin ka aiwatar da hakan. Saboda haka ciyarwa domin Allah yana

mikar da rai da halayyar mutum. Karin dadawa, ka ciyar da wani abu kalilan

wanda za ka yi da zuciya daya ya isa ya samar da lada babba a wajen Allah.

A aya ta 7cikin Suarat Al Hadeed Allah SWT ya kwadaitar damu a kan wata

hanyar da ban. Ya ce:

" ka yi imani da Allah SWT da Manzon Shi kuma ka ciyar da abinda Allah ya

maida mai tsaro".

A nan, Allah SWT yana bayyana mana cewa duk wani abu da muka mallaka wani

ya same shi kafin mu. Haka nan duk abinda muka mallaka zai kasance mallakar

wani bayan mu. Don haka, muna ajiye da ita ne na wucin-gadi ko masu rike da

amana. Don haka kada muyi wata wata wajen ciyar da abinda yake a gare mu na

wucin gadi.

Na biyu, a bayyane yake cewa sai wadanda suke da imani suke ciyarwa ta hanyar

Allah SWT za su sami gagarumar lada daga gare Shi. Muna iya yanke hukunci

wanda bai yi imani ba idan ya ciyar ba shi da lada gobe kiyama, ko da yake zai

sami sakamako a nan duiya.

A surat Al Hadeed, aya ta 10 Allah SWT ya ce :

" Wannan kai komo gare ku wajen ciyarwa saboda Allah SWT bayan duk abinda

yake sama da kasa duk na Allan ne".

Nan wata hanya ce mai ban-sha'awa wadda za ta kwadaitar da mu da shiryar da

mu mu ciyar ta hanyar Allah SWT. Misali akwai wani daga cikin mu da ya mallaki

wani bangare na sama? Hakikanin gaskiya babu. Dukkan sammai na Allah SWT

ne shi kadai. Haka nan kuma a makaman ciyar wannan hanya gaskiya duk abinda

ke a bayan kasa na Allah ne. ko da yake muna yin kuskure mu ce " wannan mota

ta ce, ko gida na ko wannan asibiti na ne. Allah SWT ya kawo kalmar sammai

yana bayyana mana cewa duka abinda yake a sammai na Allah ne kuma duk

abinda ya ke a bayan kasa na Allah ne, don haka kada mu sami wani jimami

wajen ciyarwa ta hanyar Allah SWT daga abinda yake daman can na Allah ne. Sai

Allah SWT ya gayyace mu a Surat Al Hadeed aya ta 11:

" Wa yake da ya ba Allah rance domin ya rubanya mashi kuma ya bashi lada mai

girma bayan shi?".

Me ake nufi da babbar lada 'ajarun kareem'? wannan za a fi fahimtar shi daga

wannan ayar ta Surat an Naba' aya ta 36:

" Akwai lada gare ka daga Ubangiji da Karin lada dangane ga imanin ku".

Rahamar aljannan nesa ta zarce ladar da za a bamu saboda kyawawan ayyukan

mu. A nan kari daga ladar akwai kyau daga wajen Allah SWT girman wannan

kyauta danganta ne a kan imani da niyya. Allah SWT ya banbance ta babbar lada

a bangarori da dama a cikin Al Qur'ani. Za a bamu lada domin ciyarwa don Allah

SWT dagane da imani da niyya.

Anas RA ya ruwaito cewa Annabi Muhammad SAW yace " idan mutum yana da

tafki cike da gold ba zai taba wadata ba. Wannan mutum zai so y asami wani

tafkin cike da gold. A halin gaskiya kurar kabari kadai za ta cika bakin mutum.

Bukhari.

Ubayy Bn Ka'ab RA yace wannan Hadisin an maimaita shi da yawa, mun yi

tunanin wani bangare ne na Al Qur'ni, sai da da aka saukar da Surat at Takaathur

aya ta 1-8 inda Allah SWT ya ce:

" Gasa da juna ta shagaltar da ku har sai kun ziyarci kaburra. Lallai ! za ku sani !

Har wa yau lallai za ku sani ! Lallai idan kuna sane da tabbataccen sani. Hakika za

ku ga wuta ! kuma za ku gan ta da tabbataccen gani !. A wannan rana za a

tambaye ka jin dadin da ka yi a duniya".

Dan Umar ya ruwaito cewa wani lokaci Annabi Muhammad SAW ya yiwa sahabbai

jawabi ya ce " Karanta aya 1000 ta Al Qur'ani a kowace rana" sahabbai suka ce "

wata kila wani wani zamu karanta aya 1000 na Al Qur'ani". Annabi SAW ya ce ba

za ku karanta Surat at Takaathur".

Al mazhari

Yana nufin sakon dake a wannan sura daidai yake da ayoyi dubu. Haka nan rauni

ne na mutum yayi ta tara dukiya har sai mutuwa ta riske shi. A wajibi ne wanda

yayi imani ya biya zakka wadda take 2-1/2 cikin dari na abinda mutum yake

samu. Allah SWT ya fadi zakka da salla a cikin Alqur'ani a mafi yawan lokaci. A

wata fadar sallah ma ba ta rabuwa da zakka. Khalifa Abubakar ya fahimci wannan

sosai. Ya tura runduna ga wanda su ka ki su bada zakka, duk da yake suna salla

suna azumi.

Allah SWT yace a cikin Surat al Muzzammil aya ta 20:

" Ku tsaida salla ku bada zakka ku baiwa Allah rance".

A nan Allah SWT yana shiryar damu, ba wai kawai mu biya zakka ba, mu kara

baya da kyau.

Halayen wadanda suka yi imani na gaskiya an ambace shi a wurare da daman na

Al Qur'ani mai girma. Allah SWT ya ce a cikin Surat az Zariyaat aya ta 17-19:

" Suna yin barci kadan da dare. Kafin dare a kowace rana suna neman gafarar

Allah. Kuma a cikin dukiyar su akwai rabon masakai da fakirai".

Wannan bayyanannen kaso, Allah ya sanya shi a kan zakkah a kowane lokaci 2-

1/2 kan abinda mutum ke da shi.

Allah SWT ya sake cewa a surat al Insan aya ta 8-9:

" Suna bayar da abinci ga mabukata, maraya da yan kaso, domin samun soyuwa

a wurin Allah kadai. Bamu bukatar wata lada ko godiya daga gare ku".

Wani lokaci sai mu yi tunani ko me yasa Allah SWT ya maida Annabi SAW

maraya?. Allah SWT shine mafi sani, wata kila dalili daya yana iya kasancewa

Allah SWT yana so ya gwadawa Annabi SAW yadda rayuwaar maraya take.

Wannan wani koyami ne ga wanda zai kasance rahma ga dukkan duniya.

Sahabban Annabi SAW sun sami wata irin shiriya daga Allah SWT. Misali ka tuna

aya ta 92 a Surat Aal Imran :

" Ba ka samin taqwa ta gaskiya har sai ka ciyar da abinda kafi so".

A lokacin da Abu Talha ya saurari wannan ayar, sai ya rugo wajen Annabi SAW

ya bada kambun binshi wanda ya fi kyauta. Haka nan, kuma Zaid bn Haris ya

bayar da dokin shi wanda ya fi kyauta.

Ina rokon Allah SWT ya bamu ikon bada zakka da sadaka da zuciya daya ko da

yaushe, Amin.

HALAYEN WADANDA SUKA YI IMANI

Allah SWT ya ce a surat al Jinn aya ta 14 :

" Duk wanda ya karbi Musulunci hakika ya zabi hanya madaidaiciya".

Ko bayan daukar wannan mataki na gaskiya Musulmi ba zai ce ba zai shiga

aljanna kamar yadda yahudawa da kiristoci su ke ikirari. Shiga aljanna ya

kasance ne kawai ta rahmar Allah SWT. Allah SWT ya yi bayani game da mutanen

gidan aljanna a aya ta 107 surat Aal Imran :

" Ga wadanda fuskokin su za su kasance farare, suna a cikin rahmar Allah

(aljanna) nan za su dawwama har abada".

A nan kalmar rahma an yi amfani da ita ne a maimakon aljanna yana tunatar da

mu cewa shiga aljanna sai da rahamar Allah SWT.

Allah SWT har wa yau yana shiryar da mu a cikin Al Qur'ani a kan halaye da

dama na mutane wadanda za su cancanci shiga aljanna. Wadannan halaye an

bayyana su a cikin surat Al Mu'minun da surat al Ma'arij. Za mu bi surat Al Ma'arij

aya ta 19-21.

Tun farko, Allah SWT yayi jawabi ga daukacin al'umma.

Allah SWT ya ce : " Mutane da dama basu da hakuri. Idan suka gamu da

wadansu matsaloli sai su dimauce, idan Allah ya sauya masu wannan matsi da

abu mai kyau sai su ki cika damar mutane da damar Allah".

To a nan anyi zabe daga wadannan, akwai nau'in wasu mutane na musamman da

ba su yin haka halayen shine aka yi bayanin su a surat al Ma'arij aya ta 22-25:

" Wadannan suna tsayar da sallah, wajen yin salla suna yin ta a kan lokaci cikin

nutsuwa. Na biyu suna ciyar da wani bangare na dukiyar su ga masakai da

marasa karfi".

Da ban-sha'awa mu sani Allah SWT ya tabbatar da cewa suna kyautatawa

mabukata. Allah SWT ya sake cewa wadannan masu imani suna ciyar da wani

kayyadadde lissafaffen bangare na dukiyar su ga mabukata da matalauta. Ko

kuma a ce koda yaushe suna bayar da zakka wanda aka kayyade biyu da rabi a

kowane lokaci. Sayyidina Abubakar RA ya fi kowa fahimtar wannan ayar ta tura

wata runduna su je su murkushe wadanda su ka ki su bayar da Zakka duk da

yake sun tsaida salla. An ce sallar mutum ba za ta karbu ba har sai ya bada

zakka. Shine ya sa Allah SWT ya ambace salla da zakka tare a cikin Al Qur'ani a

mafi yawan lokaci. Allah SWT ya kara shiryar da mu cewa mu bada kyauta kari a

kan bada zakka a cikin ayoyi masu yawa na Al Qur'ani. Surat al Muzzammil aya

ta 20:

" Ku tsaida salla ku bada zakka kuma ku baiwa Allah rance mai kyau".

Halaye na gaba na wadannan zababbun mutane shine yin yarda da ranar Hisabi,

ba wai a baki ba, su na sane za su kididdiga ayyukan su a ranar hisabi. Misali,

wadannan mutane su ne wadanda za a basu sakamakon su a hannun dama a

ranar hisabi, za su ce sirrin nasarar su shine surat al Haqqah aya ta 20:

" ko da yaushe mu na rayawa a ran mu za mu ga sakamakon mu".

Surat al Ma'arij aya ta 26,27,28:

" Kuma wadanda suka yi imani da ranar sakamako da wadanda suke tsoron

azabar Allah. Hakika! Azabar Allah ita ce wadda babu wanda ya tsira".

A nan, halaye na gaba na wadanda suka yi imani shine suna jin tsoron azabar

Allah. Lokacin da sahabbai suka saurari wannan ayar suka tambayi Annabi

Muhammad SAW " Ya Annabi SAW, kai ma kana jin tsoron azabar Allah? Sai ya

amsa "e! ni ma ina jin tsoron azabar Allah tunda babu wanda zai dauki kan shi ya

fi karfin azabar Allah".

Har wa yau, babu wani musulmi da zai bugi gaba yayi alfahari a kan ayyukan shi

na Musulunci sai dai yayi kuma ya ji tsoron azabar Allah. A gaba, Allah SWT ya

ce, suratul Ma'arij aya ta 29-31:

Halaye na gaba na wadannan mutane shine : " Suna kamewa daga sha'awa sai

dai ga matan su da wadanda aka kamo a wajen yaki. Basu da wani laifi a nanj.

Wadannan iyakoki wanda Allah SWT ya sanya, duk wanda ya zarce wannan ya

kasance ya zarce kan iyaka.

Nan duk wani yanayi da mutum bai bi wajen biyawa kan shi bukata idan dai ba

wannan ba ne kwata-kwata baya kan hanya, Allah SWT ya haramta shi.

Allah SWT ya ce a suratul Ma'arij aya ta 32:

Wani halayen wadannan mutanen shine : " Suna tsayar da Magana da alkawalin

su".

Cin amana da karya alkawali manyan zunubai ne.

"Annabi Muhammad SAW ya ce alkawalin wani bashi ne dole ka biya"

Suratul Ma'arij aya ta 33:

" Suna tsayuwa kyam a kan abinda suka shaida".

Wannan yana nufin sun rike a ran su alkawalin da suka yi da Allah SWT yayi da

suka karbi Musulunci :

Alma'arij aya ta 34

" Wanda suke tsare sallar su da kyau".

A nan Allah SWT ya ce wadannan mutane suna da cikakkiyar nutsuwa wajen

sallar su kuma suna yin ta da farillai da sunna.

Yana da ban-sha'awa Allah SWT ya fara wannan halaye da yin sallah kuma ya

rufe da ita. Wannan ya zamana a bayyane sallah tafi muhimmanci a wurin Allah

SWT. Shine ya sa abinda za a fara tambayar kowa shine salla a ranar hisabi. Al

Ma'arij aya ta 35:

"Allah yana yanke hukunci cewa mutane wadanda suke da wadannan halaye

wanda aka ambata a sama za a girmama su a lambun aljanna"

Wannan ya gwada akwai abubuwa da mutum zai yi ya cancanci shiga aljanna. A

gakiya, idan wani ya aikata abu daya daga cikin wadannan abubuwa yadda ya

kamata duk sauran ma za a iya samara da su a cikin sauki. Idan mutum ya aikata

abubuwan da aka zayyana zai shiga aljanna da rahmar Allah SWT. Allah SWT ka

bamu ikon mu bi wadannan da aka ambata duka cikakke.

Kyauta mafi muhimmanci da Allah SWT ya yiwa mutane shine samar da shiriya

wadda za ta fitar da mu kowane irin duhu zuwa ga haske. Allah SWT ya ce a

suratul Ahzab aya ta 43-44:

" Allah ya saukar da rahamar shi gare ka da kuma Mala'ikun shi domin ya fito da

ku daga tsananin duhu zuwa ga haske. Shi mai rahma ne ko yaushe ga masu

imani. Za a tarye su da sallama idan suka sadu da Allah. Allah ya tanadar masu

lada mai girma".

Allah SWT ya ce da Annabi Muhammad SAW, har wa-yau, aya ta 47:

" Ka yi bushara ga masu imani. Za su sami babbar kyauta daga wajen Allah".

Allah SWT ka sanya mu cikin wadanda za su sami babbar kyauta a wajen Ka,

Amin.

KIBLAH

Me 'Kibla' ta ke nufi? Wajen da ake duba a yi salla

Allah SWT yace a surat al Baqarah aya ta 115:

" Na Allah ne gabas da yamma, duk inda ka juya kan ka ko fuskar ka akwai

fuskar Allah! Hakika, Allah ya isa ga dukkan bukatun ababen halittar sa".

Yana nuna cewa babu wani kebabben bangare wajen bautar Allah SWT daya.

Idan babu wani wuri da aka tsaida Magana ta hakika kowa zai dubi bangaren a

kowane lokaci.

Menene dubarar tsaida Kibla? Mun sani azumi da tuna Allah ayyuka ne na mutum

shi kadai. Salla da aikin Hajji ana yin su ne a taron jama'a. wajen tsaida Kibla,

anyi niyyar a gwada a koyar da da'a da ka'idojin zaman tare. Muhimmiyar ka'ida

da samun hadin kai da sadaukar da kan al'umma shine samun abu daya na inda

suka dosa, wanda ya wuce wani launin fata, kabila, bangare, harshe, da kuma

kasar da ka fito. Allah SWT ya zabi KIBLA domin ya warware wadannan matsaloli

tunda wasu zabi za su kawo rarrabuwar kai maimaikon kawo hadin kan kasa.

Musulunci addini ne na dukkana Annabawa, saboda haka daya bangare daya na

bauta ya gwada kadaitakar koyarwar dukkan Annabawa.

Kasancewar KIBLA daya ga dukkan mutanen duniya ya kawo hadin kai, abu na

bai-daya a tsakanin su. Wannan umarni yana da sauki a bishi ga duk mazaje da

mata, masu ilmi da wadanda ba su da ilmi, na kauye ko na birni, masu arziki da

talakawa. Wannan ya nuna sauki da kyawun Musulunci.

Ka sani fa idan idan aka bar mutane su zartar da an sami gagarumar rashin

jituwa, amma Allah SWT cikin rahamar sa ya zartar da wannan har abada domin

ya taimaka a sami hadin kai kuma ya kawo abu na bai-daya ga kasashen

Musulmi. Lokacin da Adam AS ya zo duniya, fandeshan na dakin Allah Mala'iku

suka yi. Kiblar Adam da mutanen shi ita ce wannan kibla. Allah SWT ya ce a cikin

surat Aal Imran aya ta 36:

" Hakika daki na bauta na farko da aka sanyawa al'umma shine na Bakka

(Makka) ciki da albarka da shiryuwa ga daukacin al'umomi (mutane da aljannu) ".

kowa yana bin wannan kibla ne har lokacin Annabi Nuhu AS, rowan dufana ya

rugurguza a zamanin Annabi AS. Daga baya, Ibrahim da Isma'il AS suka sake

gina ta a bisa umarnin Allah SWT da shiryarwar shi. Wannan kuma ita ce KIBLAR

su tare da mabiyan su. Daga baya kuma aka sanya AL QUDS ga wadansu

Annabawa daga Banu Isra'ila. Wadannan Annabawa idan suna yin salla a kuds

sun kasance suna dubar inda kuds da dakin Allah SWT suna daidaita gaban su.

Har wa-yau, an karbo daga Kurtubi, lokaci da aka sanya sallah farilla ga Annabi

Muhammad SAW da mabiyan shi. Da farko KIBLAR shi ta kasance kamar ta kakan

shi Ibrahim AS. Bayan Hijira zuwa Madina, kuma kamar yadda wasu malamai

suka ce kafin Hijira zuwa Madina Allah SWT ya umarce shi ya dubi Kuds. Annabi

Muhammad SAW ya kasance yana tsayuwa tsakanin Al Hajar Aswad da Rukn Al

Yamani domin duka dakin Allah da Kuds su zamana a gaban shi. Kamar yadda

aka sami Hadisi a Bukhari, Annabi Muhammad SAW ya yi salla a Madina yana

dubar Kuds har tsawon watanni goma sha shida ko sha bakwai. Manzo SAW ya

mika wuya kwata-kwata ga umarni Allah SWT. Sannan sai yayi fata Kiblar shi

zama daya da wadda ta kasance ta Adam AS da Ibrahim AS. Allah SWT yana cika

fatan zababbun mutanen Shi. Annabi Muhammad SAW yana da cikakken fata

wannan guri nashi zai cika, ya kasance yana jiran wahyi yana ta dubar sama sai

Allah SWT ya ce a cikin Surat al Baqarah aya ta 144:

" Hakika mun ga fuskar ka tana dubar sama, hakika zamu juya Kibla ga abinda

ya fi soyuwa a gare ka. To ka juya fuskar ka ga wajen Al masjid Al haram a

Makka".

A nan wajen Allah SWT ya cika gurin Annabi Muhammad SAW. Ka rike fa kalamar

'Shatra' na nufin mutanen da suke yin salla a wasu kasashe su yi bakin kokarin

su su dubi wajen wannan masallaci. Ba wai sai sun daidaita wa daida ba. Amma

kuma wadanda suke ganin dakin Allah dole su duba daidai shi idan za su yi salla.

Tun farkon da yahudawan Madina suka samu cewa Kiblar Musulmi ita ce

masallacin al Haram ba Kuds ba sai suka maida abin barkwanci suna yi masu

dariya. Amma kuma hankalin su ya tashi da wannan sauyi. Amma matukar

Musulmi suna amfani da Kiblar da Yahudawa suke amfani da ita Musulmi sun

sami karbuwa a hannun yahudawa. Amma yanzu an rabu, Kiblar tana nufin

Musulmi sun rarraba, wasu alumma ne da ban. A nan sai yahudawa suka zafafa

adawar su ga Musulmi kuma sun dauke su makiya. Allah SWT ya ce a cikin

Baqarah aya ta 177 :

" Juyar da fuskar ku gabas ko yamma ba shi bane tsoron Allah. Tsoron Allah na

gaskiya shine mika wuya ga al'amarin Allah".

Halayen masallacin Kuds da masallacin Baitul Haram ba wani abu bane illa

martaba da girma da Allah SWT ya basu.

Ko da a cikin Annabawa, Allah SWT ya maida wasu sun dara wasu ta hanyoyi da

dama. Allah SWT ya ce a cikin Surat al Baqarah aya ta 253:

" Wadansu manzanni ! mun fifita wasunsu a kan wadansu ".

A nan wadannan guraren bauta ba su da wani matsayi banda Allah SWT ya sanya

sun zarce wadan su. Allah SWT ya sake cewa a suratul Baqarah aya ta 115:

" Na Allah ne gabas da yamma duk inda ya juya akwai fuskar Allah. Hakika Allah

ya isa ga bukatar ababen halittar shi".

Saboda da haka ba wani waje bane amma gwada da mika wuya ga al'ummar

Allah SWT shine mafi muhimmanci da bin Kibla.

Wanann sauyin Kibla ya dada fiddowa a bayyane masallacin Kuds da masallacin

Kuds da masallacin Baitul Haram ba wasu irin gumaka bane, amma dalili na

hakika shine mika wuya ga al'amurran Allah SWT. Al'amurran Allah SWT za su

kasance kai tsaye ga masallacin Kuds da masallacin Baitul Haram, mika wuya ga

bin umarni da cikakkiyar zuciya wannan dole.

Kuma akwai wani amfani sauya Al Kibla shine a tsame munafukai da Musulmi na

hakika. Allah SWT yace cikin suratul Baqarah, aya ta 143 :

" Mun maida Kibla wanda kuka kasance kuna bi, domin kawai a jarrabai wadanda

suke bin Annabi Muhammad SAW da wadanda suka juya baya".

Kamar yadda ya zo a Hadisi a cikin Musnad Ahmad wanda aka karbo daga A'isha

RA, cewa Annabi Muhammad yace " Mabiya littafi suna bakin ciki da Musulmi a

kan dalilai guda uku.

Na farko: Allah SWT ya tsaida rana ta ibada kowane sati ga al'umma da suka

wuce, asabar ga yahudawa, ranar lahadi ga kiristoci, sai kuma juma'a an zabe ta

ga Musulmi. Abu na biyu, wannnan sauyin Al Kibla. Abu na uku, shine cewa Amin

da ake yi bayan liman. Mabiya littafi basu sami wadannan abubuwa ba.

Ka rike wani lokaci Al Qur'ani yana shafe Sunnah, idan kuma ba a shafe ta ba

hukuncin daya dana Al Qur'ni. A misali, da farko Kibla ba a ambace ta ba a Al

Qur'ani Musulmi suna bin Sunnah. Sai kuma Al Qur'ani aka sauya ta amma Al

Qur'ani ya tabbatar da salloli da aka yi ta bin Sunnah ba a yi asarar su ba.

Kamar yadda ya zo a Hadisin Bukhari da Muslim, sauyin Kibla ya faru ne yayin da

Annabi Muhammad SAW yake yin sallar Asr. Ko da yake wadansu ruwayoyin sun

ce Zuhr (kamar yadda ya zo a IBN KATHEER)

Wadansu sahabban sun kamala sallar su da Annabi Muhammad SAW, sai suka

gani cewa wadansu 'yan uwan su dake makwabtakan su suna yi sallar suna dubar

Al Kuds, sai sahabban daga murya suka ce masu " Mun yi salla da Annabi SAW

muna dubar Baitullah sai suka juya yayin da suke yin salla. Ba tare da wani jinkiri

ko tambayoyi da sauransu ba. Wannan abinda ya afku ya fiddo cewa a dalilin

mutum a matsayin shaida ya isa a wadasu abubuwa.

Sauyin Al Qur'ani yaje Quba a wannan rana. Kamar yadda aka ce a Bukhari da

Muslim mutanen Quba' ma sun juya Al Kibla wajen salla a lokacin da suka sami

sanarwa daga bakin mutum daya. Wananna ya gwada yadda mutuntawa da

aminci da amana da sahabban Annabi AS suke yi.

Ya zo a Hadisin Bukhari a ruwayar Ibn Azib lokacin da aka sauya Al Kibla zuwa

masallacin Baitil Haram, mutane suka tambayi Annabi SAW game da Musulmi

wadanda suka mutum kuma suna bin a Al Kibla. Allah SWT ya amsa wannan a

aya ta gaba ta cewa sallar su ba zata kasance asara ba Allah ya karbe ta. Suratul

Baqarah aya ta 143:

" Allah ba zai taba maida imanin ku (sallar ku) ta kasance asara".

Yana da ban-sha'awa mu sani cewa imani an amfani da shi a maimakon salla a

wannan ayar. A nan babu imani matukar babu tsaida salla. A wata fadar salla ita

ce abinda yake gwada imanin mutum.

Ya Allah SWT ka bamu ikon yin salla koda yaushe domin mu kara imanin mu ya

Allah SWT da hada kan Musulmin duniya wadanda suke bin Al Kibla daya, Amin.

Hooray! Your file is uploaded and ready to be published.

Saved successfully!

Ooh no, something went wrong!