Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
You also want an ePaper? Increase the reach of your titles
YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.
HAROLD CAMPING/FAMILY RADIO

Ɗaukaka

Ga Allah
Ɗaukaka Ga Allah

(Hausa: To God Be The Glory)

Harold Camping

Family Stations, Inc.

Oakland, California, 94621 U.S.A.

Internet: www.familyradio.com

06-22-09

ii
Ɗaukaka Ga Allah

Abinda Ke Ciki

GABATARWA.........................................................................................v

Sura Ta Ɗaya: Abin mamaki da ya shafi sanin gaskiya.......................... 1

Sura ta Biyu: Rashin sahihancin fahimtar Shirin Shari’a irin ta fuskar

al’ada ...................................................................................... 7

Ina jinƙan Allah? ..................................................................... 10

Ƙaunar mutum ga mutum....................................................... 13

Sura Ta Uku: Allah Alƙalin dukan duniya ........................................... 22

Tsarin shari’a Na Allah ........................................................... 25

Menene jahannama? ............................................................... 27

Ƙorama Ta Wuta..................................................................... 27

Mai Arziki da la"azaru............................................................. 31

Sura Ta Huɗu: Yaushe ne Kristi ya mutu? ........................................... 36

Ya ƙare................................................................................... 41

Gafara mai ban al"ajibi ........................................................... 43

Sura ta Biyar:Shirin Allah na hukunci ................................................. 44

Waɗanda ba zaɓɓaɓu ba da suka mutu kafin ranar shari’a...... 48

Zaɓɓaɓu waɗanda ba a cece su ba tukuna .............................. 49

Waɗanda aka ceta kuma yanzu haka suna nan Zaune a wannan

duniyar .................................................................................. 49

Waɗanda ba zaɓɓaɓu ba da suke da rai har ranar 21 ga watan

Mayu 2011............................................................................. 50

Tashin mattatun da ba su da ceto........................................... 50

Masu bi suna Shari’anta Marasa Ceto

Yaƙin Armageddon................................................................. 54

Takaitawa............................................................................... 57

Kowanne ido zai ganshi.......................................................... 61

Sura Ta Shida: Masarautar da aka ƙirƙiro domin nuna ɗaukaka

da hikimar Kristi ................................................................................ 65

iii
Zaɓɓaɓu: Mutane miliyan 200 .................................................70

Miliyoyin mutane da basu da ceto sun mutu ba tare da sanin

fushin Allah ba........................................................................72

Sura Ta Bakwai: Ceto........................................................................ 80

Jerin Ayoyi da shafi .......................................................................... 84

iv
GABATARWA

Wannan litafin ƙarin bayani ne kan littafin nan Mun Kusa Kai Ga

Ƙarshe. A cikin littafin nan Mun Kusa Kai Ga Ƙarshe, mun iya ƙoƙari,

tare da taimakon Allah, nuna cewa Littafi Mai-Tsarki ya koyar da

sahihancin cewa farkon ranar shari’a wanda ya zo daidai da ranar

fyaucewa wato ranar 21 ga Mayu 2011. Allah ya bayar da wannan

bayanin mai ban mamaki gare mu kamar yadda ya alkawarta Allah ya

faɗa a cikin Littafin Mai-Wa’azi sura 8:5-6 cewa:

‘‘...Zuciyar mai hikima kuwa ta kan gane kwanakin da shari’a

kuma a kowane dalili akwai lokaci da shari’a...”

Allah ya ɓoye wannan bayanin lokaci da shirin Allah na shari’a

daga dukan ’yan adam har da Ikklisiya dukan tsawon zamanin Ikklisiya.

Bugu da ƙari Allah ya bar bayani a cikin Littafi Mai-Tsarki wanda ya

koyar da cewa Kristi zai dawo kamar ɓarawo da dare. Wannan ya faru ne

domin Ikkilisiya ta maida hankali a kan kai bishara a cikin duniya. (duba

Ayyukan Manzanni 1:6-8).

Da yake bayani game da lokaci yana da alaƙa da shirin shari’ar

Allah. An yiwa shirin shari’ar Allah munmunar fahimta cikin shekaru

1,955 na zamanin Ikklisiya. Duk da haka nufin Allah ne cikin wannan

lokaci na ƙarshen duniya, masu bi na gaskiya zasu faɗakar da duniya

game da tsarin lokaci na Allah da kuma niyar sa ta hallaka duniya. Ya ba

masu bi na gaskiya cikakken bayani game da lokacin ƙarshen duniya

domin dangantakar da ke tsakanin jadawalin Allah da kuma abin

mamaki da zai faru da kuma shari’a,. Ya kuma ba masu bi na gaskiya

cikakken bayani saboda kamar yadda Nuhu da Yunana suka yi, za su

gargaɗi duniya game da hukunci mai zuwa.

Wannan wahayi na ƙarshen zamani da shari’a, shaida ce ta

ƙaunar Allah da jinƙansa da bashi misaltuwa. Mutane nawa ne a garin

Nineva suka yi kuka suka roƙi Allah domin jinƙai inda annabi Yunana

yace kawai wata rana Allah na Isra’ila zai hallaka su sabili da muguntar

su? Mutane nawa ne a cikin Ikklisiya suke kuka ga Allah domin jinƙansa

sabili da an koya masu cewa wata rana Kristi zai dawo kamar ɓarawo da

dare? A hakikanin gaskiya koyaswar cewa Kristi zai dawo kamar ɓarawo

da dare, koyaswa ce marar tada hankali. Zamanin Ikklisiya ya fara ne

shekaru 1,900 da suka wuce, kuma Kristi bai zo domin ya kawo ƙarshen

duniya ba. Saboda haka zamu yi tunani cewa ba lallai zai zo a

zamaninmu ba. Ko suna sane da shi ko babu, mutanen cikin Ikklisiyai

kimanin mutane biliyan biyu, sun shiga ƙaunar wannan duniyar. Sai dai

domin abubuwa kamar yaƙi da aloba, duniyar nan wurin zama ne mai

daɗi. A nan ne ’yan adam zasu sami abokai da farin ciki da aiki da jin

daɗi da abin dogaro ga kai, da dai sauran su. Duniyar nan ba cikakka ba

ce, amma babu shakka mutane zasu gwammace su zauna a cikin ta da

v
su mutu su rasa dukan abinda ke cikinta. Saboda ba za su so suyi

tunanin cewa wannan duniya zata ƙare ba.

Saboda haka, idan ba masu bi na gaskiya da Allah ya sanar da

ainihin lokacin da duniya zata ƙare ba, da kuma masu bi da suka

gaskanta da dukan zuciyarsu cewa gaskiya ne kuma daidai ne, sauran

mutanen duniya zasu dage a kan cewa ko dai Kristi zai zo kamar ɓarawo

da dare ko kuma duniya bazata ƙare ba mundin ɗan adam yana warware

wasu matsalolin ɗumamar yanayi da sauransu.

Waɗanda zasu karanta wannan littafi kuma su yaba kawai sune

waɗanda suka dogara ga Allah kuma suka yi la’akari da cewa babbar

albarka da jinƙan Allah ne da yake bada wannan bayani ga waɗanda suka

dogara Littafi Mai-Tsarki da gaskiya. Saboda haka muna kyakkyawan

bada shawara ga mai karanta wannan littafi da ya karanta Mun Kusa Kai

Ga Ƙarshe! Ana iya samun waɗannan littatafai duka kyauta daga FAMILY

RADIO mai bukata zai iya rubutowa zuwa ga FAMILY RADIO OAKLAND

CALIFONIA,94621,USA. ko kuma ya kira wannan lamba 1-9800-543-

1495 kyauta. Za a kuma iya samunsu a shafin yanan gizo a:

www.familyradio.com

vi
SURA TA ƊAYA

Abu Mai Sarƙaƙiya Game Da Gaskiya

Tunanin mutum da abinda ya yi imani a kai ya ta’alaƙa kan

abinda ya ɗauka a matsayin gaskiya da kuma madogara. Ya yiwu an

gabatar mashi da waɗannan ra’ayoyin a lokutan baya, ko kuma waɗansu

ra’ayoyi ne da aka gabatar da su ayau. Idan aka sami sababbin ra’ayoyi,

za a tankaɗe, a auna bisa ra’ayoyin da ya ɗauka a matsayin gaskiya ya

kuma amince da su.

Hakika, lamarin ke nan yayin da ake batun fahimta irin ta addini.

Da zaran mun koyi waɗansu ra’ayoyi na addini, muka kuma amince da

su, yakan zama da wuya a sake karɓar wani ra’ayi a matsayin gaskiya,

yana da wuya mu karɓi wani ra’ayi a matsayin gaskiya da ya saɓawa

ra’ayoyin da muka riga muka yi imani da su a matsayin gaskiya.

Ta haka wanda ya sami horaswa ta Katolika zai ci gaba da rayuwa

a matsayain ɗan ikilisiyar Kotolika, Baftis kuma Baftis, haka ma mai

addinin Buda, da dai sauransu. Dalili ke nan da ya sa yawancin waɗanda

suka yi zurfi a cikin ikilisiya ba zasu yarda da cewa Allah ya gama da

Ikkilisiyoyi ba, ya kuma umurci mutane su fita daga ikkilisiyai, kana an

ɗora shaiɗan ya yi mulki a can, kuma Ruhu Mai-Tsarki ya watsar da

ikilisiyoyi saboda haka babu wanda yake ƙarƙashin ikon ikkilisiya da zai

tsira.

An yita yiwa waɗannan mutanen koyaswa, kuma sun amince da

wannan a matsayin gaskiya da cewa, ikilisiyoyin su, na Allah ne kuma

Allah ne yake mulki a bisan ta. Saboda haka ƙofofin jahannama ba za su

rinjayeta ba. Wannan fahimta, ta sami wurin zama daram a cikin tunanin

su, a matsayin gaskiya ba ja. Saboda haka, duk wata fahimta da za a

gabatar masu daga Littafi Mai-Tsarki sai an auna ta bisa ga fahimtarsu

da kuma tauhidi, wanda suka yi imani da cewa ita ce sahihiyar gaskiya.

Idan ka gabatar masu da sababin ra’ayoyi daga Littafi Mai-Tsarki

da ke koyarwa cewa mun zo ƙarshen zamani ikklisiya, ba za su yi

nazarin batun da zuciya ɗaya ba. Komi zurfin fafatun da suke yi cewa a

shirye suke su karɓi gaskiyar Littafi Mai-Tsarki, amma a zahiri, basu iya

zuwa ga sanin wannan sabuwar gaskiyar ba. Dalili ke nan da ya sa a

zamaninmu, mutane ƙalilan ne suke barin ikilisiyoyi bisa ga biyayya da

umurni da Allah ya bayar da a guje masu.

Wannan lamarin ya kasance wani abu dake da sarƙaƙiyar gaske a

zamanin mu , domin waɗansu muhimman dalilai guda uku kamar haka:

1. Muna zama a cikin duniya da take dab da ƙarshe. Kuma a

ƙarshen zamani Allah ya shirya ya ɗauke hatimin da ya sanya

kan bayanai masu yawa game da ƙarshen zamani da ke cikin

Littafi Mai-Tsarki. Saboda haka mu sa rai cewa za a sake

1
nazarin muhimman bayanai daga Littafi Mai-Tsarki da muke

tsammani gaskiya ne .

2. Muna cikin zamani na ƙarshe da ake kira zamanin ƙunci mai-

tsanani, lokacin da Allah yake gwada waɗanda suke kitan

kansu masu bi na gaskiya. Halin mai-bi na gaskiya shine

yana son ya zama mai gaskiya da biyayya da kowane abu

dake cikin Littafi Mai-Ttsarki.

3. Ta wajen waɗannan jarrabawar, Allah zai raba Alkama wato

masu bi na gaskiya daga zawan, waɗanda suka amince da

cewa su masu bi na gaskiya ne, amma ba su sami ceto ba.

Lokacin jarrabawa ya ƙunshi, dukan kwanaki 8,400, (shekaru 23)

lokacin ƙunci mai-tsanani wanda zai fara daga 21 ga watan Mayu

shekata ta 1988, wanda ya ci gaba har zuwa 21 ga Mayu shekara ta

2011. A wannan ranar, ranar hukunci zata fara, ta kuma ci gaba har

21ga Octoba shekata ta 2011.

Littafi Mai-Tsarki, littafin ruhaniya ne, hanya ɗaya rak kuma da

mutum zai iya gane gaskiyar da ke cikin Littafi Mai-Tsarki ita ce idan

Allah ya buɗe idanunsa na ruhaniya. Saboda haka, da yake mun amince

da waɗansu karkatattun ra’ayoyi a matsayin gaskiya, waɗanda ba zamu

iya rabuwa da su ba ta ƙashin kanmu, tilas mu koma ga Allah, mu roƙi

jinƙan sa, muna addu’a ya buɗe zuciyar mu ya raba mu da tunani da

ra’ayoyin da suka saɓawa Maganarsa.

Matsalarmu ta rashin iya sallama ra’ayoyin da Littafi Mai-Tsarki

ya nuna mana da cewa ba gaskiya bane yana da girma zamanin nan

dangane da wata gaskiya mai muhimmanci, watau, lokacin bayani a

Littafi Mai-Tsarki. Gaskiyar ita ce, da dama a cikinmu, muna nazarin

matsalar lokaci ta wajen yin misali da bayanan Littafi-Mai-Tsarki.

Littafin nan mai shafi 70, “Mun Kusa Kai Ga Ƙarshe”, littafi ne da

aka rubuta bayan an shafe shekara 50 ana binciken Littafi Mai-Tsarki

dangane da tarihin zamani. Bugu da ƙari, an ɗauki dubban awoyi ana

tattaunawa akan abinda ke cikin littafin a shirin “Family Radio” Dandalin

Tattaunawa. A ƙarshen dukan wannan binciken, gaskiyar ita ce, Kristi ba

zai zo kamar barawo da dare ba, amma, zai zo a rana, da wata, da

shekaran da Allah ya bayyana wa masu bi na gaskiya a cikin Littafi Mai-

Tsarki.

Yanzu, da ace an bada wannan littafin “Mun Kusa Kai Ga Ƙarshe”

ga wani ɗan Ikklisiya mai- aminci wanda ya sami koyaswa a kan cewa

Kristi zai dawo kamar ɓarawo da dare. Ya yarda ya karanta wannan

littafi, ya yi adalci ya bada hukunci na gaskiya. Bayan ya karanta shafi

kaɗan, sai ya tarar bai koyar da cewa Kristi zai zo kamar ɓarawo da dare

ba. Nan da nan zai shiga kariya, zai yi tunani cewa, ‘‘Wannan littafi yana

saɓo. Na san ayoyi da yawa da suke koyar da cewa ba wanda ya san

ranar da Kristi zai dawo. Zai zama kuskure a gareni in karanta wannan

2
littafin saɓo’’ kuma a cikin zuciyarsa, yana ganin hukumcin da ya yanke

a kan littafin nan daidai ne.

Abinda bai fahimta ba kuma ba zai fahimta ba shine kwaɗon da

ya kulle zuciyarsa, shine, tun zamanin Ikkilisiya, abin da Allah ya yarda

duk mai bi na gaskiya ya sani shi ne cewa, Kristi zai dawo kamar ɓarawo

da dare. Tuni a cikin Ayukan Manzani sura ɗaya manzani sun yi

tambaya, kamar yadda zamu karanta a aya shidda.

Sufa, da suka taru, suka tambaye shi, suka ce, Ubangiji, a

wannan lokaci ne kake mayar wa Isra’ila da mulki?

Suna son su san lokacin da mulkin Allah zai cika. Yesu ya amsa

masu a cikin aya 7 da 8.

Ya ce masu, Ba naku bane da zaku san zamanai da lokatai

waɗanda Uba ya sanya a cikin nasa hukunci. Amma, za ku karɓi

iko lokacinda Ruhu Mai-Tsarki ya zo bisanku, zaku zama shaidu

kuma cikin Urushalima da cikin dukan Yahudiya da Samariya har

kuma iyakar duniya.

Watau, akwai aiki da za a yi, aikin kai bishara ga dukan duniya.

Aikin da aka ba Ikklisiya ke nan a zamanin Ikklisiya, bai kamata kuma su

dami kansu a kan ƙarshen zamani ba.

Saboda haka, Allah ya bayyana a fili cewa abinda za a sani kawai

a zamanin Ikklisiya shine zai dawo kamar barawo da dare. Ba wanda ya

san rana ko sa’a da zai dawo. An shafe shekaru 1,900 a zamanin

Ikklisiya ba tare da an san wani abu game da lokacin dawowarsa ba.

Amma ɗan Allah na gaskiya, zai ci gaba da karanta Littafi Mai-

Tsarki kuma a kowanne lokaci yana son ya san gaskiyar Maganar Allah.

Lokacin da ya tarar a cikin Ezekiel 3:17 da Ezekiel 33, da cewa shi mai-

tsaro ne wanda tilas ya faɗakar da duniya game da lokacin dawowar

Kristi. Daga nan kuma bayani lokacin zai fara bayyana, faro daga bayanin

game da halittan duniya a 11,013 BC. A hankali za a fara gane tarihin

duniya, zai fara fahimtar muhimmancin bayanin lokaci a cikin Littafi

Mai-Tsarki.

Babu shakka wannan hanya ce da Allah ya ke taimakawa mutane

da yawa su gwada kansu, su ga ko suna bauta wa Allahn Ikklisiyarsu, ko

fastonsu, ko koyarwarsu ko wani abu dabam da Allah na Littafi Mai-

Tsarki. Wannan ya jadada cewa dukan mu mun dogara ne da bisharar

Ruhu Mai-Tsarki domin sanin gaskiya. Zai zama da ban sha’awa idan

muka ƙasƙantar da kanmu muka yi addu’a, muka amince da cewa bisa

ga iyawarmu da hikimarmu, bamu san komai ba. Za mu iya roƙon

Ubangiji ya buɗe idanunmu zuwa ga sanin gaskiya.

Akwai shirin ƙarin gawaji mai-girma da Allah ya sa a cikin Littafi

Mai- Tsarki wanda yake faruwa cikin waɗannan shekaru 23 (kwanaki

3
8,400) na kunci mai-tsanani. Wannan yana da nasaba ne da hisabi na

Allah.

Gaba dayan lokacin ikkilishiya za a iya takaita fahimtar adalcin

Allah da kuma hukumcinsa kan masu mugunta a duk zamanin Ikklisiya,

da cewa, a rana ta ƙarshe Kristi zai zo ya zauna akan dakalin shari’a.

Duk miyagu da suka mutu, zasu zo tare da waɗanda suna raye, domin

Kristi ya shiryanta su, ɗaya bayan ɗaya. Za’a same su da laifin aikata

laifufuka da dama, a kuma yanke masu hukuncin zuwa wurin da ake kira

jahanama, inda za’a yi masu azaba har abada.

A gaskiya wannan shine tunani da ke zukatan mutane yawancin

mutane a duniya waɗanda suke da wata dogara ga Littafi Mai-Tsarki.

Gaskiya ne ko suna cikin Ikklisiya ko kuma sun fice daga Ikkilisya domin

sun gane cewa zamanin Ikklisiya ya ƙare. Abinda yawancin Ikkilisiyai

suka fahimta ke nan a dukan zamanin Ikkilisiya. Saboda haka waɗannan

ƙaunatattun mutanen sun yi imani da cewa zasu iya nazarin ayoyin Littafi

Mai-Tsarki, da yadda yake da nasaba da hukunci su kai ga sanin gaskiya

ba tare da son zuciya ba. Sai dai, idan ba tare da Ruhu Mai-Tsarki ya

kwance allon zuciyarsu ba, ba za su kai ga sanin gaskiya ba.

Amma a wannan lokaci muna dab da ƙarshen zamani, kuma Allah

ya ƙara yin muhimman bayanai game da gaskiyar zamanin Ikklisiya da

kuma jaddawalin ƙarshen zamani. Ya kuma bada waɗansu sababbin

bayanai game da tsarin hukunci. Hakika, za mu gane cewa al’adan nan

ta ganin Kristi a matsayin Alkali a ranar ƙarshe, da cewa zai aika da

miyagu zuwa gidan wuta inda fushin Allah zai dauwama a kansu har

abada, bai nuna ainihin gaskiyar koyaswar Littafi Mai-Tsarki game da

tsarin shari’ar Allah ba.

Ya kamata kuma a bayyana wata matsala guda ɗaya, yayin da

muke ƙoƙarin ganin gaskiyar Littafi Mai-Tsarki. Nufin Allah ne ya bari sai

dab da ƙarshen duniya kafin ya yi bayani mai-yawa game da jaddawalin

da shirin tsarin hukucin Allah. Saboda haka Allah ya rubuta Littafi Mai-

Tsarki ta hanyar da zai kasance da ayoyi masu wuyar ganewa.

Ɗaya daga cikin hanyoyin da Allah ya yi amfani da su domin ya

zama da wuya a gane gaskiya shine, ya rubuta ayoyin da kalaman da

suke da ma’ana biyu dabam dabam da suka saɓawa juna, ra’ayi da yake

daidai da kuma wanda ba daidai ba. Misali Allah ya rubuta a cikin

Timotawus ta daya 3:15 “... Ikklisiyar Allah mai rai ke nan, jigon gaskiya

da ƙarfinta”. Bisa ga kalaman wannan shaɗarar, daidai ne a fahimce

wannan aya da cewa Ikklisiya ita ce jigo da kuma tushen gaskiya. Yadda

Ikklisiyar katolika da sababbin Ikklisiyai suke koyar da wannan ayar ke

nan.

Duk da haka, daidai ne a fahimci cewa, wannan ayar tana koyar

da cewa, Allah mai-rai shine jigo da tushen gaskiya. Allah ya tsara

wannan ayar domin ta zama tarko. Zamu iya sanin kowanne daga cikin

biyun ne daidai ta wajen bin dokokin Allah da kuma binciken Littafin

Mai-Tsarki a hankali da gwada aya da aya. Idan Ikklisiya ce jigon da

4
kuma tushen gaskiya na Littafi Mai-Tsarki, kowacce majami’a tana da

damar ruhaniya ta koyarwa, idan ya yiwu kuma, su gyara duk abin da

wata aya a cikin Littafi Mai-Tsarki take koyarwa, domin Ikklisiya ce jigon

gaskiya. A ɓangare ɗaya kuma, idan Allah shine jigo da kuma tushen

gaskiya, hanya guda ɗaya da za mu gane abinda ake koyawa a cikin ayar

da take da wuya shine, ta wajen binciken Littafi Mai-Tsarki a hankali tare

da yin addu’a ga Allah domin ya bayyana gaskiyar ta wurin Maganar sa,

Littafi Mai-Tsarki. Babu shakka gaskiyar koyarwar wannan ayar ke nan.

Haka kuma, Allah ya ɓoye gaskiya da dama a cikin Littafi Mai-

Tsarki da ke da dangantaka da shirin hukuncin Allah. Ayoyi da dama

suna koyaswa a fili kuma daidai, abinda aka saba koyarwa bisa ga al’ada

cewa, a ƙarshen duniya, Allah zai tashi dukan waɗanda suka mutu ba

tare da zama zaɓaɓɓu ba, daga mattatu domin su bayyana a gaban

shari’ar Kristi. Za a same su da laifi a kuma yanke masu hukunci maitsanani,

su kuma sha azaba can gaba a wani wurin da ake kira

jahannama.

Za a kuma iya fahimtar waɗannan ayoyin da kyau a kan cewa

suna koyarwar da ta amince da koyaswar cewa za a shafe duniya baki

ɗaya tare da dukan waɗanda ba zaɓaɓɓu ba da basu da ceto a ranar 21

ga watan Octoba shekara ta 2011.

Misali, Litttafi Mai-Tsarki, ya yi Magana kan “Madauwamiyar hallaka” ko

‘‘ƙorama ta wuta marar mutuwa’’. Za a iya fahimtar waɗannan kalmomin

da cewa irin wannan hukumcin ko kuma wutar tana da tsanani da zata

shafe wanda aka yankewa irin wannan hukumcin, yadda ba zai sake

rayuwa ba.

Ta yaya zamu gane ko menene daidai? Zamu san abinda ke

daidai yayin da muka bincike Littafi Mai-Tsarki muka tarar cewa ba a yi

amfani da wannan kalmar ‘‘rai’’, ko ‘‘rayuwa’’ dangane da waɗanda suka

mutu ba tare da sun tuba ba, da kuma waɗanda aka ta da su daga

matattu (ka dubi: Tashin waɗanda basu da ceto daga matattu a shafi ...).

Tilas mu tuna cewa sai mutum yana da rai kafin ya daure azaba.

Bugu da ƙari, Allah a cikin yalwar alherinsa ya bamu misalin

wutar har abada. Lokacin da aka hallaka Sodom wutar ta ci gaba da ci na

’yan kwanaki ƙalilan kawai. Duk da haka, an yi magana a kan wutar da ta

hallaka Saduma da Gamuratu a matsayin ‘‘wuta ta har abada’’. Mun

karanta a cikin wasiƙa ta yahuda sura 7 cewa:

Kamar yadda Saduma da Gamurata, da birane na wajensu, da shi

ke tare da su suke, bada kansu ga fasikanci, suka biɗi kwaɗai ba

irin na tabi’a ba, an nuna su, kamar misalin wuta ta har abada,

cikin hukunci da suke har abada.

Saboda haka, zamu iya tabbatar da cewa bisa ga waɗannan

dalilai da waɗansu dalilai na Littafin Mai-Tsarki, zamu iya gane cewa

fahimta irin wadda aka saba bisa al’ada bata da madogara. Idan wanda

5
ashi da ceto ya mutu, ya mutu har abada, cikin jiki da kuma ruhu. Za a

faɗaɗa wannan gaskiyar idan muka shiga sura ta gaba.

6
Sura Ta Biyu

Rashin Sahihancin Fahimtar Shirin Shari’a Irin Ta Al’ada.

A cikin ’yan shekarun da suka wuce, mun koyi cewa kafin ranar

sharia akwai kwanaki 8,400 (shekara 23) na lokacin da ake kira babban

tsanani. A wannan lokaci, Allah yana gwada dukan mutanen, da ke cikin

Ikkilisiya, ko su masu bi na gaskiya ne ko kuma babu. Wato, ko sun

ƙwallafa tunaninsu a kan koyarwar Ikklisiyarsu, ko kuma suna a shirye

su ji su kuma yi biyayya da dukan abin da Littafi Mai-Tsarki ke koyarwa.

Ko da shike yanzu ne aka bayyana waɗansu koyaswa da dama.

A lokacin babban tsanani, wanda muke ciki yanzu, mun gane

cewa Allah yana amfani da gwaje gwaje da yawa da suke bambanta

alkama da zawan. An umurta irin wannan gwadawar a cikin Ruya ta

Yohanna 3:10 inda muka karanta cewa:

Tun da ka kiyaye maganar haƙurina, ni ma zan kiyaye ka daga

sa’ar jaraba, wannan da ke zuwa bisa ga dukan duniya, domin a

jarabci mazannan duniya.

A wannan aya, wannan kalmar “sa’ar Jaraba” ko jaraba ko

gwadawa, tana da alaƙa da babban tsanani na kwanaki 8,400. A wannan

lokacin za a yi gwaje gwaje ko jarabawa da dama, waɗansu misalai da

muka koya suna nan kamar haka:

1. Zamanin Ikkilisiya ya zo ga ƙarshe.

2. Haƙiƙannin ranar sharia.

3. Ainihin fahimtar shirin shari’ar Allah.

4. Ainihin fahimtar dukan abinda samun ceto ya ƙunsa.

5. Fahimtar cewa Allah ya ɓoye gaskiya mai muhimmanci a

cikin Littafi Mai-Tsarki da ba za a bayyana ba sai an kusa

da ƙarshe.

6. Zamu aika wa duniya sakon cewa har yanzu akwai damar

samun ceto, kuma yana yiwuwa a ci gaba da samun ceto

har zuwa rana ta ƙarshe ta babban tsanani ranar 21 ga

watan Mayu, 2011.

7. Dole mu faɗakar da duniya da cewa idan ranar shari’a ta

zo, ba bu sauran damar samun ceto, ko kuma wani jinƙan

Allah.

Littafi Mai-Tsarki yana nan yau kamar yadda yake lokacin da aka

kammala rubuta shi shakaru 1,900 da suka wuce. Duk da haka sai a

lokacinmu, babu wani, komi zurfin ilimisa ko amincinsu, ko irin bautar

Allah a matsayin Mai-Cetonsu da suke yi cikin tawali’u. Babu wanda ya

iya sanin ainihin shekarar da aka yi halitta daga Littafi Mai Tsarki, da

7
shekarar da aka yi ruwan Ɗufana ko ranar da aka haifi Yesu. Haka nan

kuma, babu wanda ya iya sanin ainihin cikakken shirin shari’ar Allah.

Saboda haka, kamar yadda muka ambata a baya, a duk faɗin

zamanin Ikkilisiya abin da aka fi yarda da shi a tsakanin masana tauhida

da ɗaliban Littafi Mai-Tsarki shine cewa mutum ba zai iya sanin ainihin

lokacin da Kristi zai dawo a ƙarshen duniya ba An yarda da cewa bayanin

da ke cikin Littafi Mai-Tsarki cewa Kristi zai zo kamar ɓarawo da dare

(ITassalunikawa 5:2, IIBitrus 3:10) ya amsa tambayar nan game da

lokacin da Kristi zai dawo.

Haka nan game da yanayin shari’ar Allah bisa marasa ceto, an

fahimci cewa a ƙarshen zamani, Kristi zai shari’anta dukan marasa ceto

na duniya a fili. Za a tashi waɗanda suka mutu su kuma san abinda ke

faruwa domin a yi masu shari’a. Daga nan kuma waɗanda suke da rai a

ƙarshen zamani, da kuma waɗanda aka tashe su daga mattatu, za’a

same su da laifi a kuma hukuntasu zuwa hukunci a wani wuri da ake kira

jahannama. Ayoyi kamar su II Korintiyawa 5:10, da Romawa 14:10-11 da

sauransu, suna koyar da haka a fili.

Amma Allah yayi alkawari a cikin Mai-Wa’azi 8:5-6 inda muka

karanta cewa:

Dukan wanda yake riƙe da dokan ba za ya kusanci wuta ba;

zuciyar mai-hikima kuwa ta kan gane kwanaki da shari’a kuma

gama ga kowane al’amari akwai lokaci da shari’a. Saboda haka

zuciyar mutum da nauyi ta ke a gare shi.

A cikin Daniel 12:9 kuma Allah ya ce:

Yace, yi tafiyarka ya Daniel, gama an kuble zantuttukan, an

hatimce su har kwanakin ƙarshe.

Tun da lokaci da shari’a suna da alaƙa da ƙarshen zamani, za mu

iya sa zuciya cewa da shike muna kusa da ƙarshen, a wannan lokaci za

mu ƙara sanin abubuwa da yawa game da lokacin tarihi da kuma

cikakken shirin shari’ar Allah.

Babu shakka mun rigaya mun koya daga Littafi Mai-Tsarki baki ɗaya,

ainihin rana, da wata da shekarar da za a yi fyaucewa, watau lokacin da

za a fyauce dukan masu bada gaskiya zuwa cikin sama. Mun kuma koya

game da ainihin lokacin za a hallaka duniya da ƙasa da dukan ayyukan ta

baki ɗaya da wuta*

Haka kuma, a wannan lokacin Allah ya bamu fahimi domin mu

iya sanin ƙarin shirin hukumcin Allah. Allah ya bayyana filla filla lokacin

da al’amuran ƙarshen duniya zasu faru, wannan kuma ya taimake mu

domin mu fahimci tsarin sa na shari’a.

8
Za mu gane cewa shirin shari’ar Allah ya fara ne kafin zunubi ya

shigo duniya, kuma za a gama a lokacin aka ƙona duniya da dukan

ayyukanta. (II Bitrus 3:10).

Yayin da muke nazarin shirin shari’ar Allah, zamu yi nazarin

waɗansu muhimman kalmomi kamar, “mutuwa’’ da ‘‘hallaka”, da kuma

abubuwa kamar kunya, asarar gado, babban tsananin ciwo, daga ƙarshe

kuma da shafewa daga doron ƙasa. Amma, kafin mu yi wannan, bari mu

dubi waɗansu koyaswar ƙarya da waɗansu wahalhalun da ke cikin

fahimta irin ta al’ada game da shirin shari’ar Allah.

Kusan kowacce Ikklisiya a dukan zamanin Ikkilisiya ta gaskanta

da cewa aikinsu na farko shine koyawa mutanen yadda zasu sami ceto.

Saboda haka kowacce majami’a ta tsara shiri wanda ba ya bisa koyaswar

Littafi Mai-Tsarki, da suka gaskanta cewa yana daidai da koyarwar Littafi

Mai-Tsarki inda suke koyaswa da cewa waɗanda suke bin shirin su suna

da tabbacin ceto.

Babban abu mai muhimmanci na wannan shirinsu, shine

tsatsauran tuni cewa abinda zai maye gurbin ceto shine hallaka ta har

abada. Abinda suka fahimta game da hallaka ta har abada, shine marasa

ceto za su sha azaba a ƙalƙashin fushin Allah, na har abada abadin a

wani wurin da ake kira jahannama. Sun hakikanta cewa irin wannan

hukumcin mai tsanani kan zunubi, zai taimaki mutane su gane da irin

bukatar ceto da suke da ita.

An gaya wa mutane cewa zasu iya samun wannan ceto kuma su

sami tabbacin cewa ba za su taɓa shan azaba a jahannama ba, idan suka

bi koyarwar majamia ko ta mai-wa’azi da aminci. Ya yiwu ya ƙunshi

abubuwa kamar baftisma da ruwa, addu’ar mai-zunubi, shaidar

bangaskiya, zama memban Ikkilisiya, bada zakka, cin jibi karɓan

Almasihu, da dai sauransu. Da zarar sun sami tabbaci daga wurin fasto,

ko firis ko dattijo, ko dikon, cewa suna da ceto, kuma sun sami babbar

ta’aziyar cewa ba zasu taɓa shiga jahannama su zauna har abada ba.

Ba a daɗe ba sai wata matsala ta taso. Misali idan yaro ya mutu

ba tare da ya sami ceto ba. Da shike zunubi ɗaya zai iya sa mutun ya

zama mai laifi kamar ya ƙetare dukan dokoki (Yakub 2:10), to bisa ga

wannan koyaswar ƙaramin yaron da ya mutu ba tare da ya sami ceto ba,

zai sha wahala a jahannama har abada. Wannan yana nufin cewa za a

yiwa ƙaramin yaron hukumci sabili da zunuban da ya aikata na

yarantaka.

Shin gaskiya ne cewa Allah mai-jinƙai Allah mai-adalci zai sa

ƙaramin yaro haka ya sha baƙar wahala ta har abada domin shi ko ita

sun mutu ba tare da sun sami ceto ba? Babbar tambayar da masu ilimin

tauhidi a cikin majami’u suke fuskanta ke nan, kuma an yi ƙoƙarin

neman amsoshi da dama na waɗannan tambayoyi kuma ya zama

muhimmiyar koyaswar kowacce Ikkilisiya.

Misali Ɗarikar Roman Katolika suna da ra’ayin cewa idan an yi wa

jariri baftisma zai wanke dukan laifofinsa da suka sami tushe daga

9
zunubin Adamu. Wannan kuma zai sa yaron ya kasance ƙarƙashin

kulawa da kariyar Ikkilisiya, inda, idan ya bi dokokin Ikklisiyar a hankali

zai bada tabbacin cewa fushin Allah ba zai taɓa saukowa a bisa kan

wannan mutumin ba.

Ikkilisiyun da suka tashi a baya, suma sun biyo sahun irin

wannan shirin ko da shike sun fi kusa da gaskiya fiye da ɗarikar katolika.

Suma sun gaskanta suna kuma koyar da cewa jaririn da aka yi masa

baftisma a majami’a ya kan shiga cikin wata yarjejeniyar dangantaka ta

ruhaniya da Allah, ta yadda idan aka bi dokokin Ikklisiyar da aminci zai

sami tabbacin ceto.

Ikkilisiyan da suka bi koyaswa irin ta Arminiyawa na yanci, kamar

majami’ar baftis sun ƙirƙiro wata hanya ta daban. Sun tsaida shawara

cewa Littafi Mai-Tsarki ya koyar da cewa akwai lokacin da mutum zai

bada lissafin aikin da ya yi. Watau sai yaro ya kai waɗansu shekaru, kafin

a hukumta shi sabili da abinda ya aikata. Saboda haka idan yaro ya mutu

kafin ya kai waɗannan shekarun, Allah ba zai hukumta shi ba.

Dukan waɗannan koyaswar basu da makama a cikin Littafi Mai-

Tsarki ko da shike har wa yau ana koyas da su da hakikanin gaskiya a

cikin dukan Ikkilisiyai da ke faɗin duniya.

Ina Jinƙan Allah?

Wata matsala ta taso dangane da itifaƙin cewa hukuncin zunubi

shine a sha azaba a wani wurin da ake kira jahannama har abada.

Mutane da yawa waɗanda suka yiwa Littafi Mai-Tsarki ba’a sun yi wata

tambaya mai ma’ana cewa “Kun ce Allah na Littafi Mai-Tsarki, mai-jinƙai

ne da adalci saboda haka kun yi imani da cewa Allah mai- jinƙai da

adalci zai azabtar da mutumin da ke rayuwa mai kyau cikin mutumci ta

wurin jefa shi a wurin da ake kira jahannama wurin da shi ko ita zasu

sha matsananciyar wahala ta har abada? Wanne irin Allah ne, Allahn ku

na Littafi Mai-Tsarki? Kuma ta yaya wannan ra’ayin yayi daidai da

maganar da aka yi a cikin Littafi Mai Tsarki cewa Allah baya jin daɗin

mutuwar mugu?” (Ezekiel 18:23 da 32).

Ikkilisiyai da dama sun yi nazari a kan irin waɗannan tambayoyi,

domin haka suka ƙirƙiro da wata hanya da zata ƙarfafa mutane su

amince shirin ceton su na yi-da-kanka. Maimakon jaddada abu marar

kyau wato wahala ta har abada, sun canja yadda suke gabatar da batun

ceto zuwa bada ƙarfi kan abinda yake da kyau, suna cewa “Allah yana

ƙaunar ka kuma yana da kyakkyawan shiri domin rayuwar ka. Zaka iya

zama cikin wannan shirin ta wurin karɓar Yesu”. Watau ‘‘ka haɗa kai da

mu daga nan baka bukatar ka damu, kuma ba zaka ƙara damuwa da

fargaban da yake zuwa cikin tunanin ka da zuciyarka loto loto ba domin

ka sani cewa akwai Allah kuma wata rana dole zaka bada lissafi a

gabansa”. Waɗannan majami’un basu rabu da ra’ayin hukumci har

abada ba, amma a wurinsu wani abu ne da za a yi watsi da shi ba

abinda za a tada hankali akai bane.

10
Ya yiwu mu kuma ƙara lura cewa Littafi Mai-Tsarki ya koyar cewa:

‘‘Haƙƙin zunubi mutuwa ne...’’ (Romawa 6:23a). Koyarwa da aka saba da

ita ta al’ada tace “Hakkin zunubi.” yana nufin a rana ta ƙarshe dukan

wanda baya cikin zaɓɓaɓu na Allah, (waɗanda basu da ceto) za’a rayar

da su domin su tsaya a gaban Kristi alƙalinsu. A can za’a same su da

laifi saboda haka za a yanke masu hukumcin shan azaba a wani wuri da

ake kira jahannama.’’ Waɗanda suke da ra’ayi irin na al’ada ba zasu

yarda da wannan ba amma suna riƙe da fahimtarsu na hukunci kuma

yana nufin kuma da shike an yi cikinmu aka kuma haife mu cikin zunubi

(Zabura 51:5), Dukan jinjiri da aka zubar da cikinsa da dukan jaririn da

ya mutu wanda ba ya cikin zaɓaɓɓu, za a yanke masu wannan

matsanancin hukuncin.

Wannan mumunan ra’yin game da hukuncin Allah , wani

mummunar ra’ayin musun dokar Allah ne, an tsara wannan ra’ayin ba

tare da wani cikakken sani ba ko kuma cikin rashin sanin cewa, dukan

Littafi Mai-Tsarki dokar Allah ba ne. Saboda haka ana ganin maganar

kamar “Haƙƙin zunubi mutuwa ce” da “cikin ranar da kaci mutuwa zaka

yi lallai” kamar umurni ne daga bakin Allah maimakon ɗaukarta a

matsayin dokar Allah.

Yana da matuƙar muhimmanci mu gane cewa Maganar Allah

gaba ɗayanta tana da dangantaka da Kristi kansa. Allah ya ce Kalman

ya zama jiki, ya zamna a wurinmu (Yohanna 1:14a ). Maganar Allah tana

da cikakken iko kamar Kristi kansa. Ibraniyawa 4:12-13 ta ce:

Gama maganar Allah mai rai ce, mai aikatawa, ta fi kowanne

takobi mai kaifi biyu ci, tana kwa hudawa har zuwa rarraban rai

da ruhu da gaɓaɓuwa da ɓargo kuma, tana kwa da hanzari ga

ganewar tunanin zuciya da nufe-nufenta. Babu wani abu mai rai

kuma da ba’a bayyana a gabansa ba. Amma abubuwa duka a

tsiraice suke, buɗaɗɗu kuma, gaban idanun wannan wanda muke

gareshi.

Lokacin da Allah ya gaya wa Adamu cewa ran da ya ci daga itacen

mutuwa zai yi, Allah yana furta dokarsa ne ga Adamu. Wannan doka

tana da ikon Kristi kansa bisa kan Adamu, saboda haka lokacin da

Adamu yayi ƙetare dokar nan take aka hukunta Adamu bisa ga wannan

dokar zuwa hukuncin mutuwa.

Lokacin da Allah ya hallaka Sodoma da Gomorah da duniyar

zamanin, Nuhu, waɗannan mutanen ba su bukaci tsayawa a gaban Kristi

a matsayin alkali ba kafin a zartar da hukuncin mutuwa ba. Sun ƙetare

dokar Allah kuma duk lokacin da suka aikata zunubi dokar Allah zata

kashe su zuwa mutuwa.

A hakikanin gaskiya duk lokacin da wani wanda baya da ceto ya

mutu, ko da ta wacce hanya ya mutu, lokacin ne a ke hukunta shi a

matsayin biyan bashin zunuban sa. Domin koyaswar da aka saba da ita

11
dangane da shirin shari’ar Allah bai yi la’akari da cewa dukan Littafi Mai-

Tsarki dokar Allah ba ne, kuma kowacce kalma tana da iko kamar Kristi

kansa, shirin shari’a ne wanda mutum ya saƙa a zuciyarsa. Da shike

Allah ne ya ɓoye gaskiya mai yawa game da lokacin da kuma hukunci

domin kada a bayyana su ga ’yan adam sai kusan ƙarshen zamani, An

rubuta Littafi Mai-Tsarki a cikin harshe mai sarƙaƙiya. Nufin Allah cewa

kada kowa ya fahimci dukan abin da Littafi Mai-Tsarki yake koyarwa

game da lokaci da sharia sai a lokacin mu. Shirin Allah ne ba za a

fahimci wannan gaskiya mai muhimmanci ba sai lokacin da duniya ta zo

kusa da ƙarshe. Ta haka Allah ya bari aka ci gaba da yiwa tsarin shari’ar

Allah karkatacciyar fahimta ta alada da ake koyarwa a majami’u, yayinda

kuma ya bari Ikklisiyai suna koyar da shirin ceto irin na yi-da-kanka.

Saboda haka, har yau akwai ɗaliban Littafi Mai-Tsarki da basu da

wani mugun nufi, da suke ƙoƙarin bada hujjar fahimtar shirin Allah na

shari’a bisa ga al’ada ta wurin nazarin kalma a kan kalma, da ake samu a

Littafi Mai-Tsarki. Sai dai suna tace waɗannan kalmomi bisa ga tunanin

da suka saba da shi da gurguwar fahimtar shirin shari’ar Allah da suka

hakikanta cewa daidai ne. Wani aiki ne mawuyacin gaske domin shirin

shari’ar Allah irin na al’ada bai yarda da cikakken ikon kowace kalma a

cikin Littafi Mai-Tsarki a matsayin dokar Allah ba.

A takaice, zamu iya cewa, a duk zamanin Ikklisiya akwai waɗansu

matsalolin da ba’a warware ba dangane da gaskiyar fahimtar hukunci

kan zunubi. Za a iya gane wannan idan muka tuna cewa an rufe bayanai

masu yawa game da cikaken bayani da kuma abinda ya shafi ƙarshen

zamani a cikin Littafi Mai-Tsarki domin kada a fahimta. Allah ya sa

harshen Littafi Mai-Tsarki ya kasance da wuyar ganewa domin waɗannan

gaskiyar zata kasance a ɓoye sai kusan ƙarshen zamani.

Amma, yayin da muka doshi ƙarshen zamani, nufin Allah ne cewa

za a san bayanai masu yawa. Abin baƙin ciki shine Ikklisiyai suna

tsayayya yanzu da gaskiyar da ake bayyanawa, waɗanda suke dogara

gaba ɗaya kan shaidarsu , koyarwarsu da tauhidin da suka yi ittifaki a

kai. Haka wannan yake musamman domin zamu iya ganewa cewa

tunanin shan wuya har abada a jahannama a sakamakon zunubinsu ba

gaskiya ba ne. Saboda haka an kawar da wata babbar hanyar da ake

amfani da ita wajen ƙarfafa mutane su sami ceto.

Bugu da ƙari, majami’u sun gamsu da fahimtarsu yanzu ta Littafi

Mai-Tsarki. Basu gane ba ko kuma basu fatar gane shirin Allah cewa, a

cikin kwanakin nan na ƙarshe, za a sami ƙarin sanin gaskiya daga cikin

Littafi Mai-Tsarki. Misali mun koya daga farkon wannan bincike cewa,

duk tsawon zamanin Ikklisiya, majami’u sun yi ittifaki, bisa bincikensu

Littafi Mai-Tsarki da suka yi a hankali, cewa Kristi zai zo kamar ɓarawo

da dare. Amma yanzu da shike muna dab da ƙarshen zamani, Allah ya

ba ma masu bi na gaskiya cikakken bayani wanda ya fito daga Littafi

Mai-Tsarki kaɗai domin mu sani da cikakken tabbaci rana da wata da

shekarar da duniya zata ƙare.

12
Haka kuma, yanzu muna koya daga Littafi Mai-Tsarki bayanai

masu ɗinbin yawa game da shari’a. Ka tuna abinda muka koya daga Mai-

Wa’azi 8:5-6 inda Allah yace:

Dukan wanda ya ke riƙe da dokar ba za ya kusanci wuta ba,

zuciyar mai-hikima kwa ta kan gane kwanaki da shari’a kuma:

gama ga kowane al’amari akwai nasa lokaci da shari’a, domin

ɓacin zuciyar mutum da nauyi ya ke a gareshi.

Kada mu yi mamaki da cewa Ikkilisiyai suna gaba da ittifaki game

da lokaci, wanda muka koya daga Littafi Mai-Tsarki, kuma zasu ci gaba

da ƙin yarda da yanayin shari’a, wanda kuma ya kasance sakamakon

binciken Littafi Mai-Tsarki a hankali. Amma ya kamata muyi farin ciki

domin da yake muna kusa da ƙarshen zamani Allah yana ƙara nuna wa

masu bi na gaskiya gaskiyar Littafi Mai-Tsarki da take ɓoye a cikin Littafi

Mai-Tsarki tun shakaru 1,900 da suka wuce.

Ƙaunar Mutum Ga Mutum

Kafin mu bar binciken mu na yanzu, na fahimtar shirin shari’ar

Allah bisa ga al’ada, bari mu dubi wani abu wanda ya maida hankali a

kan wannan batu. Yana da dangantaka da umurnin Allah cewa mu

ƙaunace maƙwabtanmu.

Yesu ya yi tambaya a cikin Matta 22:36 cewa:

Malam, wacce ce babbar doka a cikin Attaaurat?

Mun karanta amsar Yesu cikin Aya 37 zuwa 40:

Yace masa, ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da

dukan ranka da dukan azancinka wannan ce babbar doka, itace

kwa ta fari. Wata kuma ta biyu mai kamaninta ke nan, kayi

ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka. Ga waɗannan doka biyu

dukan Attaurat da Annabawa suke ratayawa.

Bisa ga Yohanna 14:21 mun sani cewa mu ƙaunace Allah shine

mu kiyaye dokokinsa, kamar yadda muka karanta:

Wanda yake da dokoki na yana kwa kiyaye su shine yake ƙaunata:

wanda yana ƙaunata kuma za ya zama ƙaunatacen ubana, ni ma

zan ƙaunace shi in bayyana kaina gare shi kuma.

Mun kuma sani cewa dokokinsa sune dukan Littafi Mai-Tsarki.

Mutumin da yake da ceto, mai-bi na gaskiya yana da marmarin yin

biyyaya da dukan Littafi Mai-Tsarki.

13
Sai dai a wannan tsarin da Allah yace ka ƙaunaci Allah da dukan

zuciyarka da dukan ranka da dukan azancinka, ya bada umurni cewa ka

ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ta haka Allah yake fito da wani

ɓangare guda na ƙaunar mu zuwa gareshi ta wurin jadada bukatar mu

ƙaunaci maƙwabcin mu. Ba kawai yana neman ya jawo hankalinmu kan

ƙaunar makwabcinmu ba, amma yana kafa mana ma’aunin da za mu

auna ƙaunar mu ga maƙwabcinmu. Wato ya kamata ƙaunar mu zuwa ga

maƙwabcinmu ta zama daidai da yadda muke ƙaunar kanmu.

Mu koya daga misalin Basamariye mai kirki (Luka 10:29-37) da

cewa maƙwabchinmu shine duk wanda yake da bukatar taimako.

Wannan ya tabbatar mana da cewa duk wanda ba shi da ceto yana

bukatar taimako na ruhaniya saboda haka maƙwabcinmu ne. Saboda a

hakikanin gaskiya maƙwabcinmu shine kowa a duniya. Shi ya sa mu ka

aika da bishara mai daraja cikin duniya. Duk wanda ba shi da ceto yana

bukatar taimakonmu, Kuma babu shakka Allah yayi amfani da Littafi

Mai-Tsarki ya ceci waɗanda aka zaɓa domin a cece su.

Da shike ya kamata mu ƙaunaci maƙwabtanmu kamar kanmu. Ya

kamata mu bukaci abu mafi kyau dominsu cikin gaskiya. Abu mafi kyau

shine ceto. Amma, mene ne zai faru idan mutum ya mutu ba tare da ya

sami ceto ba? Har yanzu zamu ƙaunace shi? Littafi Mai-Tsarki ya bada

amsar wannan tambayar a cikin Matta 5:44 inda muka karanta cewa:

Amma ina ce maku, kuyi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su

kan tsananta maku, ku yi masu addu’a.

Zai zama da wuya a dama daga magabatan da zasu sami ceto.

Amma duk da haka zamu ƙaunace su. Dauda da kuma Yesu sun sun bar

mana gurbin nuna ƙauna ga waɗanda basu da ceto har ma bayan sun

mutu. A ƙalla cikin kusan shekaru 15 na rayuwar sarki Saul, ya yi ƙoƙari

ya kashe Dauda ko ta wacce hanya. Duk da haka, bayan da sarki Saul ya

mutu, Dauda ya nuna baƙin cikinsa da ƙauna a ayoyi kamar IISamaila

1:9 da 24 inda muka karanta cewa:

Ya Isra’ila an kashe darajarka a bisa maɗaukakan wuraren ka;

masu iko ƙaƙa za a kwatata faɗuwarsu...Ku ’yan matan Isra’ila,

ku yi kuka bisa Saul, shi wanda ya yafa maku mulufi mai

ƙayatarwa. Ya yi maku adon lu’u-lu’u da zinariya.

Kuma a cikin IISamaila 2:5 muka karanta cewa:

Dauda kuma ya aike manzanni zuwa wurin mazammnan Jabesh –

Gilead, ya ce masu, ma su albarka ne ku na Ubangiji da shike kun

nuna wannan alheri ga Ubangijinku wato Saul, kin bizne shi.

14
Dauda ya nuna ƙauna da girmamawa ga mattacen magabcinsa,

sarki Saul, amma ya nuna ƙauna mafi girma ga mugun ɗansa Absalom.

Lokacin da Absalom yana da shekara 25, ya fara shirin kashe mahaifinsa

Dauda. Sha’warsa ita ce ya ƙwace kujerar sarautar Isra’ila daga ubansa. A

gaskiya ma, tawayensa ya kawo rashin zaman lafiya a fili har ya tilasta

Dauda ya gudu daga Urushalima domin kada Absalom ya kashe shi.

Amma an bayyana zurfin ƙaunar Dauda zuwa ga mugun ɗansa

mai cin amana wanda daga ƙarshe shugaban mayaƙan Dauda ya kashe

shi a cikin IISamaila 18:33 inda muka karanta cewa:

Sai sarki yayi juyayi da yawa ya hau wajen benen da ke kan ƙofa, ya

yi ta kuka; yana tafiya yana cewa ya ɗana Absalom, ya ɗana, ɗana

Abasalom, da ma Allah ya yarda na mutu dominka, ya Absalom, ya

ɗana ɗana.

Ƙaunar Dauda domin Absalom ta nuna irin ƙaunar da zamu yi wa

makwabcinmu. Bai kamata mu yi farin ciki ba a kan mutuwar

magabcinmu, amma muyi baƙin ciki cewa sun fuskanci fushin Allah da

yake saukowa kan dukan waɗanda basu da ceto.

Har’ ila yau, mun ga irin ƙaunar da Kristi ya nuna ga waɗanda

zasu fuskanci fushin Allah. Mun karanta a Luka 19:41-44 cewa:

Sa’anda yayi kusa, ya hangi birni, yayi kuka a kanta, yace. Da ma

kin sani a cikin wannan rana, har ke ma, abin da ya tabbata ga

salama. Amma yanzu a ɓoye yake a idanunki. Gama kwanakin

zasu abko maki inda maƙiyanki zasu gina maki ganuwa, su sa ki

a tsaka, su tsare ki daga kowane sassa. Su fyaɗe ki a ƙasa da

’ya’yanki a cikinki, ba za su bar ko dutse ɗaya bisa wani a cikinki

ba, da shike ba ki lura da kwanakin ziyartonki ba.

A waɗannnan ayoyi mun karanta cewa Yesu yayi kuka domin

Urushalima, wadda a nan take wakiltar dukan waɗanda basu da ceto a

cikin ƙasar Isra’ila, da kuma dukan waɗanda suka rage a majami’u

waɗanda zasu fuskanci cikakken fushin Allah domin zunubansu. An

albarce su ta musamman domin sun koya daga Littafi Mai-Tsarki. Sun

koya da yawa game da ƙaunar Allah da jinƙansa. Amma sun juya

gaskiyar Littafi Mai-Tsarki zuwa koyaswar da ta gamshe su. Sun ci gaba

da tafiya cikin girman kansu. Za mu iya ganinsu a cikin ruhaniya kamar

marasa son zaman lafiya waɗanda suka cancanci fushin Allah.

Amma Yesu yayi kuka dominsu. Ka yi tunani kan cewa Allah da

kansa yana kuka domin dole ya hukunta waɗanda suka tayas masa. Ba

abin mamaki ba ne da muka karanta a cikin Ezekiel 33:11 cewa:

Sai ka ce masu, in ji Ubangiji Yahweh na rantse da raina, ba ni da

wani jin daɗin cikin mutuwar mugu...’’

15
Muna koyan cewa tilas ne Allah ya sauko da hukunci kan

ƙaunatattunmu da abokanmu da basu da ceto, wannan kuma yana cika

mu da baƙin ciki da ɓacin rai. Amma wannan ɓacin ran zai ragu ainun

domin mun san abokinmu ba zai sake wahala ba muddin ya mutu. Sai

dai idan fahimtar nan ta al’ada daidai ne, cewa marasa ceto zasu sha

azaba ta har abada a wurin da ake kira jahannama, babu shakka zamu yi

baƙin ciki ainun yayin da abokan mu marasa ceto suka mutu. Idan

abokinmu ya yi mummunar rayuwa a nan duniya, yana jin daɗi da

walwawa irin ta duniya, amma ya watsar da Littafi Mai-Tsarki, zamu ci

gaba da baƙin ciki bayan mutuwarsa idan muka yi tunani wahalar nan

marar matuƙa.

Amma yanzu, Littafi Mai-Tsarki ya yi mana gyara a fahimtar mu

ta shari’a. Ko da shike abokinmu ya mutu yana watsar Littafi Mai Tsarki,

ko da shike babu daɗi cewa an hana shi wannan kyakkyawan gado na

madauwammi, da kuma farin ciki da ɗaukaka na zama magada tare da

Kristi a sabuwar sama da sabuwar duniya, kuma ko da shike yana da

muni sanin cewa mutuwarsa hukumci ne abin kunya ƙarkashin la’anar

Allah, akwai labari mai daɗi. A ƙalla, zamu iya samun tabbacin cewa

mutuwar abokinmu, tana nufin ba zai ƙara zama ƙalƙashin tsanani da

wahala ba. Rayuwarsa ta ƙare

Abin baƙin ciki ne ganin cewa, mutane da yawa waɗanda suka

gaskanta cewa suna da ceto suna fushi mai tsanani da koyaswar da ke

cikin Littafi Mai-Tsarki kamar yadda aka bayyana a cikin wannan littafin.

Fushinsu yana bamu mamaki. Mun sani akwai mutane masu ɗunbin yawa

da suka hakikanta cewa suna da ceto amma a hakikannin gaskiya basu

da ceto. Sai dai kuma da yake sun gaskanta cewa suna da ceto, suna

ƙoƙari su yi rayuwa irin ta wanda yake da ceto. Amma domin basu da

ceto, yana nufin cewa suna ƙaunar duniyar nan da dukan abinda ke

cikinta da jikunansu da kuma zukatansu da dukan jin daɗin da duniya za

ta basu. Saboda haka, ƙoƙarin rayuwa irin ta masu ceto wani aiki ne

tuƙuru. A cikin zukatansu suna ƙaunar duniya, kuma domin sun gaskata

cewa suna da ceto, kuma sun san cewa bai kamata su ƙaunaci duniya ba,

rayuwa ta zamar masu da wahala da baƙin ciki. Tilas ne su yi rayuwa

kamar ba su son duniya, amma suna matuƙar son wannan duniya.

Matsala ta kan taso idan wani aboki ya mutu, abokin da bai damu

da Littafi Mai-Tsarki ba, wanda kuma ya ke cin duniyarsa da tsinke. Bisa

ga koyarwa irin ta al’ada dangane da shari’a, ya kamata ya sha azaba ta

har abada a wuri da ake kira jahannama. Ko Wannan da muke bayani

akansa wanda ya gaskanta yana da ceto, amma a hakikannin gaskiya ba

shi da ceto, yayi wannan mummunar tunani cewa idan shi da kansa ya

mutu, bashi da ceto bisa ga fahimta irin ta al’ada, dole a yi mashi

hukunci na har abada a wani wuri da ake kira jahannama? Abin zai yi

muni sosai.

Duk da haka, yanzu mun koya cewa wannan irin tunani irin na

al’ada na shirin hukuncin Allah kan masu zunubi bashi da makama. Yayi

16
musun jinƙai da tausayi da adalcin Allah baki ɗaya. An tsara shi ne baki

ɗaya bisa ga hikimar mutum. Ba bu gaskiya a ciki. Wannan fahimtar ta

al’ada ta nuna a fili mugunta da rashin jinƙai wanda hali ne na mutumin

da bashi da ceto. Zai yi daidai mu yi gargaɗi da cewa bai kamata mu

taɓa ƙoƙarin fassara jinƙai, da adalcin Allah bisa ga tunaninmu da

ra’ayinmu game da jinƙai da adalci ba. Allah ya bada wannan kyakyawan

alkawari a cikin Mai-Wa’azi 8:5-6.

Dukan wanda yake riƙe da dokar ba za ya kusanci wuta ba;

zuciyar mai hikima kwa ta kan gane kwanaki da shari’a kuma

gama ga kowane al’amari akwai nasa lokaci da shari’a domin

ɓacin zuciyar mutum da nauyi ya ke a gareshi.

Malaman tauhida da ɗaliban Littafi Mai-Tsarki sun shafe dubban

shekaru suna karanta waɗannan kalaman ba tare da sun fahimta ba.

Haka ta faru ne domin lokaci da shari’a suna da alaƙa da ƙarshen

zamani. Kuma nufin Allah ne ya rufe irin wannan bayani, sai ƙarshen

zamani (Daniel 12:4). Allah ya tabbatar mana da wannan, yayin da muke

shaidar yardar Allah, a wannan lokaci na tarihi, da muke kusa da ƙarshen

duniya ya bayyana da shaidu da yawa daidai rana da shekarar da duniyar

nan zata ƙare. Saboda haka yau, kowanne mutum mai -hikima wato

kowane mai-bi na gaskiya zai sani daga Littafi Mai-Tsarki shirin

jadawalin Allah na tarihi daga farko har zuwa rana ta ƙarshe (dubi Mun

Kusa Kai Ga Ƙarshe).

Amma wannan alkawali na Mai-Wa’azi 8:5-6 kuma yayi maganar

“Hukunci” wannan kalmar “Hukunci” wani lokaci ana amfani ita daidai da

kalmar “Sharia” da “dokoki da farillai. Ga misali mun karanta a cikin

Zabura 119:106 cewa, ‘‘...in yi biyayya da koyarwarka mai adalci.’’

Duk da haka, ana amfani da kalmar nan ‘‘shari’a’’ ko ‘‘shari’u’’

wajen nuna illar keta shari’ar Allah. Wannan shine hanyar da aka yi

amfani da ita a ayoyin Mai-Wa’azi da muke bincike yanzu, mun karanta

cewa, “Domin ga kowane abu, akwai lokaci da shari’a”. Wato ga kowane

abu akwai lokacin da za a kammala shi da kuma sakamakon cimma

wannan manufar. Sakamakon shine shari’a ko hukumci, idan abinda

muka aikata ya saɓawa dokar Allah.

Mun koyi cewa babbar koyaswa game da bayanin lokaci na Littafi

Mai-Tsarki ya maida hankali kan ƙarshen lokaci, yayin da za a kammala

dukan ayyukan shari’ar Allah. Saboda haka zamu iya gane dalilan da ya

sa aka haɗa lokacin da sharia a waɗannan ayoyin. Za a kammala dukan

hukumcin Allah a ƙarshen duniya.

Ba abin mamaki bane cewa Allah ya ƙara bayyana mana matsayin

al’ada da yawancin majami’u suka ɗauka da suka koyar a dukan

zamanin Ikklisiya (wato Kristi zai zo kamar ɓarawo da dare II Bitrus

3:10). Daga cikin Littafi Mai-Tsarki ne kaɗai zamu iya sanin ainihin rana

da wata da kuma shekarar da al’amuran ƙarshen zamani zasu faru. Duk

17
da haka, nufin Allah ne cewa a dukan zamanin Ikklisiya, majami’un

zasu koyar da cewa Almasihu zai zo kamar ɓarawo da dare. Mun san

wannan gaskiya ne domin mun karanta a cikin Ayukan Manzani 1:6

cewa:

Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, Ya

Ubangiji a wannan lokaci ne ka ke mayar ma Isra’ila da mulki?

Manzanin waɗanda suka jagoranci Ikklisiya ta farko, suna so su

san lokacin da Allah zai kammala dawo da mulkin Allah. A cikin

tunaninsu, suna sa rai zai kafa mulki irin na duniya. Kristi ya amsa masu

kamar yadda muka karanta a Ayyukan Manzani 1:7

Ya ce masu, ba naku bane da za ku san zamani da wokatai

waɗanda Uba ya sanya a cikin nasa hukumci

Sannan Yesu ya ƙara koyaswa game da halayen mulki Ayyukan

Manzani 1:8 na cewa:

Amma za ku karɓi iko lokacin da Ruhu Mai-Tsarki ya zo bisanku;

za ku zama shaiduna kuma cikin Urushalima, da cikin dukan

Yahudiya da Samariya har kuma iyakar duniya.

Waɗannan ayoyi uku, sun umurce mu da cewa a zamanin Ikklisiya

akwai babbar tambaya game da ƙarshen lokaci. Duk da haka majami’u a

zamanin Ikklisiya ba zasu yi sha’awar wannan batun ba, amma zasu

maida hankali ne a kan aikin da aka basu, wato su aika bishara cikin

dukan duniya. Saboda haka a cikin dukan shekarun nan 1,955, na

zamanin Ikklisiya, bisa ga fahimtarsu, babu wanda ya san lokacin da

zamani zai ƙare, amma Almasihu zai zo kamar ɓarawo da dare.

Duk da haka, kusan ƙarshen duniya, za a ƙara marmarin sanin

ainihin lokacin da duniya zata shuɗe. Saboda haka a kwanakin mu, Allah

ya buɗe idanun mu ga sanin cikakken lokacin da abubuwa na tarihi zasu

faru, yadda zamu iya sanin ainihin rana, da wata, da shekara da ƙarshen

zamani zai zo. Wannan ya ba masu bi na gaskiya damar gudanar da

hakin da ya rataya a bisansu na faɗakar da duniya. Kowanne mai-bi mai

tsaro ne. Mun karanta a cikin Ezekiel 33:2-7 cewa:

Ɗan mutum, ka yi Magana da ’ya’yan mutanenka, ka ce masu,

kaɗan an jawo ma wata ƙasa takobi, mutanen ƙasa kwa sun zaɓi

mutum guda daga cikin su, sun maishe shi mai-tsaro domin su,

shi ma, idan ya ga takobi ya faɗakar da mutane, dukan wanda ya

ji ƙarar ƙafo ya ƙyale, idan takobi ya zo, ya fizga shi, alhakin

jininsa yana bisa kansa. Ya ji busa, ya ƙyale; alhakin jinin sa yana

bisa kansa ne, gama da ya kula da faɗaka, da ya tsira da ransa.

Amma idan mai-tsaro ya ga takobi yana zuwa, ba ya yi busa ba,

18
jama’a kwa ba su sami faɗaka ba, takobi ya zo ya fizge wani

daga cikinsu; wannan mutum domin laifinsa an ɗauke shi amma

zan nemi jininsa ga hannun mai tsaro. Hakanan kai fa ɗan

mutum na sanya ka mai-tsaro ga gidan Isra’ila, domin wannan ka

ji Magana ga bakina ka yi masu faɗaka daga gareni.

A Tassalonikawa I 5:2-6 mun karanta game da juyawa daga koyaswar

cewa Kristi zai dawo kamar ɓarawo da dare zuwa koyaswar cewa mu

masu tsaro ne saboda haka shirin Allah yana kira zuwa ga sanin lokaci

da sharia.

Da yake lokaci da shari’a suna da dangantaka, wannan yana nufin

ke nan sabuwar koyarwa daga Littafi Mai-Tsarki zata maye gurbin

koyaswa irin ta ala’ada a kan shari’a?

Wannan shine ainihin gaskiyar da muka tarar. Gaskiyar ita ce

lokaci gaba ɗaya yana cikin tsarin shirin shari’ar Allah. Saboda haka,

samun sanin tsarin lokacin da al’amura na tarihin duniya ya tilasta sake

nazarin fahimta irin ta al’ada game da shirin shari’ar Allah.

Watau, bashi yiwuwa a fahimci koyarwar Littafi Mai-Tsarki game

da shari’ar sai dole mun fara koyo daga Littafi Mai-Tsarki game da

lokacin daidai. Tun da Allah ya nuna mana bayanai masu yawa sababbi,

bai kamata mu yi mamaki game da sabuwar gaskiya mai yawa da zamu

koya yanzu ba.

Yayin da daga ƙarshe Allah ya nuna mana tsarin abubuwan da

zasu faru na ƙarshen duniya, ba kawai mun gane daidai ƙarshen zamani

Ikklisiya kaɗai ba (21 Mayu, 1988) da kuma daidai tsawon lokacin

matsanancin ƙunci (kwanakin 8,400 ko kuma shekaru 23 cikakku) amma

kuma da lokacin ranar shari’a (Mayu 21, 2011 zuwa Octoba 21, 2011).

Da wannan ainihin bayanin lokacin, nan da nan zamu hanzarta ƙara koyo

sosai, game da illahirin shirin shari’ar Allah. Wannan ba abin mamaki

bane domin, kamar yadda muka bayyana, Littafi Mai-Tsarki ya danganta

lokaci da shari’a.

Kafin mu yi nazarin shirin shari’ar Allah da kyau, zai dace muyi

ɗan tsokaci game da lokacin tsanani da ke da alaƙa da ranar shari’a. Ka

tuna zamanin Ikklisiya ya ƙare ranar 21 ga watan Oktoba, 1988, wanda

kuma ita ce rana ta fari na kwanaki 8,400 da lokacin azaba. Yayinda

kuma matsanancin ƙunci zai zo ƙarshe a ranar 21 Mayu, 2011 wadda

ita ce rana ta fari ta kwanaki 153 na ranar shari’a. Akwai ayoyi guda biyu

a cikin Littafi Mai-Tsarki da suka alaƙanta ranar tsananin da ranar

shari’a. Ta farko ita ce Luka 21:22 in da muka karanta cewa:

Gama waɗannan kwanakin na ramawa ne, domin a cika dukan

abinda aka rubuta.

Ta biyun kuma ita ce IBitrus 4:17:

19
Gama lokaci yayi da shari’a zata faru a kan gidan Allah: Idan kwa

a wajenmu ta faru, ina matuƙar waɗanda basu bi bisharar Allah

ba?

“Gidan Allah” yana nufin dukan ’yan Ikklisiya da Ruhu Mai-Tsarki

ya bari, kuma ya barsu ƙarƙashin mulkin shaiɗan. Ana hukunta su ne

domin sun kauce ainun daga bishara ta gaskiya. Saboda haka suna

ƙarƙashin shari’a. Amma wannan ya banbanta nesa, da ranar shari’a,

watannin nan biyar daga 21 Mayu, 2011 zuwa Octoba 21, 2011. Lokacin

da kowane mutum a dukan faɗin duniya zai karɓi hukunci na ƙarshe

domin zunuban shi. Wannan hukumcin a gaskiya ma ba zai zo kan masu

bi na gaskiya ba, waɗanda za’a fyauce su sadu da Kristi a ranar 21 ga

Mayu, 2011.

Lokacin tsananin, lokaci ne na gwadawa, musamman a majami’u

amma kuma a cikin dukan duniya, lokacin da Allah zai ware alkama

(masu bi na gaskiya) daga ƙaya (waɗanda suke tsammani suna da ceto,

amma a hakikannin gaskiya basu da shi).

Ruya ta Yohanna 3:10 ta bayyana wannan lokacin a matsayin

‘‘Sa’ar jaraba’’, Za a kuma iya fassara kalmar a matsayin ‘‘jaraba’’ ko

“Jarabawa” mun koyi abubuwa da yawa game da gwaji, wanda Allah ya

sa domin ya zama shaida a shakaru na ƙarshe. Sun ƙunshi koyaswa mai

muhimmanci da tambayoyi kamar haka:

1. Ko Ikklisiya zata iya nuna wa wani yadda zai sami ceto?

2. Ko mun gane cewa a wannan lokaci Allah yana bayyana

waɗansu sababbin bayanai da yawa daga Littafi Mai-

Tsarki?

3. Ko mun fahimci cewa kowace kalma ta harshen Littafi

Mai-Tsarki ta ainihi ta fito ne daga bakin Allah?

4. Littafi Mai-Tsarki baki ɗaya dokar Allah ne zuwa ga ’yan

adam, kuma zai kawo hukunci idan ba a kiyayye shi ba.

5. Zamanin Ikkilisiya ya ƙare a 1988, saboda haka babu

wanda zai sami ceto muddin yana ƙarƙashin ikon

Ikkilisiya A hakikanin gaskiya ma, Allah ya sa shaiɗan a

Ikklisiyai yayi mulki a wurin. Saboda haka Allah ya umurci

waɗanda suke son yiwa Allah biyayya su fito daga

Ikklisiya.

6. Dukan zamanin Ikkilisiya, nufin Allah ne da cewa masu bi

na gaskiya zasu yi tunanin cewa Kristi zai dawo kamar

ɓarawo da dare. Amma yanzu ya kamata masu bi na

gaskiya su san ainihin rana, da wata, da shekarar

zuwansa. Wannan ya basu damar fadakar da duniya da

aminci, game da ƙarshen zamani. Idan mutane suka ci

gaba da cewa zai dawo kamar ɓarawo da dare, zai sa su ci

20
gaba da bin tafarkin da zai kaisu ga hallakar da zata abko

masu farat ɗaya. (Tassalunikawa I 5:1-4).

7. Dukan zamanin Ikkilisiya, Allah ya ƙyale aka ci gaba da

tunani irin na al’ada wanda a cikin kuskure dangane da

shirin shari’ar Allah. Amma yanzu Allah yana ƙara bamu

haske game da gaskiyar shirin shari’ar Allah. Filin gwajin

ne kuma, shin muna ƙaunar makiyanmu da gaskiya?

8. Ana gwada dukan duniya, da shike ana faɗakar da su

game da ƙarshen duniya mai zuwa, zasu ci gaba da musu

kamar yadda aka yi a duniya a zamanin Nuhu, ko kuma

waɗansu za su ji wannan faɗakarwar kamar yadda

mutanen Nineveh suka yi lokacin da Yunana ya gargaɗe

su game da halaka mai zuwa?

Allah ya faɗa a cikin Ruya ta Yohanna 3:10 cewa zai tsare masu

bi na gaskiya daga lokacin gwaji. Ga masu bi na gaskiya waɗanda suke

da sha’awar yin biyayya da dokokin Allah. Jarabawar da aka lissafta a

sama ba gwaji ba ne domin masu bin suna da niyyar yin biyayya. Amma

ga marasa bi dake cikin Ikklisiyai da kuma duniya, ya kamata kowanne

ɗaya daga cikin waɗannan jarabobi da gwaji su faɗakar da su cewa idan

sun ƙi yin biyayya suna cikin haɗarin gaske da matsala gaban Allah.

Abin alajibi, kwanaki 6,100 na ƙarshe daga cikin kwanaki 8,400

na tsanani lokaci ne da ake ceton ɗumbin mutane da babu wanda zai iya

ƙirgawa.

Duk da haka, ya kamata mu koma kan bincike domin fahimtar

ainihin tsarin shari’a na Allah. Zamu yi bincike mai zurfi a kan matsayin

Allah na Alkalin dukan duniya a Sura ta gaba.

21
Sura Ta Uku

Allah, Alƙalin Dukan Duniya

A cikin wannan binciken, muna ƙoƙarin sanin ainihin shirin

hukuncin Allah domin wannan duniyar. Tilas ne shirin hukuncin ya haɗa

da Alkali. Alƙalin Allah ne da kansa. Nan da nan a cikin zukatanmu zamu

iya ganin hoton alƙali da wanda ake tuhuma a gaban sa. Alkali yakan

saurara ya kuma yi nazari a kan shaida daga bakin shaidu da dama da

kuma wanda ake tuhuma domin sanin ko wanda ake tuhuma ya aikata

laifin ko babu, sannan ya yanke hukuncin da ya dace idan aka same shi

da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Haka ake ganin tsarin sharia yake a cikin Littafi Mai-Tsarki. A

wannan tunannin, Alkalin shine Kristi. Waɗanda ake tuhumar kuma sune

dukan waɗanda basu sami ceto ba. Lokacin shine ƙarshen duniya.

Hukuncin zai kasance zaunawa cikin matsananciyar azaba a wani wuri da

ake kira Jahannama.

Yanzu muna koyo cewa wannan ra’ayi na al’ada bashi da

makama. Yayinda aka amince da wannan ra’ayi dukan zamanin Ikklisiya,

an kafa shi ne a kan abinda mutum ya fahimta da hukunci maimakon

gaskiyar Littafi Mai-Tsarki.

Bisa adalci ga waɗanda ke riƙe da wannan ra’ayi, za mu iya gane

cewa sun fahimci haka ne bisa ga yadda Allah ya rubuta Littafi Mai-

Tsarki. Mun koyi cewa ba nufin Allah bane ya yi cikakken bayani game

da shirinsa na ƙarshen duniya, sai duniyar ta kusan ƙarshe. Saboda haka

da yake mun zo lokacin da duniya zata kawo ga ƙarshe, mun san ainihin

ƙarshin lokacin. Haka kuma yanzu ne Allah yake yin cikakken bayyani

game da shirin sa na sharia. Saboda haka a wannan lokaci da Allah yake

buɗe idanunmu, mu san gaskiyar Littafi Mai -Tsarki da ba a taɓa

bayyanawa ba a lokutan baya, Ya kamata mu koyi abin da Littafi Mai-

Tsarki ya ke koyarwa game da aikin Alkali.

A cikin littafin Alƙalawa dake Tsohon Alkawari, mun koya game

da ayyukan alƙalai kamar su Joshua, Gideon, Jephthan, Samson da

sauransu. Mun tarar cewa maƙasudin aikinsu shi ne hallaka maƙiyan

Isra’ila. Watau hakinsu ne tanadar wa al’umma, salama da zaman lafiya.

A cikin Sama’ila ta fari sura 8:20 mun karanta cewa Isra’ila ta roƙi

sarki.

Domin mu zama kamar dukan al’ummai; Sarkin mu shi hukunta

mana shari’a, shi wuce a gaban mu, shi ɗauke mana yaƙoƙinmu.

Daga kuma Alkalawa 2:16 Allah yace:

Sai Ubangiji ya tayas masu da mahukunta, waɗanda suka ce ce su

daga hannun masu washe su

22
Za mu iya ganin wannan a furuci kamar haka:

Zabura 7:8 Ya Ubangiji kai ne alƙalin dukan mutane. Ka

shari’anta mani bisa adalci na...

Zabura 7:11 Allah alƙali ne mai-adalci.

Zabura 9:19: Ka zo ya Ubangiji kada ka bari mutane su gagare

ka!

Zabura 26:1: Ka hurta rashin laifina, ya Ubangiji, Gama na yi abin

da suke daidai: Na dogara gare ka gaba ɗaya.

Zabura 72:1- 4 Ka koya wa sarki a yi shari’a da adalcinka, ya

Allah, ka kuma ba shi shari’arka, don ya yi mulkin jama’arka bisa

kan shari’a, ya kuma bi da mulki da adalci... ya yiwa talakawa

shari’ar gaskiya, ya taimaki waɗanda suke da bukata, ya kuma

hukumta azzalumai.

Zabura 103:6 Ubangiji yana gudanar da ayyuka masu adalci da

hukunci ga dukan waɗanda a ke zalumtarsu.

Romawa 14:10-11…gama dukan mu zamu tsaya a gaban

kursiyin sharia na Allah. Gama an rubuta bisa ga raina in ji

Ubangiji a gareni kowace gwiwa zata durƙusa. Kowane harshe

kuma za ya yabi Allah.

Korinthiyawa II 5:10: Gama dukan mu zamu bayyana a gaban

dakalin shari’a ta Kristi.

Ruya ta Yohanna 20:12: Na ga mattatu kuma, ƙanana da manya,

suna tsaye a gaban kursiyin; aka buɗe littatafai, aka buɗe wani

littafi kuma, littafin rai, ke nan aka yi ma mattatu shari’a kuma

bisa ga abin da aka rubuta cikin littatafai gwargwadon

ayyukansu.

Mun koya daga waɗannan ayoyin cewa alkalin yana da haƙƙin

mulki ko shugabancin, ya kuma ƙunshi tabbatar da laifi ko kuma rashin

laifi yayin shari’a. Muna koyon cewa Allah, a matsayin alkalin dukan

duniya, ya bada dokar Allah, Littafi Mai-Tsarki ɗungum, domin yin

wannan aiki na samun mutane da laifi da kuma yanke masu hukumcin

shiga jahannama. (Nan gaba zamu koyi cewa Jahannama ita ce mutuwa.)

Amma dai ya kamata a sani cewa yayinda Allah yake mulkin

duniya kowanne mai rai a duk tsawon rayuwar sa yana tsayawa a gaban

Allah a matsayin Alƙalin duniya. Allah ne yake kare matalauci, da

23
maraya, bisa ga ruhaniya, ta wurin kalmarsa kuma yana sauko da

hukumci duk lokacin da aka aikata zunubi. Yayin da Allah yake mulki a

matsayin alƙali bisan dukan duniya, Yana ɗaukar matakai da dama

domin cimma burinsa na sarauta. Ga waɗansu misalai kamar haka:

1. Allah ya hukunta zaɓɓabu kafin kafuwar duniya. Ya ɗora

hukumcin su a kan Kristi wanda yake ɗan ragon da aka

yanka tun kafawar duniya (Ruya ta Yohanna 13:8).

2. Allah ya rubuta dokar Allah (Littafi Mai-Tsarki), wanda ya

danganta da Allah kansa (Kalmar ta zama jiki (Yohanna

1:14) ta haka ya ba kalmar Allah iko daidai da Allah

domin kalmar Allah ta zartas da hukunci.

3. Ya kafa dokar da ta bayyana cewa Yesu Kristi shine

babban Firis wanda ya miƙa Dan Ragon, kuma shine Ɗan

Ragon da aka yi hadaya da shi.

4. Ya tabbatar da gaskiyar nan mai-ban mamaki cewa kunya

da la’ana da Yesu Ɗan Rago na Allah ya jimre, yayin da

ya biya bashin zunuban zaɓaɓɓu, za a ganta a fuskar

dukan mutanen duniya. Allah ya rubuta duk waɗannan

abubuwan a cikin littafi Mai-Tsarki domin dukan duniya

su karanta.

5. Ya umurta cewa sakamakon biyayyar masu bi na gaskiya

musamman kamar yadda aka nuna tashin mattatu,

hukumci ne kan marasa ceto, musamman waɗanda suke

da Littafi Mai-Tsarki.

6. Yana sauke sarakuna, ya kuma tada sarakuna.

7. Yana mulki a kan dukan al’amuran mutane.

8. Shi yake kafa lokaci na tarihi, ya kuma tabbatar da

cikaken tsarin shari’a.

9. Babu wani abu da yake faruwa, a ko’ina cikin duniya a

kowanne lokaci na tarihin duniya ba tare da sani ko

izininsa ba.

10. Za mu koyi cewa dukan ayyukan Kristi a matsayin alƙalin

dukan duniya a ranar shari’a shine ya kai dukan masu bi

na gaskiya zuwa cikin sama lafiya, ya kuma ƙarasa

hukuncinsa a bisa marasa bada gaskiya na duniya.

11. A matsayin alƙali da mai-mulkin duniya, ya ba shaiɗan

waɗansu ayyuka na mulki ya kuma bashi ikon shiga sama

lokacin shekaru 11,000 na tarihi. Kristi ya kuma kori

shaiɗan daga sama ya ƙwace ayyukansa na mulki da

dama, yayi nasara bisansa a kan giciye.

12. Allah ya kuma kafa shaiɗan a cikin Ikklisiyai domin yayi

mulki a kan kowacce Ikklisiya a cikin kwanakin nan 8,400

na babban tsanani da kuma kwanaki 153 na ranar shari’a.

24
Hakika, a matsayin Allah na alkali da mai-mulki, aikinsa ya wuce

kasancewa alƙalin mutane da aikinsa yake neman mai-laifi ko mai-

gaskiya.

Tsarin Shari’a Na Allah.

Yanzu da yake mun koya game da ayyukan da dama da aka sa

ƙarƙashin Allah a matsayin Sarki, a matsayin mai iko bisansu da kuma

alkalin dukan duniya, yanzu sai mu yi tunani a kan hukuncin da Allah ya

yanke a kan zunubi. Mun koya daga cikin Littafi Mai-Tsarki da cewa

akwai manyan fannoni guda biyar na wannan hukumcin Mai-tsanani.

Suna nan kamar haka:

1. Mutuwar “Rai a cikin Kristi”. An halicci ɗan adam da rai a cikin

Kristi wanda muke kira rai na ruhaniya. Da wannan rai na

ruhaniya ne aka hallice Adamu da duk ’yan adam. Sai dai an

ba ɗan adam sharaɗi. Idan suka yi zunubi, zasu rasa

wannan rai su kuma zama mattatu cikin ruhaniya. Irin

wannan ran ne muke da shi lokacin da Allah ya bamu sabon

rai rayayye, sai dai, a wannan lokacin ana kiransa rai na har

abada domin an shafe duk zunuban mu da jinin Kristi.

Amma lokacin da Adamu yayi rashin biyayya, ya zama

matacce cikin ruhu. Yanzu bashi da sauran rai a cikin Kristi.

Shi da sauran mutanen da suka fito daga zuriyarsa sun zama

mattatu cikin ruhaniya, mattatu cikin kura-kurai da zunubi.

2. Mutuwa ta jiki da ruhu, da muke kira mutuwa ta jiki.

3. Babban kunya.

4. Asarar gado na mulkin Allah, da zamu zauna tare da Kristi

har abada.

5. Hallaka da ta bada lamunci cewa wanda aka hukunta ba zai

sake rayuwa ba ko ta jiki ko ta ruhaniya.

A Ruyata Yohanna 20:11-13 karanta:

Na ga kuma babban farin kursiyi, da wanda ke zaune a bisansa

wanda duniya da sama suka guje ma fuskata: ba a kwa samu

masu wuri ba. Na ga mattatu kuma ƙanana da manya, suna tsaye

a gaban kursiyin, aka buɗe littatafai aka buɗe wani littafi kuma

littafin rai ke nan, aka yi wa mattatu shari’a kuma bisa ga abinda

aka rubuta cikin littatafai gwargwadon ayyukansu. Teku kuma ya

bada matattun da ke cikinsa, mutuwa da hades kuma suka bada

mattatun da ke cikinsu, aka yi masu shari’a kuma kowane mutum

gwargadon ayyukansa.

25
Wannan shine hoton (hoto mai kusurwa uku), waɗanda ba

zaɓaɓɓu ba (waɗanda Allah bai yi niyar ceto ba), tsayawa a gaban Allah.

Akwai farin kursiyi wanda ya nuna Allah ne kaɗai mai-mulki, alƙalin

dukan duniya. Allah ne kaɗai wanda zai iya zaunawa (yana mulki) a kan

kursiyi, wanda a matsayin mai- mulki mafi ɗaukaka zai kawo ƙarshen

duniya, wanda daga sama da ƙasa zasu shuɗe daga fuskarsa.

Mattatu suna tsaye a wurin, a gaban Allah. Kowane bil’adama,

duk tsawon rayuwarsa, yana tsaye a gaban Allah. A wannan karon,

dukan waɗanda suke matattu cikin ruhaniya tun daga lokacin da suke

cikin Adamu (a cikin Adamu duka matattu ne, I Korintiyawa 15:22).

Wannan yana nufin ko da shike suna raye na ɗan ƙaramin lokaci, basu da

rai a cikin Kristi daga lokacin da aka haife su. Su mattatu ne cikin

ruhaniya. A wannan hoton muna ganin littatafai a buɗe waɗanda suke

ɗauke da bayanan zunubansu. Ana yankewa waɗannan mutanen

hukumci duk lokacin da suka yi zunubi, domin Allah yana amfani da

dokarsa da aka yi amfani da ita, wanda shine Littafi Mai-Tsarki wajen

zartar da hukumci. Ana yi masu shari’a da dokar Allah duk lokacin da

suke aikata zunuban da aka rubuta a cikin waɗannan littatafai.

Akwai kuma littafin rai. Sunayensu ba su cikin littafin rai. Saboda

haka ba nufin Allah bane ya cece su. Dukansu suna ƙarƙashin hukuncin

mutuwa, daga ƙarshe kuma zai bayyana a fili cewa ba zasu sake rayuwa

ba da yake za a jefa su cikin ƙorama ta wuta. A cikin Ruya ta Yohana 20:

a aya ta 12 da 13 wannan kalmar “An hukuntasu” tana koya mana cewa

ana ci gaba da hukumta su. Saboda haka wannan ayar ta 13 tana koya

cewa a wannan hoton, waɗanda basu da ceton da suka riga suka mutu

suna cikin kabari, suna ƙarƙashin hukumcin Allah da yake Maganar Allah

ta kashe su. A matsayin matakin ƙarshe na ci gaba da shari’a Allah a

ranar shari’a, za’a fitar da su daga kaburbura domin kumyatarwa ta

ƙarshe, za a kuma hallaka su har abada.

A cikin Ruya ta Yohanna 20:13, mun karanta game da waɗanda

suke cikin teku. Ya yiwu ana magana ne a kan waɗanda suka mutu cikin

ruhaniya da suke da rai ake kuma misaltawa da iskar teku. (Ishaya

57:20; Yahuda 13), ko kuma zai iya kasancewa waɗanda suka hallaka a

cikin teku, kamar waɗanda suka hallaka a ruwan tsufana a zamanin

Nuhu. Bugu da ƙari, waɗanda suka mutu suna jahannama ko kuma suka

mutu suna kabari (wato waɗanda har yanzu suke raye amma mattatu ne

a ruhaniya, tare da waɗanda suka rigaya suka mutu kuma an binne su),

za’a kawo su zuwa kunya ta ƙarshe a gaban Allah ranar shari’a.

Daga ƙarshe, za a jefa mutuwa da jahannama ko kuma mutuwa

da kabari a cikin ƙorama ta wuta. Mun karanta a cikin IKorintiyawa

15:16 cewa:

Mutuwa ce maƙiyi na ƙarshe da za a kawas.

26
Nan gaba za mu koyi cewa ana kiran mutuwa ta biyu ƙorama ta

wuta, kuma tana jaddada cewa marasa ceto ba zasu sake farfaɗowa ba

ko kuma su rayu. Sun daina rayuwa.

Mene ne Jahannama?

Kalmar da aka fi dangantakawa da shari’ar Allah kan masu

zunubi itace kalmar “Jahannama” mene ne zamu koya game da wannan

kalmar a Littafi Mai-Tsarki? Za a iya samunta fiye da sau 30 a cikin

Tsohon Alkawari kuma a ko da yaushe kalmar Ibraniyanci ce “Sheol” An

kuma fassara kalmar nan ‘‘sheol’’ fiye da sau 30 a matsayin kalmar nan

‘‘kabari’’, sau uku a matsayin kalmar nan ‘‘rami’’.

A cikin Sabon Alkawari, ana fassara kalmar nan “hades” ta

Helenanci a matsayin ‘‘Jahannama’’ wani lokaci kuma za a iya fassara ta

da ‘‘kabari’’, Banda haka kuma, waɗansu lokatai kalmar ‘‘jahannama’’

tana fitowa ne daga kalmar Helenanci ‘‘gehenna’’ wadda ta sami asali

daga kalmar Helenanci ‘‘tartaroo’’

Za a iya fassara kalmar Ibraniyanci “sheol” da kalmar Helenanci

“hades” a matsayin ‘‘jahannama’’ ko ‘‘kabari’’ bisa ga abinda ake

magana a kai. Waɗansu lokatai fassarar ta danganta kan abinda ake

magana akai, wanda yake nuna dangantakar kalmomin nan “kabari” da

‘‘jahannama’’. Dukan kalmomin biyu suna da dangantaka da mutuwa.

Za mu fi ganewa da haka inda muka karanta cewa “Hakkin zunubi

mutuwa ne” (Romawa 6:23) da kuma “wanda yayi zunubi shi za ya

mutu”. (Ezekiel 18:20). Ya goyi bayan abinda ke cikin I Korinthiyawa

15:26 “Maƙiyi na ƙarshe da za’a kawas mutuwa ne” ya kuma sa aka

fahimci Ruyata Yohanna 21:1 inda muka karanta cewa:

Na ga sabuwar sama da sabuwar duniya kuma: gama sama ta

fari da duniya ta fari sun shuɗe; teku kuma ba shi

Sau da dama ana amfani da wannan kalmar ‘‘teku’’, a cikin Littafi

Mai-Tsarki a matsayin hoto ko kuma a bayyana ‘‘jahannama’’. Misali,

Aladun nan 2,000 da miyagun ruhohin suka shiga cikin su sun hallaka a

cikin teku (Markus 5:13). Babu sauran mutuwa ko jahannama idan shirin

Allah na shari’a ya ƙare. Mutuwa da jahannama zasu shuɗe.

Ya kamata mu gane cewa jahannama da kabari abu guda ne. Da

yake kabari yana da alaƙa da mutuwa. Wannan ya kawo mu ga tambaya

ta gaba: Mene ne ƙorama ta wuta?

Ƙorama ta Wuta

An ambaci ƙorama ta wuta a cikin ayoyi biyar na Littafi Mai-

Tsarki. Ayoyin sune:

27
Ruya ta Yohanna 19:20 Aka kama bisan tare da shi kuma mai -

ƙaryar annabci wanda ya kan aika alamu a gabansa, irin da ya

kan ruɗi masu karɓan shaidar bisan, da waɗanda ke sujada ga

gumkinsa: ake jefa su biyu da rai cikin ƙorama ta wuta mai ci da

kibiritu.

Ruya ta Yohanna 20:10 Ibilis kuma da ya ruɗe su, aka jefas da shi

cikin ƙorama ta wuta da kibiritu, inda su bisan da mai ƙaryan

annabci suke kuma, za a wulakance su dare da rana har zuwa

zamanin zamunnai

Ruya ta Yohanna 20:14-15 kuma aka jefas da mutuwa da hades

cikin ƙorama ta wuta, mutuwa ta biyu ke nan, watau ƙorama ta

wuta. Kuma wanda aka iske ba a rubuta shi cikin littafin rai ba,

aka jefas da shi cikin ƙorama ta wuta.

Ruya ta Yohanna 21:8: Amma ga matsorata, da marasa

bangaskiya, da masu ƙazamta, da masu kisan kai, da fasikai da

masu sihiri da masu bautan gumaka, da dukan maƙaryata,

rabonsu yana cikin ƙorama mai ƙonewa da wuta da kibiritu,

mutuwa ta biyu ke nan.

Abu mai muhimmancin shine, Ruya ta Yohanna 20:4 ta nuna

cewa an jefas da mutuwa da hades (ko kuma mutuwa da kabari) cikin

ƙorama ta wuta. Zaka iya tunawa mun koya a I Korintiyawa 15:16 cewa

“Maƙiyi na ƙarshe da za a hallaka shine mutuwa. Amma mun koya a cikin

waɗannan ayoyin cewa an jefas da mutuwa cikin ƙorama ta wuta, wadda

ake kira mutuwa ta biyu (Ruyata Yohanna 20:14) Banda haka kuma mun

koya daga Ruya ta Yohanna 21:1 cewa idan aka kafa sabuwar sama da

sabuwar duniya, teku (hades da mutuwa) ba za su kasance ba. Saboda

haka ƙorama ta wuta tana nuna ƙarshe kwata kwata.

Nan gaba a cikin wannan bincike, zamu koyi cewa Ubangiji Yesu

Kristi ya mutu sau biyu dangane da aikin ceton. Ya mutu kafin kafuwar

duniya a matsayin Ɗan Rago da aka yanka (Ruyata Yohanna 13:8). Ya

kuma mutu lokacin da yake kan giciye, ya nuna mana da kuma duniya

yadda ya biya bashin zunuban mu. Ninka hukumcin sa ya yi daidai da

tsarin da ke shifiɗe a cikin farawa 41:31 watau abinda aka ninka sau

biyu tabbatacen abu ne daga Allah.

Haka kuma, Allah yayi Magana game da yin hukuncin sau biyu a

kan waɗanda basu da ceto a cikin Irimiya 17:18 da Ruya ta Yohanna 18:6

inda muka karanta:

Ku saka mata kamar yadda ta bayas, ku saka mata gwargwadon

ayyukanta, riɓi biyu: cikin ƙoƙo wanda ta dama, ku dama mata so

biyu.

28
Allah ya nuna a cikin Ruya ta Yohanna 18:8.

Domin wannan fa rana ɗaya alobanta za su zo, mutuwa, da kewa

da yunwa, za’a ƙone ta sarai da wuta; gama Ubangiji Allah maiƙarfi

ne wanda ya shari’anta mata.

Allah yana koya mana a cikin wannan aya cewa a rana ɗaya,

wadda zata kasance ranar shari’a, za a yi mutuwa da fari, za a ƙona ta

da wuta. Konawa da wuta yayi daidai da abinda ke cikin II Bitrus 3:10

inda muka karanta cewa:

Amma ranar Ubangiji kamar ɓarawo zata zo; a cikinta fa,

sammai zasu shuɗe tare da ƙara mai-girma, rundunan kuma

zasu narke da ƙuna mai zafi, duniya kuwa da ayukan da ke

cikinta zasu ƙone.

Ƙonawa da wuta wadda ta kasance mutuwa ta biyu, ta danganta

mutuwa ta biyu da ƙorama ta wuta. Wannan ne lokaci na ƙarshe da ta

tabbatar da cewa ba za a sake samun wata damar rayuwa ba. Ya

danganta da kalmar nan ta helenanci “gehenna” da ake samu jefi-jefi a

cikin Littafi Mai-Tsarki wanda aka fassara da kalmar “jahannama”. Misali,

mun karanta a cikin Markus 9:43-44 cewa:

Kuma idan hanunka ya sa ka kayi tuntuɓe, ka yanke shi, gwamma

a gareka ka shiga cikin rai ɗungum da ka tafi jahannama da

hannunka biyu, cikin wuta wadda bata bituwa. Wurin da tsutsar

su bata mutuwa ba, kuma wuta bata bituwa ba.

Wutar da bata bituwa ita ce ƙorama mai-ƙonewa. Ambaton wuta

a cikin Littafi Mai-Tsarki ya na daidai da abinda aka faɗa a cikin

Ibraniyawa 12:29 inda aka kira Allah “wuta mai cinyewa” idan wutar Allah

ta cinye mutum, wannan mutum ba zai sake rayuwa ba.

Nan gaba zamu koya cewa wannan kalmar “tsutsarsu bata

mutuwa” wannan kalmar tsutsa tana da dangantaka da kunya. Cewa ba

kawai tana nufin kumyatar da waɗanda basu da ceto ta wajen yanke

masu hukumcin mutuwa ba, kuma ba mawuyacin abu bane share

wannan kunya. Haka nan wannan kalmar “wutar bata bituwa” ya nuna

cewa ba zai sake rayuwa ba.

Tilas ne mu tuna cewa a cikin Adamu, an halicci ɗan adam duka

domin ya rayu har abada, ko da yake akwai sharaɗi. Duk da haka,

saboda zunubi, ‘yan adam suka zama masu mutuwa. Amma muddin an

halicce shi a kamanin Allah ya rayu har abada, zai yiwu wani lokaci nan

gaba bayan ya biya bashin zunuban sa zai iya rayuwa kuma? amsar ita

ce, a’a! Domin jadada wannan batun Allah yayi Magana game da wutan

jahannama wanda bata bituwa, da hallaka ta har abada, da tsutsa da

29
ata mutuwa, da kuma hayaƙi hayaƙin azabar su da yake hawa sama har

abada. Dukan waɗannan kalmomin suna nuna mutuwa ta biyu ce,

ƙorama mai ƙonewa. Wutar da hallakar da hayaƙin da tsutsar, suna nan

har abada inda babu sauran rai.

Waɗannan kalaman sun nuna cewa hakika babu sauran wata

rayuwa ga waɗanda basu da ceto. Gaskiyar ita ce an rigaya an ƙona su

gaba ɗaya, saboda haka babu wani tunanin cewa zasu sake wata rayuwa.

An jadada bayanin daina rayuwa ta marasa ceto a ayoyi da dama cikin

Littafi Mai-Tsarki. Misali a cikin waɗannan ayoyin.

Nahum 1:6,8 Wanene ya iya tsayawa a gaban haushinsa? Wake da

iko shi daure zafin fushinsa? Hasallarsa tana zuba kamar wuta,

yana fasa ruwa rana tsaka. Amma da rigyawa mai malalawa za ya

sa wurin ya ƙare, sarai za ya ci duddugen maƙiyansa har cikin

dufu.

Malachi 4:1: Gama ga shi rana tana zuwa tana ƙuna kamar

tanderu; dukan masu girman kai, da dukan waɗanda ke aikin

mugunta, zasu zama tattakai ranan dake zuwa kuma zata

ƙoƙƙone su, in ji Ubangiji mai runduna, har ba zata bar masu

tushe ko reshe ba.

Ishaya 10:23: Gama Ubangiji, Yahweh mai-runduna, za ya aika

cikakiyar ƙarewa ƙadararriya ce kuwa, a tsakiyar dukan duniya.

Kalmar Ibraniyanci da aka fassara da ‘‘cikakkiyar ƙarewa’’ an

kuma fassara ta a matsayin ‘‘cinyewa’’ ko ‘‘ƙarshe’’. Mun karanta a cikin

Irimiya 46:28 cewa:

Kada ka ji tsoro ya Yakub, bawana inji Ubangiji, gama ina tare da

kai, gama zan ƙarasa al’umman nan inda na kore ka, sarai

dukansu, amma ba zan ƙarasa ka ba; amma zan yi maka horo da

shari’a, ba kwa zan bar ka ba horo ba.

Har wa yau, an yi amfani da kalmar nan “lalacewa’’ kimanin sau

100 a cikin Tsohon Alkawari da kuma sau 30 a Sabon Alkawari. Kowace

aya tana jaddada ƙarshen rayuwa. Misali: Ayuba 4:20 ta ce:

A tsakanin safiya da yamma a kan farfashe su, sukan lalace har

abada, ba mai kulawa.

Har wa yau, an yi amfani da waɗannan kalmomin “halaka” da

“Hallakarwa” fiye da sau 500 a cikin Littafi Mai-Tsarki.

A wani ɓangaren kuma, ba bu kalmar nan ‘‘azaba’’ a cikin

Tsohon Alkawari, kuma sau 22 aka yi amfani da ita a cikin Sabon

30
Alkawari. Mun gane da cewa yanayin da aka yi amfani da kalmar ya

danganta daga waɗannan.

1. Azabar marasa bi yayin da suke jin bisharar gaskiya (Ruya ta

Yohanna 11:10).

2. Azaba irin ta rashin lafiya (Matta 8:6, Matta 4:24).

3. Azaba ta harbin kunama (Ruyata Yohanna 9:5).

4. Kalmar Helenanci da aka fassarata “Azaba” an kuma fassara

ta da ‘‘ɓacin zuciya’’ ko kuma ‘‘fushi’’, lokacin da Littafi Mai-

Tsarki yayi Magana game da ruhun Lutu mai-adalci da ya

‘‘fusata’’sabili da zunuban Saduma. (Bitrus II 2:8).

5. A helenanci wannan kalmar “azaba” an fassarata “Baƙin ciki”

(Luka 2:48, Ayyukan manzani 20:38).

6. Azaba da wuta (Ruya ta Yohanna 14:10, Luka 16:24).

Mun koyi cewa ƙarshen shari’ar Allah mutuwa ce. Littafi Mai-

Tsarki ya goyi bayan wannan bayanin ta wajen amfani da kalamai kamar

“lalacewa” “hallakarwa”. Za a kuma iya gane cewa an yi amfani da

kalamai kamar, ‘‘mutuwa’’, da ‘‘mutu’’, fiye da sau 1,300 a cikin Littafi

Mai-Tsarki. Ba abin mamaki bane da Littafi Mai-Tsarki ya bayyana da

cewa maƙiyi na ƙarshe da za a hallaka shine mutuwa. (Korintiyawa

15:26)

Mai Arziki Da La’azaru

Yanzu zamu sake nazarin misalin mai-arziki da La’azaru wanda

ke cikin Luka 16. Rashin fahimtar wannan misali ya kawo rashin

fahimtar tsarin shari’ar Allah.

Misalin yayi bayani a kan mutane biyu. Mai-arziki yana da duk

abin jin daɗi da wadata da wannan duniya zata iya kawowa, amma ba shi

da ceto. Matalauci La’azaru baya da waɗannan abubuwan jin daɗi na

wannan duniya amma yana da ceto. Daga ƙarshe dukansu suka mutu,

aka binne mai-arziki shi kuma La’azaru mala’iku suka ɗauke shi zuwa

ƙirjin Ibrahim (Luka 16:22). Kasancewa a ƙirjin Ibrahim hoto ne na

kasancewa a wuri mafi albarka a gaban Allah. A binne kuma shine a sa

mutum a kabari.

Misali kuma ya ci gaba da magana tsakanin mai- arzikin da ya

mutu da Ibrahim (Allah) wanda yake cikin sama. Ka tuna mun koya cewa

kabari da mutuwa daidai suke da jahannama. Saboda haka ba kuskure

bane a ce mai arziki yana jahannama (Luka 16:23). Amma tilas ne mu

gane cewa ɗaga idanunsa ya ga la’azaru a ƙirjin ibrahim, ya kuma yi

magana da Ibrahim duka misali ne. Watau, Allah ya shimfiɗa waɗansu

jadawalin tunani ko kuma hotuna masu kusurwai uku, domin ya koya

gaskiyar ruhaniya. Waɗannan gaskiyar sun ƙunshi koyaswa kamar haka:

31
1. Mai-arziki ya roƙi Ibrahim, ya aiki la’azarun da ɗikon ruwa

domin ya sanyaya harshen sa (Luka 16: 24) babu jinƙai ko

alheri ga waɗanda suka mutu ba tare da sun sami ceto ba.

2. Akwai babban rami tsakanin sama da jahannama, sama, rai

na har abada ne, jahannama, mutuwa ce ta har abada babu

yadda waɗanda suka mutu zasu sake rayuwa.

3. Mai-arzikin yana son Ibrahim ya aiki la’azaru zuwa wajen

’yan’uwansa guda biyar domin yana tsammani wannan

mu’ujiza zata sa su zama masu bi. Gaskiyar ita ce, suna da

Musa da sauran annabawa, da kuma Littafi Mai-Tsarki. Idan

ba za su gaskata da Littafi Mai-Tsarki ba ba za su gaskanta

ba ko sun ga manyan mu’ujizai.

4. Mai arzikin yana shan azaba a cikin wuta, An yi amfani da

kalmar Helenanci da aka fasara ta da ‘‘Azaba’’ a aya 24

kawai, a ya 25 (‘‘kana shan azaba’’), a cikin Luka 2:48, da

Ayyukan Manzanni 20;38. kalmar nan ‘‘harshen wuta’’ tana

jadada cewa Allah ne yake hukumta mai-arzikin, wanda shi

wuta ne mai-cinyewa (Ibraniyawa 12:29). Kalmar nan

‘‘azaba’’ wadda, aka bayyana ta wurin amfani da ita a cikin

Ayukan Manzani 20:28 da Luka 2:48, tana nuna yadda azaba

da yake sha ta ke. Saboda haka zamu duba a hankali wannan

kalmar yadda aka yi amfani da su a cikin ayoyin nan biyu.

Ayukan Manzani 20:38, Suna baƙin ciki tun ba ma saboda

maganarsa da ya faɗa ba, cewa ba za ku ƙara ganinsa ba. Daga

nan suka rako shi har bakin jirgi.

Luka 2:48 Sa’anda suka ganshi fa suka yi al’ajibi, uwa tasa kwa ta

ce masa, ɗana, don menene kayi mana haka? Ga ubanka da ni da

baƙin ciki muka neme ka.”

A cikin waɗannan ayoyin, kalmar da aka fasara a matsayin

‘‘azaba’’ a cikin luka 16 an fasara ta da ‘‘baƙin ciki’’. Wannan baƙin cikin

baya da nasaba da ciwon cikin jiki. Baƙin cikin rashin sake ganin

ƙaunatattace ne. Mai-arzikin yana cikin azaba domin yana baƙin ciki ba

zai sake samun murna da jin daɗin da ya samu lokacin da yake raye a

duniya ba; yayinda La’azaru kuma yake nan lafiya da albarku masu girma

har abada abadin.

Watau, wannan misali na mai-arziki da la’azaru bai koya mana

wani abu game da azaba ta har abada a wani wuri da a ke kira

Jahannama ba. Yana koya mana game da hukumcin rasa duk albarkun

wannan rayuwa da rasa duk albarkan rai na har abada. Misali ya taimaka

mana mu fahimci halin da Isuwa ya shiga. Shi ɗan fari ne. Saboda haka

yana da gadon haihuwa da ya ƙunshi ruɓi biyu na gado. Duk da haka ya

32
wulakanta gadonsa na haihuwa ya sayar da shi a bakin ƙwaryar abinci

(Farawa 25:29-34)

A cikin Adamu, duk ’yan Adam suna da ’yancin ɗan fari, gadon

ɗan fari wanda ya ƙumshi rabo biyu na ɗan fari Yesu yayi bayani a

misalin da ya bayar na ɓataccen ɗa. An faɗawa babban ɗan a cikin Luka

15:31 “ɗana tuntuni kana tare da ni, dukan nawa kwa naka ne”. Gadon

haihuwar ya ƙunshi rabo na ɗan fari (kubawar sharia 21:17) “Dukan abin

da nake da shi naka ne” ya ƙunshi rai na har abada kuma magada tare da

Kristi. (Romawa 8:17)

Saboda wannan zunubin da aka misalta da ƙwaryar abinci, mun

rasa gadon haihuwarmu. Mun rasa ’yancin rayuwa cikin Kristi, wadda

take rai na har abada ga cetattu. Mun rasa ’yancin zama magada tare da

Kristi na sabuwar sama da sabuwar duniya. Wannan shine babban

hukumcin da za mu biya sabili da zunuban mu.

Kalmomi ba zasu iya misalta babbar asarar da marar ceto ya yi ba

idan zunubi ya sa ya rasa rai madawwami tare da Kristi, ba kuma zai yi

mulki tare da Kristi har abada ba kuma zai yi gado tare da shi ba a

sabuwar sama da sabuwar duniya. Babu shakka wannan zai kasance

babban ɓangare na azaba da waɗanda suka shiga wata biyar na ƙarshen

duniya zasu fuskanta. Zasu kuma tarar cewa domin an barsu a baya

lokacin fyaucewa, ba za su taɓa samun komi ba na gadon haifuwarsu.

Za a kuma iya kiran baƙin ciki da azaba na mai-arziki a kabari,

Jahannana, ya ƙara mana haske kan babbar azaba (baƙinciki) da zai

kasance tsakanin miliyoyin ’yan Ikklisiya waɗanda suka hakikanta cewa

suna da ceto amma aka barsu a baya lokacin fyaucewa. Ba abin mamaki

bane kamar yadda muke koya yanzu, suna kuka suna cizon haƙora, suna

yiwa Allah saɓo. Mun koyar cewa, babban abinda waɗanda suka gane

cewa sun rasa shiga cikin mulkin Allah har abada, zasu yi shine baƙin

ciki mai tsanani. An kuma koya wannan daga abinda Isuwa ya yi wanda

ya wulakanta gadon haihuwarsa ya sayar wa Yakub domin ƙwaryar

abinci. Mun karanta a cikin Ibraniyawa 12:16-17 cewa:

Kada wani mai-fasikanci ya kasance, ko kuwa wani marar-ibada

kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya kaɗai ya sayar

da gadonsa, na ɗan fari. Gama kun sani, ko da yana marmarin ya

gaji albarkar daga baya, aka ƙi shi, gama ba ya sami zarafin tuba

ba, duk da yake ya nema da naciya da hawaye.

Akwai kimanin mutane biliyan biyu a yau da suke kiran kansu

“Krista” kuma yawancinsu suna da alaƙa da Ikklisiya. Yayin da muke

duba Ikklisiyoyin da suke kewaye da mu, kusan dukan Ikklisiyan sun

kasa gaskatawa da gargaɗin da Littafi Mai-Tsarki yake yi masu game da

ficewa daga Ikklisiya domin Allah ya daina amfani da Ikkilisya wajen kai

Bishara. Har yanzu yawancin su sun gaskanta da cewa Kristi zai dawo

kamar ɓarawo da dare, kuma ba zamu san ainihin ranar ƙarshen zamani

33
a. Yawancin su sun dogara ne a kan bishara ta yi da kanka, kuma basu

gane da gaskiyar cewa Kristi ya yi duk abinda ake bukata domin

cetonmu ba. Yawancin su suna da ra’ayin nan na fahimtar tsarin shari’ar

Allah da ke karkatacciyar koyaswa cewa a rana ta ƙarshe za a yiwa

marasa ceto hukumci su kuma zauna a wani wuri da ake kira jahannama

har abada.

Kimanin ’yan Ikklisiya biliyan biyu zasu gane a ranar 21 ga watan

Mayu, 2011 cewa, an barsu a baya. Littafi Mai-Tsarki ya bayyana cewa

baƙin cikinsu zai kasance kamar baƙin cikin (azaba) na mai-arziki da

muka gani a cikin misalin da muka bincike. Mun karanta a cikin Luka

13:28 cewa:

Can za a yi kuka da cizon haƙora, lokacin da kun ga Ibrahim, da

Ishaku, da Yakub, da dukan annabawa cikin mulkin Allah, ku da

kanku kuwa an fitar da ku waje.

Idan ranar shari’a ta fara ranar 21 ga watan Mayu, 2011, a duk

faɗin duniya, za a canza jikunan miliyoyin masu bi na gaskiya zuwa

jikunan ruhaniya na har abada a kuma fyauce su zuwa sama, a gaban

idanun waɗanda aka bari a baya. Bugu da ƙari, za a buɗe kaburbura a

duk duniya zasu bubbuɗe, za a canza jikunan masu bi na gaskiya a

kuma fyauce su zuwa sama. Wannan ya ƙunshi, jikunan, Ibrahim, Ishaku

da Yakub. ’Yan Ikklisiyar da aka bari a baya za su yi mamakin ganin cewa

suna ƙarƙashin fushin Allah. A cikin tsananin baƙin ciki, zasu yi kuka,

suna kuma cizon haƙora, suna nuna tsananin fushinsu da Allah. Zai

zama wani lokacin baƙin ciki mai-tsanani ga dukan ’yan Ikklisiya.

Allah ya bayyana wannan a cikin ayoyi da dama, misali, Matta

8:11-12, Matta 13:49-50, Matta 13:41-42, Matta 25:30 waɗansu daga

cikin ayoyin nan sun jadada cewa ana kiran wurin inda za a yi kuka da

cizon haƙora. Su jefa su cikin buyar wuta, can za a yi kuka da cizon

haƙora. Wannan yayi dadai da ƙorafin mai-arziki a cikin Luka 16:24. ‘‘...

gama azaba na ke ji (baƙin ciki) a cikin wannan wuta. Ka tuna cewa Allah

wuta ne mai cinyewa (Ibraniyawa 12:29). Kasancewa a ƙarƙashin

fushinsa, kamar shiga cikin wuta mai ci ne.

Ta haka mun koya ta wurin wannan misalin inda aka nuna

mataccen yana Magana da Allah a sama (Ibrahim), an ba mu cikaken

bayani game da illar fushin Allah.

Hukumcin mafi muni mai kunyatarwa kuma da za a yanke a kan

duk wani laifi shine hukuncin kisa. Babu wani ciwo a jiki dake da nasaba

da hukuncin kisa, zai je, amma duk da haka ana ganinshi a matsayin

hukunci mafi tsanani, Mene ne ya sa ya zama haka?

Haka ta faru ne domin an ƙwace ’yancin rayuwa ga mutumin da

aka aiwatar da hukumcin kisa mai kunyatarwa. Zai iya kashe kansa. Zai

iya sadaukar da ransa a fagen yaƙi ko kuma ya hau tsauni. Zai iya biyan

laifin da ya aikata wajen zama a gidan kaso. Amma da zarar ’yan adam

34
sun zartar da hukunci irin na wulakanci a kansa, za a ɗauke ransa, ya

zama wanda ya fuskanci abinda ake bayyanawa a matsayin hukunci maitsanani.

Ba lallai mu iya sanin wannan ba, amma hukuncin kisan da aka

yanke mashi a duniya wani darasi wanda yake nuna yadda hukuncin

Allah zai kasance kan zunubi. A hakikanin gaskiya ma, Allah ya bayyana

a cikin Littafi Mai-Tsarki hukunci kisa mafi ƙanƙanci da aka taɓa tunani.

Wannan hukumcin kisan kuma yana da dangantaka da ceton mu. Babu

shakka muna magana ne a kan mutuwar Mai-albarka Ubangijin mu da

Mai-Ceton mu. Saboda haka ya kamata mu dubi mutuwar sa a hankali

domin ba kawai zamu koyi yadda kumyata ya yi daidai da tsarin

hukumcin Allah daga ciki ba, amma zamu ƙara koyo game da hukunci

da shari’ar Allah bisa zunubi.

35
Sura Ta Huɗu

Yaushe Ne Kristi Ya Mutu?

Bayani na farko mai-ban mamaki da muka koya yayin da muke

bincika a hankali game da abin da Allah ya koya mana a cikin Littafi Mai-

Tsarki akan aikin ceto shine an gama baki ɗaya kafin Allah ya halicci

mutum. Mun karanta a cikin Ruya Ta Yohana 13:8 ‘‘...Ɗan Ragon da yake

yankakke tun kafawar duniya.’’ Mun karanta a cikin Ibraniyawa 4:3 cewa:

Gama mu da muke bada gaskiya muna shiga cikin wannan hutu,

kamar yadda ya ce, yadda na yi rantsuwa cikin fushina, ba za su

shiga cikin hutuna ba, ko da aka gama ayyukan tun kafuwar

duniya.

Mun kuma karanta a cikin matta 25:34 cewa:

Sa’annan shi sarki za ya ce ma waɗannan da ke hannun damansa,

ku zo, ku masu albarka na ubana ku gaji mulkin da an shirya

domin ku tun kafuwar duniya.

Waɗannan ayoyin sun koya mana a fili cewa an gama dukan

ayyukan da ake bukata domin ceton mu tun kafuwar duniya.

Yanzu za mu iya sanin iya fahimtar ayoyin da suka yi magana a

kan shi a matsayin ‘‘Haifaffe shi kaɗai” Haifa na da mafari. Sai dai Kristi

yana nan tun fil-azal(kolosiyawa 1:17) Saboda haka ba shi da farko.

Amma mun karanta a cikin Romawa 1:4 cewa:

Aka aiyana, shi Ɗan Allah da iko, ta wurin Ruhu Mai-Tsaki bisa

ga tashi daga mattattu shi Yesu Kristi Ubangijinmu.

A kolosiyawa 1:18 mun karanta cewa: shi... Haifar fari daga cikin

mattatu.” Bisa ga waɗannan ayoyi, an tashi Kristi daga mattatu.

Bisa ga waɗannan ayoyin, an tashi Kristi daga matattu. Kuma da

yake shine Ɗan Ragon da aka yanka (kashe) tun daga kafawar duniya,

dole ne ya kuma tashi daga matattu tun kafuwar duniya. Za a fahimci

‘‘Daga kafawar’’ a matsayin “kafin kafuwar’’ domin mun karanta a

Ibraniyawa 1:2 cewa:

A ƙarshen waɗannan kwanaki ya yi mana Magana cikin ɗansa

wanda ya sanya magajin abu duka wanda kuma ya yi duniya ta

wurinsa.

Tun da yake tashin Kristi daga mattatu shine aikin ceto na ƙarshe

mun sani yayinda muke karantawa cikin Ibraniwa 1:2, cewa tunda Kristi a

36
matsayin Ɗan ya sa aka aiwatar da aikin ceto kafin halitta. Aikin Allah ne

kammala wannan aikin duka, sai dai tilas ya kasance gaskiya gaba ɗaya

domin Littafi Mai-Tsarki gaskiya ne. Domin haka zamu fahimci ayoyi

kamar haka:

Timottawus 1: 9-10 ta ce: wanda ya cece mu, ya kiraye mu kuma

da kira mai-tsarki, ba gwargwadon ayyukan mu ba, amma bisa

ga nasa nufi, da Alheri, wanda aka bamu cikin Kristi Yesu tun

gaban madawaman zamani, amma yanzu ya bayyana ta wurin

bayyanuwar mai-ceton mu Kristi Yesu wanda ya kawas da

mutuwa, ya haskaka rai da dauwama ta wurin bishara.

Ibraniyawa 1:5 Gama ga wanene daga cikin mala’iku ya taɓa yin

magana ya ce masa, kai ɗana ne yau na haife ka? Da kuma ni

zama uba gareshi, shi kuma za ya zama ɗa a gareni?

Yohanana 1:18 Ba wanda ya taɓa ganin Allah daɗai, haifaffe shi

kaɗai wanda ke cikin ƙirjin uba, shine ya bada labarinsa.

Matta: 3: 17 Ga kwa murya daga cikin sammai ta ce, wannan

ɗana ne ƙamnatacce na, wanda raina, yaji daɗinsa sarai.

Kristi Ya Nuna Abinda Yayi Domin Ya cecemu

Amma, idan Kristi yayi dukan aikin domin ya ceci waɗanda ya

zaɓa ya cece su (zaɓaɓɓu) kafin ya halicci duniya, menene ya sa ya sake

mutuwa a kan giciye? Allah ya amsa wannan tambayar a cikin Luka 3:6

inda Allah yace:

Dukan mai rai kwa zaya ga ceton Allah’

A cikin Bitrus 1, 1:20 ya kara cewa:

wanda aka rigaya saninsa lallai gaban kafuwar duniya, amma a

ƙarshen zamani ya bayyanu sabili da ku.

Bayyana na nufin a gani, a nuna shi, a gwada. Allah yayi tanadi

domin cetonmu, a cikin wani aiki na ƙauna da ya fi ƙarfin fahimtar

mutum. Ya aiko da Yesu wannan duniyar a cikin jiki ya kuma nuna wa

duniya abinda ya riga yayi domin biyan bashin zunuban zaɓɓaɓu.

Kristi ya yi Magana da misalai. Waɗansu lokatai misalan suna

kama da hotuna masu kusurwa uku dake bayyana gaskiyar Littafi Mai-

Tsarki. Ka tuna da wannan hoton na mai-arziki a cikin kabari da ake

kira jahannama, da yake magana da Ibrahim, wanda yake wakiltan Allah.

Yana baƙin ciki domin yayi asarar komi da kuma kasancewa yana

37
fuskantar fushin Allah. Shi kuma La’azaru da yake ƙirjin Ibrahim yana da

komai, wato, rai na har abada. Yana da cikakken kariya kuma magajin

mulki da kristi.

Wannan hoton ƙarami ne idan aka kwatanta shi da hoton rayuwar

Ubangijinmu Yesu kristi inda ya wakilci kansa, A wannan hoton mun

ganshi ya ɗauke jiki irin namu da aka haife shi ta wajen budurwa

Maryamu. Allah ya bayyana wannan a cikin Ibraniyawa 10:4-7 inda muka

karanta cewa:

Gama bashi yiwuwa jinin bajimai da na awaki shi kawas da

zunubai. Domin wannan sa’anda yana shigowa cikin duniya yace,

da hadaya da baiko ba ka so ba, Amma, jiki ka shirya mani;

Hadayu tuli na ƙonawa da na zunubi baka ji daɗin su ba?

Sa’annan na ce gani na zo (cikin littafi an rubuta a kaina) garin in

aika nufinka ya Allah.

Idan ka yarda ka lura da juyawa da aka yi daga hadaya da

bayaswa zuwa kan Yesu da kansa, wanda ya kasance jikin da aka shirya

domin ya nuna abin da ya faru kafin kafuwar duniya.

Saboda haka, lokacin da Yesu ya tafi giciye, bai je wurin domin ya

biya bashin zunubanmu ba. An biya wannan bashin fiye da shekaru

11,000 da suka wuce. Amma a cikin ƙaunarsa mai girma yana shirye ya

sha wahalar fushin Allah a madadin waɗanda ya zo domin ya ceta domin

mu gani da idanun mu (ta wurin Littafi Mai-Tsarki), babban abinda ake

bukata a biya.

Yanzu za mu iya gane dalilin da yasa yace ‘‘Ya Ubana, idan zai

yiwu ka ɗauke min wanan ƙoƙo, ba nawa nufin ba amma bari na ka nufin

shi kasance”( matta 26:35), ya kuma yi tambaya cewa: ‘‘ya Allahna ya

Allahna don me ka yasheni?’’ (Matta 27:46). Shari’ar Allah bata bukatar

biyan bashin cettatu sau biyu. Wannan ƙari ne wanda bashi da anfani,

wani muhimmin aikin da Allah ya yi. Allah ya rigaya ya shirya haka. Musa

(dokar Allah) ya buga dutsen (Kristi) sau biyu, (Littafin Lissafi 20:11)

bayan bugu ɗaya kawai ake bukata ya kawo ruwa. (Fitowa 17:6) Ishaya

40:2 tana cewa:

Kuyi Magana mai kwantad da rai ga Urushalima, kuyi mata kira,

yaƙinta ya ƙare, an gafarta laifinta gama daga hannun Ubangiji ta

karɓi alhakin dukan zunubanta riɓi biyu.

Yanzu mun gama cewa Kristi ya sha wahala sau ɗaya domin

zunubanmu, kuma ya sha wahala ta biyu domin ya nuna mana yadda ya

biya bashin zunubanmu. Yanzu za mu iya gane dalilin da ya sa Bilatus,

mai mulki na Roma ya yi ta maimaitawa akai, akai cewa ‘‘ban same shi

da wani laifi ba ( Luka 23:4-22, Yohanna 19:4-6 da kuma Matta 27:4-

24). Kristi ya tsaya a gabansa marar laifi ko kaɗan. Amma duk da haka

38
tilas a hukumta shi kamar wanda har yanzu yake ɗauke da zunuban

waɗanda aka kiraye su zuwa ga ceto domin ya nuna yadda ya sha

wahala sabili da waɗannan zunuban. Abin mamaki shi ne babban firist

ɗin ne ya yankewa Yesu hukumci. Matta 20:18 ta ce:

Gashi zamu Urushalima, kuma za a ba da Ɗan Mutun ga hannun

manyan malamai da marubuta, zasu hukunta masa mutuwa.

Yahanna 11:50-51 ta ce:

Ba ku lura kuma yana da amfani a gare ku mutun da ya mutu

saboda jama’a kada al’umma duka ta lalace wannan batu fa ya

faɗa ba bisa kansa ba amma domin shi baban malami ne

shekaran nan yayi annabci Yesu zaya mutu saboda al’umman.

kuma a cikin Yohanna 19:17 mun karata cewa:

Yahudawa suka amsa suka ce masa muna da doka bisa ga

wannan doka kwa ya kamata shi mutu domin ya maida kansa

Ɗan Allah.

A ko ina cikin Littafi Mai-Tsarki babban Limami misalin Yesu ne

babban Limami. Hakin babban Limami ne ya yanka rago.

Saboda haka Bilatus gwamna ne, wanda yake da ikon yankewa

Yesu hukuncin kisa domin ya farantawa Yahudawa rai, ya bada umarni

cewa a kashe Yesu ta hanyar giciyewa. Giciyewa bisa ga dukan alamu, ita

ce hanyar kisa mafi kunyatarwa da mutum ya shirya. Mun koyi

muhimman darussa guda uku game da giciye Yesu. Da waɗannan:

1. Kunya, da la’ana da azaba da Kristi ya daure don zunuban

mu.

2. Kunya da la’ana da tilas za a ɗora bisa waɗanda ba a cece su

ba da kuma ƙarin azaba da za’a jimre ga waɗanda zasu shiga

da rai ranar sharia.

3. Abin mamaki na gafara na dab da ƙarshe.

Lokacin da aka giciye Kristi, ya zama abin nuni ga jama’a na

mutumin da yake ƙalƙashin la’anar Allah. Domin mu gane

muhimmancin la’ana, bari mu dubi itacen ɓauren nan da Yesu ya la’anta

(Markus 11:14). An la’anta itacen ɓauren da yake wakiltar al’umar Isra’ila

duk zamanin Tsohon Alkawari lokacin da Kristi ya ce “kada kowa ya ci

‘ya’ya daga wurinka, nan gaba har abada.’’ Saboda haka la’anar itacen

ɓauren yana koya mana cewa an hallaka al’umar Isra’ila har abada, ba

kuma za a sake amfani da ita ba a matsayin hanyar samun albarka ta

ruhaniya.

39
Kazalika, yayin da aka la’anta ’yan adam domin zunubansu ya

nuna cewa dole ne a yi masu cikakken hukunci yadda dokar Allah ta

tanada, hukuncin da ƙarshen sa shine hallaka ta har abada. Mun karanta

a cikin Kubawar shari’a 28:20 cewa:

Ubangiji za ya aiko maka da la’ana da damuwa da tsautawa, cikin

dukan abinda ka ke sa hannu gareshi, har ka hallaka, ka lalace da

sauri, saboda muguntar ayyukanka inda ka yashe ni.

Daɗin daɗawa, mun karanta a cikin Kubawar sharia 28:45 cewa:

Kuma dukan waɗannan la’anoni zasu aike maka har ka hallaka

domin ba ka lura da muryar Ubangiji Allahnka ba, da zaka kiyaye

dokokinsa da farillansa waɗanda ya umurce ka da su.

Wannan la’anar ce aka ɗorawa Yesu lokacin da aka biya bashin

zunuban mu kafin kafuwar duniya: daga baya ya nuna wannan la’anar

lokacin da aka rataye shi a kan giciye kamar yadda Galatiyawa 3:13 ta ce

Kristi ya fanshe mu daga la’anar shari’a da ya zama la’ana

maimakon mu gama an rubuta kowanne wanda an rataye shi ga

itace la’ananne ne.

Saboda haka, za mu iya sani yayin da muke duban Yesu a kan

giciye ƙarƙashin la’anar Allah, wannan yana nufin duk wanda ba shi da

ceto, zai ƙarasa da hallaka ta har abada.

Bari mu duba a hankali, munin kallon giciye Yesu. Kamar yadda

muka faɗa aiwatar da hukumcin kisa ta wurin giciye ita ce hanya mafi

tsanani da rashin imani, cike da ƙeta, marar kyaun gani wadda kuma ta

fi kunyatarwa da ake ƙwace ’yancin mutum na rayuwa daga gareshi.

Akwai zafin ƙusoshin da aka buga ta hannuwa da ƙafafunsa. Akwai

kunyar ƙwace wa mutum tufafi a giciye shi tsirara, Akwai batun zama

abin kallo ga jama’a, inda jama’a masu yawa ’yan kasar sa, da kowanne

mutum a duniya zasu ga kumyatarsa. Akwai kuma gaskiyar nan cewa

zai shafe sa’oi da yawa yana daure baƙaƙen maganganu da ba’a daga

waɗanda suke so su kashe shi. Alal hakika babu wani hukumcin kisa da

yafi na giciye kunyatarwa.

Idan muka dubi Golgotha inda aka giciye Yesu, mun ga giciye

guda uku. Guda biyu daga cikinsu mutane ne da suka aikata laifi

waɗanda aka aiwatarwa hukumcin kisa ta wannan hanyar kunyatarwa. A

tsakaninsu, a kan giciye na uku, aka giciye dukan wanda Yesu ya zo

domin ya ceta. A’a ba wai muna wurin da kanmu bane. Mai-Cetonmu,

Ubangiji Yesu Kristi ne yake rataye a wurin yana nuna mana cewa, shine

ya tsaya a madadinmu. Wannan ce mutuwar da dama zamu jimre sabili

40
da zunubanmu. Littafi Mai-Tsarki ya bayyana a fili cikin Galatiyawa 2:20

cewa “An giciye ni tare da Kristi”.

An lisafta Yesu tare da masu zunubi (Ishaya 53:12, Markus

15:28). Nufin Allah ne ya nuna mana a fili shirinsa na shari’a. Da farko,

ka tuna cewa a giciye yana nufin la’anar Allah. Duk abinda ya faru a

Golgota inda giciyen suke yana cike da la’anar Allah a kanmu inda za a

iya hallaka mu har abada. Muna gani a fili mutuwa mafi ban kunya da za

mu iya tsammani. Masu laifin guda biyu da suke wakiltar dukan

mutanen duniya, suna dab da ɗanɗana hukuncin da doka ta ayyana.

“Gama hakkin zunubi mutuwa ce” (Romawa 6:23) Suna ƙarƙashin la’anar

doka. Doka ta yanke masu hukumcin kisa mai kunyatarwa da mutuwar

la’ana. Dubban mutane suna mutuwa ta hanyoyi dabam dabam, amma

babu wadda ta fi kunyatarwa kamar mutuwar giciye. Idan sun mutu, ba

zasu sake rayuwa ba. Saboda haka zasu yi asarar gado na rai na har

abada da kuma gadon sabuwar sama da sabuwar duniya. Sun biya

babban bashin daɗin da suka ji, tun da suka aikata zunubi a wannan

rayuwar.

Mun koyi cewa babban hukuncin zunubi shine asarar farin ciki da

albarkun wannan rayuwa da kuma gadon mulkin Allah, wanda ya ƙunshi

rai madawami da gadon sabuwar sama da sabuwar duniya. Gaskiya ne

waɗanda suka mutu kafin tashin mattatu ba su san wannan ba. Amma

gaskiya ce kamar yadda misalin mai arziki da la’azaru yake koyarwa a

Luka 16. Lokacin da mai arzikin ya ga La’azaru a ƙirjin Ibrahim, wanda

yake jan idannunmu na ruhaniya zuwa ga madawamin gadon mai-bi,

ya kwatanta wannan da rayuwar azaba da yake ciki inda ba zai ƙara jin

daɗin rayuwar da ya yi a lokutan baya ba, ba kuma zai sami wannan

farin ciki da murna na gadon ruhaniya ba. Hakika yana baƙin cikin gaske

domin wannan fushin Allah.

Kamar yadda muka koya, sanin wannan babbar asarar gadon

shine abin da zai faru da biliyoyin mutanen da za su shiga ranar shari’a a

wata biyar na ƙarshen zamani. Yayin da suke raye, zasu ga masu bi na

gaskiya lokacin da ake fyauce su zuwa ɗaukaka, su kuma zasu ci gaba

da zama a duniya a cikin mummunan kwarin nan na mutuwa. Wannan ya

tabbatar da cewa zunubi ya ƙunshi asarar gado. Kasancewa waɗansu sun

mutu ba tare da sanin cewa zasu yi asarar gadonsu ba, bai sake gaskiyar

cewa sun rasa gadon nan nasu mai daraja sabili da zunubansu a

matsayin hukunci ba.

Ya Ƙare

Hoto mai kusurwa uku da ake da shi wanda ya nuna yadda Yesu

ya ɗauke fushin Allah sabili da zunubanmu ya ƙare lokacin da Yesu yace

“Ya Ƙare”. Babbar azaba ce Kristi ya sha karo na biyu. Sai dai a lokaci na

biyu ba wai ƙoƙari yake yi ya biya bashin zunubanmu ba.

41
Amma domin ya nuna mana da kuma masu mulki da ikoki yadda ya sha

wahala kafin kafawar duniya domin ya biya cikakken bashin.

Sa’oi uku da aka yi na duhu, kafin Kristi ya ce ‘‘Ya Allah na, Ya

Allahna don me ka yashe ni?” ya ƙunshi hakikanin gaskiyar cewa, a

farkon zamani, Kristi ya biya cikakkken bashin zunuban mu, ya mutu ya

kuma sake tashi. An bayyana wannan gaskiya a fili cikin Zabura 16:10.

‘‘Gama ba zaka bar raina ga lahira ba” Lahira mutuwa ce. Saboda haka

kafin a kammala biyan bashin zunuban mu, dole ne Kristi ya tashi daga

mattatu. Shi ya sa daga wancan lokacin Kristi zai zama za a kira shi Ɗan

Allah kamar yadda muka karanta a Romawa 1:4. lokacin da yayi kuka a

kan giciye yace: “Ya Kare” wannan yana nufin an cika wannan hoto mai

kusurwa uku, da ya bayyana azabar Kristi ya ƙare.

Amma, kuma kafin yace ya ƙare, akwai wata gwadawa. Ita ce abin

ban mamakin na sa’oin nan uku lokacin da Allah ya juyawa Kristi baya.

Sa’oin nan uku na baƙin duhu ya nuna mummunar azabar da Kristi ya

jimre.

Sai dai, Allah ya tanada wani hoto domin ya nuna a fili gaskiyar

cewa ya mutu kuma an tashe shi daga matattu, hoto ne mai kusurwa

biyu. Kashi na farko ya nuna kaburburan da aka bubbuɗe. Bayan tashin

Yesu daga mattatu ranar lahadi da safe, jikuna da dama sun fito daga

kabarbaru suka shiga birni mai-tsarki. (Matta 27:51-53) Wannan birnin

mai- tsarki zai zama sama ne domin lokacin da labulen haikali ya tsage,

lokacin da Kristi yake kan giciye haikalin ya daina kasancewa wuri maitsarki.

Saboda haka Urushalima ta daina kasancewa birni mai-tsarki

Sabuwar Urushalima ce birni mai-tsarki, ita ce birnin samaniya. Saboda

haka jikunan nan da aka tada daga matattu alama ce ta fyaucewa. Amma

kamar yadda Allah ya sha nanatawa a IKorintiyawa 15, da ba a tashi

Kristi daga mattatu ba, da ba za a tashi kowa daga mattatu ba. Saboda

haka tashin waɗannan jikuna daga matattu ranar lahadi da safe, ya nuna

cewa babu shakka Kristi ya tashi daga mattatu.

Amma akwai kuma wani ɓangaren hoton, da aka bayar domin a

tabbatar da cewa babu shakka Kristi ya tashi daga mattatu. A cikin

ruhunsa Kristi, ya tafi sama, jikinsa ba tare da ruhunsa ba aka sa a

kabari. Yayin da yake cikin kabari, jikinsa bai ga ruɓa ba. Ba zai ga ruɓa

ba domin idan ya ruɓe, zai nuna cewa aikin da Kristi yayi, domin biyan

bashin zunuban zaɓɓaɓu tun kafin kafuwar duniya, bai ƙare gaba ɗaya

ba. Saboda haka tashin Kristi daga mattatu zai zama misali kawai.

Gaskiyar ita ce, lokacin da aka sa jikinsa a cikin kabari, a cikin

rayuwar ruhunsa, yana sama. Saboda haka a wannan hoton, Allah ya

nuna misalin fyaucewa ta wurin tashin ainihin jikinsa daga kabari, da

kuma ainihin jikunan da suka tashi wanda aka buɗe lokacin da labulen

haikali ya tsage.

Amma kafin mu bar wannan hoton na wahalar da kunya da

la’anar masu laifi da Kristi ya sha, ya kamata mu dubi waɗansu

ɓangarorin gwadawar.

42
Gafara Mai Ban Al’ajibi

Idan za’a hukunta mai laifi sabili da laifinsa, za a iya zartar masa

da hukuncin wulakanci na kisa. Babu wani begen yafe hukuncin kisa sai

ko da cikakken umurnin shugaba. A ƙasashe da dama na duniya har da

Amurka, mai mulki mafi girma yana da ikon gafartawa mai-laifin da aka

zartarwa hukuncin kisa. Saboda haka, kafin aiwatar da hukumcin

‘yan’uwan mai-laifin za su yi duk ƙoƙarinsu domin ya sami wannan

gafaran don a ceto shi daga wannan mutuwar wulakanci da kunya da

aka shirya dominsa. Babu shakka, wani lokaci akan yafewa mai laifi ana

dab da lokacin da za’a aiwatar da hukuncin kisan.

Allah ya tanada irin wannan gafara ga duk waɗanda ya zo domin

ya ceta. An bayyana wannan da yau a cikin littafin Ishaya 54:7-8 inda

Allah yace:

Don lokaci ƙanƙani na yashe ki, amma da jinƙai mai-girma zan

dawo da ke. A cikin hasala mai-zafi na ɓoye maki fuskata ɗan

lokaci kaɗan amma da madauwamin alheri zan yi maki jinƙai in ji

Ubangiji mai-fansar ki.

Kuma a Ishaya 55:7-8

Mai mugunta shi sake hanya tasa, mara adalci kuma shi bar

tunaninsa, shi komo wurin Ubangiji shi kwa zaya ji ƙansa wurin

Allahnmu, gama zaya yi gafara a yalwace. Gama kamar yadda

sammai suna nisa da duniya, haka nan kuma al’amura na sun fi

naku tsawo, tunani na kuma ya fi naku, in ji Ubangiji.

A daidai kusan ƙarshen zamani, ɗaya daga cikin ɓarayin da aka

giciye su tare da Kristi, ya ji kalmar nan ta alheri daga leɓen Yesu “yau

kana tare da ni a firadais” (Luka 23:43). Ina misalin al’ajibin! Wannan

ranar da a wurinsa ta kasance ranar mutuwar ta ƙasƙanci na mai-laifin ta

ƙarasa da shiga gida cikin daraja na Ɗan Allah. Wannan gafarar ce

kowanne zaɓɓaɓe na Allah yake samu.

43
Sura Ta Biyar

Shirin Hukuncin Allah

Yanzu da shike jinƙan Allah ya sa muna iya ganewa a fili shirin

hukuncin Allah da kuma tsarin tarihi, za mu yi ƙoƙari mu bayyana ta

iyaka iyawa. Tilas ne mu tabbatar da cewa duk itifaƙin da zamu yi ya zo

ne daga Littafi Mai-Tsarki. Suna kuma muwafaka da duk abin da ake

koyarwa a Littafi Mai-Tsarki.

A cikin shekara ta 11,013 BC Yesu Kristi, a matsayinsa na Ɗan

Allah ya hallicci duniya, domin Littafi Mai-Tsarki ya gaya mana cewa Ɗan

mahalicci ne, za mu iya sani cewa mutuwar Yesu a matsayin Ɗan Rago,

tun daga kafuwar duniya ya faru ne kafin hallitta. Ya halicci iyayen mu na

farko Adamu da Hauwa’u a cikin kamanin Allah da surarsa su yi mulkin

halittu. Su cikakku ne ta kowane fanni. Su da zuriyar su a matsayin

’ya’yan Allah kuma za su zauna tare da Allah har abada a cikin ɗaukaka

mafi girma da farin ciki. An halicce su da jiki, da lumfashin rai, da kuma

ruhu.

Allah ya fara basu dokokin da zasu yi rayuwa a cikin farin cikin

mafi girma, ya kuma fara gwada amincin su ga Allah, doka ta fari da aka

basu ita ce idan suka yiwa Allah rashin biyaya zasu mutu (Farawa 2:17).

Allah mafi sanin abu duka ne, wanda ya san cikakken bayani

game da dukan abu. Allah ya sani cewa ba da daɗewa ba, bayan halittar

ɗan adam zai yi masa rashin biyayya saboda haka tun kafin lokacin Allah

yayi tanadi domin zuriyar ’yan adam da zasu fito daga iyayen mu na fari,

Adamu da Hauwa’u, domin a cece su daga mutuwa hakkin zunubi, da

dokar Allah ta tanada.

A yayin gudanar da wannan shirin na ceto, za a ɗaukaka Allah da

kansa yayin da za a bayyana a fili halayensa na Allahntaka wanda basu

misaltuwa. Za a bayyana su ba ga mutum kaɗai ba, amma ga dukan

mulki da ikoki da ba mu san komai akai ba, amma suna nan da rai sabili

da ƙoƙarin Allah duk zamanai (Afisawa 3:10-11). Mun karanta cikin

IITassalonikawa 1:10 cewa:

Sa’anda ya zo garin a ɗaukaka shi cikin tsarkakansa a yi al’ajibi

da shi cikin dukan masu bada gaskiya cikin waccan rana (da shi

ke aka gaskata shaidarmu gareku).

Jim kaɗan bayan an halicce su cikkaku mutane, iyayen mu na

farko, (wanda a tsasonsu dukan ’yan adam suka wanzu), suka yi wa Allah

rashin biyayya, saboda haka su da dukan ’yan adam, da zasu zo daga

garesu, da ya kamata a yankewa hukuncin kisa nan take a matsayin

biyan bashin zunubansu. Amma da yake Allah ya rigaya ya biya bashin

zunuban da dama daga cikin zuriyar Adamu da Hauwa’u, mutuwa ta jiki

ba zata faru nan take ba. Zasu kasance da rai har lokacin da suka haifi

44
’ya’ya. Waɗannan ’ya’yan su ma zasu yi tsawon rai har su kai ga lokacin

da zasu haifi ’ya’ya da sauransu. Har sai an haifi dukan waɗanda Allah ya

zaɓa ya kuma ceto daga hukuncin mutuwa sakamakon zunubi. Da shike

ba za a haifi da dama daga cikin waɗanda aka zaɓa domin a cece su

daga zunubai ba sai kusan ƙarshen shekaru 13,000 bayan hallitta,

duniya za ta ci gaba daga wancan lokacin.

Saboda haka gaskiya ne cewa iyayenmu na farko, da kuma dukan

bil’adama da suka fito daga jikunansu, sun mutu da shike ba mu da

sauran rai a cikin Kristi wanda muke kira rai na ruhaniya. Kuma mun

karɓi hukuncin mutuwa ta jiki lokacin da Adamu da Hauwa’u suka yi

zunubi. Amma Allah ya tanada cewa mutane zasu kasance a raye suna

da ruhu na wani lokaci daga lokacin ɗaukar ciki zuwa bayan shekaru 900

na rayuwa ta jiki. Amma a cikin ruhaniya dukan su matattu ne. Rai cikin

Kristi wanda ya zama rai na har abada yayin da aka ceci zaɓaɓɓen, baya

cikin rayuwar waɗanda ba a cece su ba. Illar zunubi da ya shiga cikin

’yan adam lokacin da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi ya bi kan duk

zuriyarsu. Zunubi yana mulki a cikin jikinsu da kuma ruhaniya.

Littafi Mai-Tsarki ya nace cewa ’yan adam sun mutu cikin

zunubi. Shaidar wannan mutuwa ta ruhaniya shine babu mutumin da bai

taɓa aikata zunubi ba sai Yesu kaɗai. (Romawa 5:12, II Korintiyawa 5:21,

I Bitrus 2:22). Kowanne zunubi yana sa hukumcin mutuwa ta jiki da aka

zartas a kan mai zunubi ya fita fili.

Muna amfani da kalmomin nan “mutuwa ta ruhaniya” yayin da

muke magana akan wanda basu da ceto; Littafi Mai-Tsarki ya ambace su

da cewa sun “mutu cikin zunubi” (Afisawa 2:5, Kolosiyawa 2:13) An raba

su da rai a cikin Allah ta jiki da kuma ruhaniya, wanda shine rai na

ruhaniya da suke da shi daga farko kafin Adamu yayi zunubi. Ka iya

tunawa duk ’yan adam daga tsatson Adamu suka fito, saboda haka

lokacin da yayi zunubi, dukan mu muka yi zunubi (Korintiyawa I 15:22).

Ko da shike an yanke su daga rai cikin Allah, zasu ci gaba da rayuwa ta

jiki (rayuwa da sanin abinda ke faruwa kewaye da su), a cikin jiki da

kuma ruhu. Rayuwa ta jiki ta kan zo ƙarshe lokacin da mutum ya mutu,

kuma idan ba ya da ceto, cikin jiki da kuma ruhaniya, zai yi mutuwa ta

har abada. Tilas ne a ba mutum sabon ruhu da sabon jiki kafin ya sami

rai cikin Kristi ko rai na har abada.

An bada wannan ran cikin Kristi ga kowane mutum da Allah ya

zaɓa domin ya sami ceto. Ana ba da shi ga mutumin da aka zaɓa yayin

da Allah ya yi amfani da Maganar Allah a rayuwar mutumin. A daidai

lokacin za a maye tsohon jiki da ruhun mutumin da sabon rayayyen

ruhu madauwami wanda ba zai so ya sake aikata zunubi ba (IYohanna

3:9). Zai ci gaba da rayuwa a cikin mattacen jikinsa na ruhaniya amma

yana da tabbacin cewa a lokacin fyaucewa, za a sake mattacen jikinsa na

ruhaniya nan da nan zuwa rai na har abada a cikin jikin Kristi

(Tassalonikawa I 4:13-17, Korintiyawa 15:51-52).

45
Zaɓaɓɓen mutum wanda ya ɗanɗana ko kuma bai riga ya

ɗanɗana albarkan tashin mattatu na ruhu ba, da waɗanda ba zaɓɓaɓu ba

da suke da rai da kuma ruhu dake aiki, an koyar da su ta wurin Littafi

Mai-Tsarki abubuwa da yawa game da halin zunubin da suke cikin da

kuma game da halayen Allah na ɗaukaka. Muna zaune a duniya mai kyau

wadda take cike da tsirai da dabbobi da dai sauransu. waɗanda Allah ya

halitta ya kuma nuna girman ikon halittarsa.

Bugu da ƙari, ta wurin Littafi Mai-Tsarki Allah ya ba ’yan adam

dukan cikakken bayanan shirin jinƙan sa na ceton waɗanda ya zaɓa

zuwa ceto. Yanzu Allah yana nuna abubuwa filla filla wanda ya bayyana

shirinsa shekarun ƙarshen da ranakun ƙarshe na tarihi, domin muna

rayuwa ne dab da ƙarshen zamani. A cikin littafi “Mun kusa Kai Ga

Ƙarshe” mun tsara bisa ga Littafi Mai-Tsarki, daidai tsarin kowane abin

da zai faru a ƙarshen zamani.

Mun koyi cewa taron Ikklisiya ne wakilan mulkin Allah a cikin

dukan duniya na tsawon shekaru 1, 955 (AD 33 zuwa 1988 AD) daga

nan kuma ranar 21 ga watan Mayu, 1988, Allah ya gama da shirin sa na

ceto ya kuma fara shirya Ikklisiyai da duniya domin abubuwan da zasu

faru a ƙarshen zamani.

A wannan rana Allah ya sa shaiɗan a cikin dukan majami’u kuma

ya yarda masa ya yi mulki a cikin majami’un dukan duniya. Har wa yau,

Allah ya yadda da majami’u game da batun ceto. Ya fara ba waɗanda

suka rage a cikin majami’u ɓatar basira domin su gaskanta ƙarya (II

Tassalonikawa 2:11). Bugu da ƙari, an rufewa masu bi na gaskiya baki a

cikin majami’u, da shike an kore su ko kuma sun yi biyayya da dokar

Allah da su fito daga cikin su.

Waɗannan sune waɗansu daga cikin hanyoyin da Allah ya fara

amfani da su a cikin majami’u yayin da yake shirya mutane a cikin

majami’u domin su karɓi hukumcin Allah. Littafi Mai-Tsarki yayi gargaɗi

a cikin IBitrus 4:17 cewa “za a fara shari’a ta kan jama’ar Allah.”

Haka kuma, fara daga ranar 21 ga watan Mayu, 1988 an ba

shaiɗan ’yanci mai -yawa domin ya taimaka wa zunubi ya yawaita ba a

majami’u ba kawai amma har da sauran duniya. Mun karanta a cikin

Ruya ta Yohanna 13:7 cewa:

Aka yarda masa kuma shi yi yaƙi da tsarkaka, shi yi nasara da

su, aka ba shi kuma hukunci bisa kowace kabila da al’umma da

kowane harshe da iri.

A gaskiya, ranar 21 ga watan Mayu, 1988 shine mafarin wani abu

mai muhimmancin da zai faru a ƙarshen zamani na tsowon shekaru 23

cur, (kwanaki 8,400) , wanda zai kai ga ƙarshe ranar 21 ga watan Mayu,

2011. Littafi Mai-Tsarki ya kira wannan kwanaki 8,400 lokacin “babban

tsanani (Dubi shafi ....na wannan bincike).

46
Waɗannan kwanaki 8,400 na babban tsanani wanda muke rayuwa a ciki,

lokaci ne da Allah ya ke shirya majami’u a duk faɗin duniya da kuma

duniya kanta domin ƙarshen zamani.

Cikin kwanaki 2,300 na farko, (21 ga watan Mayu, 1988 zuwa

Satumba 7, 1994), kusan babu wanda ya sami ceto. Amma da yake akwai

zaɓaɓɓu da dama da Allah bai cecesu ba tukuna, ranar 7 ga watan

Satumba, 1994, Allah ya fara wani babban shirin ceto inda zai ceci

dukan zaɓaɓɓun ɗaya-ɗaya (Matta 24:22). An kawo wannan girbin masu

bada gaskiyan ne gaba ɗaya daga wajen majami’u. Zai ci gaba na tsawon

kwanaki 6,100 sauran kwanakin 8,400, na lokacin ƙunci, A cikin

kwanakin nan 6,100 majami’u da duniya suna ƙara dulmaya cikin

zunubi yayinda Allah ya ke ci gaba da shirya waɗanda ba zaɓaɓɓu ba

zuwa ceto zuwa ƙarshen su.

Sa’annan ranar 21 ga watan Mayu, 2011 shirin ceton Allah ga

duniya zai kawo ga ƙarshe ba shiri. Dukan waɗanda suka zama masu bi

na gaskiya a cikin shekaru 13,000 da suka shige, da suka mutu za a tada

jikunan su daga matattu a matsayin jikuna masu ɗaukaka na ruhaniya.

Za a ɗauke su (fyaucewa) a gaban idon dukan waɗanda basu bada

gaskiya ba kuma suna duniya a lokacin. Za a kuma canza dukan masu bi

na gaskiya da suke da rai a lokacin a fyauce su zuwa sama su zauna

tare da Kristi har abada abadin. Suma za a fyauce su a fuskar waɗanda

ba su bada gaskiya ba. Haka kuma ƙasusuwa, ko kuma abinda ya rage a

kabarbaru, ko cikin teku, ko ina da aka binne marasa ceto, zasu tashi (za

a fid da su daga wuraren da aka binne su) za su kasance ko ina a cikin

duniya suna shiri domin hallaka gaba ɗaya a ranar 21 ga watan Octoba,

2011, lokacin da za a hallaka duniya baki ɗaya da wuta (|Dubi shafi na....

zuwa... na wannan bincike). Banda haka kuma, hallaka gawarsu shine

abin kunya na ƙarshe da zasu fuskanta a gaban Allah maɗaukaki da

kuma ikoki na sama.

Lamarin da duniya take ciki zai yi muni ainun fara daga ranar 21

ga watan Mayu, 2011 ya kuma ci gaba na tsawon kwanaki 153. Littafi

Mai-Tsarki yace za’a yi kuka da cizon haƙora (Matta 8:11-12; 13:42,

Luka 13:28). Babu sauran wata damar ceto. Saboda haka babu jinƙai.

Littafi Mai-Tsarki ya bayyana wannan lokacin filla filla (Kubawar Sharia

28:16-68, Ruya ta Yohanna 9:1-2), da ya ke bayyana illar nukiliya ko

kuma wani abu da ya yi daidai da abinda yake biyo bayan ɓarnar

nukiliya. Ko da mene ne, za a ga mace mace ko’ina.

Sa’annan rana ta ƙarshe ta duniya zata zo. Mun karanta a cikin

IIBitrus 3:10...

A cikinta fa sammai zasu shuɗe tare da ƙara mai girma da ƙuna

mai zafi, duniya kwa da ayyukan da ke cikin ta zasu ƙone.

Littafi Mai-Tsarki ya gaya mana cewa a ƙarshe za a jefa mutuwa

da jahannama cikin ƙorama ta wuta (Ruya Ta Yohanna 20:14). Daɗin

47
daɗawa, Allah ya bayyana yadda ƙarshen wannan duniya zai kasance, ya

kuma nunawa ’yan adam game da madauwamiyar ɗaukakar da ta ke

jiran waɗanda Allah ya ceta. A wannan lokacin kuma, ta wurin Littafi

Mai-Tsarki Allah ya bayyayana ƙarshen mutuwa da zata afkowa kowane

mutum da Allah bai yi shirin ceta ba daga mutuwar da dole zata sauko

kan su domin zunubi

Yayinda Allah yake koya mana a fili game da shirin ceto na Allah,

mun koya daga Littafi Mai-Tsarki cewa za a iya raba mutanen duniya

ƙungiya ƙungiya. Waɗannan ƙungiyoyin suna nan kamar haka:

1. Waɗanda ba zaɓaɓɓu ba, wato, waɗanda ba a zaɓe su domin

a cece su ba, ba kuma zasu taɓa samun ceto ba, suka mutu

kafin ranar sharia.

2. Waɗanda suke zaɓaɓɓu, waɗanda tilas Allah ya cece su

domin an zaɓe su domin a cecesu, waɗanda suke da rai,

amma har yanzu ba a cece su ba.

3. Waɗanda zaɓaɓɓu ne, kuma suna da ceto kuma a yanzu

haka suna da rai a duniya.

4. Waɗanda ba zaɓaɓɓu ba, kuma ba su mutu ba.

5. Waɗanda zaɓaɓɓu ne kuma sun mutu.

Waɗanda Ba Zaɓaɓɓu Bane Waɗanda Suka Mutu Kafin Ranar Shari’a

Allah bai zaɓi mutane masu ɗinbin yawa ba domin samun ceto,

kafin kafawar duniya. Allah ne kaɗai ya san ko su wanene. Su ka yi

rayuwa a duniyar nan na wani lokaci sa’annan suka mutu. Sun mutu ba

tare da sanin cewa mutuwar su aiwatar da hukumcin kisan ne abin

kunya a idon Allah da kuma mulki da ikoki ba. Duk lokacin da suka yi

zunubi suna kunyatar da Allah suna kuma ƙara cusa kansu ƙarƙashin

la’anar Allah.

Bugu da ƙari, lokacin da suka mutu, ya yiwu suna baƙin ciki cewa

ba za su iya sake cin moriyar abubuwan jin daɗi na wannan duniya ba.

Sai dai, idan suka mutu sakamakon wani haɗari ko kuma a cikin

barcinsu, ba su ma ɗanɗana asararsu ba. Ba su san cewa mutuwarsu

tana nufin cewa hakika bashi yiwuwa su taɓa samun gagarumin gadon

da zai zama na su domin an haliccesu su zama ’ya’yan Allah ba. Da yake

kowanne mutum yana cikin Adamu, iyayen mu na farko, lokacin da aka

halicce shi, an halicce mu da ’yancin gadonsa na ɗan fari. Wannan

’yancin haihuwar ya ƙunshi gadon rai madauwami. Amma yana da

sharaɗi. Yana daidai da halin da Isuwa ya shiga. Da Isuwa bai yi zunubi

ba ta wurin watsi da gadon haihuwarsa, wanda ya zama nasa kasancewa

shine ɗan fari da aka haifa da ya ci gaba da zama nasa. Da Adamu da

Hauwa’u ba su yi zunubi ba, da sun ci gaba da riƙe gadonsu na haihuwa

har abada. Wato da ba za a taɓa fitar da su daga mulkin Allah ba. Kamar

Isuwa waɗanda suka mutu ba tare da sun sami ceto ba, sun sayar da

48
gadon haihuwarsu domin ƙwaryar abinci. Za mu iya duban ƙwaryar

abincin nan a matsayin misalin tukwici na nan take da zunubi ke

kawowa. Ya rigaya ya fara da zunubin Adamu.

Saboda haka ko da shike waɗannan mutane sun mutu ba tare da

sanin gagarumin bashin da suka biya sabili da zunubansu ba, bai sake

gaskiyar cewa sun biya bashin ba. Wannan hukumcin shine asarar gadon

haihuwarsu, wato mulkin Allah. Wannan ya nuna a fili girman jinƙan

Allah.

Sai dai, ko da shike sun mutu, kuma ba zasu ƙara sanin abinda

ke faruwa ba, Allah bai gama da su ba tukuna. Za a tashi Ƙasusuwansu,

ko abinda ya rage na mattatun jikunansu daga wurin da aka binne su

ranar 21 ga watan Mayu, 2011, ranar fyaucewa, wadda ta kasance ranar

Shari’a ta farko. Za a watsa gawarsu kamar shara ko kuma taki a ƙasa,

yadda za su kumyata ta wajen ƙazabta su da Angulaye, da karnuka, da

tsutsa da sauransu zasu yi. Karon ƙarshe, za a kumyatar da su a idon

Allah da mulki da kuma ikoki.

Daga ƙarshe, a ranar 21 ga watan Oktoba, 2011, ranar Shari’a ta

ƙarshe, za a ƙone jikunansu tare da ƙasa, da dukan duniya da wuta a

hallaka su har abada.

Zaɓaɓɓu Waɗanda Ba A Cece Su Ba Tukuna

Akwai mutane da suke duniyar nan waɗanda aka zaɓa, amma har

yanzu basu sami ceto ba. An biya bashin wannan ruƙunin mutanen

domin su zaɓaɓɓu ne na Allah, Kristi shine kuma Ragon da aka yanka

tun kafuwar duniya, an biya bashin zunuban wannan ruƙunin mutanen,

tun kafin a haife su. Saboda haka Allah ba zai hallaka su ba. Har yanzu

su mattatu ne cikin ruhaniya, amma a jiki suna da rai da ruhu dake aiki,

kamar yanayin da waɗanda ba zaɓaɓɓu na Allah ba suke ciki waɗanda

kuma daga ƙarshe za’a hallakasu har abada.

Amma da yake an rufe zunuban dukan zaɓɓaɓu ta wurin

mutuwar Yesu, dole ne Allah ya cece su (dole ya gafarta masu), kafin su

mutu cikin jiki ko kuma kafin ranar fyaucewa da zata auku ranar 21 ga

watan Mayu, 2011. A daidai lokacin da suka sami ceto zasu shiga

ruƙunin mutanen da aka ceta, waɗanda za a fyauce zuwa wurin Allah a

ranar 21 ga watan Mayu, 2011.

Waɗanda Aka Ceta Kuma Yanzu Haka Suna Nan Zaune A Wannan

Duniyar

Wannan ruƙunin mutane ya ci gaba da girma domin Allah yana

ceton ɗumbin mutane da ba wanda zai iya ƙirgawa. An rigaya an ba su

sabon ruhu rayayye, madauwami. Idan suka mutu kafin 21 ga Mayu,

2011, a cikin madauwamin ransu rayayye, nan take kuma za su yi mulki

a sama tare da Kristi. Ranar 21 ga watan Mayu, 2011, mattatun

49
jikunansu zasu fito daga kaburbura a matsayin madauwamin jiki na

ruhaniya, za a kuma fyauce jikunansu su kasance tare da Kristi. Saboda

haka duk zasu zauna cikkakun mutane cikin jiki da ruhu da zai rayu ya

kuma yi mulki tare da Kristi har abada.

Idan har yanzu suna da rai a ranar 21 ga watan Mayu, 2011, nan

take za a basu sabon jiki madauwami mai rai. Za a kuma fyauce su su

zauna tare da Kristi har abada.

Waɗanda Ba Zaɓaɓɓu Ba Da Suke Da Rai Har Ranar 21 Ga Mayu, 2011

Wannan ruƙunin mutanen da ke da yawan gaske, yaji gargaɗi

cewa ƙarshen duniya ya kusa. Amma ba su maida hankali a kai ba. Basu

maida hankali a kai ba domin basu gaskanta cewa Littafi Mai-Tsarki

Maganar Allah ba ne. Ko kuma basu kasa kunne a kan gargaɗin ba

domin sun amince da koyaswar Ikklisiyarsu cewa Kristi zai zo kamar

ɓarawo da dare, saboda haka ba su bukatar kula da koyarwar da suka

hakikanta cewa karkatacciyar koyarwa ce game da dawowar Kristi. Ko

kuma sabili da ƙaunar wannan duniya da suke yi, ba su maida hankali ga

gargaɗin ba domin basu son duniyar su ta ƙare.

Fiye da shekaru 1,900, Littafi Mai-Tsarki ya koya cewa Kristi zai

zo kamar ɓarawo da dare, kuma bai zo ba. Saboda haka mutane da yawa

suna tunani cewa ba zai zo ya kawo ƙarshen duniyan nan ba, nan da

shekaru 100 ko fi. Saboda haka zasu iya tabbacin cewa za su ci gaba da

jin daɗin wannan duniya duk tsawon rayuwarsu. Amma idan aka bada

ainihin ranar, ranar da ta rage ’yan shekaru kaɗan kawai nan gaba,

wannan ba abu mai karɓuwa ba ne gare su. Saboda haka ba su son su ji

bayanin da muka samu daga Littafi Mai-Tsarki.

A matsayin ƙarin hukucin ga mutanen da suka ji gargaɗin amma

suka ƙi biyayya da shi, wannan ruƙunin mutanen, zasu shiga da ransu

watannin nan biyar matsananta da ake kira ranar sharia da zata fara da

fyaucewar masu bi na gaskiya a ranar 21 ga watan Mayu, 2011.

Za su ga ana fyauce mutane yayin da aka bar su a baya. Za su yi kuka da

cizon haƙoransu ga Allah a cikin fushi. Daɗin daɗawa, zasu sha azaba

mai-tsanani na tsawon watanni biyar, sabili da annobar da zata fara da

babbar girgizan ƙasa a rana ta farko. Idan suka mutu a cikin watannin

nan biyar, ya yiwu kuma da dama su mutu, jikunansu zasu bazu a ko’ina

a ƙasa. Daga ƙarshe, ranar 21 ga watan Octoba, 2011, za a ƙona dukan

duniya har da ƙasa da dukan ayyukan da ke cikinta, ba zasu sake rayuwa

ba.

Tashin Matattun Da Ba Su Da Ceto

Mun koyi cewa idan wanda ba zaɓaɓɓe ba ya mutu, ya mutu cikin

jiki da kuma ruhu. Kuma ba zai sake rayuwa ba. Babu wani wuri a cikin

Littafi Mai-Tsarki da aka bayyana cewa marasa ceto da suka mutu za su

50
sake rayuwa. Amma akwai ayoyi kima da suka nuna cewa za su sake

rayuwa domin su ƙara ɗanɗana fushin Allah. Mu dubi waɗannan ayoyin a

hankali, za mu koyi cewa waɗannan ayoyi sun nuna mana yadda kunyar

da take kan waɗanda basu da ceto zata ci gaba har zuwa rana ta ƙarshe

na wannan duniyar. Mu karanta a cikin Ayyukan Manzanni 24:15 cewa:

Ina da bege ga Allah, abin da waɗannan da kansu kuma suna

sauraronsa, za a yi tashin mattatu na masu adalci da na marasa

adalci.

Mun kuma karanta a cikin Yohanna 5:28-29 cewa:

Kada ku yi mamakin wannan; gama sa’a tana zuwa, inda dukan

waɗanda suna cikin kaburbura za su ji muryatasa, su fito kuma;

waɗanda sun yi nagarta, su fito zuwa tashi na rai, waɗanda sun

yi mugunta zuwa tashi na shari’a.

A Daniel 12:2 Allah yace:

Da yawa kuwa daga cikin waɗanda suke barci cikin turɓayar ƙasa

zasu falka, waɗansu zuwa rai, na har abada waɗansu kuma zuwa

kunya da reni marar matuƙa.

Waɗannan ayoyin suna magana akan mutanen da suka mutu

waɗanda zasu falka, suna jin muryar Allah. Ta yaya wannan zata yiwu?

Idan ba a fara rayar da ba ba yadda zai iya jin muryar Allah?

Za a iya samun amsar a cikin Ezekiel 37, inda misalan biyu da

harshen da aka saba magana da shi a duniya, Allah yayi Magana game

da wannan tambaya. A cikin aya 4 da 5 Allah yace:

Ya sake ce mani, kayi annabci a bisa waɗannan ƙasusuwa, ka ce

masu, ya ku ƙasusuwa busassu, ku ji maganar Ubangiji haka nan

Ubangiji Yahweh ya ce ga shi zan sa numfashi a cikinku za ku

rayu.

A waɗannan ayoyi Allah yana cewa kafin numfashin rai ya shiga

cikin waɗannan busassun ƙassusuwan zasu iya jin Maganar Ubangiji. A

cikin ruhaniya, Allah yana cewa waɗannan da ya yi shirin ceto suna kama

da busassun ƙasusuwa da basu da rai. Sun mutu cikin ruhaniya ko da

shike suna raye cikin jiki. Amma Allah zai iya ba waɗannan mutanen da

ke mattatu ga ruhu kunnuwan ji na ruhaniya, abinda kuma yake yi yayin

da ya tashe su daga matattu cikin ruhaniya zuwa rai na har abada.

Allah kuma ya yi magana filla filla cikin kalaman duniya inda ya

ƙara cewa a cikin Ezekiel 3:12-13:

51
Ka yi annabci fa, kace masu ga shi, zan buɗe kabarbarunku, ya

mutane inji Ubangiji Yahweh, zan kuma kawo ku cikin ƙasar

Isra’ila. Za ku sakankance kwa ni ne Ubangiji sa’anda na buɗe

kabarbarunku na tsamo ku kuma daga kabarbarunku, ya

mutane na.

Za a iya fahimtar waɗannan ayoyin ta fannin ruhaniya, amma

kuma suna koya mana a zahirin gaskiyar duniya. A lokacin fyaucewa,

jikunan zaɓaɓɓu zasu ji muryarsa, su kuma fito. Za a ba jikunansu rai na

har abada domin za a tada su da jiki na ruhaniya madawwami

(IKorintiyawa 15:44).

Amma ko da shike ɗaiɗaikun jikunan zaɓaɓɓun suna Maganar

Allah kafin a basu numfashi (Ezekiel 37:4-5), ƙasusuwa ko kuma gangan

jikin waɗanda basu da ceto, yayin da suke a mace. Za su iya jin Maganar

Allah. Abin da Allah ya faɗa a cikin Ezekiel 37, shine zai iya umurtar

komi ya yi biyayya da nufinsa yadda ya ga dama. Ka tuna misali Markus

4:39 da 41 inda muka karanta cewa:

Ya farkar ya tsauta ma, iska ya ce ma teku, ka natsu, kayi shiru,

iska ta kwanta, babbar natsuwa ta samu,... suka ji tsoro ƙwarai,

suka ce ma junansu, wanene wannan fa wanda har iska da teku

suna biyayya da shi?

In har iska da raƙuman ruwa zasu yi biyayya da umurnin Yesu,

dole ne su kasance a falke domin su ji muryar sa. Haka nan za a tada

mattatun ƙasusuwan da jikunan waɗanda basu da ceto, su ji muryar

Allah ba tare da suna raye zahiri ba. Abin da zai faru ke nan lokacin da

Allah zai fitar da jikunan waɗanda suka mutu ba tare da sun sami ceto

ba, daga kabari a lokacin da ranar shari’a ta fara.

Ya kamata su san yadda Allah ya rubuta waɗannan ayoyin guda

uku a hankali waɗanda suka yi magana game da tashin mattatu. A

Ayyukan mazanni 24:15 Allah ya ce akwai tashin mattatu na marasa

adalci. Sai ka ce tashin mattatu na marasa ceto yana kama da tashin

mattatu na masu bada gaskiya, sai dai a cikin Yohanna 5:29, Allah ya

bayyana cewa za a tashi marasa ceto zuwa hallaka. kalmar nan “Hallaka”

tana nuna wani ɓangare na hukucin da marasa ceto suke sha sabili da

zunubansu. Wanne fannin hukuncin ne Allah yake magana a kai?

Aya ta uku, Daniel 12:2, ta nuna mana abin da Allah ya ke da shi

a zuciya. Tashin mattatu ne zuwa kunya. Wannan zai faru ne lokacin da

aka tada jikunan su da ƙasussuwan su daga kabarbaru aka sake jefad da

su ko ina a ƙasa, domin a kunyatar da su a idon waɗanda suke raye a

farkon ranar shari’a, da kuma gaban Allah da gaban ikokin a sammai.

An bayyana wannan abin baƙin ciki a cikin Irmiya 7:33 zuwa 8:21 inda

muka karanta cewa:

52
“Gawayen mutanen nan za su zama naman tsuntsayen sama, da

bisashen ƙasa, ba kuwa wanda za ya kore su ba. Sa’annan zan sa

muryar wasa da dariya, da muryar farin ciki da muryar ango da

muryar amarya, kuma su ƙare a biranen Yahuda da hanyoyin

Urushalima kuma gama ƙasar za ta zama kango. A loton nan, in

ji Ubangiji za su ɗauko ƙasusuwan sarakunan Yahuda da na

hakimai da na firistoci da na annabawa da na manzannin

Urushalima daga cikin kabarburan su za a shinfiɗe su a rana da

farin wata, da dukan rundunar sama waɗanda suka ƙamnace su,

suka bauta masu kuma suka bi su, suka biɗe su, suka yi masu

sujada kuma: ba za a tattara su ba, ba kuwa za a bizne su ba, za

su zama taki a bisa fuskar ƙasa.

A Nahum 3:5-6 Allah yace:

“Ga shi ina gaba da ke inji Ubangiji mai runduna, zan kuwa buɗe

asirinki a gaban fuskar ki; zan nuna ma al’ummai tsiraicin ki

kunyarki, kuma zan bayyana ga mulkoki. Zan zuba maki ƙazanta

mai ban ƙyama in maishe ki abu mummuna, in kafa ki abin kallo.

Masu Bi Suna Shari’anta Marasa Ceto

A farkon ranar sharia, 21 ga watan Mayu, 2011, lokacin da za a

ga ana fyauce jikunan mattatu na Nineba a sararin sama (fyaucewa) zuwa

cikin gajimarai domin su kasance tare da Kristi, zai kasance shari’a da

hukumci ga waɗanda aka bari a baya. Mutanen Nineba sun gane da

muguntarsu, suka ƙasƙantar da kansu suka tuba, suka ta da muryar su

ga Allah domin yayi masu jinƙai, suna begen cewa wata kila Allah ba zai

hallaka su ba. Littafi Mai-Tsarki ya shaida mana cewa Allah a cikin

jinƙansa, ya cece su.

Gaskiyar cewa sababbin jikunan mutanen Nineba da aka fyauce,

ya jaddada zunuban waɗanda aka bari a baya. Wannan kashewar zata

faru ga waɗanda suka gaskanta an cece su, amma madogarar su tana

kan Ikklisiyarsu ko baftismar su, da dai sauransu. Ta haka zasu karɓi

hukunci mai tsanani fiye da waɗanda basu san Littafi Mai-Tsarki ba.

Fyaucewar mutanen Nineba wanda zai nuna a fili cewa an cece su,

babbar shaida ce cewa waɗanda aka bari a baya basu da ceto kuma babu

shakka, zasu kasance ƙarƙashin fushin Allah. Wannan ya bayyana ayoyi

kamar waɗannan:.

Matta 12:41 Nawiyawa zasu tashi tsaye a ranar shari’a tare da

wannan tsarai, za su kuwa kashe ta: gama su suka tuba da

wa’azin Yunana ga kuwa wanda ya fi Yunana girma a nan.

53
Ruya ta Yohanna 2:26: Wanda ya yi nasara kuma, wanda ya

kiyaye ayyuka na har matuƙa, a gare shi zani bada iko bisa

al’ummai.

Ruya ta Yohanna 3:9: Ga shi na bayas daga cikin majami’ar

shaitan, waɗanda suke ce da kansu Yahudawa, ba kuwa haka

suke ba, amma suna ƙarya; ga shi zan sa su su zo su yi sujada a

gaban sawayenka, su sani kuma na ƙamnace ka.

Korintiyawa I 6:2-3: Ko kuwa ba ku sani ba tsarkaka za su yi ma

duniya sharia? Idan fa kuke yi ma duniya shari’a ba ku isa ku

shari’anta ƙanƙananan al’amura ba? Ba ku sani ba mu za mu yi

ma mala’iku shari’a, balle fa al’amuran wannan zamani.

An sake mana tuni a IBitrus 2:12 inda muka karanta cewa:

Kuna al’amura na dacewa (hali) wurin al’ummai, domin yayin da

suke kushe ku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun

ayyukan da suke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.

A cikin wannan bayanin, maganar nan ‘‘ɗaukaka Allah cikin ranar

ziyara’’ ya shafi waɗanda za a hukunta sabili da zunubansu, kamar

yadda aka gaya wa Acan ya ɗaukaka Allah, yayinda ake shirin kashe shi

domin zunubansa (Joshua 7:18-26).

Ta haka zamu fahimci cewa lokaci da waɗanda basu da ceto

suka gane cewa gaskiya ne mutum ya sami ceto, (kamar yadda

fyaucewar mutumin ta nuna) zai kawo shari’a da hukucin akan waɗanda

suke zaton cewa suna da ceto, amma yanzu suka sani cewa ba su da

ceto domin an barsu a baya a lokacin fyaucewa. Masu bi na gaskiya da

aka fyauce sun hukunta su.

Abinda zai faru ke nan a duk faɗin duniya ranar 21 ga watan

Mayu, 2011, lokacin da za a fyauce jikunan waɗanda suka mutu, tare da

duka masu bi na gaskiya da suke raye, su kasance tare da Kristi. Wannan

zata zama babban hukunci a kan duniya musamman a kan waɗanda

suke cikin majami’u a duk faɗin duniya, waɗanda kabilun nan 12 na

Isra’ila suka wakilta a zamanin Ikklisiya. (Ruya ta Yohanna 7:4-8, Matta

19:28). Zai zama shaida cewa dukan waɗanda aka bari a baya suna

ƙalƙashin shari’ar Allah.

Cikar (lamba 12) na dukan masu bi waɗanda suke mulki tare da

Kristi, zasu yi wa duniya da kuma Ikkilisiya sharia (kabilu 12, dubi Matta

19:28) da shike suna tare da Kristi har abada, kuma an hallaka duniya da

majami’u cikin ƙorama ta wuta har abada.

Yaƙin Armagaddon

54
Yaƙin Armagaddon da aka yi Magana a kai cikin Ruya ta Yohanna

shine yanzu muke bayani a kai. Mayaƙan masu bi na gaskiya da ke

zaune lafiya a lokacin tare da Kristi, ba ya shiga yaƙi na zahiri da

waɗanda basu da ceto. Sai dai za a ga gagarumar shaidar nan cewa

hakika sun sami ceto, a dukan duniya lokacin fyaucewa. Wannan zai

zama babbar shari’a, da hukunci a kan mayaƙan waɗanda ba su da ceto

da aka bari a baya a lokacin fyaucewa.

Maganar Allah kanta tana kawo hukunci a kan mai zunubi saboda

haka, kuma shaidar ceto a rayuwar waɗanda aka fyauce shine hukunci a

kan waɗanda basu da ceto. Mun karanta a cikin Ibraniyawa 11:7 cewa:.

Ta wurin bangaskiya Nuhu da aka faɗakad da shi a kan al’amuran

da ba a gani ba tukuna, domin tsoro mai ibada sai ya shirya jirgi

domin ceton gidansa ta wurin wannan fa ya kada duniya, ya

zama magajin adalci wanda ke bisa ga bangaskiya.

Da shike jirgin ya kare Nuhu daga hallaka lokacin da ruwan

Ɗufana ya sauko hukunci ne akan marasa ceto waɗanda suka hallaka a

cikin ruwa kamar yadda Maganar Allah da kanta ta kawo hukunci a kan

waɗanda suka saɓa mata.

Ta yaya mayaƙan marasa ceto zasu yi yaƙin Armageddon? Allah

ya ce a Joel 3:9-16:

Ku yi shelar wannan a wurin al’ummai ku yi shirin yaƙi ku kutta

jarumawa bari dukan mayaƙa su guso, su hau; ku bubbuga

garmunan ku a yi takubba da su lauzunan ku kuma ku yi masu

da su; bari rarrauna shi ce, ina da ƙarfi. Ku gaggauta, ku zo

dukan ku, al’ummai na kewaye ku tattaru; ya Ubangiji, ka sa

ƙarfafan ka su zo wurin. Bari al’umma su tashi tsaye, su hau

wurin kwarin Jehoshaphat gama can zan zamna garin yin shari’a

bisa dukan al’ummai na kewaye. Ku sa lauje, gama amfanin kaka

ya nuna ku zo ku taka, gama wurin matsewar ruwan anab ya

cika, randuna suna zuba gama muguntar su, tana da girma.

Babban taro, taron mai yawa cikin kwarin yankan shari’a gama

ranar Ubangiji ta kusa cikin kwari na yankan sharia. Rana da

wata sun dufunta, tamrari suna jan haskensu. Ubangiji za ya yi

ruri daga sihiyona, ya furtad da muryar sa daga sihiyona, ya

furtad da muryar sa daga Urushalima, Sammai da duniya zasu yi

rawa; amma Ubangiji za ya zama mataka ga mutanensa,

ƙaƙƙarfan wuri kuma ga yaƙin Isra’ila.

Kamar budurwai goma da aka yi maganarsu a Matta 25, waɗanda

suka falka lokacin da Angon (Kristi) ya zo, haka kuma a farkon ranar

shari’a, marasa ceto za su yi shiri su yi yaƙi da masu ceto. Yaƙinsu na

55
abban takaici ne matsanancin fushi yayin da suke yi wa Allah kuka da

cizon haƙoran su ga Allah domin barin su a baya.

Matta 7:22-23: A cikin wannan rana mutane da yawa za su ce

mani, Ubangiji, Ubangiji ba mu yi annabci da sunanka ba, da

sunanka kuma muna fitar da aljanu, da sunanka kuma muka yi

ayyuka da yawa masu iko sa’annan za su furta masu, ban taɓa

saninku ba daɗai, rabu da ni ku masu aikata mugunta.

Matta 8:11-12: kuma ina ce maku, mutane da yawa daga gabas

da yamma zasu zo, su zamna tare da Ibrahim, da Ishaku da

Yakub, cikin mulkin sammai amma za a fitar da ’ya’yan mulki

cikin baƙin duhu, can za a yi kuka da tamnar haƙora.

Matta 13:49-50: Hakanan kuma za ya zama cikin matuƙar

zamani malai’ku za su fito, su rarraba miyagu daga cikin masu

adalci, su jefa su cikin ɓuyar wuta, can za a yi kuka da cizon

haƙora.

Luka 13:26-28: Sa’annan za ku yi ta cewa, muka ci muka sha

wurinku, har ka yi koyaswa a cikin hanyoyinmu, shi ma za ya ce

ina faɗa maku dani ban san inda kuka fito ba, ku rabu da ni

dukan ku da ku ke masu aikata mugunta. Can za’a yi kuka da

cizon haƙora, lokacin da kun ga Ibrahim da Ishaku da Yakub da

dukan annabawa cikin mulkin Allah ku da kanku kuwa na fitar da

ku waje.

Ruya ta Yohanna 16:10-11: Na biyar kuma ya zubas da nasa

kasko bisa kursiyin bisani, mulkinsa kuwa ya duhunta, suka cije

harsunansu domin azaba. Kuma suka saɓa Allah na sama

saboda azabarsu da gyambunansu, ba su kwa tuba da ayyukansu

ba.

A ruya ta Yohanna 17:14 Allah ya yi Magana game da wannan

yaƙi, muka kuma karanta cewa:

Waɗannan kuma za su yi gaba da Ɗan Rago, Dan Rago kuma za

ya ci su gama shine Ubangijin iyayengiji, da Sarkin Sarakuna, su

kuma waɗanda ke tare da shi kirayayyu, zaɓaɓɓu, masu aminci

za su yi nasara.

An yi bayanin ƙarshen yaƙi, alal misali cikin Ruya ta Yohanna

19:19-21

56
Na ga bisan kuma da sarakuna na duniya, da rundunan yaƙinsu,

a tattare domin su yi yaƙi da wanda yake zamne bisa dokin, da

rundunansa kuma, aka kama bisan, tare da shi kuma mai ƙaryan

annabci, wanda ya kan aikata alamu a gabansa, irin da ya kan

ruɗe masu karɓan shaidar bisan da waɗanda ke sujada ga

gunkinsa aka jefa su biyu da rai cikin ƙorama ta wuta mai-ci da

kibiritu aka kashe sauran da takobi na wanda ya ke fitowa daga

bakinsa ke nan. Dukan tsuntsaye fa suka ƙoshi da namansu.

Mun koya da cewa ƙarshen yaƙin zai zama lokacin da Allah zai

hallaka dukan duniya.

Takaitawa

Yanzu za mu takaita abinda muka koya game da shirin shari’a na Allah

da yadda yake da dangataka da abubuwan da zasu faru na ƙarshen

zamani na wannan duniyar

1. Ra’ayin nan irin na al’ada da ke koyar da cewa ko wani marar

ceto zai tsaya a zahiri gaban Kristi a matsayin mai-shari’a, a

zartar da cewa shi mai laifi ne, a kuma yanke mashi

hukumcin shan baƙar azaba har abada a wani wurin da ake

kira jahanama, yana da rauni.

2. Zamanin Ikklisiya ya ƙare ranar 21 ga Mayu,1988. Lokaci na

gaba wanda yake kwanaki 8,400 daidai zai ƙare ranar 21 ga

Mayu, 2011. Ana kiransa lokacin tsanani.

3. An raba wannan lokaci na babban tsanani kashi biyu. Kashi

na farko ya fara ne daga 21 ga Mayu, 1988 zuwa 7 ga

Satumba, 1994. A wannan lokaci kusan babu wanda ya sami

ceto a duniya. Kashi na biyu kwanaki 6,100 ne kuma zai fara

daga 7 ga Satumba, 1994 zuwa 21 Mayu, 2011. A wannan

lokacin babu wanda zai sami ceto a cikin majami’u amma a

waje, ɗumbin jama’a mai girma suna samun ceto. Littafi Mai-

Tsarki ya jaddada cewa akwai da yawa da zasu sami ceto,

waɗanda suke da alaƙa da Isma’il, ɗan Ibrahim. Bugu da ƙari,

ya jadada cewa da dama daga cikin waɗanda daga ƙarshe ne

suka sami fahimtar Littafi Mai-Tsarki, za su riƙa zuwa cikin

mulkin Allah.

4. Duk kwanaki 8,400 na wannan lokaci na babban tsanani,

lokaci ne da Allah zai raba masu bi na gaskiya (zaɓaɓaɓu)

daga waɗanda suke cewa su masu bi ne, amma ba haka ba.

Allah yana rarrabewa ne ta wurin shirya waɗansu gwaje

gwaje, kamar yadda suke a cikin wannan tsarin.

a) Kowacce kalma daga ƙarshen da aka rubuta Littafi Mai-

Tsarki daga bakin Allah ne.

57
) Kowacce kalma a cikin Littafi Mai-Tsarki shari’ar Allah ce,

kuma yana da iko daidai da Allah kansa.

c) Ba da gaskiya aiki ne da muke yi, saboda haka ba wanda

zai bada gaskiya ta wannan hanya da cewa zai sami ceto.

Kristi ya kammala dukan aikin da mutum yake bukata

domin ya sami ceto da daɗewa kafin a haifi mutumin..

d) Ko da shike an kai kimanin shekaru 1,900 da rubuta

Littafi Mai-Tsarki, gama shi ba a ƙara waɗansu kalmomi a

kai. Ruhu Mai-Tsarki yana ƙara bayyana waɗansu

sababbin gaskiya masu girma a zamaninmu da muke

kusa da ƙarshen zamani.

e) Zamanin Ikklisiya ya shuɗe, Allah kuma ya umurci mutane

su bar majami’u. Shaiɗan yana mulki a can, kuma Allah

baya ceton mutane a cikin majami’u.

F) Yanzu Kristi ya bayyana cewa zai zo kamar ɓarawo da

dare.

g) Allah ya ba masu bi na gaskiya ainihin rana, da wata da

shekara da zai dawo domin faɗakar da duniya.

h) Allah ya ba masu bi na gaskiya sababbin bayanai daga

Littafi Mai-Tsarki game da shirin shari’ar Allah.

i) Allah yana ba duniya baki ɗaya ainihin lokacin ƙarshen

duniya domin su sami damar tuba su yi kuka ga Allah

domin neman jinƙai kamar yadda mutanen Nineveh suka

yi lokacin da Yunana ya faɗakar da su game da hukunci

mai zuwa. Waɗanda suke masu bi na gaskiya suna

damuwa da abin da Littafi Mai-Tsarki ya ke koyarwa. Suna

kuma ɗaukar shi a matsayin iyakacin ikon su. Za su duba

waɗannan koyaswar a hankali su kuma gaskanta da su.

Waɗanda kuma suka dogara ga majami’un su ko kuma

shaidar bangaskiyar majami’unsu, ko kuma tunanin

kansu, waɗannan koyaswar babban gwaji ne. Waɗanda

ba zaɓaɓɓu bane zuwa ga ceto za su sami babbar matsala

da su.

5. Babban tsananin zai kawo ga ƙarshe ranar 21 ga watan

Mayu, 2011 wanda kuma shine ranar da hukuncin da ake

kira “Ranar Ubangiji” zai faru. Ranar Hukunci zata ci gaba na

tsawon kwanaki 153, har zuwa 21 ga watan Octoba, 2011

lokacin da duniya zata ƙare.

6. Shirin ceto na Allah zai kawo ga ƙarshe ranar 21 ga watan

Mayu, 2011. A wannan ranar ne ɗauka zuwa sama

(fyaucewa) na dukan zaɓaɓɓu (cetattu na gaskiya) zata faru.

Za a tada jikunan waɗanda aka ceta zuwa jiki na ruhaniya

mai daraja. Nan da nan masu bi kuma da suke da rai a ranar

za su karɓi sabon jikin na ruhaniya, nan take, za a kuma

fyauce su zuwa sama su zauna tare da Kristi har abada.

58
7. Kusan mutane biliyan bakwai ne zasu kasance a duniya a

lokacin zasu kuma shaida fyaucewar masu bi na gaskiya. Za

a raba waɗanda aka bari a baya ruƙuni biyu. Kimanin kashi

ɗaya bisa ukunsu ko kuma biliyan biyu daga cikinsu, zasu

kasance ’yan Ikkilisiya ne. Suna da ɗan sanin gaskiyar Littafi

Mai-Tsarki sun gaskanta cewa su masu bi ne. Sauran kashin

zai ƙunshi sauran mutanen duniya da aka bari a baya.

8. Bayan wannan ranar 21 ga watan Mayu, 2011 ranar nan maiban

tsoro, ranakun da zasu biyo baya zasu kasance ne kamar

sauran ranaku a duk faɗin duniya za a ci gaba da harkokin

yau da kullum kamar yadda aka saba.

9. Sai dai a wannan ranar, za a yi babbar girgizar ƙasa yadda a

duk faɗin duniya, kabarbura da dukan maƙabartu zasu

buɗe. Jikunan mutanen da aka binne a wurin kuma za su

warwatsu a ƙasa. (sai dai jikuna masu bi na gaskiya domin,

za a sake jikunansu zuwa jiki mai daraja da za a fyauce).

10. Wannan girgizar ƙasar zata yi ɓarnar gaske a dukan duniya

wanda zai haddasa mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa

ta tsunami, da zai lalata hanyoyin ruwa da na makamashi da

sauransu. Don haka za a yi alobai masu tsanani.

11. Wannan lokacin zai zama lokacin baƙin cikin gaske ga ’yan

Ikkilisiya. Sun yi tsammani cewa sune za a fyauce. Sai

kwatsam, suka gane cewa a bar su a baya suna kuma

ƙarƙashin cikakken fushin Allah. Daga nan zasu gane cewa

ba za su ji daɗin ci gaba da zama a duniyar nan ba. Abu mafi

muni kuma shine zasu sani cewa basu da rai madawami tare

da kiristi da kuma zama magadan sabuwar sama da sabuwar

duniya. Banda haka kuma, zasu kasance a cikin kunya mai

girma a idon wanɗanda ba su san komi ba game da

Littafi Mai-Tsarki, amma yanzu suka ga cewa addininsu na

kirista ƙarya ne da na riya. Fiye da haka, zasu sha babbar

kunya a gaban Allah da mulkoki da ikokin na sama. A gaban

Allah mutuwarsu zata kasance hukumcin kisa mai ban kunya

domin suna ƙalƙashin la’anar Allah. Zasu kuma sha tsanani

na jiki sakamakon annobar da zata faru a dukan duniya.

Dukansu zasu mutu (za a yi masu kisan wulakanci a

gaban Allah). Suma zasu mutu a ranar ko kuma kafin rana ta

ƙarshe 21 ga watan Octoba, 2011.

12. Sauran ruƙunin mutanen kuma waɗanda basu taɓa cewa su

masu bi bane, waɗanda kuma aka barsu a baya lokacin da

aka fyauce masu bi na gaskiya, zasu yi baƙin cikin sanin

cewa an katse masu hanzari a irin rayuwar farin ciki da begen

irin rayuwar da suke yi a nan duniya. Suma zasu jimre

babbar azaba ta jiki wanda zata faru ta dalilin annobar da

suke jimrewa. Suma zasu kunyata a gaban Allah da

59
mulkoki da ikoki na samaniya. Suma zasu mutu, ranar ko

kuma kafin ranar ƙarshe, 21 ga watan Octoba, 2011.

Mutuwar su ma zata zama hukumcin kisa na wulakanci da

kunya a idon Allah da mulkoki da ikokin samaniya.

13. A wannan lokaci na fyaucewa, dukan kaburbura zasu buɗe

dukan gawawaki da ƙasusuwa da toka da ƙura da dukan

abinda ya rage na mutanen dake cikinsu, waɗanda kuma ba

a fyauce ba, za a warwatsa kamar taki a duniya. Angulaye, da

karnuka da tsutsotsi za su ci jikunansu. Waɗannan mutanen

a lokacin mutuwar su, basu san nauyin bashin da suka biya a

kan zunubansu ba. An binne da dama daga cikinsu cikin

karamci da girmamawa, amma a gaban Allah mutuwar su

abin kunya ce. Yawancinsu sun gane cewa mutuwarsu zata

hana su murna da bege na wannan rayuwa, amma babu

wanda ya san girman hukunci da zasu biya domin rasa gadon

haihuwarsu na ɗan fari da gadon rai na har abada da sabuwar

sama da sabuwar duniya.

14. Ta wurin ya da jikunansu daga kaburbura, wata kunya ce

kuma da dole waɗannan mutanen zasu jimre, ko da shike da

dama daga cikinsu sun mutu da daɗewa ba tare da sun sani

ba, Allah ya jaddada kunyar zunubi ta wurin buɗe kaburbura

na waɗannan mutanen domin a ƙazanta gawarsu. An

kumyatar da gawawakinsu an kunyatar da su a gaban Allah

da gaban mulki da ikoki na sammai da gaban waɗanda aka

bari a baya waɗanda zasu ɗanɗana ranar shari’a. Kumyar da

zasu sha a gaban Allah da gaban halittun sammai zata

danganta ga irin sanin da suke da shi na dokar Allah.

15. A ƙarshen kwanaki 153 na baƙar azabar da ake kira ranar

shari’a (21 ga watan Mayu, 2011 zuwa 21 ga Octoba, 2011)

ƙarshen duniyan zai zo. Duniya da dukan ayyukan ta zasu

ƙone, za a hallaka duniya ma baki ɗaya. Ba za a sake tunawa

da shekaru 13,023 na tarihin duniya da dukan abinda ya faru

a cikinta ba.

16. Masu bi na gaskiya, da za’a fyauce su zasu rayu har abada a

cikin farin ciki da murna mai girma a matsayin amaryar Kristi

wanda zasu yi mulki tare da shi na har abada.

17. Hanyar da Allah ya saba sauko da hukunci ya kuma sa maizunubi

ya jimre hukuncin zunubi kamar yadda aka bayyana a

Littafi Mai-Tsarki, ita ce dokar Allah. Amma Allah ya yi amfani

da rayuwar masu bi na gaskiya ya zama hukunci ga masu

zunubi. Wannan zai zama gaskiya a ranar fyaucewa. Duk

masu bi da aka fyauce a idon ’yan Ikklisiya waɗanda aka bari

zai zama babbar shaida cewa Maganar Allah kamar yadda

waɗanda aka fyauce suke bi, gaskiya ce kuma abin amincewa.

60
Zata zama abin nuni a fili da kuma shaida cewa ’yan Ikkilisiya

da sauran da aka bari a baya, basu yi biyayya da Maganar

Allah ba.

Irin fahimtar shirin shari’ar Allah kamar yadda aka saba bisa

al’ada, wanda yake koyas da cewa masu zunubi zasu kasance a wani

wuri da ake kira, jahannama, suna wahala mai tsanani ya saɓawa

koyarwar Littafi Mai-Tsarki.

Kowanne Ido Zai Ganshi

Kimanin shekaru 2,000 da suka wuce Ubangijinmu Yesu Kristi da kansa

ya zo duniyar nan. Ya zo a cikin jiki a matsayin Ɗan Allah da kuma Ɗan

Mutum. Dubban mutane a ƙasar Isra’ila sun sami damar ganinsa a cikin

shekarun nan kusan 40. Daga nan ya koma sama amma yayi alkawari zai

sake dawowa. A wannan lokacin ya koma sama, mala’iku biyu suka gaya

wa manzani kamar yadda muka karanta a cikin Ayyukan Manzani 1:11:

...Ku mazajen Galili don me kuke tsaye kuna duba zuwa sama,

wannan Yesu wanda aka ɗauke shi daga wurinku aka karɓe shi

sama, kamar yadda kuka ga tafiyatasa zuwa cikin sama, haka nan

zashi dawo.

Dawowa “Haka nan” magana ce mai faɗi. Zai iya nufin zai sake

dawowa kamar yadda ya tafi sama. Lokacin da ya zo da farko. Ya zo a

matsayin Ɗan Allah, da kuma Ɗan mutum. “Haka nan kuma” na iya

zama, misali, cewa zai sake dawowa a matsayin ɗan Allah amma cikin

babbar ɗaukaka. Tilas ne mu bincike Littafi Mai-Tsarki mu ƙara koya

game da ranar nan mai- ban tsoro. Dadowar Ubangiji Yesu Kristi ta

biyu.

Mun rigaya mun koya cewa tilas ne lokacin dawowar Yesu Kristi

ta biyu, ya zo daidai da lokacin fyaucewa, wadda ta zo daidai da rana ta

fari na kwanaki 153 na ranar shari’ar. Ranar ita ce 21 ga watan Mayu,

2011. A wannan ranar, kabarbura za su buɗe, za a kuma tashi dukan

gawawakin waɗanda cikin jikunan ruhaniya na ɗaukaka. Banda haka

kuma za a watsar da gawarwakin da ƙasusuwa da sauransu na dukan

waɗanda basu da ceto a ƙasa a matsayin juji. Za a canza jikunan

waɗanda har yanzu suke da rai, kuma masu bi ne na gaskiya nan da nan

zuwa jikuna na samaniya a kuma fyauce su a sararin samaniya a fuskar

waɗanda aka barsu a baya. Hakika kusan mutane biliyan 61/2 waɗanda

aka bari a baya, zasu san cewa Yesu ya zo, kuma zamu iya tabbatar da

cewa lokacin fyaucewar kowa zai ga Yesu a lokacin dawowarshi ta biyu.

Ta haka, zamu tabbatar da cewa zuwa dawowar Kristi, lokacin da

kowanne ido zai gan shi, yayi daidai da fyaucewar. Dalili ke nan da ya sa

zai zo tare da “gajimare” (Ruya ta Yohanna 1:7) tare da gajimare yana

61
nuna cewa ya zo ne domin ya yi hukunci. Ka tuna, ranar fyaucewar ita ce

kuma rana ta fari ta kwanaki 153 na ranar shari’a.

Sai dai, babu wani wuri a cikin Littafi Mai-Tsarki da ya koyar da

cewa a ranar fyaucewa, marasa ceto a duniya zasu ga Yesu ido da ido

zahiri. Duk da haka Ruya ta Yohanna 1:7 ya ce “Kowane ido kuma za ya

gan shi”.

An warware wannan matalar misali a Yohanna 1:51 inda muka

karanta cewa Yesu gaya wa:

Yace masa kuma, hakika, hakika ina ce maku zaku ga sama a

buɗe mala’ikun Allah kuma suna hawa suna sabka bisa Ɗan

Mutum.

Mun karanta a cikin Littafi Mai-Tsarki cewa Natanayilu ya ga

sama ta buɗe mala’iku kuma suna hawa suna sauka daga sama zuwa

wurin Yesu da ido ƙuru ƙuru? Hakika Littafi Mai-Tsarki bai faɗi wani abu

kamar haka ba. Amma idan muka tuna cewa za a iya fassara kalmar nan

“mala’ika” da “manzo” kuma duk mai bi na gaskiya manzo ne na

“Bishara”, da haka mun san abinda ya kamata Natanayilu ya gani.

Yayinda mutane suka sami ceto, an sa su hau cikin samaniya ta fuskar

ruhaniya cikin Kristi Yesu (Afisawa 2:6). Watau a lokacin da muka sami

ceto, mu na sama tare da Kristi cikin ruhaniya domin an bamu sababbin

jikuna na fyaucewa. Nan take zamu shiga sama domin abinda Yesu yayi

domin mu. Saboda haka tilas ne mu shiga aiki a duniyar nan mu zama

wakilan Kristi a nan duniya.

Watau, Yesu yana gaya wa Natanayilu cewa za ya ga mutane suna

samun ceto, kuma Kristi zai yi amfani da su domin shaida Bishara. Mun

ga wannan ra’ayin na ganin Kiristi nan gaba ta wajen zama shaidun

abinda Kristi yake yi yanzu, a cikin abinda Almasihu ya gaya wa mugun

babban Limamin nan, Kefas a Matta 26:63-64, inda muka karanta cewa:

Amma Yesu yayi shiru, babban malami fa ya ce masa, na gama ka

da Allah mai rai, ka faɗa mana, ko kai Kristi ne, Ɗan Allah. Yesu

ya ce masa ka faɗi, amma ina ce maku gaban nan za ku ga Ɗan

Mutum a zamne a hannun daman mulki yana zuwa kuma bisa

giza-gizan sama.

Kefas ya mutu shekaru 2,000 da suka wuce ba kuma zai ƙara

rayuwa ba, Kefas ya ga Yesu a kan giciye kuma ya kuma sani cewa Yesu

ya tashi daga mattatu. Yana da kyakkyawan sanin Littafi Mai-Tsarki na

zamaninsa (Tsohon Alkawari), ya san cewa Yesu ya cika dukan kai’dojin

zama Mai-Ceto. A matsayinsa na babban Limami ya kamata Kefas ya san

Zabura 16:10 inda muka karanta cewa:

62
Gama ba zaka bar raina ga lahira ba, ba kuwa zaka bar mai

tsarkinka shi ga ruɓa ba.

Ka duba Matta 27:62-66, Matta 28:11-15 da Daniel 7:13-14.

Abubuwa da yawa na allahntaka suna faruwa a lokacin giciye.

Abubuwan da suka yi daidai da annabcin Littafi Mai-Tsarki. Babu shakka

Kayafa, babban Firist yana sane da annabce annabce da ke cikin Tsohon

Alkawari dangane da zuwan Mai-Ceto, saboda haka ya kamata ya san

cewa Yesu Kristi ne wanda yake zuwa a matsayin babban mai-mulki na

duniya wanda kuma zai kammala shirin shari’a duka.

Bari mu koma kan annabcin nan cewa kowanne ido zai ga Yesu,

za mu san wannan manyan abubuwan da zasu faru a lokacin fyaucewa,

da kuma abubuwan da suka sa kaburbura suka buɗe zasu sa kowanne

mutum ya san cewa Kristi ya zo. Ya yiwu ya zo domin ya kamalla ceton

masu bi, ya yiwu kuma ya zo domin ya kammala hukuncin a kan

waɗanda basu da ceto.

Domin muhimancin ranar fyaucewa, yanzu za mu bincike

waɗansu wurare da suka yi magana da cewa kowa zai ga zuwan Yesu. Za

mu bincike Matta. 24:27-31 inda muka karanta cewa:

Gama kamar yadda walƙiya ta kan fito daga gabas ana kuwa

ganinta har yamma; hakanan bayanuwar ɗan mutum zata zama

inda gawa ta ke duka can angulai zasu taru. Amma nan da nan

bayan ƙuncin waɗannan kwanaki, rana zata yi dufu, wata ba

zaya bada hasken sa ba, tamraru za su faɗo daga sama, ikokin

sammai za su raurawa; sa’anan dama ta ɗan mutum zata

bayanna a sama. Sa’anan kuma dukan kabilun duniya za su yi

baƙin ciki, za su kuwa ga Ɗan Mutum yana zuwa a bisa gizagizai

na sama tare da iko da ɗaukaka mai girma. Zai kuma aika da

mala’ikunsa su kuma za su tattara zaɓaɓɓunsu daga kusurwoyi

huɗu, daga wannan iyakar sama zuwa waccan.

Waɗannan ayoyin sun koya a fili cewa zuwan Kristi zai kasance a

dukan duniya. Watau, za a ga shaidar cewa za a ganshi a ko’ina cikin

duniya. Gaskiyar cewa kabilun duniya suna makoki (aya 30) yayi daidai

da magana kamar, ‘‘kuka da cizon haƙora” da muka samu a waɗansu a

cikin Litafi Mai-Tsarki. Babu shakka dukan abinda ayoyin nan ke faɗa

sun yi daidai da abinda muka koya game da ranar fyaucewa.

Amma mene ne ya sa aka sa aya 28 a cikin wannan nassin? Yana

koyas da cewa akwai gawawaki da zai tara gaggafa. Bisa ga dukan alamu

waɗannan gaggafa sun zo ne domin su ci naman gawawakin da aka

fidda daga kuburbura. Kasancewa gawawakin yana koya mana a fili cewa

lokacin da Littafi Mai-Tsarki yayi Magana game da tashin mattatu na

masu adalci da marasa adalci, babu shakka ba wai yana nufin cewa za a

tada marasa ceto zuwa rai da zasu san ainihin abinda ke faruwa bane. A

63
maimakon haka, yana koya cewa za a tada marasa ceto (jefad da su daga

kaburbura) domin a wulankanta su. Za a kuma kumyatar da su a gaban

Allah da dukan halittun sama.

Kumyar da mutum zai sha a gaban Allah ta danganta ga zurfin

sanin Maganar Allah da mutumin yake da shi. Wannan yana daga cikin

hukuncin da za a yi masa. Dalili ke nan da yasa Yesu yace Kafarnahun

birnin da Yesu yayi aikin al’ajibi na lokaci mai tsawo, amma babu wanda

ya sami ceto, zai fuskanci hukuncin fiye da Sodom. Sodom Maganar

Allah kaɗan ne kawai ta sani. Mun karanta a Matta. 11:23-24. cewa:

Ya Kafarnahum, kuma ɗaukakar ki har sama za a yi? Hades za ki

gama da cikin saduma aka yi ayyukan masu iko waɗanda aka yi

cikinki, da ta wanzu har yau. Amma in ace maki a cikin ranar

shari’a ƙasar saduma tana da rangwami bisa gareki.

Hakanan, mai wa’azi da bashi da ceto, ko malamin Litafi Mai-

Tsarki yana kuma da rai a ranar shari’a gwargwadon sannin Litafi Mai-

Tsarki da yake da shi, haka kumyar da zai sha zata kasance a gaban

Allah da duniya, da kuma gawa lokacin da ya mutu a matsayin hukuncin

da za a yi mashi.

Wani nassi kuma da ya kamata mu duba shine Luka 17:36-37

inda muka karanta cewa:

Mutum biyu zasu kasance a gona, za a ɗauki ɗayan a bar ɗayan:

suka amsa suka ce masa, a wanne wuri Ubangiji? Ya ce masu,

inda gawa ta ke nan angulai kuma za su tattaru.

Mutum biyu suna gona. An ɗauke ɗayan. Shi ne mai bi na

gaskiya, an kuma fyauce shi zuwa sama ya zauna tare da Kristi. Mutumi

ɗayan ba shi da ceto, saboda haka aka barshi. Tambayar kuma ita ce, a

ina aka barshi? Amsa ita ce an barshi inda jikin ya ke, gaggafa kuma

suka taru. Idan Liffai Mai-Tsarki yayi Magana a kan

gaggafa”(ɗaya/mufuraɗi), yana Magana ne a kan hukuncin Allah mai

zuwa ko kuma ƙaunar Allah ta tausayi ga mutanensa. (Kubarwa Shari’a

33:11). Amma idan kalmar nan “gaggafa” jam’i ce, ana amfani da ita ne

domin nuna cewa suna ci kamar angulai ko buzuzu a kan gawa (Matta

24:28). Saboda haka, za mu gane cewa waɗanda aka bari a baya a

lokacin fyaucewa ma’abutan gawayen ne da aka fitar daga kabarbaru.

64
Sura Ta Shida

Masarautar Da Aka Ƙirƙiro Domin Nuna Ɗaukaka

Da Hikimar Kristi.

Muna binciken Litafi Mai-Tsarki da himma domin mu san ainihin

shirin Allah na sharia. Amma akwai tambaya mai muhimanci da bamu yi

ƙoƙarin amsawa ba. Amma kuwa tambaya ce mai muhimmanci da ya

zama tilas mu bincike Litafi Mai-Tsarki mu ga yadda ta bada amsa.

Tambayar itace mene ne NUFIN ALLAH NA HALLITAR DUNIYA KUMA

BAYAN SHEKARU 13, 023 YA HALLAKATA? Kafin mu fara neman amsar

wannan tambaya mai muhimmanci, ya kamata mu koyi abin da Allah ya

ce game da mulkoki da ikkokin da ya hallita a sama, saboda, zamu duba

waɗannan ayoyin.

Kolossiyawa 1:16 Gama a cikinsa aka hallita dukan abu cikin

sammai da bisa duniya kuma, abubuwa masu ganuwa da

abubuwa marasa ganuwa, ko kursiyai ko sarauta ko mulkoki ko

ikoki dukan abu ta wurinsa aka hallita su dominsa kuma.

Afisawa 3:10 Domin yanzu ta wurin Ikklisiya hikima iri iri ta

Allah ta samu ga sarautai da ikoki cikin sammai.

Litafi Mai-Tsarki ya sake Magana game da sarautai da ikoki

masu zuwa a Afisawa 1:21.

Gaba nesa da dukan sarauta, da hukuncin da iko, da mulki, da

kowane suna wanda a ke ambatonsa, ba cikin wannan zamani

kaɗai ba, amma cikin zamani mai zuwa kuma.

Har ila yau akwai ayoyi kima da suka yi magana game da sarauta

da suke da dangantaka da mulkin mutum a duniya da mulki shaiɗan a

duniya.

Romawa 8:38 Gama na kawas da shakka, ba mutuwa, ba rai, ba

mala’iku, ba sarautai, ba al’amuran yanzu, ba al’amuran na zuwa,

ba ikoki.

Afisawa 6:12 Gama kokuwarmu ba da nama da jini take ba,

amma da mulkokin da ikoki da mahukuntan wannan zamani mai

duhu, da rundunai masu ruhaniya na mugunta cikin sammai.

Kolosiyawa 2:15 Bayanda ya tuɓe ma kansa mulkoki da ikoki, ya

nuna su a sarari, yana kirari a bisansu cikin wannan.

65
Titus 3:1 Ka tuna masu su yi biyayya ga mahukunta, ga masu

iko, su ji Magana su zama shiryayyu ga kowane kyakkyawan aiki.

Afisawa 6:12 ya yi amfani da kalmar nan ‘‘cikin sammai’’ domin

yana nufin membobin Ikklisiya suna ƙoƙarin bauta wa Allah, dukan

zamanin Ikklisiya, yayin da suke ƙalƙashin ikon shaiɗan. Lokacin da

muke sake duba waɗannan ayoyi ya bayyana a fili cewa, Allah ya kafa

mulki da ikoki na sammai waɗanda suke cikin cikar mulkin Allah na

sama. Ba haka yake ba a da, amma zai ci gaba a nan gaba (Afisawa

1:21).

Idan muna binciken Litafi Mai-Tsarki domin mu san abin da

waɗannan mulkoki da suka taru suka zama mulkin Allah gaba ɗaya zasu

yi, zamu sa ran ganin waɗannan:

1. Allah ne, kaɗai maɗaukakin sarkin kowanne mulkoki da suka

shafi mulkin Allah. (Afisawa 1:19-23).

2. Manufar kowanne ɗan mulkin Allah shine ya ɗaukaka Allah.

3. Zunubi bai shafi mulkin Allah ba saboda haka bashi da wuri

a cikin waɗannan mulkoki.

4. ‘Ya’yan mulkin Allah ba sa aure basu auraswa (matta 22:30)

5. Mulkin Allah mulki ne na har abada kuma ba za a taɓa

hallaka shi ba (Daniel 6:26).

Bayan mun koyi waɗansu daga cikin muhimman abubuwa da aka

gina mulkin Allah a kai, mu kan dubi mulkin Allah da mamaki kamar

yadda a ke samu a duniya. Ya yi kamar ya saɓawa yadda ya kamata

ikokin da Allah zai yi mulki a kai su kasance.

Idan muka duba wannan mulkin a hankali, da yake da nasaba da

duniya, mun ga cewa da farko, muna ganin waɗansu abubuwan na ba

saban ba da suka saɓawa tunanin da muke da shi game da mulkin

Allah. Na farko, lokacin da Allah ya halicci wannan duniyar mai kyau, ya

sa a cikinta gonar Adnin. Mene ne ya sa Allah zai yi haka? Gona (Gonar

Adnin) a cikin duniyar da ke nuna lokacin da mulkin Allah (wanda gonar

adnin ke wakilta), zai kasance a duniya mai-zunubi.

Na biyu mene ne ya sa Allah da ya halicci wannan duniyar yake

bukatar a yi Aure da auraswa? Wannan zai kawo ƙaruwar ’yan adam,

yadda za a sami biliyoyin mutane da za su harbu da zunubi domin

dukansu suna cikin jikin Adamu.

Na uku, da shike Allah ya san tunanin zuciya kafin marmarin

aikata zunubi ya haɓaka (Ibraniyawa 4:12). Zai san burin mala’ikan nan

Lucifer na zama sarki (Ishaya 14:13-14). Mene ne ya sa ya ba Lucifer

damar shiga gonar Adnin?

Daga ƙarshe, mene ne ya sa Allah, a cikin wannan sabuwar

duniya marar aibi, ya ba bishiyar suna mai rikitarwa “Itace na sanin

nagarta da mugunta”, ya kuma bari Adamu da Hawa’u suka san da shi ta

66
wurin umurtar su kada su ci daga gare shi, ya kuma sa Lucifer ya san da

shi, da kuma umurnin nan? Amsar tana samuwa a abinda Allah ya faɗi

cikin Afisawa 3:10.

Domin yanzu ta wurin Ikkilisiya hikima iri iri ta Allah ta samu ga

sarautai da ikoki cikin sammai.

A cikin wannan aya Allah ya nuna mana cewa a dukan zamanai da

suka wuce, Allah ya halicci tsare tsare daban daban na sammai. Wannan

tsarin zai yi aiki na tsawon shekaru 13,023 zai zama abin kallo wanda

zai nuna hikima da ɗaukakar Ubangiji Yesu Kristi.

Domin cimma wannan, Allah ya halicci wata cibiyar samaniya

shekaru 13,000 da suka wuce, ita ce duniyar mu. Wata cibiya ce ta

dabam domin zata kasance da mutane a cikinta da suke aure da kuma

haifar ’ya’ya. Duk da haka, nufin Allah ne cewa wannan cibiyar da ta fara

da mutane biyu, Adamu da Hauwa’u, zasu girma su zama biliyoyin

mutane. Dabam take domin ta faɗa ƙarƙashin la’anar Allah domin

zunubi yana mulki a ko ina. Ya banbanta domin an nuna shi a fili ga

sauran tsari na sammai da Allah ya halitta tun zamanin zamanai. Ya

banbanta domin Allah ya bayyana rana, da wata, da shekarar da zata

shuɗe. Ya banbanta domin karshensa, za a ɗauki mazaunan cikinta

miliyan 200, zuwa sama a matsayin amaryar Kristi su yi mulki da Kristi

na har abada abadin.

Ya banbanta kuma domin yawancin tsawon shekarunsa yana

ƙarƙashin mulkin wani mugun mala’ika da ya faɗi mai suna Lucifer ko

shaiɗan. Bisa ga dokan mallaka, Lucifer yayi nasara bisa ’yan adam ta

wurin samun Hauwa’u da farko, da kuma Adamu su yi wa Allah rashin

biyayya. Bisa ga namu hukuncin, ya kamata da Allah ya hallaka shaiɗan

nan take domin wannan mummunan abin da ya aikata. Amma Allah ya

barshi ya zama mai mulkin duniya da abinda ke cikinta na tsawon

shekaru 11,000 na kasancewarta. A cikin irin wannan duniyar ne Allah

ya fara gina mulkin Allah a duniya.

Dukan waɗannan tambayoyin da bayanan suna da mana’a domin

Kristi shine Ɗan Ragon da aka yanka kafin kafawar duniya. Wannan ya

tabbatar mana da cewa Allah ya zaiyana mulkokin wannan duniya da

sanin cewa zata zama mulkoki na zunubi. Zata zama kuma an tsarata ta

zama mulki wanda yayi dabam da waɗanda Allah ya halitta tun zamanin

zamanai.

Amma mene ne ya sa? Mene ne ya sa aka halicce shi dabam da

sauran mulkokin, da ikoki na cikin sammai?

Abu mai-muhimmanci shine, mala’iku da dama sun haɗa baki da

Lucifer lokacin da yake ƙulla maƙarƙashiyar zama sarki. Ta haka

ƙarƙashin la’anar Allah, suka zama aljanu, ko kuma shaiɗan ko kuma

muggan ruhohi (Yahuda 6). Sai dai babu wani bayani a Littafi Mai Tsarki

game da yiwa Allah tayaswa, sai wannan kaɗai, domin haka yana nuna

67
cewa Allah ya bari wannan ya faru domin ya yaɗa nufin Allah ga wannan

duniyar.

Kasancewar Allah ya sa Lucifer a cikin Gonar Adnin, tun kafin

shaiɗan da kansa ya san yana da burin zama sarki zuciyarsa. Ishaya

14:13-14 da Ibraniyawa 4:13), irin hanyar da Allah yake amfani da

miyagu waɗansu lokatai wajen cimma manufarsa. Misalai guda biyu sune

na Nebuchanezzar sarki Babila da ’yan’uwan goma da suka sayar da

Yusufu zuwa bauta (Farawa 50:15, 20).

Allah ya sani sarai cewa biliyoyin mutane tsatson Adamu ne

(Ibraniyawa 7:9-10, Korintiyawa I 15:22). Za a yankewa dukan waɗannan

biliyoyin mutanen hukumcin mutuwa lokacin da Adamu ya yi wa Allah

tawaye, amma Allah ya riga ya yi tanadin ceton mutane miliyan 200.

Domin cimma wannan manufa, da farko Allah ya shirya littattafai biyu.

Littafi na farko ya ambaci dukan wanda zai fito daga zuriyar Adamu.

Littafi na biyu da ake kira littafin rai na Ɗan Ragon, yana da sunaye

miliyan 200 a ciki. Allah ne da kansa zai ceci waɗannan mutanen a

matsayin Mai-Cetonsu. An ɗorawa Allah da kansa, a matsayin na

Ubangiji Yesu Kristi dukan zunuban waɗannan mutanen miliyan 200.

Kuma kasancewa an same shi da laifin waɗannan zunubai, an yanke

mashi hukumcin mutuwar wulakanci a madadin waɗannan mutanen.

Shine Ɗan Ragon da aka yanka tun kafuwar duniya. Alal hakika wannan

mummunar hukunci ya sauko a kan Kristi kafin a halicci wannan duniya.

Mun karanta a cikin IBitrus 1:20 cewa:

Wanda aka rigaya saninsa lallai gaban kafuwar duniya, amma a

ƙarshen zamani ya bayyana sabili da ku.

Mun kuma karanta a Matta 25:34 cewa:

Sa’annan shi Sarkin za ya ce ma waɗannan da ke hannun

damansa, ku zo ku masu albarka na ubana ku gaji mulkin da an

shirya dominku tun kafuwar duniya.

A Timothawus II 1:9-10 kuma, mun karanta cewa:

Wanda ya cecemu, ya kiraye mu kuma da kira mai-tsarki ba

gwargwadon ayyukan mu ba, amma bisa ga nasa nufin da alheri

wanda aka bamu cikin Kristi Yesu tun gaban madawaman

zamani, amma yanzu ya bayyana ta wurin bayanuwar Mai-Ceton

mu Kristi Yesu, wanda ya kawas da mutuwa ya haskaka rai da

dauwama ta wurin bishara.

Ka duba Ibraniyawa 4:3.

Jahannama tana nufin a mutu. A mutu kuma yana nufin rai ya

tafi har abada. Misali a cikin Zabura 16:10, Yesu yace:

68
Gama ba zaka bar raina ga lahira ba ba kwa zaka bar maitsarkinka

shi ga ruba ba.

Domin ya yi nasara bisa jahannama ransa ya tashi daga mattatu.

An tabbatar da wannan a Romawa 1:4 inda muka karanta cewa:

Aka aiyana shi Ɗan Allah da Iko ta wurin Ruhu Mai-Tsarki bisa

ga tashi daga mattatu shi Yesu Kristi Ubangijinmu.

Wannan aya tana kuma koya mana cewa za a kira Kristi Ɗan

Allah ne kawai domin ya tashi daga kabari (Jahannama). Kristi ba shi da

farko, shi Allah madawammi ne tun fil azal. An jadada wannan game da

Allah bisa ga abinda Allah ya ce a cikin Yohanna 3:16 ‘‘... ya bada dansa

haifaffe shi kaɗai”. Haifaffe yana nufin yana da farko ta yaya Allah zai yi

magana cewa Kristi yana da farko?. Yana da farko da shike ya mutu ya

kuma rayu. Ta haka, tunda ya tashi daga mattatu, za a kira shi Ɗan

Allah. Ko da shi Kristi, Allah Madawammi ne, kafin ya halicci wannan

duniyar, tilas ne ya tashi daga matattu. An tabbatar da wannan a

Ibraniyawa 1:2.

Ƙarshen waɗannan kwanaki ya yi mana magana cikin Ɗansa

wanda ya sanya magajin abu duka, wanda kuma ya yi duniya ta

wurinsa.

Wannan kuma ya tabbatar da cewa an biya cikakken bashin

zunuban zaɓɓaɓu kafin a halicci duniya.

Saboda haka, ya yiwu a yi tambaya cewa: ‘‘Dole ne Kristi ya mutu

sau biyu domin ya biya cikakken bashin zunubanmu? Ka tuna da misalin

nan na tarihi a Fitowa 17:6:

Ga shi zan tsaya a gabanka can bisa Pa cikin Horeb, za ka bugi

Pa, ruwa kwa za ya fito daga cikinsa domin mutane su sha. Musa

kwa yayi haka nan a idanun dattiɓai na Isra’ila.

Pa ɗin yana wakiltan Kristi. Musa yana wakiltar dokar Allah. Ruwa

yana wakiltar bisharar ceto wadda take samuwa domin an hukunta Kristi

sabili da a cika ka’idar shari’a. A wannan karatun mun ga cewa Musa ya

buga Kristi Dutse, sau ɗaya, shari’a, da kuma ruwan (ceto) suka ɓulɓulo

daga dutsen.

Sai dai, a cikin Littafin Lissafi 20:10-11, Musa ya buga dutse sau

biyu ruwa kuma ya fito. Amma ta haka, Musa ya yi fiye da abin da Allah

ya umurce shi yayi, saboda haka aka hana Musa damar jagorancin

’ya’yan Isra’ila su ƙetare kogin Urdun zuwa ƙasar alkawari.

Watau, an buga dutsen sau biyu yayinda abinda ake bukata kawai

shine a buga sau ɗaya. An hukunta Yesu sau biyu, ko da shike abinda

69
ake bukata kawai domin cikakken biyan bashin zunubanmu shi ne

hukumci sau ɗaya kawai.

Saboda haka, muna da tabbacin cewa lokaci na biyu da aka hukunta shi

sa’adda yake kan giciye ba domin biyan bashin zunubi ba ne. Kamar

yadda muke koyo, manuni ne na yadda ya biya bashin zunubanmu kafin

halittar wannan duniya.

Zaɓaɓɓu: Mutane Miliyan 200

Abin mamaki, Allah cikin hikimarsa ya bamu yawan mutanen da

ya zaɓa domin su sami ceto.

Zamu hakikance da cewa adadin mutanen da Allah ya yi shirin

ceto, miliyan 200 ne. Wannan ya haɗa da waɗanda za’a fyauce ranar 12

ga watan Mayu, 2011. A wannan ranar za a tashi jikin kowane mai-bi na

gaskiya wanda ya rayu kuma daga baya ya mutu, zuwa sama ya zauna

tare da Kristi. Haka kuma a wannan lokacin za a ba kowanne mai bi na

gaskiya da yake da rai madawammin jiki rayayye a kuma fyauce shi

ɗungum zuwa sama.

A cikin Ruya ta Yohanna 9:14 an ambce su (masu bi na gaskiya) a

matsayin mala’iku huɗu da aka ɗaure a bakin babban kogin Affaratis.

Yayin da kogin Affaratis yake gudana ta Babila, a cikin Littafi Mai-Tsarki,

Allah yakan kamanta shi da ƙasar Alkawari, kasar Isra’ila (Farawa 15:18;

Kubawar Shari’a 1:7, 11, 24; Joshua 1:4 da sauransu). Kogin ne ya nuna

nisan girman mulkin Allah wanda aka kamanta da ƙasar Isra’ila.

Ana kwatanta dukan zaɓaɓɓu wato, waɗanda za’a fyauce, da

mulkin Allah amma an ɗaure su a gefen (kogin Affaratis) na mulkin Allah

amma gaɓar (kogin affaratis) na mulkin Allah ya yi masu iyaka. Haka ta

faru ne domin ana danganta su da mulkin Allah lokacin da ceton su ya

zama cikakke a lokacin da suka karɓi rayayyun jikunansu. Ana kiran su

mala’iku huɗu ko kuma manzanni huɗu, domin lambar nan huɗu tana

nuna cika. Lambar nan huɗu tana jaddada cewa za’a same su a cikin

dukan duniya kuma ya haɗa har da mutun na ƙarshe da ya sami ceto.

Tilas ne mu koya mu kuma fahimci cewa wannan babban gwaji

na ɗaukaka da hikimar Allah zai kasance har abada, saboda ba zai sake

faruwa ba. Mun karanta a cikin Ruya ta Yohanna 1:18.

Ni ne mai rai, na mutu ga shi kuwa ina da rai har abada, ina

kuwa da maɓulɓulai na mutuwa da na kabari.

Kalmar nan “Ina da rai har abada” ya bada tabbacin cewa wannan

abin ba zai sake faruwa ba.

An bada lambar nan miliyan 200 sau biyu. Lambar da aka bayar

a cikin Ruya ta Yohanna 9:16 ita ce ‘‘zambar miliyan dubu maitan’’

(miliyan 200). Daga baya kuma Littafi Mai-Tsarki yace... kuma na ji

70
“lissafin su”. Wannan maganar tana tabbatar mana da cewa Allah ne ya

kafa shi kuma zai cika ba da daɗewa ba Farawa 41:32.

Sun hau kan dawakai, ta haka aka danganta su da rundunan

sama da aka misalta a Ruya ta Yohanna 19:11-16 inda muka karanta

cewa:

Sai na ga sama a buɗe ga kuma wani farin doki da mahayansa

ana ce da shi mai aminci da mai-gaskiya, cikin adalci kuwa yake

yin shari’a da yaƙi kuma. Idanunsa harshen wuta ne, bisa kansa

kuma da kambin sarauta masu-yawa, yana kuwa da suna a

rubuce wanda ba mai saninsa sai shi da kansa. Yana yafe da

kuma riga yayyafafiya da jini, sunansa kuma kalmar |Allah ne.

Rudunan yaƙi kuwa waɗanda ke cikin sama suka bi shi bisa

fararen dawakai, suna yafe da linin mai labshi, fari fat, maitsabta

kuwa. Daga cikin bakin sa kuma takobi mai- kaifi yana

fitowa, domin shi bubbuga al’ummai da shi, za ya mallake su

kuma da sanda ta ƙarfe. Yana kuwa taka wurin matsewar ruwan

anab na zafin hasalar Allah mai-iko duka. A bisa riga tasa da

bisa cinya tasa kuma yana da suna a rubuce SARKIN SARAKUNA,

DA UBANGIJIN IYAYENGIJI.”

Allah ya bayyana cewa suna maida hankali kan sulusin ’yan

Adam, kamar yadda muka karanta a cikin Ruya Ta Yohanna 9;15:

Sai aka saki mala’ikun nan huɗu, waɗanda aka tanada saboda

wannan shekara, su kashe sulusin ’yan adam.

A cikin Littafi Mai-Tsarki sulusin ’yan adam yana magana ne a

kan masu bi na gaskiya, waɗanda ake samu musamman a cikin Ikkilisiya

duk faɗin duniya Mun karanta a kansu cikin Zakariya 13: 9:

Zan kuma ratsad da kashin nan na uku cikin wuta, in tsarkake

azurfa, in nuna su kamar yadda ake auna zinariya. Za su kira

sunana, ni kwa zan ji su, zan ce mutane na ne su kuma za su ce

Ubangiji Allah ne.

Amma da shike nan da nan majami’u suka ridda Allah yayi

magana a kansu musamman a cikin littafin Ruya ta Yohanna a matsayin

sulusin da Allah zai hallaka.

Allah yana sa mutane ƙarƙashin fushin Allah, a lokacin da suka

karya dokarsa. Karya dokar Allah tana yankewa mutane hukuncin

mutuwa. Amma kuma akwai hukunci ga dukan waɗanda suke cewa suna

biyayya ga Littafi Mai-Tsarki. Zai tabbatar da cewa basu yin biyayya da

shike ba a fyauce su ba. Sune sulusin na ’yan adam. Ta haka aka

71
ayyana waɗanda ba a fyauce su ba, kamar yadda muka karanta a cikin

Ruya ta Yohanna 9:17-18:

Ga kuwa yadda na ga dawakan a wahayin da aka yi mani,

mahayansu suna saye da sulkuna, launinsu ja kamar wuta, da

shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta, kawunan dawakan

kuma kamar na zaki, wuta kuma da hayaƙi da farar wuta suna

fita daga bakinsu.

Za a sake kashe waɗanda suke cewa su masu bi na gaskiya ne,

amma aka barsu a baya a lokacin fyaucewa kasancewan suna jimre

fushin Allah kamar yadda yake saukowa a ranar shari’a. Ga abinda Allah

ya ke koyarwa a cikin waɗannan ayoyin.

Matta 12:41-42 Nawiyawa za su tashi tsaye a ranar shari’a tare

da wannan tsara zasu kwa kashe ta; gama su suka tuba da

wa’azin Yunana ga kwa wanda ya fi Yunana girma a nan;

sarauniyar kudu za ta tashi tsaye a ranar shari’a tare da wannan

tsara za ta kwa kashe ta; gama daga nisan duniya ta zo garin ta

ji hikimar Solomon; ga kwa wanda ya fi Solomon girma a nan.

Luka 22:30 domin ku ci ku sha tare da ni cikin mulki na, kuma

zaku zamna bisa kursiyai kuna yin shari’a bisa kabilun Isra’ila

goma sha biyu.

Waɗannan duka suna cikin abinda masu ilimin tauhidi suke

magana akai yayinda suke batun Armaggeddon. A lokacin an rigaya an

fyauce mayaƙan masu adalci, mutanen majami’u zasu yi ta kuka da

cizon haƙora (Matta 8:11-12; 13:42, 50; 22: 13; 24:51; 25:30, Luka

13:28) domin an barsu a baya.

Miliyoyin Waɗanda Basu Da Ceto, Sun Mutu Basu Da Masaniya A Kan

Fushin Allah

Abin da ya bamu mamaki shine, mun koya cewa yawancin

mutanen da basu da ceto waɗanda suka mutu ko kuma zasu mutu kafin

ranar 21 ga watan Mayu, 2011, basu ji ko kuma sanin cewa fushin

Allah yana bisa kansu domin zunubansu ba. Ta yaya wannan zai

kasance? Mun koya cewa fushin Allah yana nan ta fannoni da dama. Ya

kuma ƙunshi waɗannan:

1. Babbar kunya.

2. Kisa (Mutuwa, Jahannama)

3. Rasa ’yancin wannan rayuwa.

72
4. Asarar gadon rai na har abada, tare da asarar gadon sabuwar

sama da sabuwar duniya.

5. Mutuwa ta har abada inda ba za’a ƙara rayuwa ba.

Yayin da dukan waɗannan hukuncin zasu sauko kan wanda bashi

da ceto, mutumin yakan mutu ba tare da ya san cewa mutuwarsa

sakamakon zunubi ne a rayuwarsa ba. Idan shi ɗan Ikkilisiya ne ya yiwu,

ya gaskanta da koyarwar nan irin ta al’ada cewa, masu zunubi za su

shiga jahannama inda zasu sha azaba ta har abada. Amma wannan ba

abin damuwa ba ne a gare shi domin ya hakikance da cewa an maye

haihuwarsa, kuma shi cikakken ɗan Ikkilisiyar ne.

A hakikanni gaskiya rayuwar yawancin ’yan Ikkilisiya yawancin

lokaci kuma a rayuwar waɗanda basu cikin Ikkilisiya sun gaskanta da

cewa mutuwa wani lokaci ne mai daraja na zuwa ƙasa mafi kyau. Ta haka

ake kallon mutuwa a matsayin nasara ko da shike ta haɗu da baƙin ciki

domin rabuwa da ƙaunatattu da kuma abubuwan jin daɗi da mutumin

yake morewa a wannan rayuwar.

Sai dai, marar ceto da ya mutu, to ya yi mutuwa ta har abada. Ba

zai taɓa ɗanɗana hukuncin Allah da sanin sa ba. Gaskiya ne a lokacin

fyaucewa, za a fidda gangan jikinsa da aka sa a kabari a kunyace, Allah

da kuma ’ya’yan mulkin sama zasu kunyata shi. Amma marar ceton da

ya mutu ba zai san abinda ke faruwa ba. Gaskiya ne yayi asarar gadon

haihuwarsa, rai na har abada da gadon sabuwar sama da sabuwar

duniya. Amma bai san wannan yana faruwa ba.

Bugu da ƙari lokacin da waɗannan mutane suke raye koyaushe

akwai babban jin daɗi da murna. Sun ɗanɗana abubuwa kamar ƙaunar

iyali da jin daɗin rayuwa a duniya mai kyau. Saboda haka, rai da mutuwa

suna da kyau ko da shi ke ba su taɓa samun ceto ba. To ina fushin Allah

a kan waɗannan mutane da basu taɓa samun ceto ba? Sai kace mun

ɓata hanya a fahimtar tsarin shari’a na Allah. Amma bamu ɓata hanya

ba. A maimakon haka, muna koya cewa, babban abinda duniyar nan ta

fi maida hankali a kai ba kan shirin ceto na Allah, ko kuma shirin

shari’a na Allah ba ne. A bisa hikima da ɗaukakar Allah ne. Ka tuna mun

koya cewa dalilin da yasa Allah ya halicci ’yan adam ya sasu a duniya

shine domin ya samar da gagarumin hoto mai kusurwa uku inda dukan

ikoki da mulkoki na sammai zasu ga babbar hikima da ɗaukakar Allah,

yayin da Allah yake shirin aikin ceto cikin fiye da shekaru 13,000 da aka

shafe ana aikata zunubi.

Saboda haka muka tarar, misali, cewa Allah yana gaba da mai

zunubi (Zabura 5:5), kasancewa fushinsa na Allantaka yana bisa kanshi,

duk da haka jinƙansa da girma yake zuwa ga hallittun sa duka har da

masu zunubi. Mun karanta a cikin Matta 5:45 cewa:

73
Domin ku zama ’ya’yan ubanku wanda ke cikin sama; gama ya

kan sa rana tasa ta fito ma miyagu da nagargaru, yakan aiko da

ruwa bisa masu adalci da marasa adalci.

Ka yi tunani a kan manyan albarkun dake ƙulɓulowa daga hasken

rana mai kyau da ruwan sama dake yiwa duniya baye. Waɗanda ba a

zaɓe su zuwa ceto ba, zasu ci moriyar waɗannan albarkun dai dai da

waɗanda suke da ceto.

An bayyana rahamar da Kristi yake da ita ga dukan ’yan adam a

wurare biyu cikin Littafi Mai-Tsarki inda muka karanta cewa Yesu yayi

kuka: Mun karanta waɗannan kalmomin masu sosa rai a cikin Yohanna

11:33-35:

Sa’adda Yesu ya ganta tana kuka, Yahudawa kuma waɗanda suka

zo tare da ita suna kuka, ya ji haushi cikin ruhunsa, yana jin zafi

a ransa, ya ce ina kuka ajiye shi? Suka ce masa Ubangiji ka zo ka

gani, Yesu yayi kuka.

Allah madawammi, Ubangiji Yesu ya nuna tausayinsa mai-girma

da cewa mutuwa ta shigo wannan duniya. Mun karanta a cikin Luka

19:41-44 cewa:

Sa’adda yayi kusa, ya hangi birni yayi kuka a kanta, ya ce da ma

kin sani a cikin wannan rana, har ke ma, abinda ya tabbata ga

salama, amma yanzu a ɓoye ya ke a idanunki. Gama kwanaki

zasu abko maki inda maƙiyanki zasu gina maki ganuwa su sa ki a

tsaka su tsare ki daga kowanne sasa, su fyaɗe ki a ƙasa, da

’ya’yanki a cikinki ba zasu bar ko dutse ɗaya bisa wani a cikinki

ba. Da shike ba ki lura da kwanakin ziyartanki ba.

Urushalima da Littafi Mai-Tsarki yake magana a kai a nan ta

ƙunshi dukan Isra’ila da dukan majami’u waɗanda suke wakiltar mulkin

Allah a duniya, suka kuma ridda. Saboda haka membobin su suna kan

hanya zuwa jahannama. Sun yi wa Allah ba’a. Sun tsara shirinsu na ceto.

Sun murɗa Littafi Mai-Tsarki da sauransu.

Duk da haka Kristi yana ta kuka domin tilas ya sauko da cikakken

fushinsa bisan su. Muna iya ganin irin ɗaukakar da Kristi yake da ita,

yayinda, ta wurin kuka kan Urushalima, ya nuna jinƙansa zuwa garemu

da mulkoki da ikokin a sammai?. Ba abin mamaki ba ne da Allah yace,

kamar yadda muka karanta cikin Ezekiel 33:11, “Bani da wani jin daɗi

cikin mutuwar mugu ba’’

Mulkoki da ikoki a duk faɗin samaniya sun shaida wannan. Sun

ga duniyar da ta shafe shekaru 11,000 ƙarƙashin mulkin mugun

mala’ikan nan da ake kira shaiɗan. Sun bayyana yadda mutane ƙalilan

suka sami ceto, mutane takwas lokacin da Allah ya gargaɗi duniya game

74
da hallaka mai zuwa a zamanin Nuhu. Suna ganin bangaskiyar Ibrahim,

da rashin bangaskiyar ’ya’yan Isra’ila, da suka hallaka a cikin jeji domin

rashin bangaskiya. Sun shaida yadda Asuriyawa da ƙasar Yahuda da

kuma Babila suka hallaka ƙasar Isra’ila domin muguntar ta.

Ta yaya Kristi zai tafiyad da duniyar dake da biliyoyin mutanen

mattatu cikin ruhaniya waɗanda shaiɗan ne yake mulkinta?

Ta yaya Kristi zai sarrafa duniyar da kowanne mutumin da ke cikinta

yake matacce cikin ruhaniya, kasancewa shi bawan zunubi ne da kuma

shaiɗan?.

Ta yaya Allah zai tafiyadda da duniya da aka la’anta wurin da

mutanen da ke cikinta la’antattu ne, daga cikinsu za a ɗebi kaɗan su

zama mutanen Allah?

Wuri na ƙarshe da za a maida hankali a kai shine Ikkilisiya ta har

abada, mutanen nan miliyan 200 da sunayen su ke cikin littafin rai na

Ɗan Rago. Ta yaya zasu zauna a ciki a kuma fitar da su daga biliyoyin

miyagun mutane da shaiɗan yake mulki bisan su, wanda yake gaba da

Kristi?

Ta yaya Allah zai tafiyad da duniyar da yawancin mutanen da ke

cikinta mattatu cikin ruhaniya, waɗanda shiɗan yake mulki a bisansu,

amma a cikin wannan duniyar akwai mutane ƙalilan da aka yi niyar ceto

amma ba su tuba ba, da kuma waɗanda basu tuba ba?

An halicci duniyar mu domin ta nuna hikima da ɗaukakar Allah a

cikin mawuyacin yanayi. Ana ganin cikar bayanuwar ɗaukakarsa ganin

cewa Allah da kansa ya zama Mai-Ceto.

Cikin waɗannan duka, mulkoki da ikoki, sun shaida jinƙai, da

alheri, da gafara, da haƙurin Allah. Sa’annan suka shaida sake haihuwa.

Allah ya ɗauki jikin mutune ya zo duniyan nan da kansa domin ya nuna

yadda ya sha wahala kafin kafuwar duniya a madadin mutanen nan

miliyan 200 da ya zo ya ceta.

Sun ganshi a matsayin malami mai tawali’u wanda bai daina

zama Allah maɗaukaki ba. Sun ganshi lokacin mutane suka raina shi

suka ƙi shi. Sun gan shi ya jimre mutuwar wulakanci, da kunya mafi

girma, yayinda aka aiwatar da hukumcin kisa na la’ana yayinda yake bisa

giciye.

Sun kuma ga jinƙansa mai-ban al’ajibi lokacin da ɗan fashin dake

gangansa a kan giciye ya kada baki yace ‘‘Ubangiji ka tuna da ni lokacin

da ka shiga mulkinka” (Luka 23:42). Nan take dab da ƙarshen rayuwar

mutumin nan, suka shaida yadda ya sami cikakken gafara.

Sun shaida ɗaukakar tashin Kristi, da kuma ceton kusan mutane

3,000 lokacin da aka sauko da Ruhu Mai-Tsarki. Ina misalin ɗaukakar

Allah, sun kuma ga ɗaukakarsa yayin da suke ganinsa a cikin dukan

waɗannan ayyukan.

Haka kuma ’yan Adam, waɗanda suke zaune a wannan duniyar

sun sami damar shaida hikima da ɗaukakar Kristi ta wurin karanta

Littafi Mai-Tsarki a hankali.

75
Amma duniya zata zo ranar da za’a fara shari’a, 21 ga watan Mayu,

2011. Fiye da mutane biliyan 6.5 za su kasance a duniya lokacin zasu

kuma shiga kwanakin nan 153 na shari’a, kuma zasu sani ba tare da

tambaya ba cewa suna ƙarƙashin fushin Allah domin zunubansu.

Yawancinsu zasu sani lokacin da suke fuskantar fushin Allah.

Mene ne ya kawo canji nan da nan? Sune mutanen da suka shafe

shekaru 13,000 suna zaune a nan duniya cikin salama. Amma idan suna

raye ranar 21 ga watan Mayu, 2011, Za a yi wata babbar girgizar ƙasa

farat ɗaya da zata kashe yawancinsu, (Ruya ta Yohanna 16:18). Mutuwa

zata kasance a ko’ina, za a yi fama da ciwo mai tsanani da azaba a

ko’ina.

Mun karanta game da banbanci ga waɗannan mutane a cikin

Luka 12:45-48:

Amma idan bawan nan ya ce cikin zuciyarsa, Ubangijina yana

jinkirin zuwa, har ya tasar ma dukan ma’aikata, maza da mata ya

ci, ya sha ya yi maye, Ubangijin wannan bawa zaya zo cikin ranar

da ba ya sa tsammani ba, cikin sa’a wanda baya sani ba, za ya

raba shi a tsaka, ya sanya masa rabonsa tare da marasa- aminci.

Wannan bawa kwa wanda ya san nufin Ubangijinsa, baya shirya

ba, za’a duke shi dayawa; Amma wanda ba ya sani ba, ya kwa yi

abinda ya isa duka, za’a duke shi kaɗan. Kuma dukan wanda an

ba shi dayawa za’a nemi dayawa a gareshi, wanda kwa an sanya

masa dayawa a hannu, a wurinsa za’a fi biɗa.

Muna rayuwa a zamanin da Allah ya bayyana ainihin lokacin da

duniya zata ƙare. An ba duniya wannan bayanin kuma mutanen duniya

suka ƙara sani, domin marasa ceto su iya yin kuka ga Allah domin

jinƙai. Ya yiwu mutane da yawa kamar mutanen Nineveh a lokacin

Yunana, za su sami jinƙan Allah.

A hakikanin gaskiya, a lokutan da suka gabata an sha jin koyaswa

cewa ranar kaza da kaza duniya zata shuɗe. Kuma a gaskiya dukan

waɗancan lokatan ba daidai ba ne. Amma a yau faɗakarwar da ake yi a

kan lokacin dawowar Kristi da kuma ranar shari’a ya banbanta da na

kwanakin baya. Ayoyin da aka ambata a baya sun nuna gagarumin

muhimmancin kasa kunne ga faɗakarwar ƙarshen lokaci da Littafi Mai-

Tsarki yake bayarwa. Misali an haɗa da waɗannan batutuwa a cikin

gargaɗin:

1. Littafi Mai-tsarki baki ɗaya dokar Allah ne, kuma kowacce

kalma daga ainihin harshen ta fito ne daga bakin Allah kai

tsaye. Saboda haka ya kamata majami’a da duniya su sani

cewa Littafi Mai-Tsarki shine mafi iko duka, fiye da wani iko

da aka sani a lokutan baya. Tilas ne a saurare shi a kuma yi

biyaya da shi.

76
2. Akwai shaidu da dama a cikin Littafi Mai-Tsarki, dangane da

ranar 21 ga watan Mayu, 2011, da 21 ga watan Octoba, 2011

da suka tabbatar da sahihancin waɗannan ranakun. Wannan

bayanai ne masu yawa da duniya bata taɓa sani ba, kuma ya

shafi dukan duniya.

3. Wannan bayanin lokacin yana samuwa a ko’ina cikin duniya a

yanar gizo da kuma gajeren zango na tashar radio. Akwai shi

kyauta a harsuna da yawa da za a iya aikawa ga dukan wanda

ya rubuto ko ya kira ya tambaya. Ya kamata kowa ya sani.

4. Mutane suna ba’a da wofinta wannan bayani, yayinda da

dama kuma suke musun gaskiyar bayanan.

5. Waɗanda ba a fyauce su ba ranar 21 ga watan Mayu. 2011,

zasu mutu a ranar ko kuma wani lokaci kafin ranar 21 ga

Octoba, 2011. A lokacin dukan duniya zata yi gobara idan

aka mutu, babu kuma wani sanin fushin Allah.

Sai dai idan ba mutuwa ta auku ba, akwai babban fahimtar

fushin Allah, kuma waɗanda suke raye, zasu ci gaba da zama ƙarƙashin

zafin aloba da zata mamaye duniya a lokacin ranar shari’a kwanakin nan

na 153 daga 21 ga watan Mayu, 2011, zuwa 21 ga watan Octoba, 2011,

zasu yi matsanancin fama da waɗannan abubuwa:

1. Kunya da la’anar zama ƙarƙashin fushin Allah.

2. Sanin cewa murna da ta’aziya da dai sauransu na wannan

duniya ya ƙare.

3. Sanin cewa basu da gado nan gaba. Mutuwa ce kawai take

jiransu, kuma wannan zai faru ne kafin 21 ga watan Oktoba,

2011.

4. Waɗanda suke raye a lokacin zasu yi fama da ciwo da raɗaɗi

na jiki.

5. Sanin cewa babu wani jinƙai daga wurin Allah. Hallakar

wannan duniya ita ce abu na ƙarshe na tarihi da mulkoki da

ikoki na cikin sammai zasu shaida. Duka ya nuna ɗaukaka da

hikimar Allah.

Wannan gabatarwa na fushin Allah mai tsanani abin ban tsoro ne.

Ya zama abin ban tsoro musamman idan muka tuna cewa zai faru ne na

’yan watanni kuma zai faru babu jinkiri.

Amma ka yi tunanin irin jinƙan Allah. Zai iya kawo ranar

fyaucewa, da ranar sharia ta wurin zuwa kamar ɓarawo da dare, daga

nan yawancin mutane na duniya zasu zama babu faɗakarwa ta kowacce

iri. Amma Allah a cikin yalwar jinƙansa, yana bamu lokacin faɗakar da

duniya game da hukunci mai zuwa. Abin baƙin ciki shine zai zo kamar

ɓarawo da dare ga waɗanda suke musun sanin wannan domin basa son

duniyar nan ta ƙare.

77
Har wayau, Allah ya bada misalin tsohon birnin Nineveh a cikin

littafin Yunana. Basu san komi ba game da Littafi Mai-Tsarki, kuma suna

da kwana 40 ko kuma ƙasa da haka da zasu ɗauki mataki game da

wannan gargaɗin. Ya kamata mu koyi darasi daga gare su.

1. Suna da cikakken imani ga Allah, basu jayayya da Allah.

2. Sun bincike kansu da aminci, sun gane cewa su masu zunubi

ne kuma sun cancanci fushin Allah.

3. Sun bayyana a fili girman tawali’un su ta wurin zaunawa a

cikin tsummoki da toka. Haka yake ga bawan mafi tawa’iu da

jami’i mafi girma da mafi daraja, sarki.

4. Sun juyo daga zunubansu, kuma nan da nan suka yi ƙoƙarin

rayuwar da zata gamshi Allah.

5. Basu nemi komi a wurin Allah ba, amma suka yi kuka ga

Allah suka ce watakila Allah zai canza tunaninsa, kuma ba

zai hallaka su ba.

Ya kamata mu maida hankali sosai ga abinda mutanen zamanin

Nuhu suka yi, lokacin da aka gargaɗe su, game da hallaka mai zuwa.

Abin tsoro ne a karanta yadda aka kwatanta hallakar zamaninmu da na

zamanin Nuhu. Mun Karanta a cikin Matta 24:37-3 cewa:

Kuma kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka nan kuma

bayanuwar Ɗan mutum zata zama; Gama kamar yadda suna ci,

suna sha suna amre, suna amraswa a cikin kwanakin da ke

gaban ruwan rigyawa, har randa Nuhu ya shiga cikin jirgi, ba su

sani ba, har rigyawa ta zo ta kwashe su duka, haka nan kuma

bayanuwar Ɗan mutum zata zama.

Abu ɗaya ya zama tabbas. Matakin da ya kamata a ɗauka kuma

wanda yake da amfani game da hallakar dake tafe ita ce canza burina, da

tunani na da niyya ta, da shiri na da bege na a nan duniya. Nan da nan,

ya kamata in sani cewa abinda ya kamata ya zama da muhimmanci da

zan maida hankali a kai shine cewa a cikin ’yan watani ƙalilan wannan

duniya zata zo ƙarshe. A cikin waɗannan watannin da suka rage wanne

abu ne mafi muhimmancin ga rayuwata da ta iyalina? Hakika bashi da

wata nasaba da ganin cewa rayuwata a nan duniya tana da daɗi.

A hakikanin gaskiya idan ni mai bi ne na gaskiya, dole in sani

cewa a matsayi na na mai-tsaro, dole in damu da cewa ba iyalai na

kaɗai ba, amma dukan duniya sun san da wannan labari mai ban tsoro

na hallaka duniya.

Watau, idan har gaskiyar gabatowar ƙarshen zamani bai sani na

sake tunani da tafiyar da harka ta ba, ya kamata in amsa wannan

tambaya: Shin na gaskata gaskiyar Littafi Mai-Tsarki cewa ranar 21 ga

78
watan Mayu, 2011 ita ce ranar fyaucewa da kuma farkon ranar sharia?

Ka tuna da faɗakarwar Luka 12:47.

Allah ɗaya ne jiya da yau, da har abada (Ibraniyawa 13:8).

Mutanen Nineveh sun nuna mana hanya, kuma ya kamata mu bi

ta hanyar yanzu da shike mun sani ba tare da wata tambaya ba cewa

ranar shari’a tayi kusa. Allah ya yi bayani da tabbacin cewa yau ana

ceton ɗumbin mutane da ba wanda zai iya ƙirgawa (Ruya ta Yohanna

7:9-14). Allah ya nace da cewa shi ba mai tara bane (Romawa 2:11).

Saboda haka akwai babban bege gare ka. Kana da babbar dama kamar

kowane mutum a cikin duniya na zama zaɓɓaɓe na Allah.

Ka fara karanta Littafi Mai-Tsarki kana kuma addu’a cewa ko

Allah zai taimake ka ka ƙara zama mai biyyaya da shi sosai. Ka roƙi Allah

ya sa ka zama mai tawali’u. Don kawai shafe shekaru kana aikin fasto

ko kuma kai memban Ikklisiya mai aminci, ba zai saka ka same

tagomashi na samun ceto ba. Babu wani wuri na alfarma. Kuma ya yiwu

majami’ar ka ko fasto, ko shaidar bangaskiya sun zama allahnka, domin

duk wani abinda muka dogara gareshi ya zame mana allah.. Ya kamata

dogararmu ta kasance a cikin Littafi Mai-Tsarki kaɗai. Ko da shike akwai

abubuwa da dama a cikin Littafi Mai-Tsarki da ba mu fahimta ba, tilas ne

mu fahimci cewa duka ya fito ne daga bakin Allah.

Kada ka daina kuka zuwa ga Allah domin neman jinƙai. Amma

kayi haka kana la’akari da cewa babu ɗaya daga cikin mu da ya cancanci

jinƙan Allah. Saboda haka zamu je gareshi, muna roƙo, muna nema ‘ya

Ubangiji ko yana iya yiwuwa ni ma in sami ceto.

79
Sura Ta Bakwai

Ceto

Su wane ne ko ina masu zunubin suke waɗanda ba za’a jefa su

cikin jahannama ba? Babu wanda ya sani. Lokacin kawai da zamu iya

hakikance cewa muna ɗaya daga cikin zaɓɓaɓu na Allah shine lokacin da

mu ka karɓi sabon ruhu rayayye daga wurin Allah. Lokacin da wannan ta

faru, zamu sani ne kawai domin Allah ya zaɓe mu mu sami ceto, kuma

ya rigaya ya tanada dukan komai domin cetonmu. Za mu sani cewa

cetonmu gaba ɗaya alheri ne da jinƙan Allah kuma babu wani abu da

muka yi da ya kaimu ga samun cetonmu.

Idan Allah ya ba mutum sabuwar zuciya da sabon ruhu (Ezekiel

36:26), Allah yana shirya wannan mutumin ne domin ya zauna tare da

shi har abada. Sabuwar zuciya ko sabon ruhu, wanda muke kuma kira

sabon ruhu rayayye, yana sake rayuwar mu yadda zamu yi marmarin

aikata nufin Allah. Bugu da ƙari, mukan damu ƙwarai idan muka aikata

zunubi, amma zai iya yiwuwa mu aikata zunubi domin muna cikin jiki

wanda ba a cece shi ba. Saboda haka kafin mu zama ’ya’yan sabuwar

sama da sabuwar duniya, za’a kuma bamu sabon ruhu rayayye. Allah zai

iya ba dukan wanda Allah ya zaɓa sabon ruhu, a kowanne lokaci na

rayuwar zaɓɓaɓen mutumin. Zai iya zama kafin haifuwa ko kuma minti

ɗaya kafin mutuwa. Aiki ne wanda Allah ya shirya gaba ɗaya.

Amma zai faru ne lokacin da zaɓaɓɓen mutumin yake ƙarƙashin

jin maganar Allah (Romawa 10:17). Shi ya sa muke ƙoƙarin ƙarfafa

kowane mutum a duniya ya saurari Littafi Mai-Tsarki. A gaskiya ma,

Allah ya ɗokace mu da mu aika da maganar Allah cikin dukan duniya,

domin kowa ya kasance ƙarƙashin jin Littafi Mai-Tsarki.

A sa mutane a cikin yanayin jin maganar Allah shine sa su

ƙarƙashin dokar da Allah ya ba ’yan adam su yi biyayya ga Littafi Mai-

Tsarki. Yin biyayya da Littafi Mai-Tsarki yana bukatar mu karanta ko mu

saurari Littafi Mai-Tsarki. An umurce mu da mu sami ceto. An umurce

mu mu tuba daga zunuban mu. An umurce mu, mu yi addu’a domin

jinƙan Allah. An umurci wanda bashi da ceto yayi ƙoƙari ya shiga mulkin

Allah (Luke 13:24). Wannan kalmar “ƙoƙari” daga kalmar Helenanci ce

wadda take nufin raɗaɗi. Kamar mai tsere ne wanda yake fama domin ya

yi nasara a tsere.

Nan ne abin alajibi na ceto yake. Domin Allah ya halicci mutum a

cikin kamanni da surarsa, ko da shike mutum mattace ne a ruhaniya, zai

yi ƙoƙari da dukan ƙarfinsa ya bi umurnin Allah. Saboda haka zai saurara

a hankali ya ji maganar Allah yana ƙoƙari yayi biyayya da umurnin Allah.

Yadda Allah ya ke danganta wannan ƙoƙari wani abu ne wanda ya fi

gaban ganewarmu. Babu shakka bai kamata mu gaskanta da cewa

ƙoƙarin da muke yi na shiga mulkin Allah wani abin yabawa ba ne ko

80
kaɗan. Ko kuma cewa ƙoƙarin da nake yi zai bani wani tabbaci da cewa

zan sami ceto.

Gaskiya ne cewa ta wurin ƙoƙarin da nake yi zan ƙara sanin

littattafan dokokin Allah wato Littafi Mai-Tsarki. Gaskiya ne a cikin

ƙoƙari na, zan ƙara neman nufin Allah, maimakon nawa nufin. Gaskiya

ne cewa a cikin ƙoƙari na zan ƙasƙantar da kaina in yi kuka ga Allah

domin jinƙan sa. Gaskiya ne a cikin ƙoƙarin da zan ƙara gane cewa dole

ne in dogara ga Ubangiji, idan shirinsa ne ya cece ni. Gaskiya ne cewa a

cikin ƙoƙari na ina da bege mai-girma cewa nima zan yi zama ɗaya daga

cikin zaɓɓaɓu na Allah. Gaskiya ne cewa a yau, Allah yana ceton ɗumbin

mutane da babu mai-iya ƙirgawa, kuma ya yiwu ni ma a zaɓe ni a cikin

waɗannan mutanen.

Gaskiya ne kuma cewa Allah yana mulki akan masu ceto da

marasa ceto. Watau Allah yana iya sa wanda ba shi da ceto ya aikata

nufinsa daga lokaci zuwa lokaci, ko da shi ke Allah ba shi da shirin ya

cece wannan mutumin. Hakanan yayinda mutumin da bashi da ceto

yake ƙoƙarin shiga mulkin Allah dukan abinda ya aikata da ya kasance

biyayya da Allah, ya yiwu Allah ne yake aiki a cikinsa ko da shike ba ya

cikin waɗanda Allah ya zaɓa. Ko kuma watakila ƙoƙarin wannan

mutumin ne, yayi biyayya ga Allah, ko kuma ya haɗa duka da aikin Allah

da aikin mutumin. Allah ne kaɗai ya san daidai abin da yake faruwa a

cikin rayuwar mutumin.

Amma duka wannan aikin Allah ne. Mutunin da bashi da ceto ba

zai iya sanin ko aikin Allah ba ne ko na shi ne yake shafar rayuwarsa.

Abinda kawai zai iya tabbatarwa shine idan ya sami ceto to ya kasance

ne gaba ɗaya aikin Kristi ne. A cikin Joel 2:12-13 mun karanta cewa:

Amma ko yanzu, in ji Ubangiji ku juyo mani da dukan zuciyarku,

tare da azumi da kuka da baƙin ciki, ku tsaga zukatanku ba

tufafinku ba, ku juyo wurin Ubangiji Allahnmu, gama shi mai

alheri ne, cike da juyayi, mai jinkirin fushi, mai yalwar jinƙai, yana

sake nufinsa a kan masifan da ya shirya.

Idan wanda ba shi da ceto ya gane cewa yana ƙara gaba da

zunubi kuma ya fi murna lokacin da yake aikata nufin Allah, yana kuma

da marmari da sha’awa yayi biyayya da dukan umurnin Littafi Mai-

Tsarki, watakila, Ruhun Allah ne yake shaida tare da nasa ruhun cewa ya

sami ceto.

Dole mu tuna cewa Allah yana da ’yanci ya umurci ’yan adam suyi

biyayya da dokokinsa. Domin an halicci ’yan adam a cikin sura da

kamanin Allah, ɗan adam kamar Allah da kansa yana ƙarƙashin dokar

Allah, Littafi Mai-Tsarki. Idan mutum yana zaune a cikin duniyar nan

kuma bai taɓa jin komai daga Littafi Mai-Tsarki ba, tilas ne Allah ya

shirya ma wannan mutum hanyar da zai kasance ƙarƙashin jin Littafi

81
Mai-Tsarki idan mutumin yana ɗaya daga cikin zaɓaɓɓu na Allah.

Wannan zai iya faruwa a kowanne lokaci cikin rayuwar mutumin.

Duk da haka Littafi Mai-Tsarki ya damu ƙwarai game da waɗanda

suka karanta Littafi Mai-Tsarki, ko suka ji umurnin Allah da kunnuwansu

amma ba su jin Littafi Mai-Tsarki. Ta yaya wannan zai kasance? Mun

kwatanta cikin Kubawar Sharia 28:45 cewa:

Kuma dukan waɗannan la’anoni za su sauko maka, su bi ka, su

cimmaka, har ka hallaka; domin ba ka lura da muryar Ubangiji

Allahnka ba, da zaka kiyaye dokokinsa da farillansa waɗanda ya

umurce ka da su.

Mun kuma karanta a cikin Irimiya 29:17-19 cewa:

In ji Ubangiji mai runduna, ga shi zai aika masu da takobi, da

yunwa da alloba, in maishe su kamar munanan ɓaure, waɗanda

ba su ciyuwa domin muninsu. Zan runtime su da takobi, da

yunwa da aloba, in bashe su domin a yi shillo da su a cikin

dukan mulkokin duniya, su zama abin la’ana, abin al’ajibi,

abin reni, abin zargi, a cikin dukan al’ummai inda na kore su,

don basu kasa kunne ga zantattukana ba, in ji Ubangiji, waɗanda

ina aike masu da su ta bakin bayina annabawa, ina assubanci ina

aikansu: amma kun ƙi ji, in ji UBANGIJI.

Kalmar nan “kasa kunne” a cikin waɗannan gargadi guda biyu,

waɗanda suka yi kama da yawancin faɗakarwar da aka rubuta a cikin

Littafi Mai-Tsarki, yana nufin a ji a kuma yi biyayya. Allah yana koya

mana cewa idan muka ji maganar Allah dake cikin Littafi Mai-Tsarki da

kunnuwan mu amma bamu yi ƙoƙari mu yi biyayya da abin da muka ji

ba, daidai yake da rashin jin maganar Allah. waɗannan mutane sun sa

kansu da gangan a waje daga inda Allah yake ceto. Ra’ayin da suke da

shi na ceto ko kuma waɗansu koyarwa na Littafi Mai-Tsarki ya hana su

ƙasƙantar da kansu su ji su kuma yi marmarin biyayya da umurnin da

gaskiyar Littafi Mai-Tsarki.

Duk da haka akwai bege kyakkyawan bege ga waɗanda suka ƙasƙantar

da kansu suka amince da zunubansu, suka kuma juyo daga tunanin da

suke da shi a da, suka yi ƙoƙarin biyayya da dukan Littafi Mai-Tsarki,

kuma suka ƙaskantar da kansu suka yi kuka ga Allah domin jinƙan sa.

Gaskiya ne Littafi Mai-Tsarki ya koyar da cewa fushin Allah yanzu

yana kan kowacce majami’a da suke samuwa a duk faɗin duniya.

Majami’u ne wakilan mulkin Allah a duniya na tsawon shekaru 1,955.

Abin baƙin ciki shine, suna amfani da sunan Allah suka riƙa koyarwa sun

kuma ci gaba da koyarwar da ta saɓawa koyarwar Littafi Mai-Tsarki,

suna cewa Littafi Mai-Tsarki ne tushen koyarwarsu. Daɗin daɗawa,

shaiɗan ne a maimakon Kristi, mai mulkinsu na ruhaniya. A yau, babu

82
wani bege ga wata Ikklisiya da ke cikin dukan duniya. Ana shirya

waɗanda suka rage a cikinsu zuwa shiga ranar shari’a.

Juyowa ne kawai daga yanayin bautar shaiɗan cikin ruhaniya da

kuma gujewa daga majami’u da kuma zuwa da karayar zuciya ta

ruhaniya ga Allah na Littafi Mai-Tsarki kuma su zama ƙarkashin jin

maganar Allah, shine begen kowane mutum.

BARI ALLAH YAYI MANA JINƘAI

83
FARAWA

2:17 44

15:18 28,70

25:29-24 33

41:32 71

50:15 68

50:20 68

FITOWA

17:6 69

LITTAFIN LISSAFI

20:11 38

KUBAWAR SHARI’A

1:7 70

11:24 70

21:17 33

28:16-68 68

28:20 40

28:45 40,82

33:11 64

JOSHUA

1:4 70

7:18-26 54

ALKALAWA

2:16 2:16

ISAMAILA

8:20 22

IISAMA’ILA

1:19 14

1:24 14

2:5 14

ƊAUKAKA GA ALLAH

Jerin Ayoyi da shafi

18:33 15

AYUBA

4:20 30

ZABURA

5:5 11

7:8 23

7:11 23

9:19 23

16:10 42,62

26:1 23

51:5 11

67:4

72:1-4 23

103:6 23

119:106 17

MAI WA’AZI

8:5-6 8,13,17

8:5-7 V

ISHAYA

10:23-26 30

14:13-14 66

40:2 38

53:12 41

54:7-8 43

55:7-8 43

57:20 26

IRMIYA

7:33-82 52

17:18 28

29:17-19 82

46:28 30

84

EZEKIEL

3:17 V

18:20 24

18:23 10

18:32 10

33:2-7 18

33 3

33:2-7 18

33:11 15

37 51

37:4-5 52

37:12-13 51

DANIEL

6:26 66

7:13-14 56

12:2 51

12:4 52

12:9 51

JOEL

2:12-13 81

3:9-16 55

YUNANA

4:11 70

NAHUM

1:6 30

1:8 30

3:5-6 53

ZACHARIA

13:9 71

MALACHI

4:1 30
MATTA

3:17 37

4:24 31

5:44 14

5:45 73

7:22-23 52

8:6 26

8:11-12 30,44,52,71

11:23-24 61

12 22,23

12:36 23

12:41 32,47

12:41,42 70

13:42 30,41,71

13:49-50 30,52

13:50 30,52

20:18 39

22:36,37-40 13

24:27-31 60,61

24:28 61,62

24:37-39 76

24:57 71

25:30 30,71

25:34 32

26:39 66

26:63-64 39

27:19 61

27:46 39

27:51-53 39

27:62-66 39

28:11-15 61

MARKUS

4:39 49

4:41 49

5:13 27

9:43-44 29

11:14 36

15:28 37

LUKA

2:48 32

3:6 37

10:29-37 14

12:45-48 76

12:47 79

13:24 80

13:26-28 56

13:28 34

15:31 33

16 31,41

16:22 31

16:23 31

16:24 24,32

16:25 31

17:36-37 56

19:41-44 15

21:22 19

22:30 72

23:4 38

23:22 39

23:42 75

23:43 43

23:46 39

YOHANA

1:14 11

1:18 37

1:51 58

3:16 69

5:28-29 51

11:33-35 74

11:50-51 39

14:21 11,12

19: 7 39

19

19:6

AYYUKAN MANZANI

1:6 9,3,18

1:6-8 v

1:7 18

1:7-8 18

1:8 18

1:11 58

20:38 31,32

86

24:15 51

ROMAWA

1:4 36,42

2:11 79

5:12 45

6:23 11,41

8:38 65

10:17 80

14:10-11 23

14:12

I KORINTHIYAWA

6:2-3 54

15:22 26,45

15:26 27,31

15:44 52

15:51-52 45

II KORINTHIYAWA

5:10 8,23

5:21 45

GALATIYAWA

2:30 40

3:13 40

AFISAWA

1:19-23 66

1:21 66

2:5 45

3:10 65

3:10-11 44

6:12 65

KOLOSIYAWA

1:16 65

1:17 36

1:18 36

2:10 65

2:13 45

2:15 65

ITASSALUNIKAWA

4:13-17 45
5:1-4 21

5:2 8

5:2-6 19

II TASSALUNIKAWA

1:10 44

2:11 43

ITIMOTHAWUS

3:15 4

II TIMOTHAWUS

1:9 37

1:9-10 37

TITUS

3:1 56,66

IBRANIYAWA

1:2 36

1:5 37

4:3 36

4:12 66

4:12-13 11

7:9-10 68

10:4-7 38

11:7 55

12:16-17 33

12:29 29,34

13:8 79

YAKUB

2:10 9

I BITRUS

1:20 37

2:12 54

2:22 45

4:17 19

II BITRUS

2:8 31

3:10 29,8

I YOHANNA

3:9 45

YAHUDA

6 67

13 26

RUYA TA YOHANNA

1:7 58

1:18 68

2:26 54

3:9 54

3:10 7

86

7:4-8 54

7:4-14 15

9:1-21 44

9:5 27

9:14 75

9:15 76

9:17-18 76

11:10 27

13:7 43

13:8 27

14:10 8

16:10-11 56

16:18 28

17:14 56

18:6 26

19:11-16 68

19:19-21 56

18:8 29

19:20 28

20:10 28

20:11-13 25

20:12 23

20:13 23

20:14 23,24

20:14-15 28

21:1 27

21:8 28