11.01.2013 Views

Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide

Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide

Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide

SHOW MORE
SHOW LESS

You also want an ePaper? Increase the reach of your titles

YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.

Dauda ya nuna ƙauna da girmamawa ga mattacen magabcinsa,

sarki Saul, amma ya nuna ƙauna mafi girma ga mugun ɗansa Absalom.

Lokacin da Absalom yana da shekara 25, ya fara shirin kashe mahaifinsa

Dauda. Sha’warsa ita ce ya ƙwace kujerar sarautar Isra’ila daga ubansa. A

gaskiya ma, tawayensa ya kawo rashin zaman lafiya a fili har ya tilasta

Dauda ya gudu daga Urushalima domin kada Absalom ya kashe shi.

Amma an bayyana zurfin ƙaunar Dauda zuwa ga mugun ɗansa

mai cin amana wanda daga ƙarshe shugaban mayaƙan Dauda ya kashe

shi a cikin IISamaila 18:33 inda muka karanta cewa:

Sai sarki yayi juyayi da yawa ya hau wajen benen da ke kan ƙofa, ya

yi ta kuka; yana tafiya yana cewa ya ɗana Absalom, ya ɗana, ɗana

Abasalom, da ma Allah ya yarda na mutu dominka, ya Absalom, ya

ɗana ɗana.

Ƙaunar Dauda domin Absalom ta nuna irin ƙaunar da zamu yi wa

makwabcinmu. Bai kamata mu yi farin ciki ba a kan mutuwar

magabcinmu, amma muyi baƙin ciki cewa sun fuskanci fushin Allah da

yake saukowa kan dukan waɗanda basu da ceto.

Har’ ila yau, mun ga irin ƙaunar da Kristi ya nuna ga waɗanda

zasu fuskanci fushin Allah. Mun karanta a Luka 19:41-44 cewa:

Sa’anda yayi kusa, ya hangi birni, yayi kuka a kanta, yace. Da ma

kin sani a cikin wannan rana, har ke ma, abin da ya tabbata ga

salama. Amma yanzu a ɓoye yake a idanunki. Gama kwanakin

zasu abko maki inda maƙiyanki zasu gina maki ganuwa, su sa ki

a tsaka, su tsare ki daga kowane sassa. Su fyaɗe ki a ƙasa da

’ya’yanki a cikinki, ba za su bar ko dutse ɗaya bisa wani a cikinki

ba, da shike ba ki lura da kwanakin ziyartonki ba.

A waɗannnan ayoyi mun karanta cewa Yesu yayi kuka domin

Urushalima, wadda a nan take wakiltar dukan waɗanda basu da ceto a

cikin ƙasar Isra’ila, da kuma dukan waɗanda suka rage a majami’u

waɗanda zasu fuskanci cikakken fushin Allah domin zunubansu. An

albarce su ta musamman domin sun koya daga Littafi Mai-Tsarki. Sun

koya da yawa game da ƙaunar Allah da jinƙansa. Amma sun juya

gaskiyar Littafi Mai-Tsarki zuwa koyaswar da ta gamshe su. Sun ci gaba

da tafiya cikin girman kansu. Za mu iya ganinsu a cikin ruhaniya kamar

marasa son zaman lafiya waɗanda suka cancanci fushin Allah.

Amma Yesu yayi kuka dominsu. Ka yi tunani kan cewa Allah da

kansa yana kuka domin dole ya hukunta waɗanda suka tayas masa. Ba

abin mamaki ba ne da muka karanta a cikin Ezekiel 33:11 cewa:

Sai ka ce masu, in ji Ubangiji Yahweh na rantse da raina, ba ni da

wani jin daɗin cikin mutuwar mugu...’’

15

Hooray! Your file is uploaded and ready to be published.

Saved successfully!

Ooh no, something went wrong!