Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Create successful ePaper yourself
Turn your PDF publications into a flip-book with our unique Google optimized e-Paper software.
4. Asarar gadon rai na har abada, tare da asarar gadon sabuwar

sama da sabuwar duniya.

5. Mutuwa ta har abada inda ba za’a ƙara rayuwa ba.

Yayin da dukan waɗannan hukuncin zasu sauko kan wanda bashi

da ceto, mutumin yakan mutu ba tare da ya san cewa mutuwarsa

sakamakon zunubi ne a rayuwarsa ba. Idan shi ɗan Ikkilisiya ne ya yiwu,

ya gaskanta da koyarwar nan irin ta al’ada cewa, masu zunubi za su

shiga jahannama inda zasu sha azaba ta har abada. Amma wannan ba

abin damuwa ba ne a gare shi domin ya hakikance da cewa an maye

haihuwarsa, kuma shi cikakken ɗan Ikkilisiyar ne.

A hakikanni gaskiya rayuwar yawancin ’yan Ikkilisiya yawancin

lokaci kuma a rayuwar waɗanda basu cikin Ikkilisiya sun gaskanta da

cewa mutuwa wani lokaci ne mai daraja na zuwa ƙasa mafi kyau. Ta haka

ake kallon mutuwa a matsayin nasara ko da shike ta haɗu da baƙin ciki

domin rabuwa da ƙaunatattu da kuma abubuwan jin daɗi da mutumin

yake morewa a wannan rayuwar.

Sai dai, marar ceto da ya mutu, to ya yi mutuwa ta har abada. Ba

zai taɓa ɗanɗana hukuncin Allah da sanin sa ba. Gaskiya ne a lokacin

fyaucewa, za a fidda gangan jikinsa da aka sa a kabari a kunyace, Allah

da kuma ’ya’yan mulkin sama zasu kunyata shi. Amma marar ceton da

ya mutu ba zai san abinda ke faruwa ba. Gaskiya ne yayi asarar gadon

haihuwarsa, rai na har abada da gadon sabuwar sama da sabuwar

duniya. Amma bai san wannan yana faruwa ba.

Bugu da ƙari lokacin da waɗannan mutane suke raye koyaushe

akwai babban jin daɗi da murna. Sun ɗanɗana abubuwa kamar ƙaunar

iyali da jin daɗin rayuwa a duniya mai kyau. Saboda haka, rai da mutuwa

suna da kyau ko da shi ke ba su taɓa samun ceto ba. To ina fushin Allah

a kan waɗannan mutane da basu taɓa samun ceto ba? Sai kace mun

ɓata hanya a fahimtar tsarin shari’a na Allah. Amma bamu ɓata hanya

ba. A maimakon haka, muna koya cewa, babban abinda duniyar nan ta

fi maida hankali a kai ba kan shirin ceto na Allah, ko kuma shirin

shari’a na Allah ba ne. A bisa hikima da ɗaukakar Allah ne. Ka tuna mun

koya cewa dalilin da yasa Allah ya halicci ’yan adam ya sasu a duniya

shine domin ya samar da gagarumin hoto mai kusurwa uku inda dukan

ikoki da mulkoki na sammai zasu ga babbar hikima da ɗaukakar Allah,

yayin da Allah yake shirin aikin ceto cikin fiye da shekaru 13,000 da aka

shafe ana aikata zunubi.

Saboda haka muka tarar, misali, cewa Allah yana gaba da mai

zunubi (Zabura 5:5), kasancewa fushinsa na Allantaka yana bisa kanshi,

duk da haka jinƙansa da girma yake zuwa ga hallittun sa duka har da

masu zunubi. Mun karanta a cikin Matta 5:45 cewa:

73