11.01.2013 Views

Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide

Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide

Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide

SHOW MORE
SHOW LESS

You also want an ePaper? Increase the reach of your titles

YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.

Alkawari. Mun gane da cewa yanayin da aka yi amfani da kalmar ya

danganta daga waɗannan.

1. Azabar marasa bi yayin da suke jin bisharar gaskiya (Ruya ta

Yohanna 11:10).

2. Azaba irin ta rashin lafiya (Matta 8:6, Matta 4:24).

3. Azaba ta harbin kunama (Ruyata Yohanna 9:5).

4. Kalmar Helenanci da aka fassarata “Azaba” an kuma fassara

ta da ‘‘ɓacin zuciya’’ ko kuma ‘‘fushi’’, lokacin da Littafi Mai-

Tsarki yayi Magana game da ruhun Lutu mai-adalci da ya

‘‘fusata’’sabili da zunuban Saduma. (Bitrus II 2:8).

5. A helenanci wannan kalmar “azaba” an fassarata “Baƙin ciki”

(Luka 2:48, Ayyukan manzani 20:38).

6. Azaba da wuta (Ruya ta Yohanna 14:10, Luka 16:24).

Mun koyi cewa ƙarshen shari’ar Allah mutuwa ce. Littafi Mai-

Tsarki ya goyi bayan wannan bayanin ta wajen amfani da kalamai kamar

“lalacewa” “hallakarwa”. Za a kuma iya gane cewa an yi amfani da

kalamai kamar, ‘‘mutuwa’’, da ‘‘mutu’’, fiye da sau 1,300 a cikin Littafi

Mai-Tsarki. Ba abin mamaki bane da Littafi Mai-Tsarki ya bayyana da

cewa maƙiyi na ƙarshe da za a hallaka shine mutuwa. (Korintiyawa

15:26)

Mai Arziki Da La’azaru

Yanzu zamu sake nazarin misalin mai-arziki da La’azaru wanda

ke cikin Luka 16. Rashin fahimtar wannan misali ya kawo rashin

fahimtar tsarin shari’ar Allah.

Misalin yayi bayani a kan mutane biyu. Mai-arziki yana da duk

abin jin daɗi da wadata da wannan duniya zata iya kawowa, amma ba shi

da ceto. Matalauci La’azaru baya da waɗannan abubuwan jin daɗi na

wannan duniya amma yana da ceto. Daga ƙarshe dukansu suka mutu,

aka binne mai-arziki shi kuma La’azaru mala’iku suka ɗauke shi zuwa

ƙirjin Ibrahim (Luka 16:22). Kasancewa a ƙirjin Ibrahim hoto ne na

kasancewa a wuri mafi albarka a gaban Allah. A binne kuma shine a sa

mutum a kabari.

Misali kuma ya ci gaba da magana tsakanin mai- arzikin da ya

mutu da Ibrahim (Allah) wanda yake cikin sama. Ka tuna mun koya cewa

kabari da mutuwa daidai suke da jahannama. Saboda haka ba kuskure

bane a ce mai arziki yana jahannama (Luka 16:23). Amma tilas ne mu

gane cewa ɗaga idanunsa ya ga la’azaru a ƙirjin ibrahim, ya kuma yi

magana da Ibrahim duka misali ne. Watau, Allah ya shimfiɗa waɗansu

jadawalin tunani ko kuma hotuna masu kusurwai uku, domin ya koya

gaskiyar ruhaniya. Waɗannan gaskiyar sun ƙunshi koyaswa kamar haka:

31

Hooray! Your file is uploaded and ready to be published.

Saved successfully!

Ooh no, something went wrong!