Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
You also want an ePaper? Increase the reach of your titles
YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.
Gafara Mai Ban Al’ajibi

Idan za’a hukunta mai laifi sabili da laifinsa, za a iya zartar masa

da hukuncin wulakanci na kisa. Babu wani begen yafe hukuncin kisa sai

ko da cikakken umurnin shugaba. A ƙasashe da dama na duniya har da

Amurka, mai mulki mafi girma yana da ikon gafartawa mai-laifin da aka

zartarwa hukuncin kisa. Saboda haka, kafin aiwatar da hukumcin

‘yan’uwan mai-laifin za su yi duk ƙoƙarinsu domin ya sami wannan

gafaran don a ceto shi daga wannan mutuwar wulakanci da kunya da

aka shirya dominsa. Babu shakka, wani lokaci akan yafewa mai laifi ana

dab da lokacin da za’a aiwatar da hukuncin kisan.

Allah ya tanada irin wannan gafara ga duk waɗanda ya zo domin

ya ceta. An bayyana wannan da yau a cikin littafin Ishaya 54:7-8 inda

Allah yace:

Don lokaci ƙanƙani na yashe ki, amma da jinƙai mai-girma zan

dawo da ke. A cikin hasala mai-zafi na ɓoye maki fuskata ɗan

lokaci kaɗan amma da madauwamin alheri zan yi maki jinƙai in ji

Ubangiji mai-fansar ki.

Kuma a Ishaya 55:7-8

Mai mugunta shi sake hanya tasa, mara adalci kuma shi bar

tunaninsa, shi komo wurin Ubangiji shi kwa zaya ji ƙansa wurin

Allahnmu, gama zaya yi gafara a yalwace. Gama kamar yadda

sammai suna nisa da duniya, haka nan kuma al’amura na sun fi

naku tsawo, tunani na kuma ya fi naku, in ji Ubangiji.

A daidai kusan ƙarshen zamani, ɗaya daga cikin ɓarayin da aka

giciye su tare da Kristi, ya ji kalmar nan ta alheri daga leɓen Yesu “yau

kana tare da ni a firadais” (Luka 23:43). Ina misalin al’ajibin! Wannan

ranar da a wurinsa ta kasance ranar mutuwar ta ƙasƙanci na mai-laifin ta

ƙarasa da shiga gida cikin daraja na Ɗan Allah. Wannan gafarar ce

kowanne zaɓɓaɓe na Allah yake samu.

43