Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
You also want an ePaper? Increase the reach of your titles
YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.
tilas a hukumta shi kamar wanda har yanzu yake ɗauke da zunuban

waɗanda aka kiraye su zuwa ga ceto domin ya nuna yadda ya sha

wahala sabili da waɗannan zunuban. Abin mamaki shi ne babban firist

ɗin ne ya yankewa Yesu hukumci. Matta 20:18 ta ce:

Gashi zamu Urushalima, kuma za a ba da Ɗan Mutun ga hannun

manyan malamai da marubuta, zasu hukunta masa mutuwa.

Yahanna 11:50-51 ta ce:

Ba ku lura kuma yana da amfani a gare ku mutun da ya mutu

saboda jama’a kada al’umma duka ta lalace wannan batu fa ya

faɗa ba bisa kansa ba amma domin shi baban malami ne

shekaran nan yayi annabci Yesu zaya mutu saboda al’umman.

kuma a cikin Yohanna 19:17 mun karata cewa:

Yahudawa suka amsa suka ce masa muna da doka bisa ga

wannan doka kwa ya kamata shi mutu domin ya maida kansa

Ɗan Allah.

A ko ina cikin Littafi Mai-Tsarki babban Limami misalin Yesu ne

babban Limami. Hakin babban Limami ne ya yanka rago.

Saboda haka Bilatus gwamna ne, wanda yake da ikon yankewa

Yesu hukuncin kisa domin ya farantawa Yahudawa rai, ya bada umarni

cewa a kashe Yesu ta hanyar giciyewa. Giciyewa bisa ga dukan alamu, ita

ce hanyar kisa mafi kunyatarwa da mutum ya shirya. Mun koyi

muhimman darussa guda uku game da giciye Yesu. Da waɗannan:

1. Kunya, da la’ana da azaba da Kristi ya daure don zunuban

mu.

2. Kunya da la’ana da tilas za a ɗora bisa waɗanda ba a cece su

ba da kuma ƙarin azaba da za’a jimre ga waɗanda zasu shiga

da rai ranar sharia.

3. Abin mamaki na gafara na dab da ƙarshe.

Lokacin da aka giciye Kristi, ya zama abin nuni ga jama’a na

mutumin da yake ƙalƙashin la’anar Allah. Domin mu gane

muhimmancin la’ana, bari mu dubi itacen ɓauren nan da Yesu ya la’anta

(Markus 11:14). An la’anta itacen ɓauren da yake wakiltar al’umar Isra’ila

duk zamanin Tsohon Alkawari lokacin da Kristi ya ce “kada kowa ya ci

‘ya’ya daga wurinka, nan gaba har abada.’’ Saboda haka la’anar itacen

ɓauren yana koya mana cewa an hallaka al’umar Isra’ila har abada, ba

kuma za a sake amfani da ita ba a matsayin hanyar samun albarka ta

ruhaniya.

39