Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
Ɗaukaka Ga Allah - Family Radio Worldwide
You also want an ePaper? Increase the reach of your titles
YUMPU automatically turns print PDFs into web optimized ePapers that Google loves.
SURA TA ƊAYA

Abu Mai Sarƙaƙiya Game Da Gaskiya

Tunanin mutum da abinda ya yi imani a kai ya ta’alaƙa kan

abinda ya ɗauka a matsayin gaskiya da kuma madogara. Ya yiwu an

gabatar mashi da waɗannan ra’ayoyin a lokutan baya, ko kuma waɗansu

ra’ayoyi ne da aka gabatar da su ayau. Idan aka sami sababbin ra’ayoyi,

za a tankaɗe, a auna bisa ra’ayoyin da ya ɗauka a matsayin gaskiya ya

kuma amince da su.

Hakika, lamarin ke nan yayin da ake batun fahimta irin ta addini.

Da zaran mun koyi waɗansu ra’ayoyi na addini, muka kuma amince da

su, yakan zama da wuya a sake karɓar wani ra’ayi a matsayin gaskiya,

yana da wuya mu karɓi wani ra’ayi a matsayin gaskiya da ya saɓawa

ra’ayoyin da muka riga muka yi imani da su a matsayin gaskiya.

Ta haka wanda ya sami horaswa ta Katolika zai ci gaba da rayuwa

a matsayain ɗan ikilisiyar Kotolika, Baftis kuma Baftis, haka ma mai

addinin Buda, da dai sauransu. Dalili ke nan da ya sa yawancin waɗanda

suka yi zurfi a cikin ikilisiya ba zasu yarda da cewa Allah ya gama da

Ikkilisiyoyi ba, ya kuma umurci mutane su fita daga ikkilisiyai, kana an

ɗora shaiɗan ya yi mulki a can, kuma Ruhu Mai-Tsarki ya watsar da

ikilisiyoyi saboda haka babu wanda yake ƙarƙashin ikon ikkilisiya da zai

tsira.

An yita yiwa waɗannan mutanen koyaswa, kuma sun amince da

wannan a matsayin gaskiya da cewa, ikilisiyoyin su, na Allah ne kuma

Allah ne yake mulki a bisan ta. Saboda haka ƙofofin jahannama ba za su

rinjayeta ba. Wannan fahimta, ta sami wurin zama daram a cikin tunanin

su, a matsayin gaskiya ba ja. Saboda haka, duk wata fahimta da za a

gabatar masu daga Littafi Mai-Tsarki sai an auna ta bisa ga fahimtarsu

da kuma tauhidi, wanda suka yi imani da cewa ita ce sahihiyar gaskiya.

Idan ka gabatar masu da sababin ra’ayoyi daga Littafi Mai-Tsarki

da ke koyarwa cewa mun zo ƙarshen zamani ikklisiya, ba za su yi

nazarin batun da zuciya ɗaya ba. Komi zurfin fafatun da suke yi cewa a

shirye suke su karɓi gaskiyar Littafi Mai-Tsarki, amma a zahiri, basu iya

zuwa ga sanin wannan sabuwar gaskiyar ba. Dalili ke nan da ya sa a

zamaninmu, mutane ƙalilan ne suke barin ikilisiyoyi bisa ga biyayya da

umurni da Allah ya bayar da a guje masu.

Wannan lamarin ya kasance wani abu dake da sarƙaƙiyar gaske a

zamanin mu , domin waɗansu muhimman dalilai guda uku kamar haka:

1. Muna zama a cikin duniya da take dab da ƙarshe. Kuma a

ƙarshen zamani Allah ya shirya ya ɗauke hatimin da ya sanya

kan bayanai masu yawa game da ƙarshen zamani da ke cikin

Littafi Mai-Tsarki. Saboda haka mu sa rai cewa za a sake

1